Complete Hausa Novels

Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 39 of 44

"yaa muhammad kayi hakuri,wannan da zafi wasan yafi dadi" kallonta yayi dukda sunkashe fitilar yankwantar da murya ya rungumota jikinshi sosai "Hafsat wannan shine auren ai,kuma bazan miki da zafi ba i promise,wancen ma bansan baki saba bane dana miki sannu, idan kika saki jikinki bazakiji zafi ba sam" batace komai ba ya koma samanta a hankali, bazatace bataji zafiba kamar yanda bazatace bata ji dadi ba wanda babu irinshi kuwa wannan karon seda yagama taji zafi kad'an,Kallonta yayi bayan ya kunna fitilar wayarshi yace

"Hafsa Allah ya barmun ke kinji,ni'imomin jikinki na dabanne,Allah ya qara miki dad'i" batace komai ba se "Zansha ruwa yaa muhammad" ruwan ya bata sannan ya dauketa zuwa bathroom.

Mom Nu'aiym
[2/21, 9:02 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

33

Washe gari kuwa haka suka tashi cikeda gajiyan tafiya,duk motsi daya da hafsat zatayi kuwa idan J.A na kanta,break fast ma dankanshi ya zauna ya feeding nata seda tayi dam abinta,sannan ya kalleta yace

"Banasanki da yawan wahala hafsat,wannan ya sanya nazo dake nan garin sabida ki huta na kula bakya san zama gu daya" kallonshi tayi da fara'a

"Amma da gaske zamu dade anan?" murmushi yayi "Ba wani dadewa dazamuyi nanda kwana biyu zamuje abj,daganan kuma muyi kwanaki biyar se mu wuce lagos bayan sati daya mu wuce london" zaro idanta tayi waje

"Da gaske yaa muhammad,to kuma zancen kayan sawa fa? Tsaki yaja cikin tsokana yace "'yar qauye siya zamuyi sekace sanda mukazo duniya da kaya mukazo, har dubai zamuje yawo" turo bakinta tayi

"Allah ni ba yar kauye bane kuma bazan maje dakai ba,ni skt zan koma abuna" murmushi yayi

"kina burgeni hafsat,rigimanki sam baya qarewa wlhy,wasa nake aike ba er qauye bace yar birni ce,kiyi hakuri muje tare kinji" shagwab'e fuska tayi

"Zakamun doki?" waro idanshi yayi waje "Lallai ma hafsatuwalle,doki fa?" shura qafa ta soma yi "Allah ni doki nake so kamun kuma idan baka mun ba bazan ma qara cin abunci ba" Duqawa yayi irin na yara da sauri ta dare ya dinga zagaye d'akin suna qyalqyale dariya atare......

*London soyayya me tsafta suke gabatarwa batare da kowa yasan cewan san d'an uwansa yake ba,shaquwa kuma me tsananin gaske ta shige tsakaninsu bazaka tab'a tunanin cewar ba auren soyayya bane sukayi, hafsat tana samun tsananin kulawa a wurin muhammad....

Wani yammaci hafsa ta siyo samosa da kanta tazo ta zauna kusa da muhammad,kallonta yayi duk tayi wani b'ulb'ul tayi ja se sheqi takeyi yace

"'yar lukuta sammun samosar ko?" kallonshi ta dago tayi da yake yana kan kujera ita kuwa a saman carpet ta baje "Bazan sammaka bafa,baka gaba abunda kamun ai cewa kayi bazaka raka niba" banza ya mata ta zauna ta cinye samosar tas,aikam kan kace meye wannan harta soma kwarara uban amai tun tana iya tashi har yakai ta kasa,tsoro me tsanani ya kama muhammad,dakyar aman ya tsagaita taje d'aki ta kwanta se numfarfashi take da k'yar seda dare ta samun kanta,haka ya kwana yana jinyar ta,washe gari kuwa asuban fari tace ita agida zatayi samosa taci,ba yanda beyi ba ta kafe dole ya sa mata ido,aikam shima tana gama ci shima se amai,daga nanfa hafsat komai taci se amai lokaci daya dukta rame tayi baqi, muhammad dai daya gaji kaita asibiti yayi gwajin farko aka tabbatar masa ciki ne da ita watanninsa uku,a yanayin irgawarsa kuwa tun tarawarsu ta farko ta samu cikin,sabida yanzu kusan watansu biyu da sati biyu basa skt,kuma kwana biyu da tarawarsu suka bar qasar,wani irin farin cikine mara misaltuwa ya ziyar cesa seya tuna da maganar zee zee

"J.A aurenka qaddara ne,cikin Nu'aiym ma qaddara ne,bazan qara haihuwa dakai ba wlhy,jiran ka nake ka sakeni in koma in auri masoyina na haqiqa abin qaunata,shina shiryawa zama uban yarana ba kai ba,wlhy na tsaneka J.A koda baka sakeni ba sena lalata mahaifata bazan qara haihuwaba kuma bazan kula ma da nuaiym ba kaje da yaronka" qwallan daya gangaro masa ya share yayi murmushi,koda sukaje gida dagata sama yayi cak yana ihun murna,kallonshi kawai takeyi sabida bata san meke faruwa ba,hasalima haushi ya bata batada lapiya yana wani ihun murna

"Hafsa na kin gamamun komai,na dade ina san in qara haifar yaro jinina,ina san yara Allah beyiba se yanzu wlhy kin gamamun komai kece hasken rayuwata,na gode Allah dakika zamto part of my life" kallon sosai ta masa tace "yaa muhammad meya faru?"

"ur pregnant my hafcy,and im so happy,i so much love my unborn baby" "ciki kuma" ta nanata a sarari,nida nake period kuma ka sani zakace ciki" a rude ya kira doctor akace su dawo,dubawa akayi haka nata tsarin yazo aka barta akan magunguna suka juya gida.....

*Nigeria*

Tunda suka dawo muhammad ya tare a part din hafsa,se rawar qafa yakeyi,motsi daya biyu seya furta "I love my unborn child,mamakinsa hafsa kullum cikin yinshi take wato dai da gaske yaa muhammad baze tab'a santa ba,ita haka zata qare duk mazan data aura basa santa,wannan mugum shuraim tsabar mugunta ya kashe mata uncle say,kullum yanzu setayi kukan rashin uncle say,dukkuwa da yake muhammad na matuqar kulawa da ita....

*Bayan watanni shida cur da auren muhammad da hafsat*

Da safe muhammad na tashi yaga hafsat gaba daya ta fito da akwatunanta ta jere ko saman mirror dinta ba komai ta kwashe komai, kallon mamaki ya mata

"Hafsat lafiya dai?" murmushi ta sakar masa

"kacika mantuwa yaa muhammad,yaufa watanni shida cur da auren mu" mamakin aane ya qaru yace

"To shine me hafsat?" juyowa tayi da kallon raini,da cikinta daya rigada ya fito tace "Gadai takar danmu nan na agreement,lokaci ya cika watanni shida,kuma indai ba neman magana zan tsaya yiba meye ze kaini kuma zaman dole,tunda har yau bakaji kana sona ba,kuma baka tab'a furtawa ba,kaga dama alqawari na maka cewar idan wata shida ta cika bakaji kana sona ba kuma baka furta ba,zan sake maka mararka kayi fitsari gidanmu zanje ka sauwaqe mun" wata iska me zafi yaja ya kuma fesar sannan ya dafe kanshi ya miqe yazo kusa da ita ya dafa kafadarta

"Haba hafsat,yanzu ke dama da gaske kike wannan maganar" dago itanta tayi ta saka acikin nashi.."Da ana wasa da agreement da akayi arubuce har akayi sign ajiki? Kokai sanda mukayi na aure dakai ka manta ne,kalleni muhammad wlhy bari kaji inna zauna dakai baka sona shegiya nake,yaronka dakake tafadar kanaso kuma rabone,inshaa Allah zan baka abunka ina haihuwa so ka aikomun takardana danni yanzu gidanmu zani.

Mom nuaiym
[2/22, 9:11 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                             34

Qura mata muhammad yayi gama daya ta gama rud'ar dashi,kanshi se wani juya masa yakeyi yama kasan cewa komai
"Nace ka sallameni malam nikan hanya nake nakuma rigada na shirya" zuwa yayi gabanta yana kallonta kallo daya zaka masa ka gano cewar hankalinsa baya jikinsa

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.