Complete Hausa Novels

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 9

Page 5

Ya ce ga direba nan da saƙo, don Allah dinner anjima ya kira su Murja da Fati ya ce su gyara mishi ita,gurin Amina ya amshi lambobinsu. Nan suka kira mazajen su suka ce zasu dinner tamkar haɗin baki kowa ya ce zai zo ya kai matarsa. Wani shegen leshi ne mara nauyi da kuma takalmi da jaka sai gyale ashe ba kayan tafiyar bane, sai da ƴan'uwan suka matsa mata ta shirya. Sabi'u ne ya ɗauke ta su kuma mazajensu ne suka ɗauke su sai gurin dinner wadda aka shirya ta a command sai ka nuna kati.

Sabi'u ya kawo musu katin amma amarya gidan Momy ta ga an nufa da ita duk da cewa dare ne ta gane layin, ta ce da direba yaya kayo nan da ni? Ya ce haka aka ce min." Tayi shiru ta bishi da ido.

*** *** ***

Gidan su Dady tamkar yau ne bikin farko ganin jama'a ta rufe fuska, tana zaune cikin mota. Sabi'u ya kira Ƴallaɓai, ya gata nan, takaici ya cika Ruƙayya. Dady yazo Sabi'u ya fito ya buɗe motar ya shiga jikinshi sanye da suit baƙaƙe. Duk ta cikin gyale take kallonshi ya yi matuƙar ƙyau, fuskarshi babu walwala ya ce "kin iso Prettyna? Yanzun zaki shiga Momy ta shirya ki." Ta dube shi baki buɗe.

"Bana shirya ba." Ya ce bazaki gane ba,zo muje ya jawo hannunta ta fisge, ta ce nifa bazan shiga ba, ya ce to shikenan ya ciro waya ya kira Momy ya ce "kizo ki fito da ita Momy wai kunya take ji." Ta harareshi na ce maka? Sai ko ga Momy har ma da wasu aminanta waɗanda suka ƙoshi.

Ruƙayya mai sa'a tunda yawanci sun so ya auri ƴaƴansu ya ƙi.

Cikin farin ciki Momy ta fito da Ruƙayya ta rungume ta suka yi cikin gida,sai ɓoye fuskarta take yi, wani ɗaki aka kaita wasu mata suka soma shiryata cikin kayan aure irin na arna, ranta ya ɓaci sam bazata iya shiga jama'a da wannan kayan ba, sai da suka kira Momy sannan ta ce Kiyi haƙuri ƴan awoyi ne. Wasu ne suka shirya muku kin ji? Haka ta haƙura aka sa mata riga doguwa mara hannu sai safar hannu tare da na kai shine ma ya rufe kafaɗun ta dogon farin takalmi suka fente mata fuska tare da gyara mata gashi.

Da ta dubi madubi sai da gabanta ya faɗi bata san ita ɗin ba ce ba ita bace. Momy da ƙawayenta sun yaba da ƙyaun da tayi, shi ko Dady sai ya ji tamkar ya ce a fasa zuwa don kar mutane su gane mishi mata. Suka shiga bayan mota aka ja su yayin da sauran motocin suke take musu baya fuskarta babu walwala ta ɗan kallo gefenshi ta ce ai wannan ɗabi'un arna ne, ya ce inji wa kice dai ba al'adar Hausawa ba ce ko larabawa suna sawa,nima ba son raina bane wasu Abokaina ne suka shirya mana har kayan sune suka kawo ta taɓe baki.

Gurin tamƙam sanda suka iso, suna fitowa haske kawai kake gani hotuna ko ta ina, gidajen T.V da masu ɗauka cikin waya. Hannu ya riƙe mata suna tafiya har kujerar da aka tanadar musu, guda ɗaya ce mai ɗan faɗi, suka zauna matsi juna mutane na ƙasa su suna sama P square ne suke waƙa a gurin anyi raye-raye. Kuɗi ake zubawa kamar ƙasa in anzo rawa Dady sai ya janyo ta jikinshi sannan suke rawar.

Haka gurin ya kasance,keck sai da ya ƙwanto da ita a kafaɗunshi sannan yasa mata a baki, haka da zai bata juice wai don mai gabatarwa ya ce ya nuna zai ci da ita, ita kam ɗan russunawa tayi da zata bashi dan bazata iya wannan abin ba, haka da za'a yi musu hoto gaban keck ɗin rungume ta ya yi tsaf. Suka koma suka zauna sannan aka soma ciye-ciye ta tuna da aminanta Armaya'u da M Bash tasan zasu yi fushi da ita in suka ji wai tayi aure duk da ita ma batasan da auran ba.

*** *** ***
Ɗaya saura aka tashi tana son taga ƴan'uwanta ina, waɗannan ai sun yi bacci ma a gidajensu, tunda suka ga abin bana ƙare bane suka tafi. Mun fito muna shiga mota ya dubeni da murmushi na ce "Allah ɗazun dan naga mutane ne shiyasa har na bada kai, ya ce na dai gode.

A gidan su Momy ban zauna ba kaya na canza na ce ni gida zanje Momy ta ce na ƙwana,na ce a'a dole Dady da wasu Abokanshi suka kaini. Sai da suka buga gida sannan aka buɗe musu ina ji Affa ya ce "lafiya cikin daren nan?" Suka ce Ruƙayya muka rako. Affa ya ce "Shirmen banza can ɗin baƙon guri ne da bata ƙwana?" Dady ya ce Momy tayi ta yi taƙi yarda.

Ita dai ta shige sai ɗaki ta cire kaya tasa rigar bacci doguwa ta kitse gashinta kitso ɗaya,ta faɗa gado. Komai haka yake dawo mata tamkar yanzun yake faruwa,ita ce ƙwance a jikin Dady wai mijinta? Ta mirgina ta rungume filo har Yanzun ƙamshin turaren Dady jikinta keyi,ƙamshin da shi kaɗai ta sani dashi tana son Dady shima tasan yanzun yana can yana tunaninta.

Wata zuciyar ta ce kodai yana can tare da matarshi, gabanta ya faɗi haka nema,yana can tare da matarshi yana gaya mata daɗaɗan kalamai,kishi ya turnuƙe ta, Dady yaci amanar son da yake mata, can ta tashi ta ɗauko wayarta bari ta kira wani yaji yanda ake ciki.

Tayi ringing sau biyu yana yankewa ana uku ya ɗauka cikin yanayin bacci yake magana...... Prettyna lafiya na neme ki ban same ki ba? Ta ce kai dai bari wai kasan menene? Ya ce a'a, ta ce aure.........bata ƙarasa ba taji ɗif ta gurin shi ashe shi da chaji ne,ta neme shi ta gaji.

Zuwa can wayar ta soma ringing a zaton ta Nuraddeen ne don haka ko number bata tsaya dubawa ba ta ɗauka tace Nuri kana jina? Gaban Dady ya faɗi, ya ce Pretty wanene Nuri? Itama gabanta ya faɗi ta ce kai mai maganar wanene? Ya ce ki dai yi hankali yanzu ke matar aure ce, shiyasa nike ta neman number ɗin ki ana ce min Number busy ashe kina ta hira da wani ƙato ko? Ta ce kaima kayi da matar ka kada ka dameni, ya ce ki iya da harshen ki kuma ni ina da izinin hira da matata amma ke baki da wannan damar ki kiyaye ina da kishi bana wasa ba. Ya kashe wayar ya jefar da ita can gefe yarinyar nan fa yaga kamar bata son shi da gaske,kai ko bata son shi zai zauna da ita koda zata rinƙa yankar naman jikinshi kullum. Alwala ya yi ya soma gayawa Allah.

Saɓanin ita data shiga kuka rurus wai ita Dady yake gaya ma yana da damar hira da wata mata? To zata nuna mishi mata suna suka tara.

*** *** ***

Da safe sai ga Sabi'u niƙi-niƙi da kayan tea, Ruƙayya suna zaune ɗakin Umma har da Affa ta ce Affa yau zan koma tunda yau Lahadi, gobe ina da aiki." Ya ce "wannan ke da mijinki,ni menene nawa?,ni da zai zo ma yau ki tare gidan shi ai da yafi min." Na ce "Affa ai min agaji in ƙarasa." Ya ce "To ai yarda da haƙuri yana gurin mijin naki ko? Ta ce"shikenan."

Misalin ƙarfe sha ɗaya ta gama kimtsawa ta ce bari inje gidan Amina. Umma ta ce kin sanar da mijinki? Babu ruwa na fa. Ran Ruƙayya ya ɓaci ta koma ɗaki ita dai bazata kirashi ta tambaye shi ba sai dai kar da taje.

Sallamarshi ce ta katse tunani. Umma ta amsa,ta jiyo shi yana gaisawa da Umma, ya ce Affa ya fita ne? Ta ce eh,ya fita. Ai Ruƙayya tana nan cikin ɗakin ta, ya ce to, tana zaune bakin gado ya shigo message take tura ma Nuraddeen tana sanar dashi abin ya faru gareta. Ya shigo da sallama ciki-ciki ta amsa, kamar ta share shi ta dai ce ina ƙwana? Ba tare da ta dubeshi ba, ya ce ban ganshi ba,ta ɗan ɗago ido ta dube shi sanye yake cikin jeans blue da farar t.shirt,ta ɗan kama shi ya yi ƙyau sosai ya fito a Son Guy ɗin shi. Ta ce waye baka gani ba? Ya ce ƙwanan da kike tambaya, ta ɗan taɓe baki ya ce bana son taɓa bakinnan in kika ƙara zanyi maganin ki.

Umma ta zo daidai ƙofar ɗakin ta ce Ruƙayya bari in shiga nan gidan mai ɗanwake." Ta ce Umma kada ki daɗe zan fita ne." Dady ya ce "ina zaki ne." Ta ce sai kaji? Ya yi ɗan murmushi mai sauti ya ce to ai dai sai na yarda sannan za'a ko? Ta yi shiru ya taso ya dawo bakin gadon, ta matsa ya ce Pretty ni kike gudu? Kar dai ki manta ni mijinki ne, ta ɗan taɓe baki, bata ankara ba taji ya kamo leɓunanta ya manna mata kiss, tayi saurin duƙar da kanta yana ta dariya tayi banza dashi.

Wayarta ta soma ringing ta sa hannu ta ɗauka Nuraddeen ne cikin fara'a ta ce "Nuri kaga text ɗina? Ya ce eh, Mustapha yazo yana ce min yaga amarya." Na ce wallahi auren dole akai min, ban san mutumin ba ai kaga kiran da aka yi min ko? Ya ce eh, ta ce To ina isowa har an ɗaura." Ya ce Allah ya yi shine mijinki sai kiyi biyayya." Ta ce nagode, ya ce yaushe zaki shigo Legos? Ta ce nan da anjima ma zan taso, ya ce to sai kin shigo. Dady dake zaune yana jinsu ya ce "mu ga wayar?" Ta ce ina ruwanka da waya ta, ya ce ki bani ko na ƙwata. Ta tura cikin bireziya, ya ce ciro ki bani tayi banza dashi, ya haɗa hannuwanta guri ɗaya, ta ce zan maka ihu ya ce Kiyi mana ya tura hannu cikin rigar ta ya ciro wayar ya tura cikin aljihun shi. Sannan ya ce ba batun tafiya yau sai gobe,in ma mutum ya yi mini gardama in hana komawar. Jin haka sai tayi shiru.

Sallama ta ji kamar muryar M Bash, da gudu ta fito tana oyoyo M Bash ɗina." Munira ta ce kada ki taɓa ni shegiya ina Kaduna ina Abuja har sai dai naga ana nuna bikin ki a T.V ai Mom ma tace tana fushi dake. Ta ce wayyo nima fa auran nan yanda ku kaji shi haka naji shi,zo dai mu shiga. Suna shiga Munira taga abokin mijinta ta ce ashe ma angon yana ciki,ai ban san kaine angon namu ba,sai da na gani ana nuna dinner a ɗin newline, Ruƙayya ta ce zauna ƙawata kina ta zuba, ta ce Armaya'u ta iso?

Ruƙayya ta ce "a'a itama tana hanya ne?" M Bash ta ce eh tana hanya jiya muka shiryo tafiyar ta kira ni da dare ta ce nasan ana bikin ki? Na ce mata na dai gani a Talabijin shine muka ce bari muji laifin me mukayi?" Dady ya ce Gaskiya bata ƙyauta ba kuma babu inda bata kai kati ba sai ku.

Ruƙayya ta harareshi sannan ta ce "ni fa ina Legos, Affa ya yi min waya wai inzo, hankali tashe nazo garin nan,jiya kamar yanzun muna hanya,wai ina zuwa na samu an ɗaura min aure da wanda ban ce ina so ba." Ta soma hawaye,M Bash ta ce "Ni fa nasha mamakin ace kinyi aure bamu ji ba." Dady ya ce "Munira ina angon naki wato shine bai zo min ɗaurin aure jiya ba?" Ta ce to ai yazo maka na wancan satin, ya ce to ni wannan na gayyace shi wancan ai a garin yake. Ruƙayya ta tsani ta tuna Dady yana da aure,duk sai taji ta tsane shi. Ta dubi Munira ta ce M Bash bari in kawo miki ruwa, Munira ta ce ina Umma? Umma ta shiga maƙota, ta fita dan kawo ma M Bash ɗin ruwa.

Dady ya ce "Munira nayi mamaki da Pretty ƙawarki ce." Munira ta ce "wai Ruƙayya Aminiya ta ce ta wuce ƙawa,B.U.K muka haɗu baka ganta gurin bikina ba?" Ya ce sam amma ta taɓa baki labari na? Ta ce kasan Ruƙayya da shegen zurfin ciki, koda wasa ko sunan ka bata taɓa kira ba." Ya ce labari na da ita aƙwai tsawo wata rana zata gaya miki." Ta ce shikenan ina kuma Zainab? Ya ce tana Abuja kin san halin ku na mata wai bazata tsaya ba ta tafi.

Ta ce abinne sati É—aya fa? Ya ce ke da kinsan son da nake ma Pretty a rashin ta ne fa na auri Zee wallahi."

Ruƙayya ta shigo da sallama ta ajiye goran ruwan swan water da lakaseera. Umma da Armaya'u suka shigo tara Ruƙayya ta fito da murna ta ce lah Umma a ina kika samo mini Sadiya? M Bash ga Armaya'u, Armaya'u ta ce ashe ta riga ni,ɗakin ta shiga itama ta ce ashe angon namu yana ciki? Ruƙayya ta taɓa baki, ya ce bakinki baya jin horo ko zan gyara mishi zama. Suka yi dariya ban da Ruƙayya.

Sun gaisa da Armaya'u take tambayar shi Zainab, ya ce tana Abuja Armaya'u ta ce lallai kaji daɗi mai mata biyu cikin sati ɗaya. Ruƙayya ta yi waje, ya ce ku daina fada naga kamar Pretty batason ana labarin Zee. Suka sa mishi dariya, ya miƙe daidai sanda Ruƙayya ta dawo ɗakin. Pretty zan tafi na barki da baƙin ki,bata tanka ba ta wuce ta zauna Armaya'u ta ce "Ruƙy ana miki magana." Ta ce me zan ce mishi na riƙe shi ne? M Bash ta ce ke dai Allah ya yi ƴar iska." Ya ce kuna nan ne? Suka ce gobe zamu tafi, ya ce Ok,zan shigo zuwa dare. Ruƙayya ta ce baka bani wayata ba, ya tafi yana faɗin da kin ƙwata ai.

Yana tafiya suka hauta da masifa ta ce ba fa sonshi nike yi ba don ma na barshi ya zauna ne shi ne harda ce min zai tafi, Armaya'u ta ce munafuka daga ganin yanda kike mai wannan kallon ƙasa-ƙasan kin sonshi,ai wannan gayen baya cikin mazan da za'a gani ace ba'a so. M Bash ta ce ƴar iska tana sonshi Ruƙy munafuka ce kin santa sumumi sumumi da ita. Ruƙayya ta ce "ko yana burge wasu banda ni yana da fa mata gaskiya bana son kishiya,auren dole ga kishiya? Ba zan iya ba." Har suna haɗa baki "Kada ki iya." M Bash ta ce dama yanzun ya ce mu daina maganar Zainab ba ƙya so." Ta ce mukayi dashi? Armaya'u ta ce ke kishiya ce zata baki tsoro? Gara ma ki tashi ki riƙe mijinki" M Bash ta ce ballantana Zainab,ni ranar da su Mom da ƙawatar suke labarinta da Mamanta duk saina raina mata wayo. Ruƙayya ta ce wacece Zainab ki bani labarin ta mana?" M Bash ta ce "Zainab Adam mahaifinta ministane haifaffen Sokoto, uwar ta ƴar Gombe ce ni ko bafullatana ce a Yoben Oho,bata da mutunci matanshi uku ance duk sai da ta koresu, harda matarshi ta farko wacce sukayi auren saurayi da budurwa, ƴaƴan ta biyu duk mata Zainab sai ƙanwar ta Jamila, sauran kishiyoyin data kora sune masu yara maza.

Ance tana ji da Zainab sai dai babu tarbiyya, tamkar karuwa haka Zainab ta rinƙa bin maza, Uban dama an gama dashi, shegen son kuɗi ne da uwar harma ƴar in gaya miki shine aka yi rufa-rufa aka bawa mijinki.

Ruƙayya ta ce "na shiga uku banason kishi da mace mai shige-shige aje a sabauta ni a banza." Armaya'u ta ce ba sai ki nemi tsari gurin Allah ba,ga addu'o'i nan na tsari. Ruƙayya ta ce nidai an haɗani da aiki ina da kishi mai tsanani musamman akan Dady wallahi da ace be aure ba bazan damu ba.

M Bash ta ce "kamar ya ya?" Nan Ruƙayya ta basu labarin farkon haɗuwarta da Dady har zuwa yanda abubuwa suka kasance ta ɗaga yatsun hannunta,kunga zobunan alƙawuran da muka yi ma juna har sau biyu. Armaya'u ku kanku shaidu ne cewa bana kula kowa, amma ba tashi ganin Dady ba sai in ganshi da budurwa, M Bash in bazaku manta ba lokacin da muka je bikin Uncle ɗin ku ban dawo Kaduna da lafiya ba." M Bash ta ce ƙwarai har Mom tasa Dakta ya duba ki." Ta ce kin tuna to lokacin ne na ganshi da wannan Zainab ɗin haka ganina na biyu,dan na uku ma tsabar wulaƙanci ban ganshi ba sune suka ganni suka rage min hanya amma ƙala bai ce min ba har na sauka, shi ne don iko aka ɗaura min aure dashi.

*** *** ***
Sun jinjina labarin data basu, sannan suka bata shawarar yanda zata zauna da mijinta. M Bash ta ce kada ki damu kin san kana naka tsarin Allah na nashi, Allah ya tsara ku biyun ne matanshi.

Armaya'u ta ce ban ma ga abin damuwa ba tun da tasan irin son da yake miki." Ruƙy ta ce ke rabamu da mazan nan munafukai ne yazo ya ce min I love You yaje ya ce mata I miss You." M Bash ta ce koma menene yanzu dai ki dage da shan kankana da aya da dabino,da ƴan kayan marmarin nan muna rainasu, aƙwai aiki zaki gane in kin kama su, kuma akwai wasu sinadarai da Mom ta bani na Arabic ne, Armaya'u ta ce nifa? M Bash ta ce a'a sai anyi bikinki zan baki, ta ce One month fa ya rage, ta ce to zan baki sai kin zo Abuja, Armaya'u ta ce zan zo amma kafin nan zan je in fara amfani dasu kankana ɗin, Ruƙayya ta ce kai ku rabu dani ya ma samu in tare gidan shi bare ma har na tsaya shan wani abu aje a ƙwararraɓa ni, dariya suka saka mata, M Bash ta ce yanzu duk kishi ne matsalar ki,kina shiga hannunshi shiru za'a ji ki tunda kina sonshi. Ruƙayya ta ce zaku sha mamaki aini bana son cin amana, kuma zan nuna mishi mu mata dabanne. M Bash ta ce ina son fita anjima mu ɗan shiga kasuwa.

Bayan sun ci sun sha girkin da Umma tai musu can gurin la'asar suka shirya zuwa kasuwa, Ruƙayya ta ce Umma zamu kasuwa, Umma ta ce ki ma mijinki waya ki sanar dashi, takaici ya cika Ruƙayya su Sadiya suka ce ki kirashi, ta ce ya tafi da wayar ai, Armaya'u ta kirashi da tawa, ta ce ai ban ma riƙe number ɗin shi ba,ke ni ban ma san me zance mishi ba." M Bash ta ce bari na kira number Al-Mustapha ya yi min text ɗin number Dadyn.

A wayar Armaya'u suka kira M Bash ta ce Ruƙy M gashi tana ringing ta amsa tana cewa me zan ce mishi? Ya ɗauka ya ce "Hello," ta yi shiru ya ce "who is speaking?" Ta ce Ni ce, duk da ciki-ciki ta yi maganar hakan be hanashi gane muryarta ba, ya ce Pretty ya ya ne? Ta ce kasuwa zamu je, tana wani ɗaure fuska tamkar tana ganinshi, ya ce to bari na turo muku direba, ta ce daka barshi zamu hau mashin.

Da sauri ya ce kada ki yarda ki hau mashin ki jira ni, ta kashe wayar ranta ɓace ta ce kunji ko ya samu na kira shi har da cewa kar na yarda na hau mashin wai mu jira shi. Armaya'u ta ce yana da gaskiya aje a yadda mishi mata, M Bash ta ce ƙyale ta da Allah da kanta zakiga ta ƙanƙame mijinta. Ruƙayya ta ce sai kuma kuyi,wayar Armaya'u ya kuma kira ya ce su fito, baya suka shiga.

Ruƙayya na ƙoƙarin shigowa bayan suka tura ta ta zauna gurin mijinta, dole ta zauna gaba tana wani zumɓura baki, ta ɗan saci kallon shi a ranta ta ce ya ci sunanshi Son Guy ko yaushe cikin gayu yake, yanzun ma jeans ne baƙi da baƙar riga mai dogon hannu ta ɗameshi, fuskarshi fes sai ƙyakƙyawan sajen da ya kewaye bakinshi zuwa gefen fuskarshi, idanunshi masu hasken nan suna birgeta.

Ya tada mota yana cewa "Wai ke kallon fa?" Gabanta ya faɗi ashe ya gane, ta dake ta ce "Me zan kalla a nan?" Ya yi murmushi sannan ya ɗan ɗaga murya ya ce wace kasuwar zamu? M Bash ta ce Ruƙy wace zamu je? Ta ce ka kaimu Abubakar Gumi, ya ce me zaki siya? Ta ce sune zasu yi siyayya, ya ce baki da kuɗi ne,in ga jakarki,ta ce a'a ni ba'a ganar min jaka,kai ka cika tsokana kayi abin da ke gabanka..........

🖊️🖊️🖊️
[8/16, 08:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.