Complete Hausa Novels

Bintoto Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bintoto_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 24 of 33

*Page 42/43*

____________________________

*ALHERI WRITER'S ASSOCIATION*📚🖊️

*A.W.A*

``` k'ungiya d'aya tamkar da dubu, burin mu shine mu fad'akar da Al'umma baki d'aya, Alheri sai d'an Alheri.... Alheri gidan kowa....```

_________________________

*Dedicated to Glowing Azee.... Marubuciyar littafin Gimbiya Azeemah, waannan pagen taki ce, son so fisabillah💔.*

******

Yanda ta kutsa kai ixuwa cikin gidan binajan yasa duka ma'aikatan gidan kasa dakatar da ita, duk da kasancewar ba sanin ta sukayi ba. Haka Bintoto kaman wacce tasan kan gidan baki d'aya ta cigaba da kutsa kai tana k'wala kirar sunan Innah...."
Kutsa kanta tayi ixuwa wani falo wanda da shiganta taji idon ta yy wani dara² saboda tsaban had'uwan shi da k'ayatuwa da kayan alatu da more rayuwa wanda tun daga farkon falon aka k'ayata shi da adon gold kaman gidan sarautan da suka amsa sunan gidan mulki da iko. Zaune naga hango ta kan wata irin sallaya mai laushi da walwali wanda taushi kan baxaka had'a shi da tattausan fure ba. Hannun ta rik'e da caxbiha tana laximun da yazame mata sababbba kullum. Hannun ta asama yake alamun tana mik'a ma Allah kukan ta da duk wani abu da yademeta. Shafawa tayi had'i da juyo bayan ta don jin kaman tsayuwar mutum a gyefen ta. Dai² Bintoto nata waige² don tarasa inda xata nufa a wannnan tanfatsetsen falon. Karaf suka had'a ido da Innah da manyan ta yakuma kama ta. A sanyaye cikin muryan Rashin gane ta da fahimta tace" sannu y'a ta, daga inah kk?.
Kallon ta Bintoto ta tsaya cak tana yi cike da d'oki da mmki murya na rawa tace" Innah". Sai kuma Hawaye ya hau bin kuncin ta tagaxa cewa komai sai sheshshek'an kuka da takeyi.

Ganin haka yasa Innah mik'ewa had'i da nufo ta tana cewa" subhanallah y'annan zauna maxa kwantar da Hankalin ki, kifad'a da muwanki inshaallah kin xo gidan waraka...

A maimakon Bintoto ta bata amsa kawai sai ta nufeta da gudu ta k'ank'ane ta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya da karyar da duk wani lago na jiki... Cikin muryan matsananncin kuka ta hau cewa" Innah ta nine fah, nine Bintoton ki....sai kuma ta kuma rushewa da wani irin matsanancin kuka tana yi tana k'arawa.
Nan take jikin Innah ya hau kerma cikin wata irin murya mai cike ta'ajibi tahau cewa" Mama na kene? Dama kina raye, ashe xamuga juna dake batare da na mutu ba.... Nan hawaye ya hau bin kuncin Innah. Sa Hannu tayi had'i da k'ara manna Bintoto da jikin ta tana mai jin wani irin sanyin da rabon taji irin tata manta a rayuwan ta. Kuka Bintoto take yyn da Innah ta fara d'an bubbuga bayan ta alamun Lallashi, dai² su Dad da Mm Queen na shigowa falon wanda ganin su da Abdulrahman yasa Inna saurin raba jikin ta dana Bintoto tana mai zaunar da itah kan d'aya daga cikin juberun falon. Cike da karamcin irin nata duk da batasan komai dan gane da su Mm Queen ba, ta nufesu tana masu lale marhaban. Had'i da masu mazauni a falon. Zama Mm Queen tayi tana tama Innah murmushi don ita dai bb bakin yin Hausa tun da ba iyawa tayi ba. Cike da mutuntawa Dad yafara gaisar da Innah had'i da Abdulrahman da yake yimata barka da gida. Cike da K'aunar D'an nata tace" yowa Abdulrahmanu badai kaine kane momun Bintoto na ba. Tafad'i tana kallon Maleek da tasaba ganin shi ta laptop din Abdulrahman. Nan ko cike da murmushi kan Abdulrahman ya bata amsa tace" Maleek yau kune a gidan nan?. Ta fad'i cike da tsananin mmki. Murmushi Maleek yy had'i da dukawa har k'asa yana fad'in Innah barka da gida mun sameku lfy?. Jin Hausan da Maleek yy yasa Bintoto k'walalo da ido waje don abun ya bata mmki nan tace" Dama Maleek ya iyah Hausa shikenan na shiga uku na, ashe duk tsiwan da zagin sa da nakeyi yanaji.... Ita a ganin ta a zuciya take maganan bata san a sarari tayi ba. Dariyan da suka saka mata ne yasa ta ta fahimci a sarari tayi, shiko Maleek d'aure fuska yy a ranshi yana cewa" zaki sani ne, zakisan waye Maleek duk ran da kk shigo Hannu nan kusa.... Ya fad'i yana ma lumshe segxy eyes d'in shi had'i da bud'e su yana mai saukesu a kan ta. Fakaitan idon su Innah tayi tana mai gallah masa harara, shiko ganin haka yasa shi mirmushi yana mai cije pink lips din sa na k'asa. Muryan Dad ne ta k'atse su da yake bud'e taron da Addu'a.... Nan hankalin kowa yadawo kansa. Yyn da anan yafarq mawa Innah bayanin tun lokacin da ya tsinci Bintoto rainon ta da mm Queen tayi har xuwa Auren ta da Maleek da kuma had'uwan ta da Abdulrahman.

Sai asannan ya nisa yana mai karkewa da cewa" Innah wannan Aure na Bintoto da Abdul maleek munyi shi ne bisa a rashin sanin ku, amma muna mai bayar da hak'uri bisa komai, don haka Idan har Bintoto tanada wanda akayi masu Alk'awarin Aure tom zan iya warware komai na Auren bintoto.

Jin maganar sa yasa kirjin Maleek ya yanke yafadi, nan take xufah tahau kaeyo masa. Ita kanta Bintoton ta rasa dalilin faduwan kurginta. Muryan Innah ne yaji tana cewa" wlh Bb komai kunnu na ma Bintoto so da kauna, kuma kome ku kayi akan ta dai² ne, Bintoto ae ta riga da tazama y'an ku, ni bani da abun cewa sai dai nace ngd Allah yasaka maku da mafificiyar Alheri.

Cike da farin ciki duka suka hau sama innah gdy, don sosai dukaji dad'in hakan. Sallaman su liman da mutanen k'uyen yasa su duka saurin amsawa. Matan mai gari dasu liman ne cike suka shigo don taya Innah murnan dawowan Bintoto. Kai a wannan rana ko sun jima cikin farin ciki da kwanciyar hankali, yyn da da yamma su Dad da Mm Queen sukayi masu sallama hadi da nufan A.B.J.

Shiko Maeek sam innah tace k'afan shi k'afan matan shi. Don haka ne ta ware masa part guda a cewan ta sai nan da sati xai tafi da Bintoton.
Sosai Maleek yaji dadin hakan don sam bai son rabuwan sa da bintoton... Itako Bintoto bayan tafyn su Mm Queen ne ta nufi side din Matan Abdulrahman da y'ay'an ta biyu da ya boye bai gaya mata ba, sai a bakin innah da matan tashigo mata sannu da hanya taji yy Aure shiyasa yanxu ta nufi side din don kunsan Bintoto har yau bata gajiya da tfy....

Ta dade a side din Najwa matar Abdulrahman don sai yamma lis ta nufi side din Innah.
Sallah tayi sannan ta nufo falo wanda anan ta cudda innah da ma'aikatan gidan suna shirya masu dinner. Zama tayi gyefen innah, tana cewa" washhh inna ta na gaji yunwa xan ci abunci. Tafafi tana dry hafi da cewa kinsam mm Queen ta koya mun cin abunci, kullum dirning dina cike da abucucuwa.

Murmushi Innah tayi hafi da ce mata" ae yana side din ku can jeda mijin mi, don haka maza tattara ki tafi sai da safe, don nasan yanxu ma sun dawo masallaci shi da Abdurrahamanu.

Zaro ido waje Bintoto tayi tana cewa inah xan tafi Innah, wai side din na Maleekk yake???......

Idan naji ruwan comment din ku anjima nayi maku sabon update, idan naji shiru kuma, nima kujini shiru.

#SHARE TO ANOTHER GRPS

MMN TEDDY🧸
08081202932.
[4/13, 1:22 PM] Maman Teddy🧸: *TYPING✍🏻*

*🌹BINTOTO🌹*

*Na Maman teddy*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.