Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 1 of 9
*FIN ƘARFI BOOK 3*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*
Page 1
Shiri sosai tayi dama Sarkin gayu ce tayi ƙyau ƙwarai dan tana da irin jikin nan da ake ce ma karuwan jiki,ko wane kaya tasa sai ya yi mata ƙyau an ɗebe su sai hotel ɗin da aka tsara haɗaɗɗiyar dinner, wacce abokan Ango suka shirya guri ya yi guri sanda suka isa,jin gaban ta bai faɗi ba yasa ta shiga cikin ƙwanciyar hankali suna zaune an soma ciye-ciye . Can sai taji gabanta ya yi mugun faɗuwa take ta ji komai ya ginshe ta duk da waƙar da mawaƙin keyi da farko ta shiga ranta, amma yanzu sai taji komai ya tsaya mata cak. Da sauri ta miƙe Sadiya da Munira suka dube ta, ina zaki? Ta ce ina zuwa,can bayan wasu ƴan labulaye taje daga inda take tana duban ƙofa. Haka kawai taji cewa yanzun zai shigo.
*** **** **** ****
Dady ya fito wanka ya kuma gajiye yake jin shi ba dan bai samu halartar ko ɗaya daga cikin programs ɗin bikin ba da zaya huta ne don yayi azumi yau kuma a wahale yake ya ɗan ja tsaki shima yana tunanin haka nan zaya haƙura asa bikinshi da Zainab ya gaji da azumin nan shi kanshi yasan yana buƙatar mace kuma yana ganin kamar yana da ƙarfin sha'awa shiyasa gara ya yi auren tunda wadda yake so bazai samu ko ganinta ba bare har ya aura.
Shadda kalar blue hularshi da duk kayan da yasa blue ne,rafar ƴan ɗari biyar ya zuba cikin aljihu ya fesa turare ya ɗauki key ɗin Hummer ya fito. A falo ya samu Sunday yana zuba Hollandia cikin firji, ya ce "Sunday kai min ɗaya cikin motar daka goge min", ya ce "Ok sir." Ya ɗauka ya fita yana matuƙar mamakin irin son da ubangidan nashi kema wannan Hollandia ya kamata campanyn ta suyi mishi ƙyauta ta musamman,ko dan tsananin ƙaunar da yake mata."
Gidan su Zainab Dady ya wuce a phone ya kirata ta fito bayan tayi sallama da mahaifiyarta, Hajiyarta tana tsananin son Æ´arta Zainab ta auri Dady ba dan komai ba sai don iyayenshi sun tara, haka kuma shima ya tara sai godiya.
Yana daga cikin mota yana kallonta ta nufoshi cikin wani leshi ɗan gaske mai kalar green yasha ado da zare silba haka sarƙa da ƴankunne suma silba jaka da takalmi sai wani ɗan mayafi ƙarami duk farare ta yi ƙyau sosai sha'awarta ta ƙaru a zuciyarshi, ta shiga motar bayan ya buɗe mata ƙamshin jikinsu ya buɗe su,ta dube shi My dear har na zaci ka fasa zuwa dani, ya ce "saboda me?" Ta ce naga goma ta wuce sannan baka kira phone ɗina ba, ya ce ina can ina tunanin yakamata mu ma azo mana dinner fa dan na gaji da rungume filo yakamata nima nasan halin da nake ciki, daɗi ya kamata ta ce ba na ce maka ba tuni, amma ka ƙi wai na jira ka,Ƙila kafi son ƙwana da filon shiyasa." Ya shafi fuskarshi ranar asabar za'a kawo lefe da komai tunda Allah yasa sun san komai dama nine matsalar kuma yanzu nima ina buƙatar auran,sati Uku zamu sa fa.?"
Cikin zumuɗi Zainab ta ce "Ya yi nima na matuƙar ƙosawa."
Ya dubeta "dame kika ƙosa?" Ta ce "Da abin da yake hana ka bacci." Kai ya girgiza yana mamakin Zainab, Sam batada irin kunyar nan ta mata, ya tuna Pretty ɗin shi, ita kam kowane lokaci ya yi mata wata magana mai ɗan nauyi takan rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta ce,kai ko? Ita kam Zainab sai dai ta biyeshi suyi,hakan baya birgeshi yana son mace mai kunya da jan aji.
Suna shiga gurin dinner yaji gabanshi ya faɗi inda sabo ya saba,ba wata Pretty ɗin shi a nan gurin, zuciyarshi ce dai kullum tana ayyana mishi sai gabanshi ya dinga faɗuwa, haka ya raya a ranshi don haka sai kawai, ya shige, sun samu an daɗe da soma dinner, amma duk da haka sai da aka sanar da zuwanshi a matsayin babban abokin ango akan idon Ruƙayya suka shigo, tana dubansu san da suka zarce kusa da ango suka zauna yayin da Zainab ta maida ɗuwawunta gurin da Ruƙayya ta tashi, gaban Ruƙayya ya faɗi ta tsorata da ganin Zainab domin ta gane wacce suka haɗu a saloon ce, ta gode Allah da yasa ta tashi don haka can ta fita duk da tsoron dake cike fal a ranta haka ta zauna a harabar Hotel ɗin tunda ga haske tamkar rana.
Sadiya ta dubi Munira "M Bash har yanzu kusan awa Ruky M bata dawo ba fa." Munira ta ce "Kai gaskiya ki je ki duba ta, tunda ba phone a hannunta bare ma mu kira."
Son Guy (kamar yadda suke kiran Dady) ya dubi Al-Mustapha.
"Ina neman afuwa Musty bamu samu isowa akan kari ba." Zainab ta ce "Ya hidimomi ango?"
Al-Mustapha ya ce da godiya.
Zainab ta dubi Munira "Amarya ya jama'a?" Munira bata gane Zainab ba, har suka gaisa suka gaisa da Sadiya basu gane ta ba, Zainab ta ce "Naga baku gane ni ba ko?" Sadiya ta ce "Ni dai ina son tuna inda muka haɗu." Zainab ta ce "A saloon." Nan take suka tuna ta, amarya sun gaisa da Son Guy inda ya yi mata ƴar tsokana. Zainab ta ce "ina ɗayar nan kuma mai gashi?." Sadiya ta ce "kina nufin Ruƙy M ko?" Ta ce "Yes ita kam bata zo ba?" Ta ce yanzun nan ta tashi ko ina ta shiga Oho, Zainab ta ce "Ashe zamu gaisa." Munira ta ce "Armaya'u ki je ki duba ta kin san fa Ruƙy ƴar daru ce zata iya tafiya gida."
Al-Mustapha ya ce "Kai Ruƙy ɗin nan tana da shagwaɓa,da ƙyar dama ta zo.
Shiru Dady ya yi yana ƴan dube-dube tamkar baisan mai suke cewa ba, amma kunnen shi yana gurin su,a ranshi kuma sai yaji yana mai tsananin son yaga Ruƙy M ɗin nan, wancan karan ya kuskure ganinta sakamakon wanka da tashi ga, yanzu kan shi sai fa yaga kalarta, shi kam dama yana matuƙar girmama mai sunan ta,yasha alwashin in har ya haifi ƴa mace sunan ta Ruƙayya. Nan ya tuno ma kanshi son Ruƙayya take hankalinshi ya tashi kanshi ya shiga sarawa nan ya ji zuciyarshi ta tsani duk wata mace, duk hirar da Al-Mustapha yake yi mishi sam bai ji ba,sai da Zainab ta ce My dear ya kamata ka duba masu waƙar nan tuntuni sai waƙa suke yi. Nan ya tashi cikin sanyin jiki yana musu liƙi, Zainab ta zuba mishi ido tana tsananin son shi ita ma nan take ta tashi taje tana mishi liƙi, Ango da amarya suma suka taso suna ma su Dady liƙi nan fa guri ya kaure mai waƙa sai rerawa yake yi.
Ruƙy wacce abin duniya ya dama sai gizo Dady ke mata tana ganin san da suke shigowa da Zainab fuskarshi wasai ƙyawun shi ya ƙaru fiye da da, wata kamala ta musamman ta sauka a fuskar shi, ya zama namiji sosai ga wani ɗan tumbin kuɗi da ya fito ya yi mishi ƙyau,a da sam bata son tumbi amma na Dady ya yi mishi ƙyau.
Hawaye suka zubo mata lallai Dady ya karya alƙawari. Ta tuna da yanda suka so juna ashe duk na baki ne,sai yanzu ma tayi wani tunani, gaskiya ya kamata ma ta gane tuntuni dan me ya hana ya neme ta tuntuni bayan rabuwar su? Kuma phone ɗin da ya bata me ya hana shi kiranta akan layin. Har ta tafi makarantar ƙwana? Duk ma shekarun nan da yana sonta daya neme ta, don haka taba kanta baki tare alƙawari sauraron duk wani wanda ya zo da sunan sonta. Kuma daga yau tayi banƙwana da garin Abuja gobe tana tafiya shikenan,in ba kuma M Bash bace ta haihu bata ƙara zuwa bare ta ganshi. Kai tana ganin ma gara ta je ta auri talaka ɗan'uwanta ya fiye mata ƙwanciyar hankali. Ga Nasir tela duk da ya yi aure har da yara uku,yana nan yana nacin ta har tayi degree ita kam yanzu zata daina biyewa ƴaƴan masu dashi ɗin nan,gara Armaya'u da M Bash suna da halin shiga law school ita kam zata je service ɗin ta ya fiye mata tana gamawa ta nemi aiki koma a ina ne kafin Allah ya bata miji, tunani bar katai sun cika ta har san da aka tashi.
Tana ganin mutane sun soma fitowa, sai ta koma can gurin motar da suka zo cikinta. Ta ganin su Armaya'u da sauran ƙawayen suna sallama da Zainab, yayin da Dady dasu Al-Mustapha suka nufo gurin da take. Tsoro ya kamata da sauri ta zaga bayan motocin ta ɓoye bayan wata.
Jikin wadda ta ɓoye ya shiga tana jin san da yake cewa Musty "Musty Allah ya bada zuriya ɗayyiba, kayi ƙoƙarin samun Baby a yau dare na farko." dariya suka saki sauran abokan suna cewa "Gaskiya ne Son Guy." Ya ce Zee zo muje dare nayi fa." Ta na barwa su Sadiya saƙon gaisuwa zuwa ga Ruƙayya, ta zo tana cewa,My dear mu tafi ko? Ya ce shiga, ta tsugunna tana jin su a bayan motar da bata zata tashi bace sai da taji ya tashi motar ta koma bayan wata da sauri.
Yana bari gurin ta miƙe tana maida numfashi taje gurinsu Munira dake ta shishshiga mota. Sadiya har tsoro ta ji ta ce daga ina? Ruƙy ta ce ku muje kawai basu jima a gidan Munira ba Abokan ango suka ƙwashe su sai gidan Mom. Sun cika su uku Munira M Bash, Sadiya Armaya'u, Ruƙayya M Sani, tayi ta yi da safe su biyo kafin su wuce, sun ce to dan ta ƙwantar da hankalinta, amma ba zasu dawo ba saboda Armaya'u Kano ta nufa, Mom ta haɗa su da kayan biki da kuma godiya tare da cewa suyi ma iyayen su ban gajiya. Dan Umma ta zo Hajiyan su Sadiya ma tazo.
Tunda suka dawo bikin Munira kullum maganar aure Umma da Affa suke mata,ita kam ta ƙosa a tura su service. Takardun na fitowa sai taga ita Legos aka tura ta, bata damu ba dan ita burinta shi ne ta matsa daga gidan.
Ta gama cin tuwon ta ƙwashe ƙwanukan har da na Umma ta nufo bakin rijiya tana wankewa, Umma dake cikin ɗakin Affa tasa baki ta kira Ruƙayya, ta amsa tare da miƙewa ta nufi ɗakin.
Gabanta ne ya faɗi san da taga takardar ta a hannun Affa, bayan ta samu guri ta zauna sai Affa ya ce "Ummanki ta sanar da ni zaki tafi Legos?" Gaban Ruƙayya yana faɗuwa ta ce "Eh, can aka tura ni ɗazun naje na amso." Ya ce "A da dai kinje Kano, yanzu ma da Kanon ne ko irin su Katsina jihohinmu na nan Arewa sai in yarda amma ba zan amince ki je gari kamar Legos ba, a'a." Shiru Ruƙayya ta yi har sai da Affa ya gama sannan ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara ne don Allah kayi haƙuri."
Ya ce "Ke ba ajin zancen aure a bakin ki sai dai na karatu,ki sani na matsu naga auren ki, Allah yasan nayi miki yanda zan iya ita wannan ƙawar taki da ku ka je biki,ba gashi ba tayi auran in ma bautar ƙasar ne ai tana ɗakinta zatayi yanzun ko?
Ruƙayya ta ce "Affa su fa karatu zasu cigaba law school zasu shiga dubu ɗari biyu da hamsin, kuma suma wata tara ne zasuyi."
Ya ce koma menene ai yanzu a ɗakinta zatayi shi yi ko? Shiru Ruƙayya tayi Affa ya cigaba da mata masifa kan aure don haka ba batun wani service.
*** *** ****
Goma daidai ta gama tsantsara ƙwalliyarta cikin Ankon bikin Munira da suka yi,ta fito ta shiga ɗakin Umma.
Umma ta ce "To maimakon ki tuna min sannan in sanar da Affanku shine ki kayi shiru." Ta ce yi haƙuri Affa zai ce a'a ne kinsan baya son yawan zuwa." Ta ce ki gaida su, Shagon kusa da lungunsu ta tsaya tayi ma su Mama da su Muhsin tsarabar chizee da bisket. A hankali take tafiya bakin shagon Nasir "Kai Oga gafa mutuniyarka." Inji wani yaron shagon shi "Wa kenan.?" Yaron ya ce "Ruƙayya,kai Oga yarinyar nan aƙwai yanga,dubi tamkar mai tausayin ƙasa , koda yake ai tana da abubuwan yangar."
Nasir ya miƙe daga aikin da yake ya fito ya tsaya suka gaisa ya ce zaya zo da dare. Bayan ta je gidan Murja sun wuce gidan Fati a can ta ce don Allah su roƙar mata Affa ya yarda ta je service suma sun mata ƙorafin aure ta yi musu ƙaryar cewa ai aƙwai wanda suka haɗu dashi bikin Munira kuma shi zata aura.
Kafin ma ta gama service komai zai kammala kuma zaya yarda tayi aikin ta. Sun yanke shawarar kan cewa Ruƙayya ta je ta samu Yaya Amina da Yaya Suwaiba da Yaya Sadiya ta gaya musu su haɗu ranar juma'a kasancewar Affa in ya dawo sallar juma'a baya komawa kasuwa shi ne suke son magana dashi.
*** *** *** ***
Yasha mamaki da ya samu gidan tamkar kasuwa, ƴan jikokinshi suka yi mishi oyoyo, ya ce biki kuke yi ne a gidan?" Ummansu wacce ta fito dan taran shi, ta ce, sun zo gaida kaine affansu." Ya ce "sai dai bayan masallaci don lokaci ya ƙore,in na dawo sai mu gaisa." Sun mishi sannu da zuwa sannan suka koma suka ci gaba da hirarsu.
Ɗakin Umman shi ma ya shigo suka dinga gaishe shi ɗaya bayan ɗaya Sadiya ce ta soma magana "Affa dama gurinka muka zo." Ya ce to ince dai lafiya? Ta ce lafiya lau dama kan zancan Ruƙayya ne. Muka ce don Allah kayi haƙuri ka barta tayi bautar ƙasar tunda wata tara ne. Suwaiba ta ce kuma Affa ai Auta tana da kamun kai munsan zata tsare kanta," Amina ta ce "Kayi haƙuri Affa wata tara kamar yau ne." Su kuma su Murja da Fati suka ce "Haƙurin da aka yi na shekaru kusan biyar ban dama na secondary ai wata tara bazaya ga gara ba.
Ya ce "To duk naji jawabin ku yanzu, Amma ban ji wacce tayi zancan aure ba,ku ɗauki misali a kanku aƙwai wacce ta wuce secondary dukkan ku? Suka ce a'a, ya ce na mata haƙuri ko ban ba? Suka ce kayi, ya ce, to ta haƙura gara ma da da tsayayye ne da sai na amince.
Sadiya ta ce "Aƙwai wanda suka yi magana, haka suka yi tayi kafin daga baya Affa ya ce yana da sharaɗin,sharaɗin sune zasu ɗauki nauyin yi mata siyayya, zuwa kuɗin mota dan bashi da kuɗi. Ya ce karatun ta ne ya cinye komai harda kuɗin da bawan Allah ya aiko mishi da zakka, suka ce mutumin nan ko wanene yana da mutunci, Allah yasaka mai da alkhairi. Umma ta ce ƙwanakin nan ba'a yi sati uku buhun shinkafa huɗu da taliya ya aiko mana gashi nan har yanzu ita muke ci Affa ya ce hakane gashi ya ƙi mu haɗu ina son in mai godiya ba hali. Yaran suka ce Allah ya saka mai da gidan aljanna shima ya biya mishi buƙatunshi.
Sun gama yanke shawarar su kowacce zata bada daidai aljihun ta mata kenan sarakan zumunci,Yaya Fati ta dubi Ruƙayya "Auta don Allah gidan mutumin nan na kusa da Bus stop zan aike ki,mai saida litattafan Hausa, ina son wani littafi ne sabon fitowa ne,na je shagon shi ya ce min suna gida.
Ruƙayya ta ce "To ki koma shagon mana tunda yanzun dai nasan baya gida ƙila ma ya kai takardun shago, Fati ta ce "Ke dai baki son zuwa ne bari in zamu wuce zan biya da kaina."
Sadiya ta dubi Fati ta ce "har yanzu kina nan da shegen karance-karancenki É—in nan."
Murja ta ce "Ai in gaya miki sai abin da ya yi gaba in dai Fati ce tunda mijinta ya É—aure mata gindi.
Fati ta ce "Dole ne ya ɗaure min tunda yana ganin amfanin shi, Allah ku kun jahilci karatun Hausa ne kawai, amma yana da fa'ida sosai matsawar za kiyi amfani da abubuwan da ki ka gani na ƙaruwa zaki koyi kula da mijinki yanda zaki zauna da kishiya da dangin miji,ban da wannan ga kalolin soyayyar da zaki ma mijinki koda gurin ƙwanciya ne, sannan....." Dundu Amina ta sakar mata tare da faɗin.
Lallai Fati Yaya Sadiya ki ke gaya ma maganar ƙwanciya da miji?.
Suwaiba ta na dariya ta ce "Allah ya ƙyauta miki Fati." Ita ko Ruƙayya sai tayi waje, Sadiya kuma ta ce "Uhm ni dai ai kallon ta nake yi." Fati ta ce "Kun ji ku da wani abu, dukkanmu ba mata ba ne.
Murja ta ce "kina da wani da yake bayani kan ƙwanciyar ki ara min." Ta ce bari in kinzo gidana sai muyi maganar.
*** *** *** ***
Ruƙayya ƴar gata sun haɗa mata komai ta tafi garin Legos. Haka aikin nasu ya yi ta cigaba ƙwanci tashi yau sati shida kenan Ruƙayya tana garin Legos, duk waɗanda suke tare tafi shaƙuwa da Nuraddeen M Adam ɗan Kano ne ko yaushe suna tare.
Yau sati ta fito sanye da baƙar doguwar riga gyalenta baƙi takalmi da kuma baƙar jaka. Ta yi ƙyau sosai, Nuraddeen ya dube ta,sai ina Ruƙy, ta ce "Ina son naje saloon gashina ya yi datti ina son na ɗan wanke, ya ce to bari muje, suna tafiya suna labari har saloon bayan an gyara mata ya nemi ta rakashi kasuwa sun shiga gari sosai kafin su ga wani super market.
Gaban Ruƙayya ya yi mugun faɗuwa, ta tsaya, Nura ya ce "Kin gaji ne?" Ta ɗan wayance.
Sosai ma, ina son na huta" ya ce "To mu ƙarasa daga nan sai gida suna shiga idon ta ya sauka akan Dady,yana tsaye yana waya ta ja gyalenta ta rufe gefen fuskanta ta kuma shige ɗaya gefen.
Dady bai kula da ita ba sai dai gaban shi ya yi mugun faɗuwa, waige-waige ya shiga yi tamkar mai neman wani. Lokaci guda kuma ya fita wajen. Sun jima sannan suka fito bata ganshi ba tanata yi ma Allah godiya. Sai dai kuma taji sanyi ganin da tai mishi. Shi kam Dady tana ganin kullum ƙara masa ƙyau ake yi,yaya zata yi da son Dady?.
*** *** *** ***
Hajja ta dubi Dady sannan ta dubi aƙwatunan gaban ta. Haƙiƙa kaya sunyi tuzuru, sai dai nace Allah yasa kada itama muji shiru irin na wancan lokacin, don wannan karon in bai yiwu ba Allah ƙauye zamu je ma samo maka mata,mun gaji da ganin ka haka,ko so kake sai na mutu? Ya ce "Allah sarki Hajja insha Allahu sai kin goya min ƴaƴa da jikoki."
Ta ce "Allah ya tsare ni in samu ma inga auran naka,ai ko yanzu nagode ma Allah.
Ya ce "To Hajja zan wuce amma ranar juma'a zan zo nan Kaduna don haka zan iso da azumi zan buɗe baki a nan, Please ai min waina da fankasu,in kuma samu Hollandia mai sanyi, ta ce Allah shi kaimu, yanzu ai kayi hankali ba irin da ba, ya ce da me nake yi? Ta ce wancan auren da kayi bai yiwu ba ai kayi rawar kai,nan fa kazo kasa ni gaba kana cewa ga waya in ma Momyn ka magana su wuce da wuri kai kayan lefe,yayi murmushin yaƙe tare da girgiza kai don Hajja ta tuno mishi wani abu mai motsa rai ya ce "Hajja bazaki gane ba ne wancan auren da man aƙwai bambanci,na tabbata inda ace Pretty ce zan aura wannan auren tabbas cewa za kiyi da,ban yi komai ba saboda rawar jiki ya tsura ma window ido tamkar a nan zai ga Pretty ɗin shi a gurin. Wasu ƙananan hawaye suka taru a zagayen ƙwayar idonshi. Ya furta a hankali "Allah ya rage ma aya zaƙi." Ya dubi Hajja har in mutu zan kasance ina son Pretty."
Hajja ta yi data sanin furta mai maganar auran shi na da,
A fili ta ce "Nasan kana son ta Yusufa, ta dalilin ta ka samu hawan jini,baka dangana da yarinyar nan ba sai da aka haɗa da roƙon Allah sannan ka lafa kayi haƙuri,matar mutum kabarin sa, ya ce "Hajja sam ban so ni aka haɗa da roƙon Allah ba wai don na dangana da son Pretty naso a ce son ta ya kashe ni,." Hajja ta ce "Ashsha! Ashsha kul na kuma ji koda bai kashe ka ba ai ya saka rayuwarka cikin wahala tunda in ciwon nan ya tashi duk hankalinmu tashi yake. Ya ce ai Dad shine ya ja min dan da basu cuci Affa sun zalunce shi ba wallahi na san ba zai hana min Pretty ba,kuma banga laifin Affa ba domin an yi mishi FIN ƘARFI, kafin Hajja ta ce wani abu wayar Dady ta shiga ƙara ya duba Hussain ne ya tuna suna can suna jiranshi game da programs ɗin bikin shi. Ya ce "Hello, Hussain sorry kuna jirana ko, ina zuwa. Ya kashe wayar sannan ya kira layin direban shi ya ce ka sameni gidan Hajja a Kabala ka hawo achaɓa kazo ka jani.
Sabi'u ya ce "To ƴallaɓai." Komawa ya yi ya jingina da kujera. Hajja ta dube shi ta ce "Ina ce kace tafiya zaka yi." Ya maida numfashi bazan iya jan motar bane shine na kira direba ya jani. Gaban Hajja ya faɗi ta ce,ba dai jikin ba ne? Ya ƙaƙaro murmushi ya ce "a'a ba jikin bane Hajja,kin san jiki da jini gashi muna yawan zirga-zirga aikin ba hutu,ta ce To bari in baka wani magani na gajiya ne shima na hawan jinin ne, ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta ta ɗauko garin magani ta miƙa mishi.
Gashi kuma kai ba gwanin shan koko ba sai kasha da Yoghurt ko Hollandia naka,ya yi,sai sannan direban ya yi mishi waya ya iso, ya ce to,gami da faɗin Hajja ni zan tafi." Ya ciro kuɗi,ba dai ki buƙatar komai ko? Ta ce a'a ba komai, ya miƙa mata kuɗin da shima bai san iyakar su ba............
🖊ï¸Â🖊ï¸Â🖊ï¸Â
[7/31, 16:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*