Bintoto Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bintoto_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 33
*Episode 4&5*
*ALHERI WRITER ASSO. 📘🖊ï¸Â*
*A.W.A*
https://www.facebook.com/10798008594602?referre,whatsap
_________________________________
```ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ƙungiya masu aiki domin taimakon Al'umma, ƙungiya masu aiki da naxari da ilimi, Alheri daƙo, Alheri gadon barci```
*SADAUKARWA*
Wannan littafi tun daga farkon shi har ƙatshen shi na sa daukar mawa iyayena Alh. Muhammad da kuma Hjy safiya. Allah yaƙara nisan ƙwana.
_____________________________
*In the name of Allah*
Haka bintoto ta wuce su tana turo ma Abdurrahamanu É—an mutsulun bakin ta.
Ta nufi rijiyan wajen gidan don ta ɗebo ruwan sanyi bayan ta surka ne tayo cikin gidan inda anan ma ta tadda inna har a lokacin masifah takeyi yyn da Abdurrahamanu yy ƙasa da murya yana ta aikin bama innah haƙuri, haka dai ta wuce su tana guntse dariya.
Koda ta shiga banɗakin sam batayi wankan ba, don a cewanta ita sam batason ganin ta tayi wakan, mai ye amfanin wankan da ake takura mun ne?, ai wankan baƙi A sarar ruwa ne da sabulu, haka ta dinga surutun ta ita kaɗai, wanda takoma ta xauna dirshan a banɗaki wanda sai da taɗau kusan awa guda a ciki sannan tana tashi ta sheƘa ma jikin ta ruwa batare da ta wanke jikin nata ba.
Fitowa tayi wanda a wannan lokacin fira innah da Abdurrahamanu sukeyi akan tabarma a filin tirɓayan gidan.
Wuce su tayi haÉ—i da nufan soron innah, wanda da dosowanta Abdurrahamanu yayi saurin kama kai haÉ—i da toshe hanci, jin yanda da giftawan ta wani irin tsami da wari mai kaman na guluma ya xiyarce shi.
Ganin hararan da innah ke watsa mai yasa shi saurin sauke hannun shi haɗi da ɗan sosa ƙƴeya.
Bayan wasu ƴan mintoci bintoto ta fito haɗi da shigarta na koɗaɗɗun atamfa wanda duka tayi haɗin gambixa, don duka riga da ban xani da ban haka ɗanƙwali da ban.
"Innah bari naje dandali na dawo.
Ta faɗi tana ƙoƙarin barin soron nasu, nan innah tace" Adawo lfy Autana akula banda tsokanan faɗa fa.
Amsa ma innah tayi da tohh sannan tayi waje
Shikuwa Abdurrahamanu bin innah yy da ido yana mmkin yanda ita a kullum bintoto batayin mata laifi koko mai tayi itah a kullum sunan ta yarinya, cike da jin haushi ya miƙe haɗi da nufan ɗakin shi.
Ita kuwa bintoto da fitan ta ba tsaya a koinah ba sai a wajen wasu yara dataga suna kokawa.
Tsayawa tayi daga baya tana kalonsu don sam faÉ—a ya rife masu ido bamasu ganta ba.
Wani ne daake kira da mahamudu ne yace"kai ne xaka bugan mun ƙanina.? Tohh yau sai nayi maka dukan tsiya naga gatan ka anan ƙauyen.
Kafin wancan yaron yy mgn tuni mahamuidu ya hau dukanshi haɗi da turmishe shi a ƙasa, saboda mahamudun ba sa'an yaron bane
Ganin haka nan yara suka hau ihu suna kirar sunan mahamudu.
Ae ganin irin dukan da mahamudu yake ma yaron nan yasa tsikar jikin bintoto tashi, nan jikin ta ke tsuma kafin kace wani abu bintoto tuni ta cafka wiyan Mahamiudu tana cewa"wato kai ga ma ƙani, shikuma bai da kowa ko, nan mahamudu ya hau zaro ido waje don yasan halin bintoto sarai da xalinci ga ƙarfi kaman shari'a, baki na rawa ya hau cewa"bintoto mao nayi maki?
Bata tsaya daka ta tashi ba, ta hau dukan shi haɗi da ɗaga shi ta nuna ma Allah ta rima da ƙasa, wanda tana bugashi da ƙasa numfashin shi ya ɗauke don ko motso baya iyayi, ae yaran dake gƴefe daganin haka suka hau gudu suna cewa Bintoto ta kashe mahamudu... Haka suke gudu suna ƙarawa iya ƙarfin su.
Maman teddy 🧸
08081202932.
[4/9, 5:59 PM] mmn Hanif paid: *Tyiping......*
*🌹BINTOTO🌹*
*Written by:*
Aysha moh'd(maman teddy🧸)
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.