Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 9 of 9
Page 9
Ya jima yana mata aune-aune tare da tambayoyi,ya tambayi Al'adar ta,ta bashi amsa tunda ta tare bata taɓa yi ba,don dama tana daɗewa batayi ba, ya ce ma Momy yana son fitsarinta, bayan ta shiga toilet tayo Momy ta kawo mishi sannan ya ɗibi jini, Momy ta ce wannan kumburin na fuskarta fa? Likita ya yi nazarin fuskar sannan ya ce ma Momy Hajiya wannan ba mari ba ne? Ya cigaba wannan babu damuwa mari ne da kuma kuka zai washe,kan Momy ya ɗaure ta maimaita a ranta mari? Yana tafiya Momy ta soma tuhumar ta akan batun mari gaske ne ko ko faɗin likita ne?
Hawaye ya soma bin kumatun Ruƙayya ta ce a'a ba mari bane, Momy tayi ta yi amma Ruƙayya ta ce ba rigima sukayi ba,ta ce to ina direban da kika zo dashi? Ta ce a'a ita kaɗai tazo a motar haya, ta koma ta ƙwanta jikinta na cigaba da rawa, Momy ta ce gashi bai bada magani ba ya ce sai ya dawo zai je yayo test ta kawo mata tea mai kauri,ta ɗan sha Momy ta kira wayar Dady, ya ce Momyna ina shirin kiranki ki ka kirani yi haƙuri yau duk ban kira ku ba.
Ta ce kaini ba wannan ba me yasa ka turo Ruƙayya babu lafiya kuma a motar haya? Zumbur ya miƙe daga kan kujerar shi tuni rannan nashi ya soma zugi a ranshi ya ce motar haya? Babu izni lallai kuwa, amma ya yi ƙoƙari ya ce tanace sai tazo Momy, direban su ya fita Ni ku Sabi'u zai kaini ofis,ta ce wannan ba dalili bane me yasa tunda kasan bata lafiya baka tuƙa kanka Sabi'u ya kawo ta ba,ta numfasa aƙwai abinda ya faru kuke ɓoye min kai da ita domin likita ya ce mari ne yasa fuskarta ta kumbura.
Ni ba mahaukaciya ba ce Dady yanda nasan ka keson Ruƙayya in ba akwai wani abu ba da zaka bar komai ne kuzo tare, amma koma menene ku kuka sani, tunda kunƙi faɗa, ta kashe wayar ta tazo gaban Ruƙayya tana faɗin ke mace ce ke zai ƙwara gara ma ki...... Aman da ya taso ma Ruƙayya shi ne yasa Momy saurin tare ta tare da yin shiru da ƙyar suka isa toilet ta dinga ƙwarara amai tamkar zata amayar da ƴan hanjinta. Hankalin Momy ya yi matukar ttashi ta kuma kiran likitan ta shaida mishi ya ce yana nan zuwa so yake sai ya gama test.
Kafin wani lokaci ta galabaita,tuni numfashinta ya soma ɗaukewa, to amai ya yi yawa ga cikinta bata ci komai ba. Tsoro ya cika Momy ta yiwa likitan waya ya kai sau shida, sannan ya iso gudu-gudu bayan ceto numfashinta sannan yasa mata ruwa tare da allurai cikin ruwan nan da nan ta samu bacci, likita ya miƙa ma Momy takardun yana murmushi ya ce Hajiya ga sakamakon test ɗin yarinya tana da juna biyu.
Da sauri Momy ta miƙe da gaske Doctor? Likitan ya ce tabbas ga shaida nan cikin takardu, alhmdllh ita ce kalmar da Momy take ta faɗi tare da yiwa likitan godiya, bayan tafiyarshi Momy ta je ta zauna kusa da Ruƙayya tana shafa gefen fuskar Ruƙayyan hawayen farin ciki suka zo mata shekaru sama da talatin da biyar basu ji kukan ƙaramin yaro a gidan su ba sai dai na jama'a in sun zo. Wani sabon son Ruƙayya ya ƙara shigar ta, Allah ka bamu masu albarka, ta furta tare da miƙewa, wayarta ta ɗauka ta kira maigidan, ya ce yaya dai Madam? Ta ce goron albishir nake son ka bani, ya ce goro? Ta ce yes,ina sauraren ka. Ya ce to na baki duk abin da kika zaɓa don nasan baki albishirin banza, ta ce ƴarmu Ruƙayya mata Son ɗin ka tana da ciki yanzun haka gata nan, ya ce Alhamdulillahi gani nan zuwa.
Kafin yazo sai da ya kira Son É—in nashi yana murna da faÉ—in congrats My Son ina farin ciki tamkar ranar da likita ya sanar dani cikin ka, Allah ya bamu masu albarka ya kashe wayar.
Dady ya ɗaure haƙiƙa ƙila gatse yake mishi mahaifin nashi,yana nufin ya yiwa Ruƙayya wulaƙanci ba haka ba murnar me zaiyi mishi? Nan ya samu kanshi da tunanin ya ƙyauta mata kuwa? Can kuma wata zuciyar ta ce ita ta ƙyauta maka kenan da tayi sanadin sunnar ma'aiki, ya miƙe yana shirin fita a ranshi yana raya zai matsa sai ta faɗi gurin da taje ta yo asirin nan dan ma ita ce taci albarkacin so.
Bai samu jirgi ba dole Sabi'u ya jashi a mota, sun isa Kaduna ana magriba, don haka shima masallaci ya wuce, yana dawowa gurinsu,sai dai ba kowa, duk suna bedroom É—in Momy can ya tadda Pretty É—in shi tana ta bacci su kuma Momy da Hajja da tazo dubata suna cin abinci.
Ya shiga da sallama yana raba ido suka amsa idonshi ya sauka kanta tana ƙwance da sauri ya isa gurinta a ruɗe ganin ana yi mata ƙarin ruwa gashi ta rame tamkar ta daɗe tana ciwo ya zauna yana shafa fuskarta, Momy haka Pretty tasha wahala? Tana murmushi ta ce kai kayi wauta sannan kana cewa tasha wahala? Bayan kai kasa ta biyo motar haya,suma ta dinga yi min ɗazun, ya ce suma Momy cikin tsoro, ta ce ƙwarai kuwa,ai tunda likita ya yi mata allura shikenan tayi bacci ta tashi ɗazun ta kuma komawa gata dai har Yanzun ya dubi Dad ya ce Dad Allah ya soni da Pretty ta rasu ya zanyi?.
Hajja ta ce ba gani ba inta rasu, ya ce a'a bafa zan iya da tsuhuwa ba, Momy ta ce ai da tsohuwar zuma ake magani, ya ce a'a yanzun an daina sai sabuwa farar saƙa,duk suka saka dariya ya ce Momy me likitan ya ce game da jikin nata? Dad ya soma murmushi dama Momyn taka bata sanar maka ba na kira ka ina taya ka murnar zan samu jika,ya tsura mishi ido, Dad da gaske kana nufin Pretty tana da ciki? Momy ta ce ƙwarai ƙyautar da Ubangiji ya yi maka kenan kana wasa da ita ka barta ta kamo hanya cikin murna ya cicciɓeta tana bacci cikin firgici ta farka tana yunƙurin amai, Momy ta ce ai gashi nan zaka taso aman.
Nan ko ta soma sharara shi har shi sai da shi kanshi ya tsorata likitan dai aka kuma kira yazo ya ce bebyn nan yana wahalar da Maman shi, Dady ya ce Dakta ya ya za'ayi ta daina wannan aman ne? Doctor ya can wannan kam sai dai haƙuri dan bazai dena ba har sai cikin yayi ƙwari sosai sai dai muyi ta sa mata ruwa kawai.
Bayan likitan ya maida mata ruwan tare da wasu allurai ta koma baccinta, Dady hankalinshi ya tashi su Momy da Hajja suka dinga ƙwantar mai da hankali, Dad ya tafi maida tsohuwa gida, Hajja ta tafi tana mai tausayin Ruƙayya shi kam Dady ya ƙe ƙashe ƙasa ya ce nan zai ƙwana dole Momy ta tafi saman Dad.
Ciwo ance in yaji dare domin a wannan daren har wasiyya Ruƙayya ta soma bari inda take cewa ya yafe mata kuma yasa su Affa da Umma da Yayyanta su yafe mata,ba shiri Dady ya yi ma su Momy waya ya ce suzo Pretty zata mutu,suna zuwa suka sare, domin lokacin da suka zo jikin nata ya yi tsanani tana ta neman gafara sumanta biyu,ruɗewa ta ƙarshe Dady ya yi,kiran sallar farko suka nufi asibiti inda yace da likitan shi dai kam ya haƙura da cikin da ƙyar su Momy suka shawo kanshi ya haƙura aka bar cikin,satin ta ɗaya a asibiti taɗan samu ƙwarin jiki bata cin komai sai tuwon Hajja da miyar yakuwa kullum sai an yo yaje ya amso su Affa da Umma da sauran Yayyanta kuwa kullum sai sun zo Dady ne me gaya musu ina da ciki ne duk abokanshi sun sani kai har Armaya'u da Sadiya duk ya yaɗani don haka kullum cikin ƴan dubiya muke,an sallameni kamar yau washegari ya koma.
Kafin ya tafi sai da ya tada fitina domin su Momy sunce zasu gyara mata sasanta ta koma ta ce ita dai anan zata zauna ɗakin Momy, Momy ta ce shikenan ma nima zanfi son haka don inma kina can zan raba hankali na biyu ne, Dady ya ce shida so yake su tafi tare, ta ce a'a,su Momy suka ɗaure mata gindin zama, bayan fitar Momy ya zauna kusa da ita ya ce Pretty ki dubi girman Allah da girman son da nake miki ki gayan gurin da kikaje aka yo ma Zainab wannan asirin nasa a karya, zalunci ba ƙyau kefa kike min wa'azi.
Takaici ya kamata hawaye ya soma zubo mata ya ce kash kinga matsalar ki to menene abin kuka,Ni ba abinda zan miki, ta ce nifa Dady ban mata komai ba ƙarya kake son in maka? Allah ban san komai game da abin da kake tuhuma ta ba,yaja tsaki aike aƙwai ki da gaddama ne, Allah in har baki faɗa ba sai na haɗa ki da Affa,ido ta tsura mishi a ranta tana tuna kafin aurensu tamkar ya haɗiye ta, yanzun kam gashi zaune yana ƙulla mata sharri,sharrin ma gaya masa aka yi yaci ya auna amma ya hau kai ya zauna, ta ƙwanta tare da faɗin ka gaya masa mana,ta cigaba gaskiya nifa na gaji ban iya faɗa ba bazan iya zama da mafaɗaci ba ka gane? Auren nan babu dole dama sai da nace a'a aka matsa min, wani sabon haushin ne ya kamashi ya ce cikin masifar tashi dama na sani ba sona kike yi ba, to amma ai sai kibar masu sona su so ni ko? Sai kije ki mana mugunta.
Aure kuma da kike faÉ—in babu dole shine kuwa dole domin ba saki cikin shi duk wahala dole ki jure, ya fita gara ma ki faÉ—a min gurin da ki ka yo wannan mugun abun dan kin san ni ba mazinaci bane bare in bi na waje bazanje ina kallon matata kuma batada amfani a gurina ba.
Ya fita ta ƙwanta tana kuka,jin shigowar Momy sai tayi tamkar tana bacci shiru tayi tana tuna kai aure yana da daɗi da wuya, amma wuyar tafi yawa, shiyasa kowa sai ya ce Allah ya bada zaman haƙuri Allah ya saɓa halayya, gaskiya ne ta tuna yanda Affanta da Umma kai har da yayyenta suka yi ta jaddada mata kalmar nan ta haƙuri,lallai dole tayi haƙuri.
*** *** ***
Lokacin da Dady ya isa gida Zainab suna tare da Sunday ya soma zuga mata kira tsoro ya kama su amma sai ta ɓoye shi cikin wardrobe ta fito tamkar mai bacci tana mishi sannu da zuwa,ya zauna ta kawo mishi Hollandia mai sanyi ya ce ina Sunday ya shirya min table ina jin yunwa sosai,ta ɗan daburce,na na aike shi gidanmu, to bari inyi wanka in yaso ke sai kije ki min abinda zan ci tunda kin aike shi me ya hana ki aiki direba? Sunday ba ɗan aike bane,ta ce yi haƙuri,ya nufi ɗakinshi ita kuma ta nufi kitchen sai da ta tabbatar ya shiga ɗakin sannan ta fito ta buɗe Sunday,a sittin ɗin shi ya fito yanda yake gudun yaso bata dariya duk abinda aka ce babu gaskiya aƙwai matsala, Allah ka tsaremu da shiga halaka.
Momy da Dad suna ji da Ruƙayya tamkar ƙwai duk abinda take so shi za a bata har sai ya hau kanta yanzun an tashi daga tuwon Hajja an koma ɗan waken Umma kullum direba sai yaje ya karɓo, Hollandia ko abin har tsoro yake basu dashi take karyawa haka cikin dare, ta murmure sosai, wannan karon Dady satin shi uku sannan yazo.
Ya sameta tayi gayu sosai cikin material mai bulun fulawoyi tayi ɓul,ɓul gwanin sha'awa dan cikin yasata haske,ta ɗaure gashin ta daya sha gyara salon taje aka gyara mata, Momy sun tafi biki ita kaɗai ce a gidan ya zuba mata ido. Ta ce mishi sannu da zuwa ya hanya? Ya ce lafiya lau Pretty gaskiya kinji sauƙi kin yi ƙyau wannan karon zamu koma Abuja ko? Nan take tasha mur,tayi kicin-kicin da rai gaskiya kada ma ka soma babu inda zanje bayan haka ma ina jiran na haihu nayi gaba rayuwa da kai Dady ba zata yiwu min ba, dole in haƙura da kai.
Ya ce haba Pretty yanzun daga zuwa na,kin tareni da wannan maganar ko ruwa baki bani ba,in kina furta rabuwa tsakaninmu,ji nake tamkar kina watsamin ruwan zafi, babu wannan a tsarin aurenmu ki tuna wahalar da nasha a kanki,nasha wahala a kanki, ta ce shi ne yasa yanzun ka ke fanshe wahalar ka a kaina? Ya ce duk mu bar maganar naji baza muje Abuja ba, amma sai mu koma sashenmu in yaso in na tafi saiki dawo nan. Ta ce a'a nifa ba zanje ko'ina ba,me kake son su Momy su ɗaukeni? Ya ce to ni shikenan sai nayi ta zama cikin ƙunci alhalin ina da mata har biyu gaskiya Pretty ki duba dai.
A ranta ta ce tunda kanada buƙata ai dole ka ƙwantar da murya, inda maza suke bata mamaki kenan ko sarki ne yakan hura hancinshi a fada daya shigo gida gaban mace koda sa'ar ƴarshi ce dole ya yi biyayya ya ƙwantar da murya,tana tunani bata san ma har yazo kusa da ita ya zauna ba, sai dai ji tayi ya jawo ta jikinshi tayi mutsu-mutsu alamar ƙwacewa ya ce haba Pretty ki ji tausayi na mana? Ta ce cikin shagwaɓa baka ce nai muku asiri ba? Da yake namiji wawane wani sa'in sai ya ce nima Zainab ce ta ce min ke ce kikayi mana,ta ce kayi bincike ka gane, ya ce ni kaina bana gane kaina ƙwanan nan ban san meke sani yin wasu abubuwan ba,in ina son inyi tunani sai na kasa kome yasa? Ta ce kana addu'a,yayi shiru can ya ce gaskiya bana addu'a akan matsalar.
Ta ce ai kaji matsalar ga addu'o'i nan cikin husnil muslim kana dashi wasu ma suna kanka amma ka kasa, ya ce haka ne zan kula yanzun ya zamuyi? Ta ce likita ya ce fa na huta, ya soma kiran layin likitan ta tsura mishi ido dariya yake bata duk ya birkice sun gaisa da likitan ko kunya yake tambayar likitan ko zai iya kusantar matarsa yanzun don yaga taji sauƙi sosai likitan ya ce me zai hana? Yanzun ne ma zakafi samun natsuwa domin mace in tanada ciki ta kanfi sanda take amarya sai dai ka biya sannu a hankali.
Ya dubeta yana murmushi ina Momy ta je ta ce taje biki nasan ta kusa dawowa ya kamo hannunta zo muje in nuna miki wani abu a sasanmu,ya jata in so ya haÉ—u da so sai soyewa, abinda ya faru kenan, Dady kam ya shiga ruÉ—u. Sanda suka dawo sasan Momy ta jima da dawowa ta ce mijinki yazo ne shiyasa na neme ki na rasa naso in kira wayarki sai kuma na ganta a kan gado.
Kunya ta kama Ruƙayya ta sosa wuyanta ta ce eh dama shi ne yazo,shi kam dariya yake mata ya ce Momy ƴar taki taji sauƙi na ce ko zamu koma tare ne? Ruƙayya ta yi saurin cewa Allah nifa bazan je ba Momy, Momy ta ce in dai zaki bishi to ku tafi,ta ce ni bazan je ba ta turo baki Momy ta ce shikenan daina fushi.
Ƙwana uku ya yi sai sun fita wai gurin likita Momy har dariya suke bata ita za'ayi wa wayo, ya tafi da ƴar nutsuwa tunda tana yawan matsa mishi yanayin addu'o'i duk sati ɗaya sai yazo Momy tasa ta share sashen su in yazo sai ta koma can in ya tafi ta dawo gurin Momy,sai dai shegen faɗan nan na nan amma ba kamar da ba, Ruƙayya anyi ƙyau kamar ta fashe cikin ya fito gwanin sha'awa.
Zainab dai batasan Ruƙayya tana da ciki ba,sai wannan dawowar da Dady ya yi inda yake ce mata Pretty ta shiga watan haihuwar ta zai koma Kaduna kullum ya dinga zuwa Abuja ofis, ta ce ai wai kana nufin Ruƙayya ciki ne da ita? Ya ce au baki sani ba? Ai ta kusa haihuwa, kinga ke kaɗai na manta ban gaya miki ba.
Nan ta miƙe cikin tashin hankali lallai Dady ka kasa nema min magani balle in samu lafiya, amma ita kai mata ciki,koda yake ƙila nice bakason na haihu shiyasa, ya ce ke kada fa ki dameni, kinga nasan kin gama zubar da ƙwayoyin ki a titi zaki min surutun banza kodan kinga ban gaya miki sakamakon da likitan ya gaya min ba to tunda kinso ji yanzu zakiji ya ce bazaki haihu ba sakamakon shan ƙwayoyin hana haihuwa, magani kije can ki nema da kanki nidai tunda nasan lafiya ta qalau shikenan ya sa kai ya wuce.
Mantuwar da Dady ya yi itace ta dawo dashi gida,sai da ya bincike ɗakinshi kaf baiga jakar ba, kuɗi ne Naira miliyan uku da dubu ɗari baƙwai ba canji duk daloline na America zai biya cikon kuɗin wani inji daya siya da wani banki suka yi gwanjo amma ya nemi jakar ya rasa,ɗakin Zainab ya nufa yasan tana nan tana shegen baccinta da ta iya.
Gabanshi ne Ya yi mummunan faɗuwa mai zai gani Sunday da Zainab,sam basu san yana tsaye ba ma da ƙarfi ya furta innalillahi ya nufi gurinsu wani abin da yafi ɗaure mishi kai da sun ganshi amma sun kasa barin abin da suke, ya ɗauki waya ya kira Hajiyar Zainab ya ce tazo yanzun nan ya fito ya ja musu ƙofa don takaici hawaye yana zubo mishi, to dama asirin in sun fara masha'arsu sai sun kai awa biyar sannan zasu dawo hankalinsu kuma shigar su kenan ya dawo don haka har Hajiya ta zo ya ce ta shiga ɗaki gashi nan zuwa, ta zata faɗa sukayi tana shiga ta samu saɓanin haka.
Shi kam jami'an tsaro ya kira a waya sannan ya shiga ɗakin wani abin mamaki tana jansu tana duka suna komawa suna mannewa har sanda jami'an suka zo abin da yake faruwa kenan Hajiyarta sai kuka take yi sai da mutane suka cika ɗakin tankam sannan fa sun cika lokacin su da dukan da ƴan sanda suka dinga musu, Dady ya wuce ya ɗauko jakarshi da yazo nema a gefen gado,ƴan sanda suka tasa su suna kuka, Hajiya tana ta ba Dady haƙuri, ya ce ai haƙuri yana gurinku ko kina ganin zan kuma zama da annoba? Ai Zainab annoba ce kema ki fita kafin nasa a kama ki.
Ya zauna jagwaf akan kujerar ofis ɗin shi ya kulle kanshi ya yi kuka har ya gaji, Sunday yaronshi daya ba amana, Zainab matarshi wane irin ƙwazo ne baya dashi? Amma har sai ta nemi Sunday? Lallai mutum ba abin yarda bane.
Allah sarki Pretty matar da kullum yake zargin ta da yiwa Zainab asiri ya dubi hannunshi yanda ran nan ya wawwanka ma fuskarta mari,ya miƙe ya ji ma sam tsani wannan gidan don haka gidan hutawarshi ya nufa dake area 2 ya shiga ya ƙwanta bai jima ba bacci ya yi gaba dashi ya jima a ƙwance.
Sanda ya farka sai yana jin shi wani irin tamkar an sauke mishi wasu kaya masu shegen nauyi. Yana zaune komai ya dinga dawo mishi sabo yana ta nazarin abubuwa ya É—auko wayoyinshi missed calls barkatai cikin kowacce waya,na sirikinshi sun fi yawa,yana ganin girman mahaifin Zainab shi ne ma dalilin da yasa baya kallon wasu abubuwan da Zainab É—in take mishi a zaman su.
Don haka sai ya soma neman layin shi,sun gaisa inda Dady ya bashi haƙurin rashin ɗaukar kiranshi yana bacci ne ya ce ba komai dama shima ya kira shi ne dan ya bashi haƙuri game da abubuwan da suka yi ta faruwa nan Dady ya koro mishi komai game da irin zaman nasu.
Satar da ta dinga yi mishi kai har yanda ya ɗauki watanni baya iya saduwa da ita duk saida ya zayyane mishi a ƙarshe ya ce ya sake ta saki uku. Sam minista bai damu da hakan ba don shima yau ya gaji yana zuwa gidan zai sahale wa Hajiya sai dai albarkacin ƴaƴanta ta zauna a gidan,shi kam dama yana neman wata ƙanwar abokinshi,bazawara ce kuma yana da tabbacin yarinya ce mai hankali sai ya koma sabon gidan daya jima yana ƙerawa gidan da Hajiya ta ci burin zama,sai dai yasan yanzu kash sai haƙuri.
Garin Abuja ya yi mishi zafi ya tsani gidan nashi, don haka a wannan yammacin ya kira wayar Sabi'u ya shirya musu zuwa Kaduna, Sabi'u ya ce Oga zamuyi dare a hanya. Ya ce Allah zai kare,koda ya shiga gidan É—akinshi ya wuce kai tsaye be koyi wanka ba ya canza kaya ya É—ibi kuÉ—aÉ—e ya fita.
Sun isa Kaduna ana sallar isha'i, don haka suna tsayawa sai masallaci, Ruƙayya tana kitchen riƙe da kula ta fito zataje ɗakin Momy, sai kawai sukayi kiciɓis da Dady ta yi sororo tana dubanshi ya tako zuwa gabanta, ganinshi tayi ya rame,ya kamo hannunta, Pretty ina Momy? Ta kalli sashen Dad ya ce tana saman Dad ne? Ta kaɗa a hankali ta ce Eh,ya tsurawa hannuwanta ido Pretty hannuwanki sun kunbura ne ko? Nan ma kai ta kaɗa ya ce ki zauna bari naga su Momy ya zaunar da ita tamkar mai ɗora ƙwai kan kanfa. Ya yi sama da sauri,ita kam kullum tana mamakin Dady tamkar mai aljanu.
Ta miƙe gara ma taje ta gyara musu gefen su don wancan Zuwan da ya yi irin masifar da ya dinga mata,wai shi baya son ƙazanta,tasan zai zo amma bata sa an gyara ba,da tace mishi wazan sa? Sai ya ce mata Oho miki, to Momy ƴan aikin ta bana ƙwana ba ne suna gamawa suke tafiya, girki tafi son tayi da kanta ita ba yara ba bare ta ce matsalar yara ko zasu ɓata gidan da dai sauransu.
Haka ta zage tana ta faman gyara, da É—akinshi ta soma duk da babu wani datti dama, sannan ta koma É—akinta zuwa falo.
Shi kam wannan lokacin yana can yana zayyane ma su Momy abubuwan da suka faru. Sun sha mamaki Momy ta ce ai dama rashin bincike a aure matsala ne, Dad ya ce aini na nemi sani da mahaifinta naji an yabe shi, Momy ta ce mahaifinta zama yake a gida? Dady ya ce shima yau ɗin nan ya ce zaije ya rabu da uwar shima ya gaji, Momy ta ce Allah sarki Ruƙayya nifa nasan zuwan nan ba lafiya ba, Dady ya ce Ni kaina Momy inna tuna marin da nayi mata duk sai naji kunya. Yanzun sai ka bata haƙuri cewar Dad, ya ce dole ma, duk tare suka sauko sun zauna falo suka ce ya kira ta,ya duba bata ɗakin Momy bata toilet bata kitchen yazo yana huci ya ce ban ganta ba, Momy ta ce duba sasanku,nan ya sameta tana ta goge goge ta gama shara da alama duk ta gaji.
Da gudu ya isa gurinta ya rungumo ta "haba Pretty, haba Pretty ya ya zaki zo kina aiki haka bayan kinsan cewa baki da ishasshiyar lafiya, daga yau bana son kina komai kin ji ko? Kallonshi kawai take.
Su Momy sukai mata bayanin komai tare da bata haƙuri akan duk abubuwan da Dady ya yi mata, shima Dady ya ƙara neman afuwa,ta ce ita dama bata riƙe shi a ranta ba,koda suka ci abinci suka nufi sashensu ta kasa sakin jiki dashi, ya ce haba Pretty na ni ne fa dadynki mai son nan naki kin tuna? Ki share komai ki tuno da farkon aurenmu, yanzun na zama naki ke ke ɗaya ko? Ya ɗaga mata gira.
Ta dubeshi da murmushi shikenan Dady komai ya wuce na yafe maka.
"Yauwa My Pretty, nagode."
Ya ƙara matsowa daf da ita yana yi mata wani irin kallo mai tattare da tsananin so da ƙauna. Itama kallon nashi take yi cike da wani irin yanayi mai cike da tsantsar so.
"Come to me My Pretty,I want as some thing please come." Murya ƙasa-ƙasa yake faɗar maganar,a hankali tabi umarninsa kafin wani lokaci suka shiga farantawa junansu rai, sai gashi sun dawo kamar yau ne daren farkon su na amarci.
*** *** ***
Haka suka cigaba da zaman su shi da Pretty cikin ƙwanciyar hankali da farantawa juna, Allah ya basu ƴaƴa biyu mace da namiji ƙyawawa dasu.
Hankalin kowa ya ƙwanta, kowa sai farin ciki yake, yanzu Dady bashi da wata sauran damuwa. Ruƙayya ta zage damtse kullum faranta ran Dady take. Wannan shi ne abin da yasa iyayensu suka cigaba da yi musu addu'a tare da fatan alkhairi cikin alfahari da jin daɗin zaman aurensu.
Alhamdulillahi
Ƙarshen littafin FIN ƘARFI
Taku Halima Abdullahi K Mashi.