Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 9
Page 8
Ruƙayya da taga shiru a ranta ta ce namiji sai a barshi,ta samu guri ta zauna ta ciro waya ta soma kiran Armaya'u, "Sadiya ƴan fatakol amaryar shitu," Sadiya ta ce ƴar gidan Dady ai na zaci ni baza'a kirani ai min sallama ba, jiya munyi waya da M Bash take ce min zaga duniya da bebyn naki." Ruƙayya ta ce lallai ma M Bash har ta gaya miki ina ce ma Dady beby?" Ta ce dole ne ta gaya min tunda mun kawo ki ne kina kukan bana son shi, sai kuma a jiki kin koma ce masa beby inye! Ƴar gidan bebynta." Ruƙayya ta ce ta naki ne? Zan haɗa ki da Shitu in ce yayi miki kishiya. Sadiya ta ce don ke kinada ita?.
Ruƙayya ta ce to yanzu dai sai mun dawo, ta ce ku dawo lafiya ki samo tsarabar Baby boy. Rukayya ta ce baki ce twins ba, ta kashe wayar, sannan ne suka fito tare da Zainab tana manne da jikinshi.
Ruƙayya ta miƙe tana faɗin "To Zainab sai mun dawo." Ta yatsina baki ta dubi Dady ta ce My dear sai ka dawo ka kular min da kanka, ya ce kada ki damu Zee nima ki kular min da kanki da gida,bana son yawo mara dalili ta ce dan wannan kada ka damu.
Ruƙayya dai tayi gaba kishi ko a mota sam taƙi sakin fuska sosai ya kula da haka sai abin ma ya soma bashi dariya, ita fa tace sai yaje ya ma Zee sallama, amma kuma sai ta kama shan kunu,ya raya tsokanar ta ya ɗauki wayarshi ya kira yarinyar dake nacin son shi kullum tayi ta damunshi da kira. Tasha mamakin kiran nashi dan bai taɓa kiranta ba, ringing ɗin farko ta ɗauka yace Aysha ƴanmatan gari, ta ce a'a ku ne masu gari Alhaji Yusuf,yau wace rana an kira ni? Ya ce tafiya zamuyi da amarya, shi ne nace bari in kira muyi sallama don kada ki kira waya kiji shiru kin san bana son haka.
Ruƙayya ta warce wayar ta kashe sannan ta tura a jakarta, ya dubeta "Pretty ya ya zaki min haka? Muna sallama da budurwa......." Wani kallo da ta watso mishi ne yasa ya yi shiru tamkar ya ƙwashe da dariya, amma ya dake ta ce tun kan muje airport tsaya in sauka."
Ya ce saboda me? Ta ce nidai na fasa zuwa kaje ku tafi da A'ishan ka da Zainab. Ya jawo ta haba Pretty na,ta ture shi kai na kula na mamajo ne sarkin mata, saura ta huÉ—u, ya ce haba kamar wani bazazzagi? Ta ce kaima gara ba zazzagen da kai,ni da gaske fa nike bazan je ba,ya bar dariyar da yake yi ganin da gaske take. Ya ce wasa nake miki Pretty kin san ke kaÉ—ai ce My Sweet one, My everlasting, My dear one,kin san Allah da in rasa ki a duniya,gara ace babu rayuwa ta.
Ta harareshi daɗin bakin namiji shi kake min,ya ce haba My Pretty kin san wuyan da nasha a kanki kuwa? Bayan ciwo da rashin ƙwanciyar hankali ga tsabar sha'awa da begen ki,bazan gaji da gaya miki sau uku ina zuwa aikin hajji inyi ɗawafi in rungume ka'aba ina kuka ina gaya ma Allah Ruƙayya, Ruƙayya. Ya ya zaya bani nayi wasa dake? Ranar da aka ɗaura min aure dake sai da nayi azumi uku dan nuna godiya ta ga maƙaginmu." Ya ɗan saurara sannan ya cigaba, "Yanzu burina na gaba inga kin cikamin gida da yara,don Allah tafiyar nan kar ki bari mu dawo baki bani Baby ba kin ji?" Ta ɗan kama kunnenshi ɗaya ta ɗan ja sannan ta ce "Allah zaka roƙa ya bamu masu albarka," ya ce kullum cikin roƙonshi nike sannan zan zage damtse a wannan tafiyar kema ki dage,inga kina ɗan aman nan na masu ciki,jaye fuska tayi tare da faɗin nidai babu ruwana.
***. **** ***
England suka fara yada zango cikin wani shahararren hotel.
Wai! Naso ace kuna nan a gurin ku ga soyayya da kanta, Tabbas Ruƙayya ta yarda beby ɗin ta ita kaɗai yake so Son ya manta da kowa da komai daga bautar Allah sai ta Pretty itace ta tuna mishi da abubuwan da ya dace ya yi kiran ƴan Nigeria zuwa ƴan kasuwancinshi,yau da suka cika sati biyu yakamata su bar ƙasar amma sai yaji baya son tafiya sai da suka ƙara ƙwana biyar.
*** *** ***
Rayuwarsu ta England ta tsaya mishi a rai ya rubuta cikin ƙundin tarihin sa, haka na Germany su kansu mutan ƙasar sunyi sha'awar su, kasancewar yana da abokan hulɗar kasuwancinshi sai dai ya ce wannan karon ba kasuwanci ya zo ba, don haka ko England bai nemi abokanshi ba, da gaske Dady shi kam ya dage sai ya samu beby, don haka ko yaushe suna garin majidaɗi gashi Pretty ɗin tashi ta shagwaɓar dashi ta ririta shi. Wani lokacin ma in ya matsa mata da maganar samun beby sai tace kaine bakada beby,nikam ina dashi ta jawo shi zo ma inyi feeding ɗin ka. Duk sunyi ƙyau har sun gaji Ruƙayya ga wasu hips sun zauna fata ta goge tayi shar, wani ƙyau kuma da shegen ƙwarjini sai ka dubi Dady.
Don haka sabon kishin sa ne yake cin Pretty É—in tashi ko yaya taga matan turawan nan suna kallonshi tamkar zasu haÉ—iye. Haka nan shima bai cika son maza na kallonta ba.
Daga sati biyun da suka ce zasuyi sai da suka yi sati biyar dan ma Dad yanata waya, My Son ka dawo kan harkokin ka fa,ga kuma Zainab da duk sanda ya kirata ta dinga kuka kenan,wai ita ta gaji da rashin shi,da yaga shi yanada wata ita fa? Yasan tanada shegiyar jaraba ya ce bari ya tausaya mata su dawo. Sun yo tsaraba harda ta tsiya, shi dai Dady yawancin nashi duk kayan beby ne duk da baiga cikin ba yana sa ran samu tunda yasan lafiyar shi qalau,sai na Zainab da su Momy ta matsa mishi yayi musu tashi duk da ya bata iyayen kuÉ—i tayi ta ta.
A gajiye suka iso gida gurin ƙarfe biyu dan sun ƙwana a Legos sannan suka biyo jirgin Kaduna. Zainab ta taresu babu yabo ba fallasa,sun gaisa da Ruƙayya sai dai ta firgita da ƙyan da Ruƙayya tayi. Hatta muryarta ta ƙara zaƙi da sanyi ta ɗaure tasa Sunday ya shirya musu abinci duk tana yi ne bisa umarnin bokansu da ya ce kada ta tare su da tashin hankali ya ce cikin lalama zata shanmace su ta tarwatsa su ta hanyar saka musu sihirin cikin abinci ko abin sha wanda ake buƙatar su ci su biyun a lokaci ɗaya. Taso ta haɗa baki da Sunday sai dai tasan cewa Sunday ba zai taɓa yarda da buƙatar ta ba, amma ko a shegen Hollandian nasu zata zuba musu su sha suyi ta zabga faɗa kamar yanda Boka ya yi ma Hajiya bayani.
Ƙwanansu uku da dawowa suka nufi Kaduna sun cika dangi da tsaraba kowa sai tsiya ake ma Ruƙayya wai ko an samo ne ganin yanda tai ƙyau ƙwana ɗaya suka dawo.
A hanya ne Momy tayi ma Dady waya take tuhumar shi anya Pretty ɗin tashi batada ciki kuwa? Ya ce har yanzu indai ba ɓoye min take ba, bayan sun gama wayar yake ce mata Pretty me yasa kowa ya ganki sai ya yi min zancen ciki? Ko dai gaske ne?" Ta ce haba dai da baka sani ba? Allah bani da komai nima haka suke ta damuna, ya ce Allah ya amsa bakinsu, ta yi shiru tana murmushi.
Gidan Munira M Bash ma da taje, Munira ta ce Allah kinada shigar ciki dubi yanda ƙirjinki ya cika dam. Ruƙayya ta musa, M Bash ta ce yaushe ki kayi al'adar ki ta ƙarshe?.
Ruƙayya ta ce "aini tunda nayi aure,ko ince tunda na tare banyi al'ada ba,kin san tunda na samu sauƙin al'ada na dena ciwon cikin nan to sai inyi wata uku biyu banyi ba, Munira ta ce ƙila ma ya shige baki sani ba, ta ce a'a M Bash da naji canji a jikina haka Munira ta haƙura ba don ta yarda ba.
Zainab taso sa musu magani cikin abinci ko Hollandia amma Sunday ya bi ya kanainaye komai tare da sa ido kamar yasan me take son yi. Zaman gidan Dady babu yabo babu fallasa, shima kamar ya É—an soma jin daÉ—in zaman nasu tunda yanzun Zee ta É—an rage matsala kaÉ—an,satin su biyu da dawowa daga tafiya Zainab ta ce mishi zasu je garin su Hajiyanta.
Dady be musa ya ce sati nawa zakuyi? Ta ce ba zamu fi ƙwana uku ba, ya ce maimakon kuyi koda sati ɗaya, haushi ya kamata ta ce don ka gaji da ganina komin kora da hali? Ya ce a'a naga ƙwana uku yaushe aka gaisa da dangi? Ya cika ta da kuɗi ga waɗanda ta sata,har ƙofar ɗakin Ruƙayya taje tai mata sallama, Ruƙayya ko har ƙasa ta rakata inda direba zai ɗauke ta zuwa gidansu, tunda da Hajiyarta zasuyi tafiyar,ta shiga motar tana faɗin zaki ci mai garin garinku wannan tafiyar dan ke zanyi ta da bebyn naki,dama kun ishi mutane da beby beby, zan gyara muku zama a ranta take saƙa wannan abun,sun isa suka tadda Hajiyarta har ta shirya don haka ta sauka motar mijinta ta shiga gida, suka rankaya. Bala direban Hajiya shi ne ya jasu suka ɗauki hanyar Minna.
Zahiri ba garin su Hajiya zasu ba,gurin Boka kanfa suka nufa, domin ta kasa amfani da maganin.
*** *** ***
Bayan zuwan su Minna sun ɗauki hanyar Bidda. Suka yanke suka shiga cikin wani ƙursumin daji sun wuce ƙauyuka da yawa har duhun dare ya soma shigowa kafin suka zo wani bakin rafi Zainab ta dubi Hajiya ta ce "Hajiya ba dai ruwan nan zamu shiga ba?" Hajiya ta ce ga masu fito nan za mu bar motar mu hau ƙwale-ƙwale, tsoro ya kama Zainab ta ce na shiga uku! Gaskiya Hajiya mu haƙura mu koma yaushe zan shiga ruwa ban taɓa shiga ƙwale-ƙwale ba, Hajiya ta ce da Allah ni yi min shiru saboda uban wa zan shiga ruwan ba saboda ke ba,sai mun koma ki damu mutane.
Sun shiga ruwa Zainab ga tsoro ga faɗan Hajiya,har suka fita. Daga nan suka yanki wani daji a ƙafa,gurin duk ƙarafa ne irin dutsinan nan masu faɗi can suka hango bukkar Bokan,suna isa Bala ya ce Hajiya ina son yin sallah don na tabbata yanzun anyi isha'i. Ta ce sai ka koma can baya nan ba gurin sallah, ya saki baki yana dubanta nan kuwa ya juya ya ce zan jira ku gurin mota in ma ƙwana ne sai in ƙwana ciki, ta ce haka ya yi,ya juya yana tunanin halin Hajiya shi kam ya kusan barin aikin nan, ya tafi ga yunwa ga gajiya ga rashin sallah.
Su kam suna tsugunne gaban Boka bayan ya zunduma ashar sannan ya hau zagin Zainab kaga Æ´ar tsinanninya Æ´ar abun uba mu baki maganinmu ki ajiye? Ke sarkin tsoro to bama bawa mai tsoro magani, ya É—ago maganin ya nuna mata kinganshi nan mun saka aljani ya É—auko mana abun mu Æ´ar tselan uwa,sai kuma bada kuÉ—i sannan mu maida miki,mamaki ya cika Zainab da taga maganinta.
Hajiya ta ce godiya muke Boka a yanzun muna neman afuwa a gurinka ka bamu taimako,ya dubi Zainab da idanunsa jajaye bakinsa ɗoyi na fita duk sanda ya buɗe, ya ce in na baki bakiyi ba to zan barki da aljanu su bi min haƙƙina,ƙa'idar maganina sati ɗaya in ya wuce zanyi hukunci ya ce ya kika ce? Ta ce zanyi, ya ce kisa ko rashin lafiya kike son a ɗorawa ja'irin mijinki da matarsa?.
Ta ce nafi son na faɗan suyi ta zabga faɗa, ya ce kin samu gashi,ya miƙa mata maganinshi na farko daya bata ya ce kije kisa cikin abinci ko ruwan sha ki tabbatar sun sha tare lokacin zukatansu zasuyi zafi su dinga jin zafin juna, amma fa in kika bari ɗaya ya ci wanda ya cin shine zai zama mai zafin rai kuma asirin zai karye bada jimawa ba, sannan asirinki zai tonu, Hajiya ta ce Boka matsalar ta yaron gidan dake musu aiki yasa mata ido, ya yi dariya ya kai hannu kan wasu ƙoƙuna ya ciro wani ɗan ƙullin magani ya yi surkulle ya miƙa mata, riƙe wannan zaiyi maganin shegen yaron.
Zaki mallake shi yanda ko uwarshi ki ka ce ya kashe zai aikata bare sama wata magani, ta ce to ya zanyi Boka?
Ya ce "Kiyi tsirara sannan ki shafe jikinki gargaɗi kada ki yarda ya shafi gabanki,da kin yarda ya shafi gabanki sai dai kiyi haƙuri yaron zai amfana dake,Ta dubi Boka da sauri,ya cigaba sosai daga nan zai bi umarnin ki in kuma kika bari maganin ya taɓa gaban yaron zai liƙe miki kema haka.
Hajiya ta ce "to Boka tayi amfani dashi gurin mijinta mana maimakon ta mallake wani sai ta mallake mijinta." Ya ɗaga sauti da ƙarfi kul! Kul! Tayi amfani dashi gurin mai sallah, mijinta yana sallah aljanun mu zasu ƙone in mun turasu gurinshi ke kar ki fara uwarshi tana tsaye kanshi tana yawan yi mishi addu'a.
Zainab ta ce to Boka a canzan wani, ya ce ina ai sharaɗi magani shine dole ayi in an karɓa,in kuma anƙi aga ɓacin rai,ku tashi ƴan tselan uwa maganar kuɗin aiki sai magani ya ci zan fanshe a jikinki,kije da kuɗin ki dinga shan madara rana ɗaya zan zo in shanye peak zaki sha sau uku a rana zan zo miki insha jikinki da zaran kinyi amfani da maganina ya ci,ku ɓace min a nan bari jinnu su kai ku gurin motarku, kafin suyi magana sai jinsu su kai fuu anyi waje dasu sai tif a ƙasa kusa da mota, cikin tsoro Bala ya buɗe mota ya leƙo bai gane su ba saboda dare, ya soma addu'a, Hajiya ta ce Bala ya gane muryarta ya ce Hajiya kune? Suka ce Eh maza tada mota mu bar dajin nan haka suka kamo hanya sha biyu suka zo wani ƙauye, dole suka nemi gidan maigari don ƙwana.
Washegari suka ɗauko hanya a cikin Minna sukayi masauki cikin wani hotel don su ƙwana biyu tunda sunce ƙwana uku Bala ma sun kama mishi nashi ɗakin. Zainab dai ba'a cikin sukuni ta ƙosa a koma tayi gaggawar aikata aikin Boka gashi ya ce ta dinga shan madara zai zo yasha a jikinta abin ya yi mata yawa.
Tun safe suka ɗauko hanyar Abuja sha biyu suka shigo dan ma sun samu matsalar mota a hanya. Daidai lokacin Pretty da bebyn ta suna gida suna shagwaɓa juna, kullum da ƙyer yake tashi ofis. Yanzu da suka zube a falo tana sanye da gajeren wando na jeans sai riga ɗamamma sai gashin ta gefe ta kama da ribon shima kalar wandon, tayi ƙyau kanta yana jikinshi yana wasa da gashin kanta, ta ce beby yaushe zan koma aiki ne? Ya ce an kusa gama ofis ɗin ki na Kaduna? Kuma gashi ban son muyi nisa ace sai weekend zan ganki? Ta ce niko nafi son haka saboda nafi son in ganni daga ni sai kai,ya ƙara jawo ta jikinshi ina sonki da yawa Pretty har ban san kalar son da nike miki ba.
Ta ce nafi sonka fiye da yanda kake sona, ya ce ban yarda ba Pretty, ta ce me zan maka ka yarda? Ya ce tashi... sallamar Zainab ce ta dakatar dasu dan tuni take kallonsu amma basu san ta shigo ba. Dady ya ce "har kun dawo?" Ta ce Umm ta wuce É—akinta.
Ruƙayya ta tashi tana mata sannu da zuwa kyar ta amsa ta shige ɗaki.
Misalin sha ɗaya Ruƙayya tana ɗakinta bacci ga zazzaɓi wanda ya zamar mata ƙa'ida duk ranar Allah zuwa yamma sai ya sauka taƙi sanar da Dady ne dan tasan zai ce suje asibiti, ita ko bata son zuwa,tasan gajiya ce bata gama sakinta ba.
Zainab ta leƙa kicin taga Sunday yana ta aiki ta koma ɗaki ta haɗa asirin da aka bata,ta cire kaya ta maka a jikinta maimakon shafawa ya ko gangaro ya shiga gurin da ba'a so nan ta tuna da gudu ta shige toilet ta shiga yin tsarki sai dai kash ya riga ya shiga,ta fito da yaƙinin bazaiyi komai ba, tunda ta wanke wayar kicin ta kira Sunday ya ɗauka ya ce Yes Madam za'a kawo wani abu ne? Ta ce kawo min Hollandia mai sanyi ya ce Ok ya ɗauko yana mamakin me yasa yau Madam zata sha Hollandia ita da bata son shi.
Ya tura ƙofa ya shiga bai ganta ba don haka ya nufi madubin ta dan ya aje mata. Ya juyo zai fito suka yi karo, tsoro ya kama shi a yanayin da ya ganta,da sauri ya juya tare da rufe idon shi bakinshi yana rawa ya ce sorry Madam.......katse shi tayi ta hanyar ɗora hannuwanta a kafaɗunshi, fargaba ya cika shi jikinshi yana ta ɓari tsam ta rungume shi tuni shirinta ya soma ratsa shi ya fara miƙa mazantakarshi ta tashi dama ya soma maida martanin abin da take mishi sun lula cikin shagala da ta ɗauke su tsawon awa biyar.
Bayan dawowa haiyacin su sai tsoro ya kama Sunday ya yin da Zainab ta soma kukan ƙarya tana faɗin daga tana mishi wasa shine zai yi mata haka? To zata sanar da Oga nan ya zube yana bata haƙuri yana kuka,ta ce saka kayan ka duk abinda na ce kayi zakayi? Ya ce zaiyi ko menene ta ciro garin magani ta ce wannan cikin Hollandia zaka saka ka tabbatar Oganka da wancan shegiyar matan sun ci, ya ce to ya saka shi a aljihu.
Ya ko saka kuma yanata gadin shi don kada wani cikin su yasha shi kaɗai sai da dare sannan suka zauna dinner Ruƙayya tasha gayu cikin super fara, yayin da Zainab aka sa farin les,ta saki fuska har su Ruƙayya suna mamaki a zukatan su.
Sunday ya yi ta jera abinci a gabansu Zainab ce da maigidan don haka ta soma zuba mishi.
Sun fara cin abinci kafin daga baya ya jawo Hollandia ya yi sanyi yanda Dady yake buƙata don haka Zainab ta zuba mishi ya soma ɗaɗɗaka ya ce Pretty ga mai sanyi fa, ta ce kasan duk yanda nake son Hollandia ƴan ƙwanakin nan ko ƙamshin ta bana son ji, ya ce kin sha da yawa ne ya hau miki kai ko? Ta ce ƙila haka ne, ya ce ni kam koda zan sha goma a rana ba zai ginsheni ba.
Cikin Zainab ya kaɗa kar dai matar nan taƙi sha ta ƙaƙaro murmushi Ruƙayya ke yau bazaki sha bane? Dubi yanda raɓa ke zuba jikin kofin da My dear yasha Ruƙayya ta duba sannan ta ce yau dai banjin sha. Tamkar Zainab ta fasa ihu don haushi, ta rasa me ke mata daɗi ji take kamar tai ma Ruƙayya ɗura,har ma Ruƙayya tasha jinin jikinta shi ko gogan yama daina cin abincin sai faman banƙarar Hollandia yake yi jinshi yake tamkar yana yawo ne a sama dan daɗi. Ruƙayya ta fara tashi tai musu saida safe kafin Zainab ma ta tashi ta nufi ɗakin ta ta kira Hajiyarta ta shaida mata Ruƙayya fa bata sha ba, faɗa Hajiya ta soma tare da zagin Zainab ɗin.
*** *** ***
Bacci mai nauyi ya ɗauki Dady bisa gadonshi ko addu'a baiyi ba daƙyar ma yayi wanka wata sabuwa Zainab tana fitowa dan zuwa ɗakin maigidan sai taga Sunday tsaye a falo,suna haɗa ido saita birkice ta kirashi ɗakinta shima abin da ya hana shi bacci kenan, suka lula cikin masha'a tsawon lokaci mai yawa sannan suka tashi cikin firgici,ya ƙwashi kayanshi ya yi waje yayin ta kama kuka menene haka daga sau ɗaya.
Kiran sallah ya farkar da Dady bayan yayi sallah ya rasa me ya hana Zainab zuwa É—akinsa? Ya san dai ko faÉ—a sukayi zata zo bare ba faÉ—a, Pretty ce gimbiya bata zuwa É—akinshi sai dai shi ya bita.
Yana wanka zuciyarshi zugi take yi tana zafi ya fito ya shirya kan dinnig babu komai sannan mata biyun babu ko ɗaya takaici ya kama shi ya ce Zainab! Ke Zainab, kai Sunday" a firgice suka fito a zatonsu asirin su ya tonu kowa yana ƙyarma ya fito, yanda jikinsu ke rawa sai suka bashi mamaki, ya ce har yanzu babu komai na break fast harna shirya zan fita,kema mara amfani bazaki matsa mishi ya shirya ba? Ya shiga faɗan rashin dalili, suka yi ajiyar zuciya ta soma cewa, My dear kayi hakuri bari inje in duba da kaina tsaki ya yi ya nufi waje.
Wasa-wasa Dady ya canza ya zama masifaffe Ruƙayya ma tsoron shi take,tun daga ranar da yayi ma Zainab duka akan wai ta fita bata sanar dashi ba, bayan yasan tana fitar bai ɗauki mataki ba sai yanzu, yau ita keda Dady ta saba shi ke zuwa ɗakinta don haka koda aka gama cin abinci sai tayi ɗaki gurin cin abincin ma a ɗari-ɗari akeyin shi sai faman harare-harare yake yana jiran ganin mistake Allah dai yasa aka gama qalau. Ruƙayya na tashi shima ya tashi ya yi ɗakinshi. Zainab tayi kitchen gurin Sunday ta ce ya fa shigo tana jiranshi ya ce to.
A ran Dady faɗi yake yau zaiyi maganin Pretty wato ita tana taƙama yana sonta shi ne haƙƙinshi ma sai ya bi ita tafi ƙarfin zuwa ɗakinshi to yau kam bazai je ba,har gurin biyu taji shiru kamar ta share sai kuma da ta ce bari taje tunda yanzun ya zama a lallaɓa. Sai dai tana fitowa Sunday ta gani zai shiga ɗakin Zainab daga shi sai gajeren wando,bai ganta ba don haka ya shige.
Kamar ta tsaya sai kuma ta wuce. A rigingine ta same shi fuskarshi tana kallon silin ta zauna gefen gadon bayan ta rufe ƙofar ya tashi yana hararar ta ya ce waton Ni Ban isa ba ko? Ta ce me ya faru ne? Ya soma ɗaga murya ƴar rainin wayo dole ki ce min me ya faru? Tunda ni kinga ina son ki sai ki ka maidani sakarai sai dai in ina buƙatar ki ni na biki ɗakinki ko? Ta ce to yi haƙuri bebyna sam faɗa baya yi maka ƙyau ta ƙarasa magana tana tura bakinta cikin nashi. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya shiga neman lada. Irin Haka Pretty take yi tana lallaɓa shi in abin yazo kanta,ga ciwon da ko'ina na jikinta yake mata zazzaɓin rana duk ta faɗa tamkar ba ita ba.
Shi da kanshi ya tsare ta wai sai ta faɗi mishi dalilin ramarta, ta ce ko faɗan ka Dady shi kaɗai zai ramar dani tunda da ba haka kake ba, ya ce tunda ga kare ba dole ki ce min mafaɗaci ba,kina taƙama ina sonki shiyasa kowacce magana tazo bakin ki sai ki yaɓa min,ta soma hawaye tana faɗin To kayi haƙuri shikenan, ya ce ai dole kiyi kuka tunda Allah ya hore miki idon kuka da bada haƙuri,tama rasa me zata ce ya dinga shiga yana fita sannan ya yi tsaki ya wuce.
Shiru tayi tana tunanin irin wannan hali da Dady ya canza, inda ma abin ya ɗan mata sauƙi ba ita ɗaya yake mawa ba.
Wani sabon lamarin kuma duk sanda Dady ya nemi Zainab dan zuwa garin majidaɗi sai ya zama ba namiji ba,ya kasa aiwatar da komai sai dai ya haƙura bugu da ƙari kullum da dare sai taga Bokan nan cikin mafarkin ta yazo yana amfana da ita ga wani ɗoyi da yake yi ban da liƙewa juna da suke yi ita da Sunday da rana da dare in ba ita keda miji ba.
Abun ya soma damun Dady ya tsare Zainab yana tambayarta me yasa baya amfani a gurinta amma gurin Ruƙayya lafiyarshi qalau? Ta ce itama bata sani ba wai amma da Hajiya ta nemo magani wai ance Ruƙayya ce tayi mata asiri ya yi shiru yana son yayi nazari amma ya kasa natsuwa zuciyarshi tana ta faman tafarfasa tana shaida mishi gaske ne, in ba haka ba yaya za'a ce gurinta kaɗai yake namiji gurin kishiyarta shima mace ne? Wato duk son da yake nuna ma Pretty bata gani ko? Ya tashi fuu ya fita.
Tana ƙwance tayo amai ta gaji ga zazzaɓi, Dady ya shigo a fusace ta ɗago tana dubanshi, tsoro ne ya kamata ganin bata taɓa ganinshi cikin irin wannan fushin ba duk da cewa yana saurin fushi ƙwanan nan amma na yau dabanne. Tsura mata ido ya yi sannan ya girgiza kai,kin bani mamaki Ruƙayya, da sauri ta dube shi tana zaton tun ranar farko da suka haɗu ta ce mishi sunanta Ruƙayya ya maimaita faɗin sunan bai ƙara kiran Ruƙayya ba sai dai Pretty don haka sai taji wani sabon tsoro ya shige ta,ta zuba mishi ido ya ce ashe haka halinki yake? Ashe wa'azin ƙarya kike min ke munafuka ce? Cikin rawar murya ta ce me nayi Dady? Ya ce da Allah ni rufe min baki,wai duk son da nike nuna miki,be ishe ki ba sai kin shiga bokaye da malamai shi ne kika je kika yi ma Zainab asiri kada inyi sunnah da ita sai dai ke ko?
Ta zaro idanu tare da faɗin "haba Dady wannan sharrin daga ina?" Ya ko ɗaga hannu ya wanke ta da mari ji kake tau, ta firgice ta riƙe gurin,Ni ka duka bada haƙƙina ba Dady? Ya ce na mare ki in kika ƙara magana kuma sai na zane ki.. kuka ta cigaba da yi,shi ko faɗi yake shawara ɗaya zan baki kiyi gaggawar zuwa gurin da aka yi sihirin a karya shi tun kafin in yanke hukuncin daya dace a kanki shikenan don Allah ya jarabce ni da sonki, shikenan sai ki maidani ɗan iska, yasa kai ya fita.
Taci kuka har ta gode Allah jikinta ya É—au zafi kafin wayewar gari ta galabaita amma duk da haka ta yanke shawarar tafiya Kaduna. Ta haÉ—a kayan da zata iya É—auka ko wanka batayi ba,ta zura silifas tana fitowa direba ya taso Madam ina zaki je ne? Ta ce a'a ba nisa zanyi ba, ta fita tayi tafiya mai nisa sannan ta samu mota shata ta É—auke ta suka tafi, tasha ta kaita ta shiga motar Kaduna.
Kamar taje gidansu amma sai ta tuna yasan zata ci ƙaniyarta gurin Affansu don haka sai ta wuce gidan su sashen su Momy ta shiga Momy ɗin bata nan ta zube kayan tayi ƙwanciyarta.
Momy ta shigo da jaka ta soma cin karo ta dubi gadonta, Ruƙayya ta gani ƙudundune tana rawar sanyi da sauri ta nufi gadon, Ruƙayya lafiya? Ta buɗe ta a wuyanta tasa hannu zafi taji mai tsanani, ta ce innalillahi keda wa kika zo? Duk ta ruɗe cikin ruɗu ta ɗauki waya ta kira likitansu.
Ya ce gashi nan zuwa ta koma gurin Ruƙayya ta ce keda Dady ɗin ku ka zo? Hannu ta girgiza alamun a'a ita kaɗai ta zo. Abin ya ɗaure kan Momy ta ce yasan baki da lafiya ya barki kika taho? Likitan ne ya yi ma Momy waya cewa ya iso........
🖊ï¸ðŸ–Šï¸ðŸ–Šï¸
[9/1, 13:10] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*