Complete Hausa Novels

Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 24 of 44

Tunda haleema taji zancen auren hafsat da say zeyi seta tashi hankalinta ta sani sarai boka ya sanar mata ba ita ba haihuwa har abada sannan kuma gashi yanzu sam asiri ya dena tasiri akan sa,bokansu ya sanar musu sun sanar mata cewar lallai ya riqe addininsa yafi karfinsu ko kusantar sa ma gaba daya bazasu iyaba, wurin ummansu taje ta zayyane mata komai atake kuwa aka shirya cewan ayi airin akan hafsat gaba daya tunda itace banza.....hmmmmm

Say yana zaune tare da hafsat suna hira muhammad ya shigo cikeda taqama yaud'inma acikin shigarsa ta shadda fara amma ba babbar riga bace, yau dinkine dai na zamani me kyau komai nasa fari,hannu ya miqa masa suka gaisa sannan ya mayarda dubansa akan hafsat da alokaci daya qirjinta ya soma dokawa

"Hafsat ya jikin ki?" kallon sa tayi tace

"Naji sauqi Alhamdulillah" shiru sukayi dukansu su uku can muhammad yace "Ke baki iya gaisuwa bane,ko bakisan girman manya bane?" idon tane ya ciciko sannan tace

"Kayi hakuri yaa muhammad" dan guntun tsaki yaja sannan yace

"Mesa zakiyi karyan bakya gani kuma bayan sarai idanki lapiyanshi qalau,bayan yanzu gashinan kina kallo na kuma kallo daya na miki na tabbatar kina gani kema kuma kina kallo na ido cikin ido duk sanda nayi magana" shiru tayi yayinda say ya miqe tsaye yace

"Amma yallabai anya bakayi shishigi da yawa ba kuwa,baka ganin cewar mu doctors mune mukeda haqqin komai nata bawai kaiba,kuma mun tabbatar cewar idan nata bashida lapiya kai miye naka aciki? Kuma idan taimakonta zakayi mu bawai mun kasa bane ka barshi kawai mune family nata zamu mata komai ma har fita wajen" shiru ne ya ratsa wurin dukkansu sun bata dakiku suna kallon juna kafin muhammad yace

"mesa arayuwa zaka kalli girma na kace zaka kirb'a mun k'arya,zanyi magana a d'aga licence dinka na zama likita idan dai har tsabar hauka wannan idan ne zaka ce baya gani" jin ankira hauka ya sanya say ya dago da fuskarsa gaba daya cikeda fusata

"Kai waye? Mekake taqama dashi? Me kuma kakejin ka isa kayi da zaka kalli tsabar idona kace dani mahaukaci,dakake iqirarin cewar zaka sanya akarbe license dina mesa kai bazaka qwace ba idan ka isa,tunda nake ganin mahaukata bantaba ganin mara hankali irin kaba,tayaya zaka kalli idan mutum kace masa mahaukaci beside waye ma ya baka damar yi mana iko anan?" wani murmushin qasaita yayi sannan ya shafi gemunsa yace

"Ba license d'inka ba har abu mafi muhimmanci arayuwarka zan iya kwace wa shine rayuwarka,kuma wlhy kaf fadin Nigeria ba wanda ya isa yamun komai,kuma zaka gani wlhy,ke kuma karna dawo asibitin baki gayawa doctors masu hankali kina gani dakyau ba" yana gama fad'ar hakan ya juya ya fita hafsat ta kasa koda motsi dakyar ta hadiye wasu yawu sannan ta furta

"kayi hakuri uncle say ka rabu dashi,wannan mutumin na tsaneshi wlhy" matsowa yayi kusa da ita yace "Mesa nakejin matukar tsoro da yawaitar fad'uwar gaba hafsat? Gabaki daya banjin dadin tawa rayuwar sekace nine nake ciwo,wlhy hafsat hankalina baya kwance,bawai wannan muhammad dinba da kalamansa aa, komai ma senake ga kamar mutuwa zanyi ayanda nakejin duniyar tanamun qunci" zare idanta tayi waje

"Haba Uncle sayyeed? Ya kake magana haka? Inshaa Allah atare zamu rayu babu abunda ze sameka,kuma inshaa Allah atare zamu mutu" murmushi ya sakar mata yace

"Zanje gida na dawo nanba jimawa inshaa Allah" batayi magana ba haka yaja kofar ya fita, ita dinma dai haka kawai takejin tsananin faduwar gaba me tsanani,hankalinta sam baya jikinta,koda momy tazo bayan isha abinci kurin tabata sukayi sallah seta kwanta,say yazo sun dan taba hira,wuraren karfe tara yamata sallama akan seda safe ze dawo,har kuma ze fita ya dawo ya kalketa yace

"Hafsat idan har Allah yasanya wani abun yafaru dani kimin adu'a ita kadaice nake buqata agareki" kura masa ido tayi dukta rude murya na rawa ta furta

" mesa kake irin wannan tunanin wai? Sabida kawai wannan muhammad din yayi wannan furucin seka damu,inshaa Allah ba abunda ze iya yi maka" murmushi ya sakar mata

"Hafsa nafasan waye muhammad,sam yayi furucin dayayi ne sabida kawai ransa ya b'aci amma mutum ne me nagarta sosai,matsalar sa d'aya kafirar zuciya da rashin human relation amma hes a nice person" shiru ta masa kawai amma bawai danta yarda ba,tanaso ta tsani muhammad dinnan amma zuciyarta taqi aminta da tsanar tasan......

Wuraren sha dayan dare unle say ya dawo wurin hafsat,zama yayi kusa da ita yamata a dua lokacin tamayi bacci sannan ya kashe fitilar dakin ya fito ganin ko momy bacci ya kwashe ta batare data kashe fitilar ba,yana barin dakin ya kula da mutumin daya wuce part din fuskarsa a rufe da mask se suaune kansa yakeyi,harya wuce kuma seyakasa nutsuwa ya dawo baya gaba daya,binsa yayi yaga lallai dakin ya dosa,ya murda sad'af sad'af ya shige aikam say da sauri ya biyo bayansa shima yafada dakin,ganin yayi mutumin ya dauki filo ya danne fuskar hafsa se shura kafa takeyi acikin duhun dakin,kuka kura yayi yayi kanshi aikam fada ya kaure har suka tashi momy,da sauri ta haska torch light dinta tana ganin haka ta kunna fitilar dakin kokawa suke sosai da sauri ta kwallah kara,amma kan wani ya farga kasancewar darene har mutuminnan ya daga wuqa ya cakawa uncle say a qahon zuci har wurare biyu......ko kafin mutane su zo wancan mutumin ya gudu,hafsat ma ta farka tuni sakkowa tayi tama manta zancen karaya,sayyeed kuwa tuni rayuwa tayi halinta,se kuka takeyi tamkar ranta ze fita a haka doctors dake nan sukaxo,kowa se hawaye yakeyi ana fadar mutuwarsa ....

Mom nuaiym
[2/9, 8:55 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

23

Ba shakka hafsat ta gama haukacewa da mutuwar uncle say,tsakani da Allah tanki tana gani aka fita da gawarsa wanda ko ba'a gaya mata ba ta tabbatar wlhy ya mutu,ko dan ganin jinin daya zuba ajikinsa, kasa zama tayi asibiti dole aka wuce da ita gidansu.......tunda hafsa taje gida take kuka ba qaqqautawa shi kanshi shaam din ya girgiza da mutuwar sayyeed,musamman da yake ko a dakin da hafsat take aka kashe shi,kuma ita bata gane wanda ya danne mata fuska ba da filo,kasancewar acikin dubu ne farkawar momy ne ta ga sayyeed.....

Da yamma yan sanda sukazo gunsu da tambayoyi kallon ta sukayi bayan ta momy ta gama fadar iya abunda ta sani suka ce da hafsat

"Hafsat dukda yake munsha mamakin ance kinada matsalar ido,amma se gashi faruwar abinnan idon naki ya bude,muna san sanin shin sanda abun ya faru kina ganine? Ko kuma aa bayan faruwar abun kika soma gani" kallon dan sandan tayi gaba daya gani tayi ya gama raina mata idan dai har karatun datayi na lauya harta zama qwararriya ba shirme bane a yanda ta fahimci kalamansa zarkin nasa akanta ya fara shi

"Tun ranar danayi a hatsari na farfado komai ina ganinsa lapiya lau" gyaran zamansa yayi ya kalleta sannan yace

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.