Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 28 of 44
"Yanzu sanar dani me dame kike buqata,bazakiyi shagalin biki ba,ni zanyi dinner da reception sabida yanzu ne zanyi auren soyayya na kuma zab'ina" kallon shi tayi tana kuka tace
"yaa muhammad dan Allah kayi hakuri" dagowa yayi a karo na farko "Hakurin me kike bani" kukan ta ne ya tsananta ta dukar da kanta taci gaba da yi,tafi minti talatin tana kuka amma bece da ita komai ba seda dan kanta tayi shiru,kanta ne ya soma sara mata ta bud'e mitar da nufin wucewa cikin gida yace cikin izzah
"Nine nace dake na gaji dajin wannan zazzaqar waqar da kika sakani agaba kina reramun? Maza dawo kici gaba dayi harse ya isheni" kallonshi tayi cikeda mamaki idanta ya kad'a yayi jajir,yakuma cewa
"Dawo mana nace ki rufe murfin" a hankali ta sako kafafunta ciki batare da tayi magana ba
"Kalli idanki hafsat,duk yayi ja sabida bakyajin magana,nace dake kukan na menene amma kinki ji,kin zauna kina kuka sekace wacce ke rero waqa,idan ba so kike na sassab'a miki ba karna kuma ganin hawayenki wlhy,sanar dani yanzu tsakanin ki da Allah menene kikewa kukan?" sadda kanta tayi kasa tace "Auren ne bana so" kallonta yayi ya sakar mata murmushi
"Banida maganin wannan gaskia,so kiyita kukan,shika d'aine damuwar kodai da wata bayan wannan?" sadda kanta tai a qasa tace
"So nakeyi ka tausayawa rayuwa ta ka agazamun ka bar aurennan har nan da wata biyu na roqe ka yaa muhammad dan Allah" kura mata ido yayi na yan dakiku kan yace
"sekin mun alqawari guda biyu,tsakaninki da Allah" kallonshi tayi amma batace dashi komai ba yace
"Na farko sekinmun alqawarin bazaki taba kawo matsala me kamada kin fasa auren ba idan na qara miki lokaci,na biyu kuma sekin mun alqawarin bazaki sakeyin kukannan agaba naba sabida gaskia banaso yana batan rai" yawu ta had'iya tace
"Abba haris ya sanar dani muhimmancin Alqwari sabida haka bazan taba fasa auren kaba,sedai idan kaine kace ka fasa,kukan ma zan kwatanta" gyada kanshi yayi yace
"Nima ai alqawarin auren ki nayi,idan ko bazaki karya ba ni mezesa na karya, nasan muhimmancin alqawari ai,kije na yadda nanda watanni uku idan munada rayuwa se ayi auren" godiya ta masa ya tsare ta akan setayi dariya seda tayi dariyar kuwa sannan suka rabu,se dadi takeji......
Shaam ba kad'an ba yake jin yana san baby,sedai be sanar da kowa zancen ba se daddy kasance war shi abba haris har wannan lokacin fushi yake dashi,sedama hafsa ta saka baki yake dan sake masa kadan,cikin sirri kuwa aka shirya auren sa da baby tare da nasu hafsa,sam haleemah batasan wainar da ake toyawa ba,tunda taji hafsa zata auri wani shikenan hankalinta ya kwanta......
Hafsa gabaki daya ta rame tayi baqi,sam wani jarababben tsoron muhammad takeyi gashi abu mafi ban mamaki shine tunda ya tafi akan ya dage zancen aurensu be qara zuwa wurin taba kuma gabki daya ya dena kiranta,ita kuma duk sanda tayi yunqurin kiransa se gabanta ya fad'i, huda ce ta fad'o mata arai ta d'auki wayar ta kirata,komai da ake ciki ta sanar mata,hudan kuwa ta bata shawaran akan lallai ta kirasa,kuma ta basa kulawa as if tana matukar sanshi,wasan da yake so su buga idan ba ta wannan hanyarr ta biyo masa ba lallai akwai matsala,sabida ya shirya daukar fan sane,sosai tayi wa huda godiya koda sun dade basu hadu ba amma sosai suke hurda,huda yanzu tana germany itada mijinta.
Cikin sanyin jiki kuwa tayi kiransa a waya,kamar baze daga bama,se can taji muryarsa me saukar mata da fad'uwar gaba yace
"Hello" sanda ta d'anyi jimm sannan tace "Yaa muhammad Barka da yamma" gyaran murya yayi yace
"Barka dai" a ta k'aice,jikinta ne ya qarayin sanyi tace "Dafatar kana lafiya"
"Ina lafiya" itace amsar daya bata,runtse idonta tayi sannan ta kara budewa tace
"Yaa muhammad ka gane me magana kuwa" kamar baze amsata ba yace
"Na gane mana ba hafsa bace?"
"Ea nice ya kwana biyu?" tafad'a cikeda jin zafin wulakancin data janyowa kanta
"Lafiya lau,ya akayi ne?" dafe kanta tayi dayake barazanar rabe wa gida biyu tace
"Dama naga kusan watanni biyu ban jika ba,shine nace Allah ya sanya lafiya"
"Lafiya lau mana,me zan miki to? Ina auren Agreement ne zamuyi,sekace wata soyayya ke tsakaninmu dazanta damunki,kokuma daze kasance komai nawa sekin sani?" kasa hakuri tayi tace
"Koda na kirak bakaji na ambaci soyayya ba ai,danni a wannan zamanin banajin ma akwai soyayya,kurin dai kamata ya sanya nayi kiranka sabida ni nasanta" sarai ya sani magana ta gaya masa,amma seya dake yace
"Ni ai tun farko na sanar dake yanzu ne zanyi auren soyayah, kuma zab'ina bakijiba ne,kece bakya sona so meye zesanya na nanuqe miki?" jan dogon numfashi tayi sannan ta furzar da wani iska me zafi tace cikin wata rikitacciyar murya
"Yaa muhammad" shiru ya mata tace "Why?" cikin dakakkiyar murya yace
"Hafsatu manga yar sarki wacce maza ke rarrashi,koba haka taken yake ba?" ganin ze raina mata hankali ya sanya tankashe wayar ta ajiye,be kuma kiraba se qarar shigowar message taji a wayarta kamar haka
"This should the very first and last time dazaki ajiye mun waya,koda mun gama magana kuwa lallai nine zan zama na farko da zan ajiye" jikintane ya qara macewa jin kalamansa ta daga waya takuma kiransa yana d'agaba tace dashi
"Yaa muhammad kayi hakuri" cikin sanyin murya yace "wuyarta ka bani hakuri kai tsaye za'a wuce wurin,dama gobe zanzo zancen kayan lefenki ki shirya zuwa dubai"
"To Allah ya kara girma na gode sosai"
"Se anjima" shine abunda ya fada a zatonta ya ajiye wayar ashe be kashe ba,ajiye tata wayar tayi ta sanya hannunta a kirjinta ta shiga rero kuka tana sambatu ta shiga uku,ita dai batayi sa'an zuwanta duniya yazatyi da masifan yaa muhammad,tunda tasan hankalinta take kwasar bakin cikin d'a miji,da karfi ta furta
"Allah na tuba ka yafeni,Allah idan na aikata wani laifin ake jarabtana da wannan masifun Allah na tuba ka yafeni,kuma ka bani ikon cinye jarawar nan daka dauramun" kuka take sosai,muhammad dake saurarenta ma dafe kanshi yayi,ba abunda ke hanashi zuwa gun hafsa illah wannan kukan nata,ya tsani kukan ta masifaffen tausayinta yakeji,shidai bazece yana santa ba kuma bawai wata manufa ta cutar da ita yake da itaba kurun dai tausayinta yakeji yana gani kamar lallai idan ta auri wani zatasha wuya ne,tunda kuwa ya binciki tarihin rayuwar ta kaf,ya sani sarai dabe biyo mata ta wannan hanyar ba,shaam zata komawa kuma matar sa ma masiface a wurinta,kwanciya yayi ya runtse idansa yana mejin zafin zubar hawayenta.....
Menen ra'ayoyinku game da auren hafsat da muhammad? Ina tsumayin jin comments naku.
Vote plss
Mom Nu'aiym ca
[2/12, 8:21 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
26
Washe gari da yamma hafsat tana kwance mero ta shigo tace da ita
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.