Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 30 of 44
"Hafsat ki fito idan kina masauki ina reception na hotel din" da mamaki ta kalli Aunty surayya dake gefenta tana uban mita,sannan tace dashi "A dubai din?" tsaki yaja yace
"Noo a india,danla malama kizo ina reception ma wurin nace dake ko mun fara wasan banza ne haka?" cikin jin zafin gwasaletan da yayi tace "Kayi hakuri ganinan zuwa" kallonta surayya ta
"Keda waye kuma Ina zakije?"
"Muhammad ne wai yana wajen reception ashe yazo,kuma shi da number shi yake amfani niban sani ba" kallon ta tayi "Au dama shima zezo kika barni ina surfa mar ashar?"
"wlhy Aunty bansan zezo ba,ni kawai zancen dan rakiya yamun" jinjina kai Aunty tayi
"Wannan shegen muhammad din anyi miskilin masifa,ko wa yakewa iya shegen oho,jeki kiji" batace komai ba ta zari dan mitsitin mayafi tafito ga rigar irin straight gown din nan ne na roba ya kameta over, tun daga nesa tana ganin fuskarsa tasan akwai magana a d'an tsorace ta karaso wurin da yake,zama tayi kusa dashi a kujerar da yake tace
"Sannu da zuwa yaa muhammad ya hanya?" kallonta yayi fuskarnan a daure yace "Banasan ya hanyar ki sabida jirgi daya muka zo daku ai,sannan wlhy mintuna goma na baki ki sako sutura dan wannan bakida banbanci tsirara,idan kuma na kuma ganinki da makaman ciyar wannan shigan wlhy sena sassab'a miki,sekace ba 'yar musulmi ba" kallonshi tayi se a lokacin ta tuna yanayinta,waifa ita tayi shigar ne a zuwan tazo garin farar fata kartayi qauyanci, jiki a mace ta miqe,zuwa tayi ta cire kayan ta sako abaya baqa har qasa tayi talha ta fito,surayya na ganin yanayinta tasan shigarta yayiwa masifa amma dai vata dameta da tambaya ba,koda tazo baya nan,wayarta ta daga takirashi amma be dauka ba,anan ta zauna tafi 30 mnt be dawo ba ta qara wayar tashi gaba daya ma tajita a kashe,gwiwa a sace ta koma dakin tace da Aunty surayya wai yace gobe zasuyi magana,kallo daya surayya ta mata kuwa ta fahimci da babbar matsala.......
Washe gari tun asuba ta koma parlor tayi kiransa a waya,yana kallonta harta tsinke be daga ba, kusan 3 msd col,kawai seta fara hawaye tama rasa dalilin daya sanya take damuwa dashi zuciyarta sam batayi adalciba,data saka masa wannan tsoron na muhammad,tana cikin wannan tunanin taji qarar shigowar message
"Room no 10,2nd floor" shine abinda ya aiko mata sarai tabgane nufinsa ta sameshi acan,miqewa tayi ta saka hijab dinta tayi hanyar daze sadata da wurin....knockin tayi yazo ya bude fuskarsa a hade,gaidashi tayi sannan ya janye mata ta shige a daya daga cikin kujerun parlor din ta zauna,ta qura masa ido,shima din ita yake kallo,yaukam seda tagaji da kallon nashi ido cikin ido sannan tace "Kayi hakuri bazan qaraba inshaa Allah" amaimakon ya baiwa maganarta muhimmanci se cewa yayi da ita "Meya faru kike kirana daga yin sallan asuba?" tama rasa mezata ce masa,se kawai ta miqe "zan koma bacci zanyi" tazaci ze dakatar da ita amma bece mata komai ba harta fice,a ranta kuwa taji zafin sa sosai....
*Nigeria*
Sun dawo lapiya dauke da lefe da ban mamaki, har masifa su daddy sukayi,amma surayya tace dasu tamasa magana yace hafsa matar sace,babu kuwa wanda ze qayyade masa yawan suturun dayake buqatar wadata su da ita,kuma ya jibgo dogwayen riguna da qananun kaya over.......Aikam rana daya akayi daurin auren muhammad da hafsat,se kuma Shammaz da maryam,kuma aranar aka kai amaren biyu,wanda sam koda ma akayi auren hajia halima batada labari tana wurin gantalen ta dubai,acewarta taje saro kaya shikuwa da gayya ya ganta,yan uwanta kuwa dasuka ga pictures na ebar hankali da ba indiya se hankalinsu ya mugun tashi,amma sam basu sanar mata wai shaam yayi sabuwar amarya ba.......
Hafsat kuwa tunda yan kai Amarya suka watse wuraren karfe goma na dare seta soma jin tsoron zaman gidan ita kadai, shi kuwa be leqo bama se sha daya da rabi, Abinci ya kawo mata sannan ya sanya hannu ya yane mayafin dake jikinta ya ajiye gefe ya kalleta, "Kina bazawara wani kunya zakiji,zaki wani lullub'e fuska" sosai maganar sa ya doki qirjinta amma bata nuna masa komai ba kurun dai murmushi tayi masa,ganin haka ya sanya yace "Kici abinci kazane da drinks ga youghurt da ice cream idan zaki sha" kallon su tayi tace "Gaskia Alhamdulillah na koshi,sedai zuwa safiya" miqewa yayi be wani damuba,kizo ki kulle kofofin gidan ni zan tafi seda safe" ko motsawa batayi ba daga inda take sabida mamakin daya bata,to gidan uban wa ze kwana?" ta tambayi kanta,ganin fa tsorone ze hallakata ya sanya harya kai parlor ta rugo ta riqe masa hannu,da mamaki ya kalleta tace dashi
"Yaa muhammad zan bika dan Allah" juyowa yayi yabfuskance ta gaba daya "Ina zaki bini hafsat?"
"Inda zakaje mana"
"Ba inda zani fa, gidan zainab zanje na kwana,kishiyarki" tafi minti uku tana kallanshi, juyawa yayi ze fita ta riqe masa hannu again "Bazan iya kwana anan ni kadai ba,tsoro nakeji" murmushi yayi
"Ni ban aureki danna tayaki kwana ba hajiya,ko mun rubuta haka acikin agreement namu?" gaba ki daya tsoro ne ya taso mata ta kalleshi sosai tace cikin dakiya idanta yayi ja sosai amma batasan tayi kuka "Na tuna kuwa babu wannan acikin rubutaccen auren mu,na manta bayan signing takardar yarjejeniya da mukayi ta aure,wurin daurin auren ma mun rubuta cewar kalar auren namu na dabanne ba wanda musulunci ya tsara ba,Kaje amma karka qara kawomun komai daya shafi rayuwar aure,idan bazamu kwana a tare ba babu wani abu dazakamun na aure,na yarda haka tsarin namu auren yake,kaje plss" tafad'a tana me d'addage hannayenta duka biyu alamar naci ka fam, matsowa yayi daf da ita ya sanya hannunsa asaman waist nata yamatse ta sosai da jikinsa yace "Ni kike gayawa magana hafsa? Sabida kin samu sake ko? Yanzu ma idanta ta dago sukayi kaura dana juna tace cikin jin haushin sa
"So nake muyi sighning wani yarjejeniya kanka tafi" sakinta yayi yace yana murmushi muje gayamun wane iri ne?" zama sukayi a kujerun parlor tace
"Sona ke mu kwana a roof daya,muci abinci atare,mu sake wa juna soyayya,mu aminta mudin masoya ne,idan har akayi watanni shida kaci cewar baka buqatar tarawa dani,kuma bakaji sona ko daya a ranka ba,to ka rabu dani,kuma tsakani da Allah zamuyi" kallonta yayi ya kwashe da dariya ya sani yanajin tausayinta amma sam baya santa wlhy, yakuma san baze taba san taba,da wannan ya aminta suka rubuta suka ajiye.....
Hafsat ta kuma yin wauta a karo na biyu,yaya kuke zanin wannan zaman? Ze dore kuwa?" anya hafsat bata kirawa kanta zawarci na biyu ba bayan shaam ya aure fara me gashi abinshi? Muje zuwa dai.....
Votes pls
[2/13, 9:28 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
27
Muhammad a d'akinsa ya kwana yayinda hafsa ta kwana a nata d'akin,wata hatsabibiyar rigar bacci ta saka iya cinya,da saninta ta cire bra,pant kawai ne ajikinta se wannan rigar,sumar kanta datasha gyara ta gama barbajewa har saman goshinta daga bed room nata tafito zuwa kitchen,a parlor ta hangoshi zaune duk da zuciyarta takad'a qirjinta se dokawa yakeyi amma haka ta daure,tasani idan bata koyawa kanta rashin tsoron shiba akwai matsala,kallon ta yayi sosai ya raya aranshi so take taja ra'ayinshi wanda baze tab'a faruwa ba har gaban abada, bata ko kalli inda yake ba tayi gaba abinta zuwa kitchen,d'an guntun tsaki yaja ya mayarda dubanshi zuwaga film dayake kalla, Ha d'adden break fast tabshirya musu,finger sandwichs da chocolate sandwich,se kuma coffee amor da vegetable potatoe, tun yana daure wa har qamshin yasoma jan hankalinsa,ogar bata baro ktchn ba sanda ta hada samosa, jere komai tayi a fankacecen dining table,ta bude dining shelf ta baje komai da komai da ake buqata,bata wani kalleshiba sabida sam ma yi tayi tamkar bata kula dashi ba,dakinta ta wuce tasha wanka da wata doguwar rigar dress maroon color ta tufke gashin kanta da farin ribon,se flat shoe data saka shima fari qal, har tsakiyar falon ta sameshi kusa dashi sosai ta zauna ta kalleshi dauke da fara'a sosai a fuskarta,tana bude bakinta qamshi alawar datakesha ya daki hancin sa dauke kanshi yayi gefe d'aya
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.