Complete Hausa Novels

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 9

Page 7

Saboda yanayin zuwan da Dady ya yi mata. lokaci mai tsawo Dady yana babban birnin majidaÉ—i kafin ya rungume Pretty É—in shi tsam.

Farin ciki da wani shegen sonta ne suke ƙara ratsa shi, tsawon minti goma ya buɗe ido ya dubi fuskarta idonta yana rufe sai dai zufa da hawaye sun ma fuskar kaca-kaca ya tashi zaune ya jawo kanta ya ɗora kan cinyarshi da zanin gado yake share mata fuska yana faɗin "sannu Pretty kin ji Allah ya shi miki albarka lallai ke wata abin alfahari na ce sannu ƴar halak bari nayi wanka kema sai kiyi ko?" Ya gyara mata ƙwanciya ya shiga toilet.

Farin ciki ran Ruƙayya kar ki tona, domin ta zama cikin matan da mazajensu suke alfahari da su ta tattala budurcinta yayin ƴan matancinta, ta kawo shi inda ya dace,bata damu da ciwon da jikinta yake yi ba ga sanyi yana ratsa ta,tasa hannu ta janyo bargo ta rufa,san da ya fito jikinta ya ɗime da zazzaɓi ya ɗan ja bargon tashi kiyi wanka,ta kuma ƙudundunewa haƙoranta suka soma haɗuwa da ƴan uwansu, sanyi ta faɗa cikin ƙerma ya hau gadon shima ya shiga bargon jikinta har rawa yake yi, "innalillahi." Ya dubi agogo ƙarfe uku gashi basu da ko farasitimol wayar Momy ya kira duk ya ruɗe, tana jin ya ce Momy, ta yunƙura don Allah Dady kar ka tashe ta ka rufa mana asiri,bai jira jin zancen ta ba ya sake faɗin Momy, Momy ta ce lafiya cikin daren nan? Ya ce Pretty ba lafiya kuna da farasitimol inzo in amsa? Da safe sai muje asibiti, ta ce ka tsaya a gurin ta bari na zo, ya ce to,ya ɗauko mata rigar bacci mai ɗan kauri ya ce bari in saka miki ga Momy nan zuwa. Da sauri ta tashi zaune ta saka rigar a jikinta, ya je ya buɗe Momy ta shigo da magani Ruƙayya ta kasa kallonta, Momy ta ce kawo mata ruwa tasha maganin, tana sha ta ƙwanta. Can bacci ya ɗauke ta Momy tayi musu sai da safe ta tafi, jikinta ya shige ya ƙwanta ya ɗora kanta saman ƙirjinshi tayi ajiyar zuciya ta cigaba da bacci.

Shi kam yana jin ajiyar numfashinta sonta yana ƙara shigar shi so tsansta mai cike da yarda mai tsafta.

Bai san yayi kuskure ba sai da safe da ta kasa tashi tayi wanka, suna cikin ƴar dabarar yanda zata miƙe sai suka ji sallamar Momy ba kunya ya ce Yauwa Momy taimaka mata, kunya ta kama Ruƙayya ba shiri ta miƙe ta fara takawa cikin dauriya ta shige toilet Momy ba yarinya ba ce ta fahimci komai musamman da taje bakin gadon ta kakkaɓe musu shinfida ta ce in tasha koda tea ne sai ta ƙwanta. Alamar da ta gani kan shinfiɗar ya tabbatar mata ɗan ta ya yi sa'a don haka tace ya kawo sabon zanin gado ta matsa kusa da toilet ta ce ƴata ki shiga ruwan zafi sosai kisa dettol kin ji." A ranta ta ce shikenan mai aukuwa ta auku.

*** *** ***

Ƙwana uku Dady da Momynshi suna tattalin Pretty ɗin tashi, tun tana kunya har ta daina. A gabanta Momy tai mishi faɗa cewa ka gwada mata ƙarfi ne Dady? Shiru ya yi yana shafa kanshi. Ta fito wanka ta zauna gaban madubi tana ƙwalliya tayi ƙyau ita kanta tasan tana amarci,gashin ta sai ƙyalli yake gashi tasa material mai fulawoyi ruwan madara,ta taje kanta gashin ya sauka har kafaɗunta ta soma fesa tararuka Dady ya shigo yana shaƙar ƙamshin turarenta,bayanta ya tsaya tana ƙoƙarin ɗaura ɗan ƙwali ya amsa ya aje.

"Nafi son ganinki haka My Pretty" ya duka ya saka fuskarshi a gefen wuyanta duk suna kallon madubi ya ce kinada ƙyau Prettyna, ta ce na kai kane? Ya ce kenan muna kama, yaushe ne zaki bani Baby shekaru na sun soma shurawa ina son yara." Kunya ta ji ta runtse ido ta ce ko yau ne Allah ya kawo zan baka, ya ce ƴan biyu nake so,ta ce to ka gayawa Allah.

*** *** ***

Wata rayuwa Dady ya nuna wa Pretty ɗin shi a wannan ƴan ƙwanakin nan mai matuƙar daɗi, itama yanzu tasan babban birnin majidaɗi, yanzun haka da take ƙwance saman kujera rungume da filon kujerar layin M Bash take kira dan neman ƙarin bayani akan wasu turaruka cikin kayan gyaran jikin da Mom ta kawo mata.

Bayan ta ɗauka Ruƙayya ta hau mata tsiya da cewa "haba M Bash kamar kun kawo gawa rami keda Armaya'u babu ko waya, Munira ta ce gara mu barku ku ci amarci babu takura." Ta ce muna ci kam lallai garin daɗi yana gidan aure amma sai ansha wuya ake shan daɗi, M Bash ta ce shegiya Ruƙy kinji maji daɗi ne ina fushin da ake yi da angon? Ta ce da kenan aiko da ɗin ma ina son kayana rashin fahimta ne yanzu kuma mun fahimci juna duk wata mata tana bayana, ko bai faɗa ba haka ne. Don haka bata gabana yanzu ma ina gaban turarukan da Mom ta bani ina son kiyi min bayanin su. Turare in zaki ƙwanta ki shafa kaɗan,garin maganin kisa zuma zaki ganta cikin ƴar leda sai kisa ruwa, kaɗan zakiyi amfani dashi zaki sha mamaki. Suna sallama Dady ya shigo ta yarda wayar saman kujera ta miƙe suka maƙale juna ya ce "ina son ki Pretty." Ta ce "I love You My Yusuf ina sonka." Tamkar ya haɗiyeta yaja hannunta suka fita gaban wata ƴar mitsilar mota fara tas ya tsayar da ita sannan yaja hannunta ya saka mata key sannan ya raɗa mata ƙyautar budurcinki nagode,rungume shi tayi.

Momy tana hangen su daga saman bene ranta ƙal farin ciki, ta ce ka nuna ma Momy ma." Ya ce ita ce ta zaɓar miki zan dinga koya miki duk Sunday,Ni kuma menene tukwicina?" Ta ɗan sake shi tayi taku biyu zuwa uku ta juyo ta ƙyafta mishi ido ɗaya tace to night, ya biyo ta yajata jikinshi me zaki bani? Ta ce zan kaika babban birnin majidaɗi zaka sha mamaki.

Ya kam sha mamakin har yaso ya zauce shiyasa ya ce ya fasa barin ta Kaduna kamar yanda da farko ta buƙata. Ya ce ai tana da ɗaki a Abuja Momy tasa baki da cewa kibi mijinki ƴata kar ki damu da kishiya,ke dai ki zama mai biyayya da ƙyautatawa shi ya ɗibi kayan ta aƙwati biyu haka kit ɗin ta da abubuwan ƙamshi na kimtsa jiki, basu samu Zainab ɗin a gida ba ɗakinta ya buɗe mata ta shiga ya taimaka mata gurin gyara ɗakin duk da cewa a gyare yake.

Suka shirya kayanta cikin dirowa, Sunday ya gabatar musu da abinci a dining table sun sha Hollandia kafin suka shige toilet,ƙiri-ƙiri Ruƙayya ta hana Dady ya sanar da kowa cewa yana cikin Abuja duk da ɗinbin jama'ar dake son ganinshi ba cewa tayi kada ya kira su ba a'a idan tana gabanshi ya kan mance kowa da komai sai Pretty.

Zainab sai bayan isha'i ta dawo suna ƙwance kan doguwar kujera duka su biyu, suna kallo tare da ƴan wasanni da suka saba ma juna turus ta tsaya tana dubansu. Kishi da fargaban rashin samunta da Dady baiyi a gida ba ta ɗaure ta ce "Sannunku." Dady ya dubeta rai a ɓace amma sai ya share don kada ya yi mata cin fuska gaban kishiya ya ce "yauwa Zee,ina kika je?" Ta ce naje na dubo Hajiya ta bataji daɗi ba, ya ce Allah ya sauwaƙe ya dubi Pretty ɗin shi da kishi ya hanata ko motsi ya ce Pretty ga Zee ta dawo ta daure ta yunƙura ta tashi zaune suka dubi juna cikin ido,gaban Zainab ya yi mummunan faɗuwa ganin Ruƙayya ta ce, Ruky dama kece kishiyata? Ruƙayya ta ce oh baki sani ba ko? Wallahi ni ce ya ƙwana biyu? Zainab ta haɗiye miyau da ƙyer ta ce lafiya lau ta nufi ɗakin ta lallai sai ta dage kafin ta ƙwace Dady,nan taji tsanar Ruƙayya ta shige ta.

Ruƙayya ta fito daga wanka ta gama shirin ƙwanciya. Yau kam tasan sai dai ta rungumi filonta,tana shirin kulle ƙofa Dady ya shigo ta ce na zata ka ƙwanta? Ya ce a ina? Ta ce ɗakin matarka mana, ya ce a'a,ta tsaya ban gane a'a ba ai can zaka ƙwana ko ka manta ne? Ya yi shiru tazo ta shige jikinshi ka je can haƙƙinta ne ƙwananta ne gobe sai ka raba mana ƙwana in ɗai ɗai ko biyu bazan taɓa so ka zama mara adalci ba don ina son ka zama Yusuf ɗina har cikin aljanna." Ya zuba mata ido in sumbace ki? Ta ce kaɗan kar ka zarme.

Sai da ta ƙwace kanta ta tura shi ta rufe ƙofa kan gado ta faɗa ta rungume filo wasu ƙananan ƙwalla suka zubo mata Dadynta yana tare da kishiyarta.

Da safe ta fito wanka ta zauna gaban madubi in kinga yanda take tsara ƙwalliya sai kiyi tsammanin shi ta karanta a makaranta. Ta gama aka taje gashi wata shegiyar shadda tasa,tasha ado ta zuba ɗauri tamkar zata je liyafa dama gashi har Yanzun lallen amarcinta na nan wata shahararriyar mai dayis tayi mata,wato Sadiya layin ƴan kifi Allah ya yi mata baiwar zana shi tamkar daga India ta koyo,in tayi maka ya yi wata bai goge ba, amarya sak kalolin turaruka ta fesa sai ƙamshi yake tashi.

Dady ya turo ƙofa a hankali ya shigo kayan bacci ne a jikinshi wani abu taji ya tukare ta a ƙirji amma sai ta danne ta rage tsawo, ina ƙwana? Ya shafi fuskarta lafiya Prettyna kin tashi lafiya? Ta ce lafiya, ya ce zo muje dining room,ta ce baka zuwa ofis ne yau? Ya ce zanje, ta ce bakayi wanka ba, ya ce zanyi muje kiyi break ta ce a'a sai kayi wanka yaso ya shiga toilet ɗin ta tace a'a sai dai yaje can inda ya ƙwana.

Ɗakinshi ya nufa sai da ya shirya sannan ya shigo ta fesa masa turarenta sannan ta ce ba haka ake yi ba,kaje ɗakin matarka sannan ka turo ta kirani ya ce ai kema matata ce kije ki kira ta, ta ce sai ranar da ka ƙwana ɗakina,kana namiji Dady sai na koya maka yanda zaka zauna damu, ya fita sai lokacin ya tashe ta daga bacci tun bayan da ta bar ɗakinshi da asubahi. Brush kawai tayi sannan ta fito ya ce je ki kira mana Pretty muyi break.

Ta ƙwanƙwasa ƙofar, Ruƙayya ta leƙo,kizo inji My dear tana wani yanga ita a dole ta ƙwana da miji dariya ma ta ba Ruƙayya, Sai dai ita kam taji zafi da kishin wannan gayun da Ruƙayya tayi gurin cin abinci tana rawar kan haɗa mishi gara a gabanshi shi kam hankalin nan nashi yana gurin Pretty sai taka mata ƙafa yake yi. Bayan sun gama ya yi musu nasihar zaman lafiya, sannan ya fita.

Ita dai Ruƙayya tun da ta shige ɗakinta ta ɗauki waya taga Dady ya lodo mata kuɗi har dubu biyar, shi ta soma kira tai mishi godiya, sannan ta cigaba da kiran ƴan'uwa da abokan arziƙi. Can da rana Dady ya kira ta ya tambayar taci abinci ko? Ta ce shifa? Ya ce Sunday ya kawo mishi amma bai fara ci ba." Ta ce "kaci yanzu zan je naci." Ita kuma taƙi fita ne saboda tana jin Zainab da ƙawayenta ne ko ƴan'uwanta ne Oho sun cika falon.

Biyar dai dai Dady ya shigo lokacin Pretty É—in tashi ta ci gayu cikin material ja, Zainab a saye da riga da wando ita a dole Æ´ar boko, aka je aka rungumo miji,gaban Pretty ya tsaya ta ce sannu da zuwa Babyna ya ce yauwa My Pretty, Zainab ta ja shi zo muje kayi wanka My dear, ya ce Prettyna bari in fito kin ji? Ta danne sannan ta ce sai na ganka.

Ɗaki ta koma ta shiga nazari lallai zama da kishiya sai ka dage, amma zata nuna mata ita za'a ma salo? kissa Zainab ta shiga nunawa yana shiga wanka itama ta shige wai zatayi mishi,tasan yanda take hillatar maza cikin sauƙi ta shawo kansa take ta fita dan cusawa Ruƙayya haushi. Amma kash bata nan ta koma ɗaki, jallabiya Dady ya saka shima cikin saurin yaje gurin Pretty ya zauna dining table yana faɗin har ta tashi Zainab dake tsaye cikin haushin yanda yake ta zumuɗin fitowar kishiyarta, sai ta ce bari na kirata,bata jiraba ta nufi ɗakin Ruƙayya daga ita sai zani ɗaurin ƙirji da ƙaramin tawul a kanta ta ƙwanƙwasa ƙofa sau biyu Ruƙayya ta buɗe Zainab ta cire tawul ɗin kanta tana faman tsane ɗan diddigar gashinta ita dole tayu wankan tsarki, Ruƙayya kizo inji My dear,nasan kin gaji da jiran shi yana can yana neman lada tana magana tana karairaya.

Haƙiƙa saƙonta ya isa ga Ruƙayya sai dai abinka ga lauya sai ta ce to muje. Cikin murmushi ta dafa Zainab ɗin ta cigaba da faɗin kin san duk inda Babyna zai je ya samo lada zan fiso ai naga saurin shi don Allah Zainab ki rinƙa bashi haƙƙinshi yanda ya dace banda sauri." Ta yi gaba zo muje mana.

Haushi ya kama Zainab bata so haka ba,kai wannan ƴar bariki ce sai ta ƙara ƙaimi maimakon taje gunsu sai ta tafi ɗaki ita ko Ruƙayya firij ta nufa ta ɗauko Hollandia mai sanyi ta cika kofi ta miƙa mishi tare da faɗin sha Babyna. Itama kanta tana mamakin yanda tasa mishi suna,kai kishiya tana sa mutum ya yi abin da bai shirya ba. Gayu Zainab tayi ta zauna tana karairaya, amma duk hankalinshi yana kan Pretty ɗin shi yakan manta kowa bare wata Zainab hakan yana ɗaga hankalin Zainab matuƙa. Ya yin da Ruƙayya taga fushi bazai mata ba gara ta zage ta ƙara kanainaye Dadynta hakanne ma yasa ta dage sai da ya kaita gidan aminiyarta Munira M Bash, ta yini sun je gidan Mom inda suka samo tsarabobi masu ƙyau Munira ta cusa mata ra'ayin saka ƙananun kaya ta ce da sune ta ƙara riƙe wuyan Mustapha. Basu bar gidan sai da suka je kasuwa ta ƙwaso wanduna zuwa siket da shegun riguna na ƴan gayun zamani suna shigowa Dady na zuwa,ya ɗauki matarshi sai gida.

A ƙwanakin girkinta Dady ya shiga ruɗu tare da ƙara sonta ya nane mata koda rana sai ya baro komai ya dawo ganinta bata sani ba ya soma shirya musu yawon shaƙatawa duk da ɗinbin aikin dake gabanshi, sai ana gobe tafiya sannan ya ce ta shirya su je Kaduna. Zainab ta soma masifa ya za'ayi ranar girkinta suje Kaduna, ya ce sallama zamu je yau zamu dawo, ta tsaya sororo ina kuma zaku? Ya ce wasu kaya zanje dubawa a England ina da mata biyu ba zanje na zauna gwauro ba ta ce to ai sai kaje dani tunda nice uwargida, ya ce sai wani lokacin yanzun da Pretty zamu je wasu abubuwan suna buƙatar sai da lauya, kuma kin san ita lauya ce sannan......." Ta ce kai dai kace kawai an mallake ka da,da ita kake zuwa? Ya ce to haka ɗin ne.

Umma ta ji daɗin ganin ƴar Autarta yanda tayi ƙyau gwanin sha'awa shima Affa haka yaji daɗi ganin ta ƙwantar da hankalinta yasan suna zaman lafiya daga gani. Momy ma tayi farin ciki ganin cikin ƴan ƙwanakin nan Dady ya yi ƙyau ga ƙwanciyar hankali, lallai Ruƙayya tana kula da shi kuma rai a bashi abin da yake so, duk kan kafet suka zauna tana bakin gado sha'awa suke bata, wani son Ruƙayya take ji a ranta. Ruƙayya ta ce Momy ina wuni? Ta amsa da lafiya lau ƴata,ya ya baƙon guri da abokiyar zaman taki? Ta ce lafiya lau tama ce agaishe ku," Dady ya dubeta da yaushe ta ce a gaida Momy? Harara Ruƙayya tayi mishi, cikin murmushi ta ce ina ruwanka? Momy ta ce ato sanda zata ce kana ina? Ya yi dariya shikenan.

Dad ma ya shigo sun gaisa shi kam ya kasa barma ranshi sai da yace ƴata wane abinci ki ke ba My Son? Naga ya ƙara zama gentleman ga ƙoshin lafiya yana yawo a jikinshi." Kunya ce ta kama Ruƙayya ta durƙusa tana gaishe shi ya ce ai mun gaisa, Dady ya ce tana kula da ni Dad fiye da yanda kake zato ya shafi gefen fuskarta ashe har yanzu tana sona da,ta ce bata sona Momy ta ce bana gaya maka ba dama kaƙi yarda. Ruƙayya ta ɓoye fuskarta cikin cinyar ta. Momy ta ce to maza ku ɗau hanya kada dare ya yi muku a hanya.

Ya bi Dad samanshi dan su É—an zanta harkar kasuwanci. Ya yin da Momy take tambayar ta badai wata matsala tsakanin ta da Zainab? ta ce babu komai.

Sun ɗau hanya Sabi'u direba ke jansu suna baya suna soyewa kanta ƙwance bisa jikinshi tana ta mishi shagwaɓa ita dai yaje da Zainab domin ta ce ita ya kamata ya soma fita da ita ya ce "Haba Pretty in banda ke ban ga matar da zata samu wannan damar ba, sannan ta ce bata so." Ta tashi zaune sannan tasa hannu ta ƙara jan labulen daya shiga tsakaninsu da mai tuƙinsu wato Sabi'u, ta sanyaya murya ta ce "Ni fa nafi son komai kayi adalci saboda mu gudu tare mu tsira tare." Ya ja leɓenta ya ce da ba dake nace zanje ba da yanzun ana nan ana zunɓura min baki.

To dukkan ku Matana ne da wacce naga dama da ita zanje." Ta ce Allah ko zan ji haushi daga baya zan gane kayi adalci ne, ya ce to duk naji bayan na gama mana komai shikenan sai na fasa ko mekike nufi?"

Tayi fari da idanuwanta ina nufin a cikin biyu ayi ɗaya ko dai ka tafi da ita ko kuma ayi ƙuri'a, ya ce kamar ya ya? Ta ce zaka samu paper ka rubuta zaman gida ɗayar ka rubuta tafiya ka bamu ita zata soma ɗauka kafin ni, duk wacce ta ɗauki zaman gida shikenan a tafi da ƴar'uwarta, hankalina zaifi ƙwanciya, ya ce Ni dai kin tadamin nawa" ta shiga shafa gefen fuskarshi in Allah yasa dani zaka ba makawa ka riƙe wannan.

Zainab kam da suka tafi Hajiyarta ta kirata tana faɗa mata abubuwan da suke faruwa ita kanta Hajiyar ta damu. Cikin masifa ta ce ke wato bakisan yanda zaki ƙwaci kanki ba? To kada ki sake ki yarda idan yazo ki hau masifa kice ke baki yarda ba sai dai ya barku ku duka,in kuma dole ne zuwan yaje daku ku duka,kin ji ko? Tunda yaƙi ki haɗa da masifa da kissa shi kanshi asirin ba daina shi zamuyi ba, canza wani malamin zamu yi. Ta ce to Hajiya.

*** *** ***

Jibgegiyar motar dake ɗauke dasu tayi parking a gurin daya dace cikin harabar gidan suka fito, Sabi'u ya yi gaba da motar ya kaita mazauninsu ita da taƙwarorinta,su kam ciki suka yi da sallama suka shiga falo.

Tana zaune amma bata amsa ba sanye take da atamfa super baƙa da jajayen falawoyi ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana girgizata. Tana cika tana batsewa.

Ruƙayya ta dubeta "sannu da gida Zainab su Momy sun ce a gaisheki." Buɗar bakin ta sai tace "yauwa sannu da yawon cin amana,aini ban taɓa fita dashi ranar girkin ki ba." Ruƙayya ta ce "To kiyi haƙuri in girkina yazo kema ku tafi ko ina ne, ta wuce ɗaki cikin takaici.

Dady ya dubi Zainab "ke wai bakida tunani ne kina nufin banida ikon yin yanda nike so da gidana, saboda kada ranki ya ɓaci? Ki maida hankalinki." Ya faɗa yana tafiya, ta ce Allah zai saka min, ya juyo yana dubanta ta nufi ɗakin ta, kalmar Allah zai saka mata ta zauna mishi a cikin rai ko dai gaske ne ya zalunce ta? Ya tuna ɗazunnan Ruƙayya ta dage tana mishi mita wai bai dace yaje da ita ba shi dama tafiyar nan fa ya ƙirƙireta ne don kanshi da kuma Pretty baiga amfanin tafiyar ba in har baije da ita ba. Wanka ya yi sannan yayi alwala kasancewar masallacin da tazara shiyasa sai yayi isha'i, bayan isha'in ne ya tara su dan yi musu ƙuri'a Zainab ya fara ba ta ɗauka sannan Pretty.

Hannu yana rawa Zainab ta buɗe cikin ikon Allah zaman gida ta samu nan ta soma hawaye kan cewa wannan wani munafunci ne aka haɗa don a ɓadda tunaninta, Ruƙayya ta ce Babyna na yarda ku tafi, ya ce ki min shiru ban yarda ba, ta tashi taje ta ɗauko biro da takarda tazo nan ta rubuta da taje har shaida tayi ma ɗayar sannan da tazo ta rubuta tafiya a mai shaidar ɗayar kuma ta rubuta zaman gida,ta ƙudundune ta zuba a ƙasa ya ce ta soma ɗauka,nan Allah ya nuna mata nashi ikon ta rasa mai shaidar ta ɗauki ɗaya sannan Ruƙayya ta ɗauki nata, Zainab ta katseshi da faɗin tab wallahi ban yarda ba.

A fusace Dady ya ce nima banason ki yarda ki ɗauki mataki kin ji ko? Ya miƙe yana faɗin banza mara hankalin kiyi abin da kanki son ranki a biye miki yanzu kice baki yarda ba, to kada ki yarda ɗin wawiya." Ya nufi gurin cin abinci.

Ranar dai ƙwana suka yi rigima har ta kaiga ya shashsheƙa mata mari, tare da buɗe ƙofarshi ya ce taje ɗakinta cikin daren bata bari gari ya waye ba ta kira Hajiyarta tana kuka tana gaya mata yanda abin ya kasance mata, Hajiya ta ce ƙyale shi su tafi. Insha Allah da rigima zasu dawo ko nawa zamu kashe ƴan iska zasu gane kurensu matsiyatan banza,in tana taƙamar asiri ne muma mun iya har gun tsafin da ake son kaini ina ƙi wannan karon zan je.

Zainab ta ce kije Hajiya wallahi na tsani in buɗe ido inga ƴar iskar matar nan baya gajiya da kallonta sai ka ce T.V,ko nauyi na baya ji gani gata amma bashida lokaci na. Wata ran ma in zai kirani da sunan da yake kiran ta fa zakiji ya kirani, Hajiya ta ce kada ki damu,zan gyara masa saiti,ki barsu su tafi ke dai ki tabbatar kin shaƙi kuɗi, ta ce ba wani abu.

*** *** ***

Tunda tayi sallah ta shiga shiri yanzu kam ƙal take jin ta ba wani zargin an ƙwari Zainab, yawancin kayan da suka siyo da M Bash shi ta ɗauka.

Ya shigo ya ce "bari in taya ki kema sai kije ki taya ni." Zainab kam tana ɗakinta har suka gama shiri Sunday shine ya fitar musu da kayan Dady ya kira wayar Zainab kamar ta share sai kuma ta ɗauka, ya ce ki fito zamu tafi, ta kashe kusan minti biyar ta fito, Ruƙayya ta dubeta cikin fara'a ta ce "Zainab zamu tafi." Ta dubeta ta ja tsaki "Dady gani." Ya ce zamu tafi ne, ta ce nan zakai min sallama saboda ni ba a bakin komai nike ba. To Allah ya kiyaye hanya ta wuce abin ta ta shige ɗakinta, ya ce Pretty muje kawai, Ruƙayya ta ce a'a kaje kuyi sallama ka bar mata komai, ya ce kinga check nan zan bata taƙi tsayawa,ki muje kawai ai na ajiye mata komai abinda babu ga Sunday nan sai ya amso mata dama ganin dama ne yasa zan bata kuɗin ba tsoro ba, komai da an mata ta ce an cuceta anyi meye meye?" Ruƙayya ta ce Haba don Allah kayi haƙuri kaje ka bata."

Ya nufi ɗakin fuska babu walwala, kuka ya sameta take yi ta kifa kanta, tausayinta yaji don haka ya isa gurinta ya kamota ya miƙar da ita ya rungume wani sabon kukan kissa ta saki yayi ta lallashi tare da bata check ɗin dubu ɗari ya ce in basu isheta ba zai sa a ƙara mata wasu cikin account ɗin ta. Ta yi ta janshi da ƴan wasanni dan dai ta nuna ma Ruƙayya itama yana yi da ita, ya ce to bari muje Zee, ta dama ka ƙosa ka tafi ne ko? Cikin shagwaɓa ya ce a'a Zee kece duk sanda muka zauna sai kin ja munyi rigima, ta shiga kissing ɗin shi a baki tana cewa in sun itama aje da ita, ya ce kar ki damu.

🖊️🖊️🖊️
[8/31, 19:10] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.