Bakin Rijiya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bakin_Rijiya_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 29 of 44
"Kulele kije guest parlor muhammad yana jiranki yace wai baya samun wayanki" k'irjinta ne ya dan doka ta dago ta kalli meron
"Ke kika ganshi da kanki?" kallon ta mero tayi,batun yauba ta fahimci ko zancen muhammad akayi hafsat tsorata takeyi tausayin tane ya kamata tace tana dafa kafad'arta
"Inshaa Allah babu abinda ze sameki,kuma inaji ajikina tarayyarki da wannan muhammad d'in alkhairi ne mutum ne me nagarta sosai na kula da hakan tun a yanayin gaisawar da yakeyi da mutane,dan Allah ki saisaita nutsuwarki gu d'aya" batace komai ba ta sanya hijab dinta ta sauka zuwa qasan......Da sallama ta shiga parlor d'in kanta a kasa,ansawa yayi batare daya kalli inda take ba,karasowa tayi ta zauna kusa a kujerar dake fuskantar tasa tace
"Ina wuni yaa muhammad?" Amaimakon ya amsa ta seya wurgo mata tambaya
"Mesa kika kashe wayanki,bayan na sanr dake tun jiya yau zanzo?" kanta a kasa yayinda qirjinta keci gaba da uban dokawa tace
"Banida caji ne"
"Bakuda wutane?" ya wurgo mata wannan tambayar cikin tane ya juya ta dago da sauri suka had'a ido saurin janye nata idan tayi sannan tace
"Da Akwai wuta caja nane ya lala ce" D'an kishin gida yayi sannan yace
"Mesa baki saka layinki a wayan dana baki ba,kumama mesa bakya amfani da ita tunda na kawo miki ita da layine a ciki"
"Kayi hakuri" shine abunda ta furta,ya tsani wannan ban haqurin na hafsat wlhy ita komai se ban hakuri qara tubire fuskar sa yayi yace
"Zancen zuwa dubai ne had'o kayan lefe,idan ina irqawa daidai yau saura 27 day's daurin aure,so inasan sanin keda wa kuke da intl pasport wacce ayau zaku iya tashi zuwa dubai ko gobe a misali?" kanta a qasa tace
"Nida khairiyya ne,amma inaga anan ma za'a iya siya ai base anje dubai ba" kallonta yayi na yan daqiqu sannan yace
"Ba zuwa nayi ki bani shawara ba umarnin tafiyar nake baki hafsat,abu d'ayane zaki riqe mu zauna lafiya shine rashin yimun gaddama,nine da kaina zan sanarwa da Abba haris zancen tafiyar nanda kwana biyu zakuyi tafiyar,yanzu zamuje gidan Abba haris mu karbi pasport din nata,kema ki bani naki daga can zan masa bayanin tafiyar,akwai kayan dana saka aka kawo daga saudi wasu daga dubai,suma zamuje ki duba ,kayan gidane abinda be miki ba ki fada a sauya wani" kallonshi tayi taso tace dashi ai su daddy zasu siya mata kayan daki,amma tunawa da tayi yace bayasan gaddama ya sanya taja bakinta ta guntse....
Abba haris bayan ya gama jin bayanin muhammad tare dajin cewar wannan tsarin sane kana yanaso ma aqara sati biyu akan ranar daurin auren kasancewar bayaso a samo matsala tunda tafiya na Allah ne,be masa gaddama ba sedai yace sedai suyi tafiyar tare da babbar Aunty d'insu Aunty surayya,sabida zamanto warsu mata qananun yara,zuwan na surayya kuwa shine ze dauki nauyin sa,idan har mijinta ya Aminta,kara kallon abban yayi yace
"Abba zancen kaya gida kuma,dan Allah karkuga kamar na raina iyawar ku kawai dai tsarinane nine nake siyan kayan gidana da komai,matana ta farko ma nina mata, sabida haka hafsat ma na riga na siya komai,kayan kitchen ne kawai bana siya,amma komai nine nakeyi" nisawa Abba yayi
"Bazamu hanaka yiwa matarka alkhairi ba,sedai muma haqqin mune muyiwa hafsat, gyaran daki sabida haka zamu bata kud'inta tsaba,shawarar yanda zatayi dasu kuwa ze shiga tsakanin kai da ita ne,sabida kaine mijinta" Godiya yayi sosai sannan yamasa sallama,waya yawa hafsat tafito suka kama hanyar zuwa ganin kaya,kallonta yayi sosai ya furta
"Hafsat karki qara yimun karya daga yau,a ina kika samu cajin yanzu? Kuma naga wayar kusan full ma? Bakida labarin karya ba kyau,kuma batada kad'an?" sosai taji kunya wannan ya sanya ta sauke kanta qasa tace "Insha Allah bazan kara ba kayi hakuri" murmushi yayi
"Mesa kika kashe wayar ki?" murya a kasa tace
"Nima dai yau sena tashi banso a kirani,shiyasa kawai amma ba komai" be kara cewa komai ba ita mad'in shiru tayi sanda suka isa wani qayataccen gida me kyawun gaske,tun a gaban gidan zakaga had'uwarsa da qayatuwarsa ba karya...Gate din automatic ne wannan ya sanya ya bud'e kanshi yana ganin dosowar motar, a wani farfajiyar ajiye motoci ya ajiye motarsa wanda had'uwars ba'a ma maganarta, kallon ta yayi yace "Bismillah muje ciki" Batayi musu ba kawai ta bishi suka wuce,ta bayanshi take se kallon cikar halittarsa takeyi yanayin halinsa yanayin maganarsa da uban ikon sa,wata kofa taga ya sakawa wani card lokaci d'aya ta wangale,kai tsaye ciki suka shiga tun a parlor ta raina dukiyar datake taqamar wai suna da ita,gabaki dayan parlor din komai na ciki gold ne se daukar ido yakeyi,dakuna guda biyar ne acikin gidan kuma flate ne me masifar kyau se paluka guda uku da fankacecen ktchn wanda ya gama hadewa da tsadaddiyar carbinet,gas cooker ne kawai aciki se freezer ta kwance da double door,a bed rooms din kuwa duka english bed's ne aciki,dayan dakin red and white,dayan blue wanda shi kuma akwai parlor aciki da lubby me kyau ga coffee chairs a walk way na zuwa barin,kuma komai light blue ne da white,dayan dakin purple dayan kuma pink $ white se thee green wanda aciki duk shine yafi burgeta,ko wane daki da toilet nashi,wanda a iya Bathrooms din idan aka barka zaka kwana kana kallon abubuwan ban mamaki,gidan ya hadu over bayan sun dawo parlor ne ya kalleta yace
"Hafsatu manga,sanar dani tsakani da Allah ina kike buqatar a sauya miki?inda bakyso,ma'ana abun be miki ba?" kallon shi ta d'anyi sannan tace
"Ni ko ina ma yamun ko ince yamun yawa ma,wancen corridor dinne kawai za'a saka mun console,se dining shelf dababu awurin dining,shima kuma zanwa daddy magana,nagode sosai Allah ya qara girma yakuma kara budi,Allah jikan iyaye kuma ya biya bukatocinka na alkhairi" har cikin ranshi yaji dad'in adu'arta tunawa yayi da Zainab wacce sam bata taba cewa dashi ci kanka ba duk girman alkhairin daze mata kuwa,murmushi ya sakar mata yace
"Kinsan ni kwangila na bayar bansan wai ya kamata su zauna awurin ba,yanzu kawai muje shops asiya choice naki,ba wani su daddy" kallonshi tayi
"To ai yaa muham......shhhhhh yafada hade da daura hannunsa asaman lips nashi,tunawa tayi da gargad'insa na rashin son gaddama ya sanya tayi gum da bakin nata,koda suka fito kasa hakura tayi dama hafsa akwai surutu tace dashi
"Yaa muhammad gidannan yayi kyau sosai wlhy" Bece da ita komai ba kurun murmushi ya mata......
*Bayan kwana uku*
Hakan kuwa Akayi,da hafsat da khairii da Aunty surayya suka dauki hanyar dubai a ranar wata wednesday,har suka isa suka kwana suna mamakin hali irin na muhammad,be basu ko sisin siyayyar lefenba,illah kawai tunkan su isa ya sanar dasu akwai driver daze kaisu masauki daga airport,kuma suna cin abincin wurin wanda menu kawai ake kawo wa su selecting,haushi duk ya gama kama hafsat kusamman ya da Aunty surayyah ke faman masifa akan ya rainawa mutane hankali,ko cewa akayi dashi basuda aikin yi,Wayan hafsa ne tayi qara tana dubawa taga number dinshi,a dake ta daga wayar sabida ba shakka ta shaqa yau kam,yace da ita
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.