Complete Hausa Novels

Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 4 of 9

Page 4

An kuma bani ita a karo na biyu kuma insha Allah ranar sati za'a É—aura mana aure.

Ta harareshi kai amma bakada kai duk yaushe kayi auren ko sati ɗaya ba'a yi ba sannan ka soma zancan wani auran? Ya ce Hajja koda mata huɗu na aura a wancan satin aka ce ga Ruƙayya sai na saki ɗaya na aureta,ke ko yanzun da ba'a ɗaura da Zainab ba ko ranar ɗaurin auren ne wallahi fasawa zanyi dan dai sanda na ganta banida tabbacin ko tana da aure ko bata dashi,kar in fasa ya zama tanada aure. Hajja ta ce yaushe ka ganta kuma wayace maka batada aure? Ya yi murmushi ya ce ƙarewar rashin aure ma an bani ita,yau su Dad zasu je gurin Affa a gama komai nan ya koro mata labarin tun daga farko har zuwa yanzun daya je gurin Affa. Hajja ta yi fatan alheri tare da roƙon shi kan ya lallashi Zainab dan kishiya aƙwai ciwo, kayi adalci, ya ce insha Allah.

Kula aka ci mai da waina dan ya kaima Zainab,a phone ya kira Dad ya sanar dashi yanda sukayi da Affa,kai tsaye sashen shi ya nufa ƙwance kan kujera ya samu Zainab Sam bata san ya shiga ba, ya tsaya kanta sai faman hawaye take zubarwa tausayinta ne ya ɗarsu a ranshi,a hankali ya ajiye kular sannan ya isa gurinta ya tsugunna ya ce Zee a cikin taushin murya, da kiranta ta juyo ta dubeshi, shima ya dubeta suka yi wa juna murmushi.

"Haba Zainab menene haka? Kina son ki ganni cikin tashin hankali ne? Ta fashe da kuka, Dady dubi fa da wayewar gari har ka tafi gurin wata kayo break,ba abin da ke ɓata min rai ace ko one week ba'ayi da auranmu ba har zakayi wani Please ka duba fa." Shiru Dady ya yi jin tatsuniyar ta a ranshi ya ce in ma kina tunanin zan fasa gara kin bari, amma a fili sai ya ce hakanan ki zauna kina kuka ƙila ma baki karya ba, hannunshi yasa ya share mata hawaye ya miƙe ina zuwa ya ce mata sannan ya nufi kitchen ya ɗauko plate waina ya zuba mata a baki yake bata tana zuba shagwaɓa ta ce ya yi mata wanka, ya ce to yanda kika ce ai haka za'ayi soyayya aka tsaya yi a bayin kafin daga bisani ya yi mata wankan sannan shima ya yi.

*** *** ***

Su Affa sun tarbi su Dad hannu biyu shagon gidan maƙwafcin Affa nan suka shiga tarihi ne ya maimaita kan shi wato inda aka taɓa karɓar sadakin na Ruƙayya yau ma gasu nan. Bayan gaishe-gaishe sai kuma ban haƙuri ya biyo baya inda Dad yake ƙara ba Affa haƙuri game da FIN ƘARFIN da aka mishi ya nuna cewa ba laifin shi bane laifin Alhaji Jega ne, yanzu haka sun daɗe da yin hannun riga da Jegan sakamakon cutar da ya yi mishi har ta Naira miliyan talatin da biyar ya cigaba da cewa filin nan na farko da na soma amsa gurin mahaifinku gwamnati ta bani,to sun saidashi miliyan arba'in da biyar. Sai ya kawo min miliyan goma wai haka aka saida, yanzun ma nakun ma na maida muku kayan ku,zamu sa lokaci muje in maida muku abin ku cikin bainar jama'a.

Affa ya ce dama ka barshi Alhaji." Dad ya ce "a'a aiko da, ɗin bansan cewa FIN ƘARFI ya yi maku ba, wallahi da bazan shiga abin ba.

Sannan suka koma ga batun yara inda Dad ke cewa Malam Sani Allah dai ya rubuta Ruƙayya dai My Son shine mijinta, Affa ya ce komai ai na Allah ne, abokin Dad ya ce tun ran gini ran zane inji masu hikima, abokan Affa biyu suka ce haka ne.

Dad ya ce sai muje batun sadaki ko? Affa ya ce Naira dubu goma shi ne sadakin dana yanke mata. Dad ya dubi abokinshi ya ce kaji fa Alhaji Bukar lau ƴa ce fa sukutum wai dubu goma, sukayi ƴar dariya sannan Affa ya ce ƙarancin sadaki shine mafi albarka Dad ya ce hakane sai dai har ga Allah naji babu yawa kace dai Allah ya sanya alkhairi kawai muke so,ai naji daɗi sosai ko batun aikin ta dama mu ma muna buƙatar lauya a campanyn Dady ɗin nan Kaduna da na Abuja shi kenan riba biyu, suka yi dariya, Affa ya ce haka ne gida bai ƙoshi ba ai ba'a kaima wasu ba, suka ce hakane.

Dad ya ce to batun rana fa yaushe ne ɗaurin auren? Affa ya ce wannan kuma Yusufa ne mai ajewa dama haka na sanar dashi, Dad ya ce bari na kirashi, daidai lokacin Dady yana ƙwance kan doguwar kujera Zainab tana zaune kan kafet amma ta jingina da jikin kujerar da Dady ke kai,kanta ma yana gefen ƙirjin Dady remote ne a hannunta ta kamo wata channel da ake film ɗin batsa, Dady ya ce No canza mana banason wannan channel ɗin ta ce "haba My dear daga ni sai kai fa,ka bari mu kalla." Ya ce a'a bana cikin masu kallon haramun, wannan haramun ne mutum ya kalli tsiraicin wani, don haka kamo min MBC Action ta soma searching cikin zunɓura baki, wayarshi ta soma ruri,da sauri ya ɗauka don yaji ringing ɗin daya sama Dad ɗin shi ne, ya ce Hello Dad,nan gefen kuma Dad ya ce yauwa munzo da yaushe kake son a ɗaura auran? Dady ya ce Dad wannan Saturday ɗin nake so." Dad ya ce My Son bazaka bari sai week na sama ba? Sannan an buga I.V, Dady ya ce ai Dad bar zancen I.V ko ana gobe za'a ɗaura aure muna da masu buga cart,bana son na kuma rasata ya ɗan kalli sashen da Zainab take, sai ya miƙe ya fita yana cewa Dad kaji? Ya ce shikenan.

Take a nan Dady ya yi sujjada yana mai godiya ga Allah gefen su Momy ya shiga dan sanar da ita, itama tayi farin ciki tare da yi mishi nasiha game da mata biyu, sannan ta ce Ruƙayyan yanzun ta sani? Ya ce a'a bata sani ba zan dai je gidan su a bani number ɗin ta da kuma adireshin gurin da take, Momy ta ce kai Babana burin ya cika, ya ce Momy ai Allah baya bacci, zuwa na hajji sau uku banda Ruƙayya babu abinda nike roƙa gurin Ubangiji sai gashi ya amsa min ya bani ita a lokacin da na soma ɗebe tsammanin samunta, wata ƴar ƙwalla ta taru mishi gefen ido, Momy tausayin ɗan nata ya kamata don haka yana fita alwala ta ɗaura don nuna godiyar ta gurin Ubangiji ta kuma roƙa mishi zaman lafiya, Allah ya kuma kare shi. Shirye-shiryen biki ya kan kama,ana jibi ɗaurin aure abokan Dady da abokan kasuwancin shi dake ƙasashe daban-daban suka soma zuwa, waɗanda basu sami zuwa wancan ba, wasu kuma sai mamaki suke yi me yasa Dady aure biyu? Ya dawo daga masaukin baƙi inda ya sauke su a Darba Hotel. Bayan ganin sun samu komai ya nufi gida yau kam sai ya ji muryar Pretty.

Sai da ya yi shirin bacci sannan ya soma neman layin ta, lokacin tana tsaka da karatun wani Nobel don ɗebe mata kewar damuwar da take ciki ta rasa kullum cikin faɗuwar gaba take a ƴan ƙwanakinnan Nuri ya kan ce mata ta yawaita addu'a sai tace ita dai tana ganin gida kamar ba lafiya. Ta kira su Murja da Fati duk sun ce mata kowa lafiya,to me yasa ranta be mata daɗi?.

Wayarta ta soma ringing takai hannu ta ɗauka,baƙuwar lamba ta gani mamaki ya kamata,dan ba kowa yasan ta da waya ba, ta ɗauka tare da faɗin.

"Salamu alaikum."

Ya Salam! Ita ce kalmar da Dady yaso furtawa ta ce wa yake magana? Ya ce Dady ne Pretty,nan da nan gabanta ya faɗi tayi shiru ta kasa magana, ya ce kinyi murna da jina? Wani irin baƙin ciki taji da ta tuna wai Dadynta. Daya ganta ya yi banza da ita? Dady da ya karya alƙawarinta? Dadyn da yazo har gidan su don gaya mata auran shi? Sai taja tsaki ta kashe, ya kuma kira taƙi ɗauka ya yi ya gaji amma bai daina ba,da ta gaji sai ta kashe wayar gaba ɗaya.

Washegari jajibarin ɗaurin aure duk su Amina sun hallara don yin aiki da wayar Fati Affa ya yi amfani ya kira Ruƙayya, cikin faɗuwar gaba ta ɗauka jin muryar Affa duk sai tsoro ya kamata, shi kenan Umma ta rasu, haka ta raya a zuciyarta, ya ce Ruƙayya ko zaki iya zuwa gida sai ki koma ranar Lahadi." Nan take tace waya rasu Affa? Ya ce a'a babu wanda ya rasu,ko gobe ma zaki iya zuwa, kada ki damu ba wani abu bane.

Sam bata cikin haiyacin ta gani take an ɓoye mata ne babu wanda bata kira ba cikin Yayyanta amma duk sun ce ba komai kuma basu san kiran da Affa yake mata ba,kona menene?.

Nuraddeen ta kira take sanar dashi abin da yake faruwa, yazo gurinta suna tattauna maganar ya ce ta ƙwantar da hankalinta insha Allahu babu komai, kuma ta bar tafiyar sai gobe, tun da yau lokaci ya ƙure,

*** **** ****

Tun Asubahi tana cikin motar mocopolo duk ta ƙosa ta ganta gida dan jin meke faruwa?.

Wayewar garin wato ranar ɗaurin aure ai kada kuso kuga ango wanda dama ƙwana ya yi bai runtsa ba,nafilfili yake yi yana roƙon Allah kar ya kawo sanadin fasa auran. Da safen ne yana fitowa wanka.

Zainab ta kirashi inda take mishi ƙorafin rashin kiranta tunda ta dawo, har ga Allah shi yama manta da wata Zainab baya tuna komai sai Pretty ɗin shi. Ya ce "Kiyi haƙuri abubuwa sun min yawa yasu Hajiya?" Ta ce lafiya,dama ina son kuɗi ne. Ya ce me zakiyi dasu ne? Bana baki dubu hamsin da zaki tafi ba? Ta ce To ai anayin kayan faɗar kishiya kuma ba kai min ba, ya ce aiko ita ma Pretty ɗin ba riga na mata kayan ba tukunna, ta ce to nidai kuɗin zaka bani, ya ce,zan turo miki, ta ce nawa? Abin ya soma bashi haushi ya ce yanda naga dama ya kashe wayar,shi fa haushin ta yake ji itace dai bata sani ba.

Yana gama shiri gurin abokanshi ya nufa can ya yi break. Hira suke suna ta shaƙiyancin su, yayin da gidan su Momy ya ɗinke da jama'a wannan karon har da Hafsi tazo da yaranta guda biyu daga Kalaba inda mijinta yake aiki. Aure kawai za'a ɗaura amma an cika fiye da wancan satin.

Dady kuwa yasaka kaya sun kai kala goma Yana cirewa sai yaga basu dace da É—aurin auren ba, duk da kasancewar kayan sababbi ne. Duk yasa aka siyo su daga Togo aka kaisu É—inki.

A ƙarshe ya haƙura cikin wata shegiyar mai masifar ƙyau, green dark hular dama tare aka kawo su,yana fitowa sai da ya birge abokanshi gurin Momy ya shiga tana cikin ƙawayenta babu wanda Dady bai birge ba, Momy kam Babu wanda ya kai ta farin ciki wannan rana, ɗan ta ya samu abin da yafi so.

Hatta motar da Dady ya hau wannan rana sabuwa ce mai shegen tsada,so kam abokanshi kayan su iri ɗaya suka sa wani farin yadi mai shegen tsada suka ɗinka gaba ɗayansu abin birgewa har da waɗanda ba baƙaƙen fata ba wasu turawa. Su Sadiƙ ne suka ɗinka duk wanda yazo indai aboki ne sai a bashi yasa. Unguwar Kabala ta ɗinke da jama'a tamkar taron idi. Tun daga farkon layin har ƙarshe dole ne sai anyi amfani da lasifiƙa wurin ɗaurin auren.

**** **** ****

Ruƙayya da yake tasowar ƙarfe huɗun Asubahi suka yi kuma motar tayi shegen gudu, huɗu saura suka sauka. Mashin ta hau zuwa Kabala suna kusanto unguwar tasu gabanta ya na ƙara faɗuwa. Sanye take da wani leshi purple ba wata ƙwalliya da tayi amma hakan birge wasu take. Sun ratsa layin nasu cike da jama'a tayi mamaki yau ba juma'a ba wannan ma an watse.

Lungunsu ta sauka ta sallami mai mashin yanda taga mutane suna kallonta sai ta ƙara tsinkewa, tana shiga gidansu taga matan maƙwafta da Yayyanta ai sai ta saki jakar hannunta tana kuma duban ɗakin Affa an ɗaga labule ga dangin babanta maza na Katsina. Yaya Murja ta ce "Oyoyo ga Ruƙayya." Sauran suka fito sun kula a firgice take, ta ce "ina Umma?" Suka ce gata nan a ɗakinta, ta faɗa ɗakin ga mamakin ta sai taga Umma zaune tasha ƙwalliya sai tayi ajiyar zuciya hankalinta ya ɗan ƙwanta ta ce "Wayyo har naji daɗi wallahi nasha ke ce babu a firgice nazo garin nan, wai meke faruwa ne? Yayyanta da suka zagaye da ita suka ce zakiji gurin Affa da ya dawo ba mutuwa bace,sai taji koma menene da sauƙi.

Bayan ta ci abinci sama-sama tayi wanka bata kai ga shafa mai ba, Yaya Murja ta ce Affa nason ganinta, hijabi ta saka kan zaninta iya ƙirji tayi ɗakin Umma yanzu duk maƙwafta sun tafi sai Yayyanta,ta zauna ta gaida Affa ya amsa cike da murna shima yasha ado, ya ce Ruƙayya nasan cewa ke kullum mai biyayya ce ina matuƙar alfahari dake. Shiyasa a yau na ɗaura miki aure ba tare da na nemi izni ko yardar ki ba. Nasan ba zaki bani kunya ba, kanta a ƙasa dama tunda taga ba mutuwa ba ce tasan dai baya wuce haka.

Gabanta yana faÉ—uwa ranta yana raya mata shikenan sun bar juna da Dady. Amma sai taji gara da hakan tunda ita ta kasa sauraron kowa.

Ta ɗago idonta yana ɗigar da hawaye ta ce Affa nagode Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,ba zanƙi zaɓin ka ba." Affa ya ce nagode Ruƙayya amma ban ji kin tambaya wanene mijin ba? Ta ce ai Affa ba sai na tambaya ko wanene ba, tunda dai yayi maka nima yayi min." Affa ya faɗaɗa fara'arshi ya ce To albishirin ki. Ta ɗago tana dubanshi bata ce komai ba ya cigaba.

Dadynki wato Yusufa Allah ya yarda shine dai mijinki." Ido ta tsura ma Affa tana tunanin ko mafarki ne...... Shin ba wancan satin taji yana sanar da Affa auranshi ba? Shine ya ganta ya yi banza da ita shine ya karya alƙawarin ta da har yanzu ita tana tare da alƙawarinsu.

Ta dubi zoben hannunta ta girgiza. Affa ban son Dady,da ne na soshi yanzun bazan iya auran shi ba ka zaɓa min wani cikin kuka rurus take maganar.

Affa ya saki baki yana kallon ta,a zaton shi daya faɗa zata hau murna amma sai yaga akasin hakan,. Ya ce "Kina son shi Ruƙayya da,nine na hana a yanzun kada ki damu na yarda nine ma na fara amince mishi. Na ce Affa duk abinda Dad ɗin shi ya yi maka? Ni dai bana son shi, Affa ya ce Kiyi haƙuri Ruƙayya lokaci ya riga ya ƙure,an riga an ɗaura aure,kije nasan insha Allahu ba zakiyi kuka da Dady ba. Ki riƙe shi zaɓina kiyi biyayyar nan dai da kika sa ba."

Ta ce "To nagode Affa." Ta tashi kuka sosai take yi su Yayyanta sun sha mamakin wai Ruƙayya ke kukan bata son Dady. Murja ta ce me yayi miki? Ta ce cikin kuka "babu ni dai bana son shi,ko da ɗin ma dan dai bansan ciwon kaina bane." Su Yaya Sadiya da Yaya Suwaiba tashi suka yi daga gurinta suka ce kar ta soshi shegiya. Amina kuwa dama Dady tai ma waya cewar Ruƙayya tana isowa, ta kirashi ta sanar dashi a waya, haka kuwa tayi yanzu sai ga wayarshi yana sanar da ita gasu nan shi da wasu Abokanshi ya ce kice mata tayi ƙyau dan Abokaina sun matsu su ga wacece wannan ta haukatar musu da gentleman ɗin su? Amina ta yi dariya ta ce "To ƙanina."

Da farko cewa tayi ba zata ba sai da Umma tai mata tatas ta ce ta zauna ɗin,ai mu bamu isa da ita ba sannan fa su Murja suka lallaɓa ta suka gyara ta sosai wani jan leshi suka zaɓo mata cikin kayan ta dan ba'a riga an kawo lefe ba,farin takalmi da gyale suka bata ta fita tana zunɓura baki.

Sun kai su ashirin abokanshi suna sanye da cikin anko na ɗaurin aure,nan taja gyale ta rufe fuskarta. Shi kam Dady wani ƙwarjininta ya ji matuƙa sai yaji yana jin shakkar ta, Sadiƙ ya ce "baki isa ba ai ki buɗe mana fuska mu ganki." Dady kam kasa magana ya yi ya jingina da bango yana kallonta.

Ta buɗe fuska ta ce "Ina wunin ku." Suka amsa suna ta yi mata tsiya ta rikita musu aboki. Ta ƙi magana sai murmushin dole take yi saboda kada ta bada shi,ta ɗan dubeshi ta ɗan ranƙwafa ta ce ina yini? Kamar an sashi cikin aljanna ya ce lafiya lau Pretty na suna ta damun ki ko? Ta ɗan haɗe hannayenta guri guda ta ce ba komai. Abokansa suka ce to sai mun haɗu gurin dinner ta dubeshi yanzun za'ayi dinner ba zaku bari sai lokacin tarewa ba? Suka ce a'a wannan wasu ne suka shirya muku, ta ce To Allah ya kaimu anjiman. Suka tafi suna yaba tsarin yarinyar har sha'awar tarbiyyarta, wasu ko cewa suke kaga wai lafiyayyen jiki? Dole Son Guy ya ruɗe.

Bayan sun tafi ya rage shi da ita ya miƙe yana duban fuskarta. Ta ci magani tamkar ba ita ba, Ya ce Pretty na gashi dai Allah ya......" Ta ɗago idanun nan nata waɗanda suke matuƙar birgeshi, ta ɓalla mishi harara,nan take ya yi shiru ta ce "Dady manyan ƙasa,nifa yanzun ba Ruƙayyan da bace da ka sani, yanzun wannan babu Dady a ranta kamar yanda ya manta da ita, kada kaga cewa Affa ya cusa maka ni,ka ɗauka ina son ka har yanzu? Ya yi murmushi ya ce Pretty kenan,ai ni burina in aure ki,ko ki soni ko ki ƙini Pretty ni mijinki ne nasan kuma ina sonki. Ko? Ta dube shi kamar gaske ya ce da wasa ne?"

Ta ɗan yi murmushin takaici sannan ta ce wannan damuwarka ce nidai bana sonka." Da sauri ya dubeta ta ce Yes,da na soka lokacin bansan menene so ba bansan ƙwalitis ɗin maza ba, yanzun na gane kai ba irin wanda nike so bane." Ido ya tsura mata, maganar ta ta taɓa shi sosai yasa hannu ya shafi fuskarshi sannan ya fesar da wani zazzafan huci, ya dubeta yanzu ya ya zakiyi dani? cikin sanyin murya ya yi maganar. Ta ce "inka gaji ka sake ni ba."

Ya yi murmushi ki sake sabon tunani, domin babu saki cikin auranmu. Ya take yazo gabanta yasa hannunshi ya ɗago fuskarta dube ni nan Pretty ya kausasa murya,sau uku a jere ina zuwa ƙasa mai tsarki ina rungumi ka'aba ɗakin Allah ina hawaye ina Allah ka bani Ruƙayya, Ruƙayya, Ruƙayya nake faɗi, sannan ya bani inyi wasa dake? Sorry ai mutu ka raba ni dake Pretty zan koma wannan shekarar ni dake inyi ɗawafi in kuma rungume ka'aba in gode ma Allah."

Ya saki fuskata ki shirya da ƙyau Sabi'u zai kawo miki kayan da zakiyi amfani dasu gurin dinner ina son a haska min ke yau gidajen T.V na duniya su san nine mijin." Ya juya ya tafi ta ɗaga murya.

"Ba inda zan je don kaji."bai ko juyo ba ya tafi ranshi na suya wai shi Pretty ta ce bata so. Gudun kada abokanshi su gane yasa ya saki jikinshi tamkar baya cikin damuwa.

Ta nufi gida rai ɓace, Yaya Murja ta ce "Haka ki kaje musu turɓunɓun ba ƙyan gani? Fati ta ce ai Ruƙayya har ma da iskanci ke in Dady bai ƙiki ba ai ko bazaki gujeshi ba duk da yana namiji yafi ki komai, ta ce ni ina ruwana da ƙyan shi Ni bana son shi. Amina ta ce munafuka bari ta shige gidan shiru zakuji ta." Ta ce Allah ya kiyaye,nan dai sukayi ta tsokanar ta.

An dawo sallar magriba Affa ya ce kai kowa ta tafi gidanta, Ruƙayya ta soma musu dariya. Suka ce kema ai tazo kanki yarinya." Ta ce "eh dai ai ba yau ba." Dady ya kira Amina........

🖊️🖊️🖊️
[8/13, 08:28] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*

*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.