Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 44
Mom Nua'iym
      Â
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
  Love story 2018
Billy galadanchi
Wattpad@galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Â
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
                 06
Jiki ba k'wari ta juya zuwa d'akinta,sam hankalin hafsat beyi yawan dazatayi zurfin tunaniba ta kasa tariyo komai,wayarta ta ciro daga k'asan filo ta kira huda,d'agawar farko tace
"Huda dan Allah kina ina yanzu??" da mamaki hudan tace "Ina kan hanyar zuwa gun Ashraf tela" to yayi nima ganinan zuwa da maganar danike so muyi" kan huda tayi magana ta katse wayan,da sauri ta zari hijab tayi k'asa a hanya tayi karo da yaa shaam ko kallonshi batayiba sabida hankalinta sam baya jikinta,driver din momy ta gani tayi kiranshi da hannu,ta fada mota sukayi gaba....a shagon janyo hannun huda tayi suka dawo mota ta kalleta bayan tayiwa driver din umarni daya fita waje tace
"Huda wai da gaske sosai ni Hafsat ina san yaa shammaz??" kallon ta huda tayi cikeda nutsuwa tace
"Ban fahimce kiba?" kwashe komai tayi dataji su momy na fada ta gayawa huda ta qara da cewan "ke kadaine zaki iya fadamun gaskia dan Allah waida gaske wannan abun danaketaji gameda yaa shaam shine so? Kuma shi din suwaye iyayenshi??" sosai huda ta gano hafsat kuruciya ya mata yawa, banda haka ina zatasan su waye iyayen shaam,ni sawa tayi tace "poojah ki nutsu mana,zancen gaskiya ko shakka banayi kina san yayanki kuma sosai bawai kadanba,amma abunda nakeso dake shine kibi komai a hankali sabida kinga already an kusa aurenshi kuma tunda su momy basusan kinji maganar suba karki fadawa kowa karkuma ki nuna musu,wannan abun dakikeji idan yana waya da wacce ze aura da kuma idan ana zancen aurenshi shi ake kira kishi,kuma kishin ya miki yawa ina tausaya miki sabida tunkan kisan meye so da kishi kika fara kinsan kuwa illan kishi a tattare dake? Kishi masifane kamar yanda yake halittane na Allah ajikin d'an adam sedai da yake na wani yafi na wani zafin,dan Allah hafsat ki daure ki yakice sanshi a ranki,a yanda na fahimta da kika masa bayanin abinda kikeji game dashi sarai ya gano sanshi kike sabida baya muradin ki yasanya yace karki sanar wa kowa,ki manta dashi kici gaba da kallonshi a matsayin yayanki uwa d'aya uba d'aya" hawayen daketa faman tarewane suka gangaro mata tace
"Huda lallai so masifa ne kuma kishi fitinane,indai haka so yake to a gaskiya da matsala,ni bansan sanda na fara sanshiba tayaya zakice in cire sanshi a raina? Nida bansan yanda ya shiga ba ya zansan yanda zan cire?? Wlhy bazan iyaba" tausayinta huda taji ta janyota ta rungume tana bubbuga bayanta a hankali,a haka suka rabu jiki ba k'wari.....
*Bayan sati biyu*
Sosai aka cashe wurin bikin yaa shaam kuma acikin part d'inshi dake gidan anan aka kawo amarya Haleematu,yau sati daya kenan da tariyarta,kullum hafsat ke zuwa tayata aiki,kasancewar ba abinda takeyi agidan,ta d'auki shawarar qawarta ta dena nuna komai a idon mutane harma momy ta soma qaryata zancen cewar hafsat tana san yayan nata....yauma kamar kullum tana kitchen din Aunty haleema tana tayata aiki,suna d'an tab'a hira yaa shaam ya shigo,ba kunya suka rungume juna har tana manna masa sumba a wuya
" Baby yadai? Bana hanaki yawan aikinnan ba? Kije ki huta mana tunda ga Hafsat ta iya komai" kallon shi tai cikeda kissa tace
"Haba honey yaya daga zuwan yarinya tayani aiki seka wani ce na barta tayi,nooo ni banasan small oga ta tasha wahala" hancinta ya danja ta saka qara yace "Kinga Baby da gaske ki rage yawan aikinnan ita wannan sakaryar yarinyar shagwab'abb'iyan yarinyane yanzu take koyan aiki ki barta ta koya kekuwa semu huta abunmu" wani langwabe kai tayi tace "Haba shaam meye hakannan wai,nika tafi idan muka gama zanzo" hannu biyu ya saka dukda zaman ta katuwa ya dauketa yabar kitchen din da ita,ita kuwa dama gulmane haka takeso ya sanya bata wani musa masa ba, hannu hafsat ta sanya ta share k'wallan daya kwaranyo mata
"Yaa Allah ka yayemun wannan masifar,Allah ka rabani da k'aunar yaa shaam,Allah ka ciremun kishinsa,Allah ka kawomun agaji" wannan itace adu'ar datakeyi a sarari cikin kuka,tafi mintuna biyar a haka,kanta barwa Allah taci gaba da aikinta.....haka rayuwa taci gaba wa hafsat kullum itace da bauta agidan yaa shaam sekace wata yar aiki,shi kuwa kullum kwanan duniya qara tsanarta yakeyi yakuma rasa dalilin tsanar dayake wa kanwar tashi wanda a sanda tana qarama bashida wacce takeso sama da ita,amma yanzu tun sanda yagano sanshi takeyi seya dauki hakan a matsayin raini ya d'auki karan tsana ya d'aura mata kullum acikin bautawa gidanshi take ita kuwa yi hawai takeyi domin ta faranta masa,momy kuwa komai akan idonta take tafiya yanda ake takurawa yarta ba karamun damunta yakeba,duk kuma sanda tayi magana sekaga fuskar daddy ta sauya akan hakan.
Hafsat da huda sun samu admsn a Usman d'an fodiyo university dake sokoto,inda dukkansu suke karantar English,dabadan hafsat tanada kokari ba dabazata gane komai ba a makaranta kasancewar gaba daya hankalinta yana kan yaa shaam kullum kwanann duniya da begensa take kwana kuma take tashi,shekarunta goma sha shida yanzu yakamata ace ta qara girma irinna tashen balagan nan amma sam damuwa ya hana ta,tanaso ta yakice wa kanta soyayyar yaa shaam amma ta kasa,ganin rayuwar gidan yamata k'unci ya sanya tabar sama road gaba daya ta tattare kayanta tace gidan Abba haris zataje gun khairiyyah dayake itace tsarar haihuwarta,momy bata hanataba kasancewar tasani sarai 'yar tata tana cikin damuwa,gwara ma tane candin kota samu sassaucin abinda yayan nata kemata wannan kenan.
Tunda hafsat takoma gidan Abba haris se kewar shaam ya taso mata,shaam seyayi sati biyu bezo wurinsu abba haris ba,dukkuwa dayake sune iyayensa na ainahi,sabida kawaici,lokacin da yayan abban haris yayi aure wato mahaifin hafsat yajima be haihuba kai har haris yayi aure suka haifi shaam,shine fa suka baiwa yayanshi shi na har abada ganin yana matukar san y'ay'a amma Allah be kawo masa ba shiya sanya hafsat datazo sanda ba'a zataba bata gane cewar ba mahaifansu daya ba na haihuwa se daga bisani,domin kuwa an cire rai kamar daga sama Allah ya kawowa haj nasara cikinta samun hafsat be sauya komai ba na dangane dankaunar dasu momy da daddy kewa shaam ba......duk tabi ta qara yamutsewa batada kiza kiza,har Abba haris ya fahimci haka,kuma yayi juyin duniyarnan amma sam tace ita ba abunda ike damunta,da wannan yayi kiran khairiyya yace lallai tabi yar uwarta taji meke damunta cikin hikima domin ya kula ko wannan dawowan da tayi da dalili. Da dare hafsat ta tashi kukan data sama na rashin yayanta,wayanta ta dauko ta qurawa hotonsa ido a sarari kuwa tana kuka tace
"yaa Allah ina rokonka,ya ubangijin sammai da kassai,ya Allah ka ceceni Allah ka cire mun san yaa shaam a zuciyana,Allah ka rabani da kaunarshi,Allah ka ceci rayuwata karna mutu"" kuka me tsanani ya kwace mata khairiyya da ke kwance tana kallonta tana kuma saurarenta da mamaki tazo ta dafa tace
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.