Complete Hausa Novels

Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 44

"Hafsat yaa shaam kuma? So? So naji kina ambata,shine zaki bari san dan uwanki ya hallakaki har haka? Kinga kuwa yanda kika dawo sekace ba poojah kulelen daddy ba? Meyasa zakiyi shiru kibar abu aranki bayan kuma kinada gatan da za'a miki abinda kikeso?" tana kuka ta kasa magana dakyar khairrii ta rarrasheta tayi shiru sannan ta kalleta tace

"Anya khairiyyah yaa shaam ze tab'a sona kuwa? Baze taba sona ba shekaru biyu kenan da yasan i a sanshi amma banda tsana ba abunda yake qara nunamun kullum,ina kyautata zaton a duk fadin duniyarnan a zuciyar yaa shaam wanda ya tsana ni kebin shedan,nikuwa bansan mesaba nayi rashin sa'an zuwana duniya wlhy inaga san yaa shaam ne zeyi ajalina amma dan Allah karki sanarwa kowa kinji?" hannunta ta kama tace

"Wlhy bazan barki cikin azaba bayan inada maganinta,wlhy sena gayawa Abba gobe da safe tayaya poojah?? Tayaya san dan uwanki ze illataki bayan kinada gatanki? Ni gaskiya sena fad'a" kwanciya tayi ajikin khairiyya tama kasa magana......washe gari khairii ko breakfast batayiba taje ta kwashe komai ta sanarwa Abba,aikam ya hau bambami yace

"Amma shine kulelen tayi shiru,shekaru biyu tun lokacin aurenshi fa kenan,lallai wannan yarinyar tasha wahala wlhy bazata sab'uba dole dan ubanshi seya aureta shi kuwa kodan halaccin ubanta akanshi,maza tashi kije anjima zan nemeku" tana barin wurin ya daga waya ya kira yayanshi da shaam akan zezo gidan ya samesu akwai magana,da khairii da Hafsat dakuma umman su khairri aka je.....bayan an gaggaisa ya kalki yayan nashi yace

"Yaya wannan ramar da damuwar da hafsat ke kici duk akan tanasan yayanta ne shaam aurenshi take sanyi ni kuwa na yanke hukuncin ayi auren tunda yanada halin yin hakan" tamkar saukar aradu haka yaa shaam yaji wani maganar da sauri ya d'ago ya kalli abba haris,daddy ne yace

"Haris ai ita kace tana sanshi shifa bamuji ta bakinsa ba,kai shammaz menene ra'ayinka?" k'asa yayi da kanshi kan yace "Daddy ni bawai bana san hafsat bane ba amma dama tun farko ita na fara aura amma sam ni ba tsarin mata biyu a ra'ayina tayi hakuri kawai ta nemi wani" umma ce ta yanka masa wani mari dabesan da zuwansa ba "Kai mara hankalin inane dazaka taramu anan ka gaya mana wani tsari to bari kaji wallahil azeem ko yanzu na mutu indai ba hafsat ce tace bata sankaba bazata aure kaba kaine kaqi wlhy Allah ya isa ban yafe maka ba indai kaine ka kuma cewa bazaka auretaba" se huci take abba haris ma yace "Lallai wannan anyi dan banzan yaro,toka sani ninan na yanke hukunci kuma wlhy koda wasa kakuma furta bakaso na sallamawa duniya kai aure kuma nanda sati biyu masu zuwa zan daura idan muka kaima ita ka dawo mana da gawarta washe gari tsabar rashin san rugura tsari" shidai bece komai ba yayinda hafsat se kuka takeyi daddy yace

"haris ina darai zaka yankewa shaam hukunci? Ina nine ubansa? To baza ai masa auren dole ba indai ina numfashi" ran abba haris ya baci ya kalli yayanshi yace

"yaya iya tsawon zamana dakai ban taba maka musu ba amma wlhy wannan karon bazan lamunta a cutar mun da 'ya ba,wlhy indai har ina numfashi nanda sati biyu zan daura aurensu sannan kuma idan yace yafasa Allah ya isa tsakanina dashi" jikin daddy ne yayi sanyi kuma harga Allah shima yanasan auren,momy ma dadi fal aranta sabida tasani hafsat nasan shaam sosai......bayan sun watse hafsat na d'akinta yayinda kahirri ke toilet shaam ya shigo tamkar wani mayunwacin zaki,tana ganin ta mike a tsorace,Da baya da baya take tafiya har suka isa bango,ya sanya hannunshi ya matse hannunta sosai yace "Kika zab'i aurena bayan kinsan na tsaneki ko? Kika zab'i aurena bayan kinsan zakisha uquba a hannuna? Kika zab'i had'ani da iyayena sabida tsabar san zuciya ko?? Wlhy ki sani se kin gwammace kid'a da karatu indai muddin kika yarda kika shigo hannuna,sekin gwammace da bakizo duniyaba sekin kasa tantance nine kuwa kobani bane,shawara nake baki ki janye inba haka ba ko hmmm wlhy senci qaniyarki da mai da yaji,k'aramar yarinya se iskanci banza tambad'addi'ya....yana kaiwa nan ya saketa ya juya,ita yauma ta kasa koda kukanne sabida bakin ciki,gashi sam bazata fasa aurenshiba koda ze yanakatane gida biyu idan anyi auren......hmmm hafsat kenan anya baki daukowa kanki masifa ba kuwa??....

Mon Nua'iym
[1/21, 7:15 AM] Mmn Sadeeq: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

Wannan shafin nakine kyauta Aunty me jiddah musa,Allahu ya wadata ki da hasken rayuwa ya sanyaki a aljannarsa madaukakiya

08
Mamakine ya kama hafsat sanda ta farka taga har qarfe tara ta gota sauqinta daya tana fashin sallah,jiki ba kwari ta tashi ta shige toilet tayi wanka ta sanya rigarta mara nauyi pink color doguwace har qasa ta sanya kula bayan ta tufke kanta a tsakiya sannan ta fito zuwa ktchn indomie da kwai ta dafa ta dawo parlor tad'an tsakura kad'an ita har yanzu ta kasa gane meyene yake damunta wasu lokutan tanaso tayi kuka amma fir se hawayen suqi zuwa tama kasa tunanin komai gaba d'aya,ta kunna uban fankacecen tvn dake cikin parlor din amma takasa fahimtar me akeyi abinda yafi bata mamaki shine batasan tunanin me takeyiba idan za'a yankata batasn me take tunaniba abu daya ta sani shine wani zafi na musamman zuciyarta ke azabtar da ita dashi wanda kuruciyarta ta sanya ta kasa gane dalilin zugin....a haka yaa shaam ya shigo ya sameta bayan yayi amfani da key dinshi yashigo gidan kasancewar yayita faman knocking bata bude ba,kallon tsana ya wurga mata sannan yace " ke hafsat dama tsabar rainin hankaline ya sanya kina jina ina knocking kikamun banza?" gani ko motsi batayiba ya sanya ya matsa kusa da ita ya doddoki kafad'arta firgigit ta dawo daga duniyar tunanin dataje,da sauri ta miqe tsaye tace cikin tsoro "Na'am yaa shaam" harara da kallo me nuna tsananin tsana ya rabita dashi

"kina nufin duk wannan knocking dana jima inayi bakijiba,tsabar zamanki sokuwa,kinzo kin tasa tv a gaba kina kallo,Dabadan gidanmu daya ba kuma nasan acikin daula kika taso danace ke dinnan anyi daqiqiyar yar qauye,zuwa nayi inji meyene ya hanaki zuwa ki taya haleemah ku hada breakfast kokuma harkin fara tunanin cewar kishiyar kice kin fara kishi da ita?? Sadda kanta tayi kasa tanaso tayi hawaye koda wannan gululun bakin cikin datakejin ya tasomata ze kwanta amma ina sam ta kasa takuma rasa dalili,abin se yawo yakeyi yana mata sintiri tsakanin maqoshinta zuwa cikin yayan hanjinta dakyar ta iya furta kalmar

"kayi hakuri na makarane" tsaki yaja "ki tabbatar kinje yanzu kun daura girkin rana da ita sabida ba baiwar gidan uban kowa bace dazata girka abinci agidan,kuma ni bazanci abuncin yar aiki ba" Batace komai ba ta juya da siririyar halittarta zuwa ciki domin dauko hijabi,wani tsakin taji yaja a sarari ya furta " Sabida ansan ba wanda ze daukeki da wannan bushashen kunkurun tamkar na marainiyar kaza shine za'a cinnamun,mace se kace allo samb'al haka" sarai ta jiyoshi wani azababben baqin cikine ya dunqule ya sake taso mata mara misaltuwa fatanta daya tasamu tayi hawaye koda ta samu salama amma sam abun yaci tura ta kasa,da wannan ta dauko hijab dinta tafito,bayanshi tabi har sashen haleema ba wani nisa a tsakaninsu kofa kawaice part din kofofinsu suna kallon juna,suna shiga parlor din haleemah ta taso ta rungume shaam,shi kuwa ya manna mata sumba a goshi bayan ya sauke hannayenshi a saman faffad'an kuib'inta ya sauke yana me shafar manya manyan mazaunanta,wani shagwab'ewa tayi tace

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.