Complete Hausa Novels

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 9

Page 2

Baisan yawan su ba, ya ce "gashi na cin goro, wannan kuma ki ba ma Saude." Ta ce mungode Allah shi albarka ya biya buƙatu. Ya ce amin Hajja nagode, ta ce a'a nice da godiya Yusufa aini sai hamdala da Ubangiji ya barni da raina, da ubanka ne me min komai gashi har mun kai matsayin da ya haifeka gashi kaima kana kula dani, ya ce duk albarkarki muke nema Hajja.

Har waje ta rakashi inda ya shiga mota direba yaja shi suka tafi.

*** *** *** ***

Yau kam a gajiye Ruƙayya ta taso daga kotun da aka tura ta game da wata shari'a. Bakin gate suka yi kiciɓis da Nuraddeen Kano. Ya ce a'a Ruƙy yana ganin ki haka hula a hannu jaka hannu gari yai sanyi? Ta ce kai dai bari kawai Nuri,yau ɗin nan na gaji sosai fa ta nufi ɗakin su ta shiga sai da ta huta tayi wanka taci abinci sannan ta yi sallah.

Washegari tana ɗauraye after dress ɗin ta da T shirt ɗin ta,Nura ya sameta Ruƙy ina tunanin duk ma yanda za'ayi gobe Friday koda yamma ne zan je Kano, ta ce ka dawo yaushe? Ya ce Sunday ko Monday." Ta ce Kash, nima da ina da issasun kuɗi da mun je sai nima na sauka Kaduna,in yaso in kana dawowa sai na baka adireshin gidan mu sai mu dawo.

Ya ce "Oh muje in kuÉ—in naki sun kasa sai na cika miki dan nima sai a hankali,allwasce É—ina ne na wancan watan ta ce aini nawa tuni sun sha aiki.

Ranar juma'a tunda safe suka soma shiri,tasowar asuba suka yi,dan haka huɗu tai musu a Kaduna. Sun tsaya a garejin Mando nan Ruƙayya ta sauka,Nura ya rako ta inda yake cewa gashi ba waya a hannunki bare in na shigo unguwarku na kira ki. Ya kamata ace kina da waya fa ba girmanki ba ne. Ta yi dariya sannan ta ce Nuri kenan,Ni nan daka ganni ban so na riƙe waya ba ne, Amma ko ada,na riƙe waya a lokacin da sai wanda ya isa ne yake riƙewa, kuma ma yanzun ban ga dama bane, amma ka bari insha Allahu sai dai kaji calling ɗina. Alƙawari zan kiraka da layina, ya ce shikenan.

Mashin ta samu ɗari uku tun daga Mando gareji zuwa Kabala su kenan kuɗin ta dan haka ta ce muje ai gida nazo kuma bana son shiga mota ga hadari yana ta harhaɗowa gara na isa gida akan kari,bana son ruwa ya taɓa lafiya ta. Sun iso daf da shiga Kabala suna kan titin independence aka soma tsula ruwa nan kuma mashin tayi faci. Ruƙayya ta ce "Oh ni Ruƙy ya zanyi kenan? Ta sauka ta bashi ɗari ukun ya ce "Yaya zaki bani duka gashi bamu kai ba? Ta ce ba komai kaje kawai bari na taka, ya ce ga ruwa? Ta ce kar ka damu,tana tafiya duk ta jiƙe.

Tun daga nesa Sabi'u ya dubi ubangidansa "Ƴallaɓai ga wata can tana buƙatar taimako." Dady ya amsa ba tare da ya ɗago ba, ya ce "A taimaka mata." Ya rufe baki tare da faɗuwar gaba irin wacce bai taɓa ji ba, ya kai hange ga yarinyar da Sabi'u ya ce su taimaka mata,da tazara tsakanin su kuma shekaru baƙwai masu ƙyau bai ganta ba, amma sai da ya gane ta. Ko shakka ba zaya yi ba waccan Pretty ɗin shi ce, domin duk da basa tare kuma idanunshi sun daina ganin ta wannan ba zai hana zuciyarshi kullum karanta surar ta ba, haka yake tsarata kullum.

Sanye take da jallabiya doguwa baƙa haɗe da gyalenta,jaka da takalmin ta ma duk baƙaƙe ne,sai dai ta jiƙe sharkaf har ɗiga take yi.

Jijiyoyin jikin Dady suka tsaya cak, komai ya daina kai saƙo a jikinshi lokacin da ya tsinkayi muryar Ruƙayya suna magana da direba yana cewa baiwar Allah shigo mu taimaka miki ta ce "a'a, nagode Malam na kusa gida gashi kuma duk na jiƙe,ka na jiƙa muku kujera." Ya ce, bakomai shigo taimako ne ai."

Sam Ruƙayya bata ga Dady ba kasancewar motar na waje baya ganin na ciki, amma shi Dady yana ganin ta, tana shaga gaban motar gabanta ya faɗi sai dai har ga Allah bata zata da wani cikin motar ba, don haka sai tayi addu'a a ranta dan kar ta faɗa mugun hannu.

Ta ɓalle maɓallan gaban abayar ta cire sai ga riga T.Shirt mai ɗauka da rubutun N.Y.S.C ta bayyana da wandon ta, ta zage jakar hannunta ta ciro rigar sanyin N.Y.S.C tasa ta ɗaura gyale kamar ɗan ƙwali sannan ta ciro hijabi ƙarami tasa ta maida abaya cikin jaka. Ƙamshin da take shaƙa da faɗuwar gabanta da yaa tsananta sune suka tuna mata da wani abu, tabbas duk inda turaren nan ya fito daga gurin Dady ne, domin tun da suka rabu da Dady bata kuma jin ƙamshin nan ba sai yau.

Ya Allah! Ta faɗa cikin wata muguwar faɗuwar gaba, lokacin da ta dubi madubi ta ga Dady zaune a bayanta. Daga nan bata kuma motsi ba sai ƙwatancen da ta dinga ma direba har lungunsu. Ta ce da direba nagode fa, ya ce bakomai." Ta buɗe mota ta fita.sannan ta saci kallon Dady ta rufe ta tafi, zuciyarta cike da mamakin Dady. Lallai duniya wai kamar Dady ya ganta ya share ta, hawaye ya zubo mata tayi nadamar zuwan ta Kaduna a yau.

Shi kam Dady be ma san anzo har Ruƙayya ta fita ba,haƙiƙa jikinshi ya mutu, zuciyarshi ba ta tare dashi,yana tunanin dama Pretty bata yi aure ba,ko ko tayi ta cigaba da karatun a gidan mijinta? Auren ya mutu ne? Ko ko mijinne ya mutu? Ko ko da auren ta? Wanene zai bashi wannan amsar. Ganin Ruƙayya ya tsorata Dady gami da firgita shi, ta taɗo mishi da wata sabuwar muhimmiyar soyayyar ta.

A fili ya ce "Wannan karon ko Pretty tana da aure ko batada shi, koma wanene mijinta sai ya bai mishi Pretty É—in shi,kai koma ta halin yaya ne shi bazaya barta ba,bai san sun iso gidan Hajja ba sai dai ya ji Sabi'u na cewa.

"Ƴallaɓai mun iso." Ga zaton shi gidan su Ruƙayyan, sai yaga gidan Hajja nan ya soma tunanin kodai mafarki ne? Kai ba mafarki bane. Ya dubi Sabi'u ya ce "ina Pretty ɗin fa? Kan Sabi'u ya ɗaure ya ce,wace Pretty kuma ko wacce muka ɗauko? Dady ya ce "Eh," Sabi'u ya ce ai mun sauke gida Ƴallaɓai baka kula bane." Nan Dady ya wayance ya ce "Ok." Ya shiga gidan Hajja ya bar Sabi'u da mamakin halin da Ƴallaɓai ya shiga kan yarinyar nan,a ranshi ya ce koda yake fa yarinyar ta haɗu dole Oga ya ruɗe har magana yake shi kaɗai ina jin shi.

*** *** *** ***

Yaraf ya zube a kujerar falon Hajja,Saude da ke jira abinci akan centre table tana faɗin "Uban masu gida kasha hanya,in fatan dai baka sha dukan ruwa ba?" Da ƙyar ya ce sannu Saude ina Hajja? Ta ce gata nan zuwa tana ɗauro alwala ne, sama-sama suka gaisa da Hajja don haka ta tasa shi da tambayoyi jikinne Yusufa ko ko gajiya ce?.

Numfashinsa yana sama-sama ya ce "Duk aƙwai." Ta ce "To ai gara ka je asibiti ko? Ya ce "wannan bana asibiti bane ku barni na huta bana son magana." Duk shiru suka yi,yana ƙwance har aka kira magriba, ya yunƙura da ƙyar ya tafi sallah. Hollandia kawai ya ɗaɗɗaka baici komai ba ya kira direba a waya ya zo ya ɗauke shi. Hajja ta yi tayi ya ci abinci kasancewar ya yi azumi ya ce "Kiyi haƙuri Hajja ba zan iya cin komai ba, ina cikin damuwa ki min addu'a." Ido ta bishi da shi har ya shiga cikin mota sam baya tare da tunanin shi, tunanin shi kawai ta ina zaya fara da wannan lamarin.?

A hankali ya ce "Sabi'u kaini gida gurin Momy."

Yana zube gabanta kan kafet ya yin da take zaune kan kujera, gabanta sai faÉ—uwa yake yi saboda bata san dame ya zo ba. Kallonsa tayi yana bata tausayi dan tuni Dady ya mance da ake dariya,ko yanayi su dai ya daina musu.

Sannan ya zama miskilin gaske ga zafin rai da ya koya waɗannan halayen sama taka ya same su tun bayan da ya gama jinyar rashin Ruƙayya, sai dai har Yanzun yana basu girman su tare da musu biyayya.

Ganin bashi da niyyar magana yasa ta ce "Dady menene damuwarka? Ya dubeta idanunshi sun kada sunyi ja ya ce "Momy naga Pretty, Momy Ruƙayya na gani. Shin da gaske ne tayi aure kamar yanda kuka sanar da ni?.

Gaban Momy ya yi mummunan faɗuwa cikin tsoro ta ce "Haka magabatanta suka sanar damu." Ta cigaba "Ka nutsu Dady kaida gobe kamar yanzu ka zama Ango." Dubi yanda gidan nan ya cika da ƴan biki sannan ka zo min da labarin ka ga Ruƙayya me ganinta zaya amfana maka a halin yanzu?"

Ya yi wani murmushi irin na ɓacin ran nan ya girgiza kai shi kam yana mamakin yanda kowa ya kasa gane irin son da yake ma Pretty, ya furzar da wani huci mai zafi sannan ya ce.

"Momy aini nama manta da wani labarin zan yi aure, domin dama a rashin Pretty zan auri Zainab, kuma yanzu na ganta don haka har ga Allah na manta da wani batun aure.

Gaban Momy ya faÉ—i,dan tasan zaya iya fasawa don haka sai ta soma lallashinsa.

"Haba Dady yanzu, wannan girmanmu ne,ace wancan karon mu tara mutane abu bai yiwu ba, yanzu ma mu ƙara maimaita na da? Ka tuna burinmu muga ƴaƴanka shekarun mu sun tsawaita. Haba Dady ko so kake sai mun mutu sannan zaka yi?"

Hawaye suka zubo ma Momy abin da ko cikin mafarkin shi baya son gani,wato kukan Momy.

Da sauri ya isa gabanta

"Kimin afuwa Momyna." Ya sa hannu yana share mata hawayen, "Kada ki min haka Momy, abin zaya yi min yawa,ban sama kaina son Pretty ba daga Allah ne,nima na kasa control ɗin kai na ne, Momy ki fahimce ni." Ido ta zuba mishi gami da tausaya mishi, don haka sai ta ce "Dady kai namiji ne mijin mace huɗu,kana da izinin auran Zainab da Ruƙayya har ma da wasu biyu idan kana da buƙata. Yayi shiru na wasu lokuta sannan ya ce "Shikenan ku ci gaba da bikin ku." Ta ce "To amma nafi son ka ƙwantar da hankalinka kada ciwon ka ya tashi,ka bi komai a sannu har a gama wannan ko.? To kawai ya ce mata, ya miƙe ya nufi shashin daya gina wani tsatsaran plate mai ƙyau a cikin gidan nasu.

Kai tsaye bedroom ɗin shi ya nufa ya shige toilet duk da sanyin da garin ya ɗauka sakamakon ruwan saman da ake yi tun yammacin na yau,bai hana shi sakarwa kanshi ruwan sanyi ba sai da yaji sanyin yana ratsashi sannan ya fito mai ya shafa ya saka jeans baƙi da ƴar shirt sannan ya ɗauko wata rigar sanyi jibgegiya mai laushi ya saka yasa hularta. Har lokacin sanyi yake ji, zazzaɓi ne ya sani amma sai ya share ya tsani shan magani ya ɗauki key ɗin mota ya fito.

Yana ƙoƙarin shiga motar,motar Hussain tana shigowa, dole ya tsaya ya ƙaraso kasancewar har Yanzun ana ɗan yayyafi sai ya shiga gaban motar Hussain ɗaya gefen, suka yi hannu, Hussain ya ce Ango ya za'ayi ne? Ni ɗazun na kiraka muna ƙoƙarin tafiya sai kuma ka ce min kana hanyar zuwa Kaduna. Shi ne abin ya bani mamaki tunda nasan yau aƙwai wani program shi ne ka taho? Yanzun dai nace bari na zo naji goben sai mubi jirgi da wuri ko?"

Dady ya ɗan takure jikinshi saboda sanyi sannan ya ce "kune zaku tafi da su Saddiƙ saboda ni bana jin daɗi zan zo daga bayan ku,ku tafi da su Dad tunda suma jirgi zasu bi, amma fa sha biyu zasu tashi gidana zaku sauka Sunday yana nan munyi waya dashi zaku samu komai, sannan aƙwai Abokaina nacan su Sagir matansu zasuyi ma matanku tarba sosai,ba wata matsala ku cigaba da gabatar da komai kar ku damu da cewa sai nazo.

Hussain ya ce "Daka É—aure munje kada ita Zainab É—in ta zama cikin damuwa." Ya ce ,no ba damuwa zan mata waya yanzu ma gurin Dakta zan je,kaje gida ai zamu haÉ—u gobe É—in." Hussain ya ce "To bari na kaika sai na dawo da kai." Dady ya ce "a'a nan kusa muke ka tafi gidan shi zan je.

Hussain ya tafi sannan Dady ya É—auki mota ya fita.

Kai tsaye Kabala ya nufa bakin lungun su Ruƙayya nan ya tsaya. Saboda yayyafi ba yara don haka sai ya kashe motar sannan ya shiga lungun gidan,yana nan yanda yake sai dai ya samu canje-canje,wato ƴar kwaskwarima yana tsaye daf da ƙofar gidan yana jiyo ɗan motsi baisan ko na wanene ba,ya yanke hukuncin ya yi sallama.

Ruƙayya suna zaune da Umma taji gabanta ya faɗi domin tasan Dady ne,dama ƙarfin hali tayi dan kada su Umma su gane tana cikin damuwa,dan haka sai ta daure har suke hira tana ba Umma labarin Legos. Har sai da Affa ya shigo ta gaida shi suka ɗan yi hira kafin kiran magriba. Saboda ruwa tunda ya tafi sallar magriba bai dawo ba ko sun haɗa sallar ne ko kuma ya tsaya sai isha'i ne bata sani ba.

Umma ta dubeta kamar ana sallama ko? Ta ce naji ƙila gurin Affa aka zo,ta ce A'isha tana ɗaki tana sallah je ki tura ta taji,ɗakin ta nufa gurin A'isha ƴar gidan Yaya Sadiya tace je ki waje zakiga wani mutum in ya tambayi ki Affa kice baya nan.

Yana tsaye ta fito tai mishi sannu ya amsa da yauwa ƴan mata, ta ce kana neman Affa ne? Ya ce a'a Ruƙayya tana nan? Ta ce Eh, ya ce kirata ki ce tazo, ta gaya ma Ruƙayya Aunty wai ke ake nema, ta ce kije ki ce mata nayi bacci,ta zo tace tayi bacci, ya yi murmushi sannan ya ce ita tace kice tayi bacci? A'isha ta ce Eh, ya ce "To koma ki ce mata wai Dady ne yace zai jira ta har sanda zata tashi,tana gaya ma Ruƙayya, ta ce shegiya kin ce mishi ne ni nace ina bacci? Ta ce Eh, Ruƙayya ta kai mata duka maimakon ki ce a'a, A'isha ta ce ai na manta ne Aunty.

Zazzaɓi sosai ya rufe Dady amma yana jingine jikin gidan Affa dan ma an samu yayyafin ya yi sauƙi a haka Affa ya shigo lungun haska tocila lokacin kuma goma ta ɗan shige shima Affan sun tsaya sasanta wani aure ne ya ga mutum tsaye gashi ba wutar lantarki. Ya yi gyaran murya sannan ya ce "wanene?" Dady ya tsugunna ƙasa "Affa sannu da zuwa." Affa ya ce yauwa ban shaida ka ba fa." Dady ya ce nine Yusuf,kan Affa ya kuma ɗaurewa ya haska shi da tocila sannan ya ce Wane Yusuf fa? Dady ya ce "Baka gane ni ba Affa?" Affa ya ce "shigo dai muji."sun zauna sannan Affa ya gane shi cikin mamaki ya ce Yusufa ai wallahi ban shaida ka ba sam ganinka nayi kayi min ƙiba.

Dady ya yi murmushi sannan ya ɗan russuna yana gaida Affa, Affa ya ce ya bayan saduwa kuma Yusufa shiru? Dady ya ce tunda muka bar nan bani da isasshen lafiya waje aka fidda ni dana dawo kuma sai harkokina suka koma Abuja, yanzun can nake,ai na zazzo bana samun ka sai dai na bada saƙo gurin mai shagon can."

Affa cike da mamaki ya ce "Dama kai ne ke aiko min da saƙon nan?" Dady ya ce "Nine Affa." Affa ya ce "Madallah to ya iyalin kuma." Dady ya ce "To ana dai niyya." Affa ya ce kana nufin har yau bakayi aure ba?" Dady ya ce "Eh, to gobe ne dai ɗaurin auren." Ya ce "Allah sarki a ina ne? Dady ya ce ba anan bane can ne Abuja." Ya ce "to Allah yasa alkhairi. Yana son ya sako zancen Ruƙayya kuma ya kasa don bai san me Affa zai ce mishi ba.

Ba ya son ya ji Affa ya ce yayi haƙuri,don haka sai yayi shiru. Sun ɗan taɓa hira sannan Affa ya ce "naga kamar kana rawar sanyi." Dady ya ce bana jin daɗi ne, Affa ya ce to kaje kasha magani ka huta zama da ciwo babu amfani, to kawai ya ce amma can ƙasan ranshi yana cewa,ga maganin nan a gidan ka. Sun yi sallama akan zaya kuma zuwa kafin ya tafi.

Da ƙyar ya kai kanshi gida. Kai tsaye sashen sa ya wuce, cikin bargo ya ƙudundune haka ya ƙwana yana rawar sanyi.

Washegari Dad yaga basu haÉ—u sallar asubahi ba, kuma bai shigo ba, gidan cike da baki ya kira layin Dady tayi ringing har ta katse ba'a É—auka ba,kusan sau biyar yana kira,wayar tana falo yana jiyo kukanta amma ba zai iya tashi ba.

Dad ya juya ya kira layin Momy wacce dama tana kan hanyar shigowa, ta ƙaraso bedroom ɗin shi riƙe da wayar ta tana ringing ta ce gani ma dama nan zan shigo, ya ce wai ina Dady ne? Bamu yi sallah dashi ba yanzu har taƙwas tayi bai shigo ba.

Gaban Momy ya faɗi ta ce "Ina jin ƙila baya jin daɗi yana can sashin sa. Ta fita shima Dad ya ɗauko sandarsa ya nufo waje yana dogarawa ne saboda ciwon ƙafa dake damunsa.

Baƙin Yola dake ɗakin Momy suka fito suna gaida Dad sanda ya fito ya nufi sashin Dady tuni Momy ta kusan shiga, baya falon dan shi kanshi key ɗin shi gaya nan akan wani ɗan kucilin firji wanda sam saboda ƙanƙantar sa baiyi kama da firji ba,ta nufi bedroom ɗin shi,ta matuƙar tsorata da taga yana maƙyarkyata akan gado da sauri ta cire masa bargo tana masa sannu, ta ce haka ka ƙwana? Kai kawai ya ɗaga mata daidai nan Dad ya shigo,ganin jikin Dady yasa tsoro ya kama shi.

Waya ya yima family Doctor ɗin sa,nan da nan sai gashi ya duba shi. Dady mura ce da ƴar damuwa ke damun shi,muran ce ma tasa masa zazzaɓi ya yi masa allurai dan ya samu bacci sannan ya rubuta magunguna. Dad ya ce to ban da abin Son menene na shiga damuwa,kai da zaka shiga sabuwar rayuwa. Momy ta ce ban sanar da kai bane jiya fa yaga Ruƙayya domin hankalinshi tashe ya zo min. Gaban Dad ya yi mugun faɗuwa a zuciyarshi ya ce innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.

Kasa magana ya yi har sai da Dakta ya tafi bacci mai nauyi ya ɗauki Dady, Dad ya dubi Momy ya ce "Hajiya yanzun ya ya zamuyi ne? Momy ta ce "Uhm kai dai bari, haka za'a cigaba da biki kawai,in matar ta zo in tana kula dashi ƙila ya mance da Ruƙayya." Dad ya ce "In ma za'a bashi ba sai ya aura ya haɗa su ba."

Ta ce haka ne abin nan ya isheni. Ya ce bari in angama wannan zan je Katsina filin nan da aka maida gurin sha'anin biki ana bada haya to nan ne gonar tasu mahaifin Ruƙayya zan bashi in huta nima bada zalunci nayi ba duk laifin Jega ne shi ya shirya komai, to na haƙura nima cutata ya yi tunda kinga na daɗe da sallamar shi macuci ne na ƙarshe." Momy ta ce "Hakan ya yi sai mu nema masa auran Ruƙayya."

🖊️🖊️🖊️
[8/2, 07:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.