Complete Hausa Novels

Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 44

"Momy dan Allah kiyi hakuri,wlhy Aunty Haleema ne batada lapiya inaga kamar bazan samu damar shigowa ba yau,kinga ita kadaice bazan barta haka ba" murmushi momyn tayi tace "Eyyah Allah sarki Allah ya bata lapiya ki gaida ta kinji,yanzu se yaushe??"

"gobe sha biyu nake qare lectures inshaa Allah daga school se gidanki momy karki damu" "To Allah ya kaimu hafsat Allah ya miki albarka kinji" Ameen kawai tace ta ajiye wayan sannan ta juya zuwa kitchn din,dafa wani tayi bata saka yaji ba ta kawo,ai loman farko ta zubar aqasa ta kalli yaa shaam fuskar nan harta soma kawo ruwa "Yaa shaam kaci kaji wlhy ba taste yanzu fa ko d'an green pepper ta saka man amma haka tayishi,Allah ni bazan ciba kuma" Tsaki hafsat taja bada shirinta,dama fa hafsat gwanar rashin kunya ce kurin tsoron yaa shaam ne ke durqusar da ita,yau kam ta cika fam

"Gaskiya Aunty haleema bansan ya kikeso na miki ba na dafa wancan kince bazakiciba na dafa wannan indomie kince yaji,na kuma dafa wani kince ba yaji ni kije ki dafa da kanki,ko aikin bauta nazo na muku wlhy ko zaku kasheni bazan dafa muku wani ba" kallon mamaki shaam ya mata domin shi har tasoma bashi tausayi ya matso kusa da ita yace "Jeki kitchen ki dafa mata me abunda takeso" tsayuwa tayi a wurin taqi koda motsi,saukar wani kyakyawan mari taji seda ta ga wasu taurari na musamman,yace "ina wasa dakene? Nace kije ki dafa mata wani" kamar yanda batayi magana ba haka bata koda motsa ba da wannan ya shaam ya soma dukanta tamkar wani mahaukaci baji ba gani seda haleemah taga tayi lilis sannan ta saka kukan muna furci tazo tana qwatar hafsat "shaam dan Allah kayi hak'uri,idan ka illatar da qanwarka ni za'aga laifina kuma kaga ai tama gaji ni dama ba ina nufin ta dafa wani bane,nama ji na qoshi tea ma ya isheni,miqewa tayi tsaye ita kuwa tayi hanyar waje har wannan lokacin bakinta be mutuba tana kaiwa kofa tace "kuma wlhy ko zaku kasheni na dena muku girki kenan har abada" bebi ta kanta ba ya dawo wurin haleemh da rarrashi......

Bayan magrib tana d'akinta tana rusar uban kuka abinta shaam ya shigo,zama yayi kusa da ita da yace "Hafsat ni kikewa baqar magana??" bata kulashiba yace "Kinaso na ci gaba da lallasaki kenan?" budar bakinta se cewa tayi

"ka lallasanin ai akwai Allah,kuma wlhy duk wanda yaci zalina Allah ya isa" mamakin kalamanta yakeyi "waye yake koyar dake rashin kunya hafsat?" nurguda bakinta tayi sannan tace

"Wanda suke cin zalina kullum kuma Allah ya isa" miqewa yayi yace "hafsat kin janyowa kanki zaman bakar uquba a gidannan sabida kinga ina miki wasa shine kikemun wulaknci san ranki ko? Wato ke kin isa lallai kuwa zakisha baqar wuya a hannuna" bata kulashiba taci gaba da kukanta yayi ficewarshi yana mejin tsananin tsanar hafsat,tundaga wannan ranar kuwa shaam komai qanqantar laifi idan hafsat ta masa se duka har yakasance daga dazan ya sanyata abu jikinta ze soma rawa,kuma da sauri takeyi,sedai kwanakinnan batada lapiya ko kadan, da wannan ta sameshi tace dashi "Yaa shaam kwanakinnan da zazzab'i sosai nake kwana ko zakaje dani clinic dinka a dubani" kallon ta yayi ya rufe jaridar dake hannunshi " A matsayinki nawa zakijemun clinic? Kinga nawa clinic ma na masu matsalar zuciyane,sabida haka kije wani asibitin kawai" batace masa komai ba taje gun huda daganan suka wuce wurin mijin ta dayake shima likitane,binciken farko ya fito da tambarin heart problem ajiki,sosai sadeeq ya shiga cikin shock,huda ya fara kira a gefe yace

"Baby wai anya qawarki ba kashe kanta takeso tayi akarin banza ba @kan soyayya kinsan kuwa ciwon zuciyane da ita,fisa bilillah @her age gaskiya bance ba'a samun irin wayannan cases dinba sabida yanzu irin wayannan cutukan sun yi yawa a wurin yarama harda hawan jini,amma ni tausayi take bani gaskiya me take sakawa a zuci har haka,jininta mafa hawa yakeyi" dafe kai huda tayi tace dashi "Hubby kasanme har fa dukanta yakeyi sannan ko kwanciyar aure bayayi da ita,ga school ga problem dinshi girki mafa ita kewa matarshi ko sau daya betaba kwana a bangarentaba,ga hafsat da zurfin ciki tacika barwa kanta abubuwa ni wlhy har naji kaina yana ciwo ma,yanzu meye solution?" dafe kanshi yayi yace "Amma gaskiya shaam ya bani kunya wane irin sakarai ne qanwarka guda daya matar da iyayenta suka nuna maka so tamkar sune suka haifeka shine tsabar mugunta yarinya ko 17 bata hada ba zaka hadata da ciwon zuciya mugun banza" wurin hafsa suka koma dakyar sadiq ya tattaro nutsuwarsa ya shaidawa hafsat komai cikeda rarrashi da nuna mata hanyoyin dazatabi tunda abin beyi nisaba,sosai hafsat tayi kuka sannan ta nuna musu su rufa mata asiri karsu sanar wa kowa,hakan dai aka bata magunguna ta koma gida da damuwa me dinbin yawa wacce ta ninka tada,tundaga wannan lokacin hafsat ta dawo sukuku sam bata walwala gashi batada lapiya a haka har Haleemah ta haifi yaro namiji,wanda bataje wankan gidan ba kuma tanayin 40 days aka maidashi kwana wurin hafsat,komai wahalar khaleefa hafsat keyi baji ba gani, harma ya saba sedai yasha madara wasu lokutan idan ya tashi a bacci da dare ya saka kuka setayi ta rarshinsa idan yaqi itabdinma seta saka mar kuka suyitayi se me aikinta tazo ta karb'eshi.......a haka har khaleefa yayi wata hudu a duniya,san suniya shaam ya dauka ya daura akan yaronnan bama a san ranshi yake barinshi kwana acan ba,danma bayason bacin ran haleema na......

Ranar wata juma'a Cikin dare khaleefa ya tashi da wani irin ciwon da hafsat ta kasa gane na menene,kuka yake tayi tamkar me yana zabure zabure,hankalin hafsat ya tashi ta dauki wayarta tayita kiran shaam baya dagawa,takira haleemah akayi rejectin call din sannan kuma aka kashe ma wayar gaba daya,shaam yaga ta kuma kiranshi yace "Haleemah lafiya kuwa? Kodai in daga inji menene dalilin kiran naga bata taba yin hakan ba?" wani narkewa haleemah tayi tace "Boo me dan Allah manta da ita,nasan kuka khaleefa ke mata shiya sanya kaga ina ce maka akaishi acan kar ya hanamu walawa" biyeta yayi sukayita har kofar gidan tazo ta bubbuga suka mata banza,koda ta koma yaron baya motsi lokacin ma karfe biyar na asuba,da kukanta takira shi again be daga ba,ta aika masa message "Yaa shaam nayita kiranka inaga fa Khaleefa ya rasu" yana fitowa daga gun alwala yaji aran message yaje ya duba a rude ya gayawa haleema da salla be dameta ba tana baccinta aibhar ture juna sukeyi sabida tsabar gidi mewa,banka kofar sukayi suka sameta rungume da gawar tana uban kuka,

"yaa shaam kunga illan rashin daga waya ko? Shine inata kiranku yaron nan se zabura yakeyi amma kuka qi dagawa wlhy kungani ya mutu" ta sake fashewa da kuka,ai shaam na dubawa yaga da gaske ya mutu ya soma jibgar hafsat

"yanzu tsabar bakida mutunci shine kika kashemun yaro,dama wannan qiyayyar taki akanshi ta wuce tunani wlhy kema sena kasheki,jibgarta ya hauyi baji ba gani haleema se kuka takeyi ta dauki gawar se jijigawa takeyi,dakyar yadena dukanta yace dan ubanki kije na sakeki saki d'aya ki barmun gidana........yana kaiwa nan yabar dakin yana me karbar gawar yana kuka,wayanta ta janyo da kyar ta kira Abba haris,yana dagwa dak'yar tace "Abba kazo ka daukeni yaa shammaz ya sakeni kuma so yakeyi ya kasheni da duka,banama iya tashi".............

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.