Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Fin Karfi Part 3 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 9
Page 3
Dad ya ce "Ni dai koda ba zan nema mai auran ta ba in basu in huta."
*** *** *** ***
An É—auro aure amma hankalin amarya a tashe don haka ba'a samu yin biki a can Abuja ba aka tarkato aka taho da amarya.
Dady ya farka bacci, Zainab ya gani zaune gefen shi tayi ado sosai sai dai hankalinta a tashe yake. Ya yi ƙoƙari ya yunƙura ya tashi zaune ya ce "Zee yaushe ki ka zo?" Ta ce "Tare muka zo dasu Dad da Abokanka,tasa hannu a wuyansa, jikinka babu zafi ka ji sauƙi." Ya ce "Alhamdulillahi." ta ce "To zaka yi wanka ne?" Ya ce da ruwa mai zafi. Ya fito wankan su Momy suka shigo duba shi abokanshi ma dana can Abuja dana nan duk sun cika falon shima yana jin su sai dai jikin babu ƙarfi sannan zuciyarshi na gurin Pretty da son ganin ta.
***. *** ***
Affa ya dubi Umma ya ce "Af har zan fita na manta ban sanar dake ba jiya yaron nan Yusufa da dare ya shigo yake sanar dani É—aurin auren shi,kin ji ikon Allah duk shekarun nan baiyi auran ba."
Umma ta ce "Oh ikon Allah, to Allah ya sanya alkhairi." Affa ya ce "kuma kin ji ashe duk saƙon nan shi ne yake aiko mana ina ta neman mai kawowa ashe shi ne." Umma ta ce aini zuciyata ta raya shi ne domin naga buhun shinkafar nan mai tumatur kuma ita ce yake kawo mana da, sanda yake neman Ruƙayya." Affa ya ce "ai koda aka fasa auran yaso ya cigaba da kawowa na hana tunda suka zo nan da uwarshi nace kada ya ƙara kawo mana komai mungode." Umma ta ce "Allah ya basu zaman lafiya," Affa ya ce Amin.
Duk zancen nan da suke yi a kunnen Ruƙayya abin duniya ya ishe ta sam ita fa da tasan haka zata fuskanta a zuwannan da bata zo ba, duk da tana shirin wai cire son Dady daga ranta, sai dai abin da yake ɓata mata rai shine har yanzu zuciyarta Dady kawai take ma dariya,yaya zata yi ne domin a ganinta shi Dady bai yi mata adalci ba har manta da ita yayi ya ganta ya yi kamar bai ganta ba, ƙarshen wulaƙanci shi ne ya tako har gida ya shaidawa Affanta auran shi ƙila ma da ita yaso ya shaidawa taƙi fitowa daya kira ta.
*** *** ***
Daran ranar Dady ya raka abokanshi na Abuja masaukin baƙinsu dake nan cikin layin su. Yayin da ƴan'uwan amarya suke can sashin su Momy.
Ya dawo ya zauna a falo tunanin shi ɗaya yana son zuwa gurin Pretty,ƙwarai ya so yaje yau da dare sai dai abokai ne ba zasu barshi ya fita shi ɗaya ba.
Sannan bai san yaya zasuyi da Affa ba ita kanta Pretty bai san nufin ta akan shi ba,ga zaton shi Zainab can gurin su Momy zata ƙwana, amma sai ji ya yi an dafashi ta ce "Tunanin me kake yi My dear?" Ya dubeta "Zee me yasa ba zaki je ki ƙwanta ba?" Ta ce Momy ta ce nazo saboda baka jin daɗi don kada ka ƙwana kai ɗaya,na shigo kuma sai na same ka kana tunani." A ranshi ya ce "Kada ki yarda ki san tunanin da zuciyata take yi." Ya miƙe "To muje." Bayi ta shiga tayo wanka, ta shafa turaruka tare da wasu sirrika da Hajiyarta ta bata,dan ma abin bai zo musu yarda suke so ba. Sun so kece raini a bikin musamman ranar dinner aƙwai shiri na musamman da Hajiyar taso tai mata, sai dai Kash! Rashin lafiyar Dady hakan bai samu ba.
Yana ƙwance rigingine ta zo ta ƙwanta kusa dashi tana kiran sunanshi a hankali yayin da ƙamshin daddaɗan turare ke tashi a jikinta.
Cikin natsuwa da hikima ta dinga janshi da hira tare da nuna masa irin so da ƙaunar da take yi masa domin ya samu ƙwanciyar hankali, dangane da fahimta da ta fara yi yana cikin damuwa.
Lamo ya ƙwanta tana jikinshi tana sharar bacci. Shi kam yana tunanin Pretty gani yake kamar bai mata adalci ba, yana ƙwance da wata ba Pretty ba. Yasan yau inda Pretty ce daran nan sai Allah kawai, amma yanda Zee ta nuna zalamar ta ta bashi haushi ace mace ba kara ba kunya shi bai son haka, to amma ba yanda zaya yi tunda matarsa ce sannan shima mabuƙaci ne.
Washegari da safe an aiko musu da break fast daga cikin gida. Shi kam bai ma tashi ba tunda ya yi sallah sai kusan sha É—aya. Ta zauna tana salo a gabanshi ya rasa sam bata birgeshi amma ya ya zaya yi wani sashe na zuciyarshi ya tuna mishi da wani abu da ya faru tsakanin Hussain da Madam É—in shi, ya ce mishi first night É—in su tasha wahala don sai da Dakta ya duba ta,da ya ce mishi nauyi kasa kaji mata ciwo? Sai ya ce kasan ita mace in virgin ce dole tasha wuya." Ya dubi Zainab sai yaji ranshi ya sosu, kenan dole wani ya santa, shi sam dai baiyi sa'a ba, domin bai kasance mazinaci ba.
Shiru kawai ya yi amma bashida walwala. Misalin biyar ya shirya ya nufi Kabala, bayan ya dawo raka abokanshi kai tsaye gidan Affa ya yi da shirin ko ta ƙwana.
Daidai wannan lokacin Ruƙayya ta dawo daga gidan Yaya Suwaiba ita da A'isha,tazo tana cewa Umma ni ƴar gata ce kinga itama Yaya Suwaiba ta cika ni da kuɗi." Umma ta ce "To Allah ya yi muku albarka dukkan ku." Ruƙayya ta ce Ummanmu "Yaya Murja ta sai min waya, Yaya Fati ta sai min layi ta cika shi da kuɗi, Yaya Murja ta yi min shopping Yaya Amina kuɗi kai na gode Allah." Umma ta ce shine abin godiya. Ruƙayya ta ce bari nasa number Nura inji ko yana hanya koma ya zo, Umma ta ce tafiyar dare zakuyi kenan dai? Ruƙayya ta ce tafi ƙwanciyar hankali hanyar Legos ɗin Allah dai ya kaimu lafiya." Umma ta ce Amin.
Tana kira Nuraddeen ya ce saukar su kenan, yake mata tsiyar waya da cewa tazo ta matsa samari sun fito da waya." Ta ce Wayyo Nuri,wa ya gaya maka? Ba ni da saurayi, ya yi dariya Ruƙayya kenan, yanzu ya ya zan kawo kaina unguwarku? Ta ce shiga motar kasuwa ce market in kun iso sai ka hau ta Kabala kuna zuwa bus stop kai min waya sai nazo na ɗauke ka, ya ce bari na hau Kabala ina zan ce,ka ce Kabala in kun zo sai ku miƙo daga Bus stop kuyo ƙasa ka kirani zan fito na jiraka.
Haka kuwa aka yi,nan bakin lungunsu ta jirashi,yana isowa suka tari juna cikin farin ciki da murna har cikin gida suka shiga ya gaida iyayen ta cikin girmamawa. Bai taɓa zaton Ruƙayya ƴar talakawa ba ce sai dai ya jinjina ma iyayenta dattawa ne masu ƙoƙari sun birgeshi yanda suka tsaya ma ƴarsu tayi karatu. Abinci ta gabatar mishi sannan ta shiga shiri.
Suna sallama da su Umma da Affa,aka yi sallama da Affa a waje. Sun fito dan kada su ƙara dare cak numfashinta yaso ya ɗauke,da suka yi ido huɗu da Dady yana tsugunne gaban Affa. A take ta ɗaure fuska sam bata son ganin shi,tana ganin shi mugu ne bashi da adalci. Tunda ganin shi babu abin da yake ƙara mata sai tashin hankali, suka jero da Nuraddeen, shi ko numfashinsa ɗaukewa ya yi ya kasa cigaba da gaishe da Affan, ya shiga ruɗani,ya ya ma haka Ruƙayya da wani?.
Kusa da Affa suka russuna sai mun dawo Affa." Ya ce Allah ya kiyaye hanya,kasa motsi Dady ya yi har suka wuce su. Affa ya ce "Ruƙayya ga Yusufa ko baki gane shi bane?" Ba tare da ta dubeshi ba tace"Oh ban ganshi ba ina gajiya?" Ta wuce cikin ko in kula.
Ba Dady ba hatta Affa yasha mamakin ta,zama Dady ya yi tare da saka kanshi cikin gwiwoyinshi sai da suka kai ƙarshen lungunsu sannan ta juyo ta dubeshi. Tsaki tayi sannan ta kauda kai jikinta babu ƙarfi jakar hannunta ta faɗi Nuri ya dubeta ya ya ne Ruƙayya idanunta ne suka ciko da hawaye cikin rawar murya ta ce bakomai, ya ɗaukar mata jakar ya ce yi sauri gurin da zamu hau motar Legos da nisa sosai.
Sai da suka zauna a mota sun ɗau hanyar Legas sannan ya yi ta janta da hira tare da bata labarin yarinyar da zaya aura sannan ta ɗan washe dan ya kula tana cikin damuwa baya son mata tambaya ƙila ba zata so yasan damuwar ta ba. Tana cikin wannan halin yana dai tunanin duk yanda akayi aƙwai wani abu tsakanin ta da mutumin da ya taras gurin Affanta,dan da fara'arta ta fito tana ganinshi sai kawai ta canza fuska. Kuma shima ya shiga ruɗani sakamakon ganinta.
Affa ya maido hankalinshi gurin Dady ganin shi ya yi zaune ya haɗa kai da gwiwa, ya ce "lafiya Yusufa?" Hannu yasa a kafaɗun Dady yana cewa "Taso haba Yusufa ya ya zaka zauna ƙasa." Jikinshi babu lakka ya tashi jiri yake gani don haka ya yi saurin dafa bango, Affa ya kula da haka don haka sai ya ce, zauna kan dakalin nan.
Dady ya zauna Affa ma ya zauna gefen shi Shiru kusan minti uku sannan Affa ya dubi Dady wanda zufa take keto masa, ya ce " Yusufa ka daina jin jirin?" Ya É—ago ya dubi Affa idanunshi sun kaÉ—a sunyi jajir ya ce ya lafa, sai dai naga Dakta ne saboda hawan jini na keson tashi, Affa ya yi shiru sai yana tuhumar kansa,anya ya yi ma yarannan adalci kuwa?.
In zaya iya tunawa tunda ya hana Ruƙayya Dady ko sunan shi bai kuma jin ta ambata ba, kuma yasan tana tsananin son shi, sannan bai ji daɗin yanda ta nuna mishi ba a yau shi har kunya yaji,yasan kuma har Yanzun tana sonshi hasalima a kanshine taƙi aure.
Ya dubi Dady tausayin shi yaji don zai yi matuƙar wuya bata sanadiyyar Ruƙayya ya haɗu da wannan mugun ciwon ba,haƙiƙa ya yi kuskure domin ba Dady ne ya yi mishi laifi ba Alhaji Mansur ne.
Ya dubi Dady ya ce "Yusufa meke tafe dakai kazo ne dan kai min sallama kamar yanda kayi alƙawari?" Wata wawuyar ajiyar zuciya ya saki sai da ya ɗan huta na saƙwanni sannan ya ce Affa na zo ne dama sai kuma ya tuna kodai Ruƙayya tana da aure? Don haka sai ya yi ɗan tsaki ya ce ko da yake gaisheka dama na zo yi. Affa ya ɗago ido dan ganin shin Yusufa da gaske har zuciyarshi ya zo gaida shi ne? Dan tun kan yanda ya amsa ma ya gane yana cikin wani hali,ga mamakin sa sai yaga hawaye suna zuba daga idon Yusufan nan da nan Affa ya ruɗe tare da faɗin "Subuhanallah me yake faruwa?" Dady ya sauko daga dakalin tsugunnawa ya yi gaban Affa ya rasa me zai ce ya yi shiru sai dai zubar da hawaye yake yi, shima Affa kasa magana ya yi hannu yasa akan Dady yana cewa "Menene damuwar ka Yusufa,sanar dani ko zan iya taimaka maka domin nima ubanka ne." Shiru Dady ya yi dan rasa ta inda zai zancen,kiran sallar da aka yi ne yasa Dady ajiyar zuciya sannan ya ɗaga ido ya dubi Affa. Affan ne yace suje suyi sallah in yaso sai suyi maganar cikin tsanaki.
Bayan dawowarsu daga masallaci ɗakin Affa suka yada zango. Shi Affan yasan matsalar Dady Ruƙayya ce to baya son ya soma kawo mishi zancan ta, tunda ya riga ya yi aure, shi kam Dady ya samu natsuwa kaɗan da ya yi sallah don haka ya raya ma ranshi koda Affan zai hana shi Ruƙayya sai ya sanar dashi har Yanzun yana sonta don haka sai ya gyara zama.
Affa ka gafarce ni nasan cewa ka riga ka ƙwaɓe ni da batun Ruƙayya sai dai amma har Yanzun ita zuciyata ke so,ka taimaka min Affa nasha wahala kanta, kada kai min horo da laifin da ba nawa ba laifin wani baya shafar wani na jira Ruƙayya auran ta ya mutu har na gaji sai dai yanzu bansani ba koya mutu ne ya matsa ya kama ƙafar Affa. Don son Manzon Allah kai min agaji."
Jikin Affa babu ƙarfi ya ce "Yusufa haƙiƙa na yanke maka hukunci da ba kaine kayi laifin ba, kuma ina maka albishir da na baka Ruƙayya a karo na biyu duk san da ka shirya ko gobe ne kazo a ɗaura aure. Sannan ina mai farin cikin shaida maka Ruƙayya batayi aure ba karatu tayi yanzu haka tana bauta ma ƙasa ne a Legos.
Daskarewa Dady ya yi a gurin gani yake yi mafarki ne nan ƴan minti na zaya farka haka nan yasan tsokana ce kawai Affa ba da gaske yake ba. Affa ya kula da nufin Dady dan haka sai yace kada ka damu kaje kayi shawara da magabatanka,sam Dady bai san lokacin da ya rungume Affa yana faɗin "Affa kaima Allah ya yi maka abin da ka ke so duniya da lahira, Allah ya jiƙan magabata." Ya miƙe,na tafi Affa sai ka ganni.
*** *** ***
Kai tsaye gurin Momy ya nufa tana sallar isha'i,san da ya shiga yama manta cewa baiyi isha'in ba, koda yake akan hanya ta same shi.
Ya yi ƙwance kan gadon Momy idanunshi lumshe farin cikin shi ya yi mai yawa wai shi ne Affa ya amincemawa ya auri Pretty shin gaske ne ko kuma mafarkin daya saba ne?
Momy ta kai hannu ta dafa ƙafarshi "Yaya dai Babana? Ya ɗago da sauri kuma cikin fara'a ya ce Momy Affa ya kuma bani Ruƙayya, Momy ki tayani murna ina son ta sosai, tayi shiru tana kallon shi gani take ya soma taɓuwa ne,ganin bata ce komai ba yasa ya ce Momy kice wani abu Please cikin sigar shagwaɓa ya yi maganar Momy dariya tayi ta ce kafa girma Dady, ya ce ni dai kimin zancan Pretty,ta ce Nasan ba haka bane janka yake, ya ce "taso muje kiji a gunsa ya ce ko gobe ne na shirya nazo a ɗaura mana aure." Momy ta ce "Haba Dadyna duka fa satin nan aka ɗaura auran ka,shin ya ya za'ayi ka kuma wani? Bayan haka Ruƙayya ma batayi aure ba?" Ya ce "batayi aure ba tama gama karatu, yanzu service take yi a Legos Momy sai kinga yanda Ruƙayya ta zama Pretty ɗin ta sosai. Ya yi sujjada yana ma Allah godiya.
Shima Dad ya yi farin ciki dan kullum burin shi yaga dariyar ɗan tilon ɗana shi dan haka ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba goben nan zaya je godiya tare da kai komai, wani satin kuma a ɗaura ma Son ɗin shi aure.
Cikin farin ciki ya tura ƙofar falonshi, Zainab ta dubeshi ta miƙe ta nufo shi My dear ina ka shiga ne ? Ya rungume ta ina cikin farin ciki,itama ta soma murna,sanar dani me ya faru? Ya ƙara rungume ta,an bani Pretty ɗina wai yau nine zan auri Pretty ɗina, cikin sauri ta ture shi tana mishi wani mugun kallo,kasan abin da kake faɗa kuwa,kasan ni wacece ɗin ka kake min wannan maganar?" Ta soma kuka shekaran jiya fa aka ɗaura bikinn mu, amma kace zaka ƙara aure? Wannan wane irin wulaƙanci ne? Haba Dady."
Ya hau kujera ya zauna,ta juya zata shige bedroom, ya ce ke Zainab zo nan." Yanda ya daka mata tsawa shiyasa ta dawo ta zauna ya ce dube ni nan, ta dubeshi kinsan na taɓa ce miki bake kaɗai bace? Cikin kuka ta ce to amma da wuri haka? Ya ce saurareni Pretty ita ce rayuwa ta duk wanda yasan ni yasan halin da na shiga domin ta, ƙarshe ma a rashin tane na aure ki so Please ki bini a hankali kan Pretty komai zai iya faruwa kada ki ɓata min farin ciki na,ya riga ta shiga bedroom ɗin kai tsaye toilet ya nufa,laf ya yi cikin baho yana tunanin Pretty ina ma yana da number ta,ya kirata su sha hira,can cikin nisan da ya yi a tunaninta ya jiyo kukan Zainab.
Cikin hanzari ya fito tana ƙwance kan gado tana kuka. A hankali ya isa gurinta kallonta ya yi tana bashi tausayi ya zauna kusa da ita yasa hannu ya dafata tare da cewa "Zee.. Zee taso kiji." Ya ɗagota ta ƙwanta a kafaɗarshi tana shashshekar kuka ya ce "Zee son da kike min na gaskiya ne kuwa? Ta dube shi cikin shashsheka ta ce me yasa kake shakka? Tayi ajiyar zuciya sannan ta ci gaba "Ka daina shakka akan son da nake ma." Ya ce to in har kina sona dole kiso Pretty,kar ki zaton cin fuska nake miki, tsakanina da Allah nake sanar dake,ko iyayena sanin mahimmancin a gare shi ne dalilin daya sa zasu goya min baya. Zee inda kinsan halin da na shiga kan Pretty bama zakiyi magana ba shawarar da zan baki itace in baki son ta ki koyi yanda zaki sota dan auran ta ba fashi kuma gaskiya ni bazan iya zama inuwa ɗaya da maƙiyina ba,na sani kema ina son ki tunda ni ne na ajiye ki haka auran Pretty ba shi ne zai sa na wulaƙanta ki ko na daina sonki ba,ke dai ki bani goyan baya. Tasan duk abinda ya faɗa hakan yake nufi,garama ta haƙuri dan haka sai ta zame ta ƙwanta akan gadon shima bai ce komai ba ya koma toilet ya ɗauro alwala yazo ya shiga jero nafiloli dan nuna godiyar shi ga Ubangiji.
Washegari tun da sassafe Dady ya taka gidan Affa dan sanar dashi zuwan Dad É—inshi tare da tambayar yaushe ya kamata zuwan nasu ya kama? Da yamma ko da daddare? Affa ya ce da dare bayan isha'i ai zai fi ko?" Dady ya ce to shikenan Affa,yana son bashi kuÉ—i yana ganin kada Affa ya yi faÉ—a, daga nan gidan Hajja ya zarce.
*** *** ***
Saude tana ƙofar kicin kusa da ita wata ƴar matashiyar yarinya ce tana wanke-wanke ya ce "Saude ina ƙwana?" Ta ce lafiya lau uban masu gida yaya amarya? Ya ce lafiya ina uwar gidana? Ta ce tana ciki ai zata ka daina yi damu, ya yi murmushi ya ce da tsohuwar zuma ake magani Ni na isa in yar da Hajja? Ya faɗa daidai lokacin da yake ƙoƙarin shiga falon Hajja, tana zaune kan kujera tana kallon T.V ya yi murmushi sannan ya ce Hajja sarkin kallon T.V ga kuma wannan uban gilashin. Ya ce me kike kallo ne? Ta ce Oho ga dai shi nan Ni ba jin abin da suke faɗa ni keyi ba ina dai binsu da ido, ya yi murmushi ya ce ina ƙwana an tashi lafiya,? Ta ce lafiya lau, ya kishiya ba haushi? Ya dubeta ban gane wa kenan ba? Ta ba haushi nake tambaya,kan Dady ya ɗaure ya ce nifa ban san ta ba, Hajja ta na dariya tace kai dai turawa sun gama dakai komai na Hausa baka san shi ba,to ina amarsu ta ango, ya ce Oh Zainab tana gida ni naji kin kirata da wani suna.
Ta yi murmushi ta ce ba dai kazo karyawa bane? Dan mun cireka a gandu, ya ce ni da wani albishir ma nazo miki, ta ce name? Ya gyara zama na wani auran, ya yi maganar fuska ba wasa,hakan ya sa ta cire gilashin idonta ta tsura mishi ido ta ce ka fahimtar dani kaine zaka ƙara auran ko wa? Da gadara ya ce ni ne nan,kinsan wadda zan aura? Ya ce Pretty.......
🖊ï¸ðŸ–Šï¸ðŸ–Šï¸
[8/2, 21:24] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 3*
*LITTAFIN*
*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*