Complete Hausa Novels

Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 16 of 44

" Shaammaz kaji qanwarka ta samu gurbin karatu a india,tana can mumbai tana sha'ani abinta banji ka sanya albarka ba" Dan tab'e baki yayi sannan yace "ni anawa tsarin banason banso yarinya taje wani qasar karatu,kawai dai ina mata fatan alkhairi,banza kowa ya masa aka ci gaba da hira,shi dama abba baya amsa koda gaisuwarsa ne......

Kwance hafsat take tana karatu Dr.say ya kirata, "Uncle say ina wuni" kwaikwayar maganarta yayi sannan yace "Duk wannan ladabun baze hanani zazzanekiba,an gayamun bakyashan magani mesa haka?" shagwab'ewa tayi

"Allah ni uncle say ka yarda dani ina shan magani,sameera fa qarya takemun"

"Naji amma mesa bakya shansa akan tsari,Allah idan kukayi hutu punishment dinki shine bazakizo Nigeria ba" kukan shagwaba ta saka masa dakyar ya hakura sannan sukayi sallama....

Mom Nu'aiym
[1/25, 8:54 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                 
*wannan shafin nakine kyauta Ta ma'aiki,inajin dadin comment naki Allah yabar zumunci*

15
Tun bayanda su hafsat sukaji labarin auren uncle say sataji gaba d'aya duniyar ta mata qunci tayaya ma uncle say ze hanata zuwa hutu,ace bikinshi sukutum wai bada ita za'ayi yishiba,gaskia abu beyi ba kam wannan ya sanya taketa fushi dashi,shi kuwa ya kafe akan bazata zoba wanda wannan umarni ne na abba haris,bayaso ya hanata da kanshi amma sam bayaso tazo ta sake tada hankalinta akan shammaz gashi ance su kula sabida matsalar ta na heart,haka akayi bikin tanata qunci batazo ba,gashi su sumayya da suhaila duk sun tafi itada da khairii ne kawai shekara d'aya kenan rabonsu da gidan.......

*Bayan shekara Biyu*

*Takun saqa*

Ba kad'an ba hafsat kejin dad'i zatazo hutu Nigeria bayan shekaru biyu cur datayi harma da yan watanni bata Nigeria,tsakanin itada khairii bazakace wa yafi wani zumud'i ba,koda jirginsu ya sauka hafsat ji takeyi tamkar ta bangaje dukkanin mutanen dake tafiyar yangarnan ta sauko,sabida ba qaramun missing gida tayiba, A yangace yangar dabata san sanda ta koyeshiba take tafiya,ba shakka wanda yasan waccen siririyar hafsat kamar ka busata ta fadi baze yarda cewar wannan data tara mula mulan abun zama da iyayen heeps tare da doka dokan breast cewa itace hafsat d'in daba,sanye take da straight skirt na roba light blue da top red wacce ta d'ameta takuma bayya no ainahin surar da Allah ya mata,ga wani tsukakken flat tommy da bazaka tab'a yadda cewar mamallakiyar wannan booties ne dashiba,tamkar arayuwa ba'a saka masa komai aciki,sanye a idonta dan qareren qaton shade ne me kyau,a saman kanta sirirn fayafine ta yane kanta dashi,tun daga kan goshinta har girar idonta gargasa ne baqae wuluk se sheqi sukeyi,lallai hafsat tayi kyau, takuma qara girma side bag ce me kyau kalar ja rataye a kafad'arta yayinda a k'afarta take sanye da wages blue masu kayu matuqa, khairii ma irin shiga d'aya sukayi kalace kawai ta banbata domin kuwa ita pink and white tayi,sunyi kyau matuka,Abba haris suka fara hangowa inda basuyi qasa a gwiba suka zarce wurinsu suka rungume shi suna murna,

"Abba kai kad'ai kazo ina su momy?" hafsat ta tambaya cikeda k'osawa,murmushi yayi yace "Nine nace kowa ya zauna ba wanda zw biyoni duk suna gidana ku kadai ake jira yau daddy ma na gayyata can sabida yara nema zasu dawo" murmushi tayi sukayi gaba abunsu zuwa mota.......murna sosai akayi domin zuwansu anyi girke girke na masifa masu matukar qayatarwa da dai hafsat nak tayi kasancewar ta jima rabon dataci abuncin gida,su momy suka wuce ita kuwa tace bazata ba se gobe,da dare bayan sun huta wayanta ya soma ya ringing tana dubawa taga sunan uncle say,qin d'agawa tayi gaba d'aya ta turo baki tamkar zatayi kuka kuma kamar yana ganinta,kallonta khaiirii tayi "Uncle say nefa ki d'aga mana" harara ta wurgo mata sannannta tsiyayar da hawayen datake ta faman tarewa "Bazan d'agaba ai cewa yayi dani shine ze dakkomu daga airport shine be zoba kuma na kirasa yama kashe wayan" murmushi kawai khairi tayi indai fad'ane dama tasaba ganin sunayi batanan sanda suke shiryawa abunsu....

Washe gari yamma liqis hafsat tace da driver ya ajiyeta gunsu momynta,haka ta shirya ta wuce yauma kalar dressing na jiya tayi sedai wannan karon lemon green and orange tayi ga alama wannan dressing shine d'abi'ar ta yanzu,a baking katafaren gate d'in gidan tace driver ya ajiyeta yayi tafiyarsa,ba komai a hannunta se wayarta kirar iphone 7 da side bag lemon green dake rataye a kafad'arta,koda ta shigo gate d'in gidan wayarta take dannawa,acikin qatoton madubin idon dake idonta,murmushi takeyi har fararen haqoranta suka bayyana ganin khairii na mata iya shege kan whatssapp akan tafiyanta gida, jitayi ance

"Hafsat ce" D'agowa tayi fuska a had'e jin muryar me mata magana tana taunar cingam dake bakinta,batace dashi kanzil ba ta wuce taci gaba da tafiya abunta,mamakinta ne ya kama shaam ganin abunda ta masa,se wani yanga takeyi yayinda duk taku d'aya se yalwataccen qugunta yayi magana,ko kallon inda yake bata qara yiba tayi gaba,sosai tabashi mamaki ya had'iye wani yawu me d'aci a rayuwarshi yace "Lallai idan kika zomun da raini sekin gane kuskurenki" ...

A parlor ta tsaya suna gaggai sawa dasu momy da daddy,daddy kallonta yayi "Lallai kulelen daddy girma yazo miki kinga yanda kika dawo kuwa,kuma yanzu naga ba rigima" murmushi kawai tayi batace komai ba, shine ya kuma cewa "Banga jakar kayankiba na zata zakizo gidane ai" sosai kanta tayi tace "Daddy nan gidan ba kowa ni gobe zan koma Allah kuwan"

"Ni bazan takurakiba kulele so karki damu kinji" Miqewa da zummar zuwa kitchen ta hadaw onion samosa da ta zame mata jiki,kullum setaci ko a can dama abuncin suce,kan taje ko ina sega yaa shaam ya shigo ko kallonshi batayi kuma kowa ya kula da hakan shi kuwa ya qurawa yalwataccen gashinta ido harta b'acewa ganinsa,zama yayi kusa da daddy cikeda fusata yace "Daddy kagan kuwa hafsat wulakancin datamun ko gaisawa mafa batayi daniba ko kallona ma batayiba" murmushi daddy yayi yace "kayi hakuri zan mata magana,wataqil fushi takeyi dakai har yanzu" bece kanzil ba harta dawo d'auke da plate dinta na onions samasas ta zauna kusa da momy

"Mommy zakiji samosar albasa zallah,da dad'i wlhy" kallonta momy tayi ta d'an b'ata fuska "Hafsat mesa baki gaida yayan kiba,ko baki ganshi bane?" cikeda rashin kulawa tace "A a momy waye kuma yayan nawa naban gaidaba,nina gaisa da duk wani jinina dama wanda ba jinina ba a gidannan kumafa kina kallo"

"yayanki shammaz nake magana,hafsat" d'an tab'e baki tayi ta yamutsa fuska "Hmmm lallai ma mommy,bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane,ina nayi matsayin dazan gayarda d'anku,kuma ni wlhy Allah ya kiyaye ya zama yayana" mamakin kalamanta kowa keyi daddy yace cikin fushi "Hafsat kinad hankali kuwa,a gabanmu kike fad'ar wai shammaz ba yayanki bane" turo baki tayi ta soma hawaye sannan ta miqe ta tattare mayafinta ta yane kanta ta wurga wayarta ajaka ta shuri takalminta,wlhy indai kukace zakuna takurani akan gaida wannan wlhy bazan qara zuwa muku ba,ku tambayeshi mana yaya mukayi dashi,ai mun raba duk wata alaqa tsakanina dashi to meye kuwa ruwansa dani" tana kaiwa nan tafito daga main parlor d'n tana kuka, Ganin Uncle say a tsaye jikin motarshi ya sanya ta qara turo baki takuma qara sautin kukan datake har tana doka kafarta a qasa,da sauri yazo kusa da ita

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.