Complete Hausa Novels

Bintoto Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bintoto_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 33

*Episode 7*

*Written by:*
Aysha moh'd(maman teddy🧸)

*ALHERI WRITER ASSO. 📘🖊️*

*A.W.A*

https://www.facebook.com/10798008594602?referre,whatsap

_________________________________

```ƙungiya ɗaya tamkar da dubu, ƙungiya masu aiki domin taimakon Al'umma, ƙungiya masu aiki da naxari da ilimi, Alheri daƙo, Alheri gadon barci```

______________________________

Don hakane rayuwar ƙauyen keyi masu daɗi Shiyasa kuma kowa yasan waye bintoto don kowa yasab ba cikakkiyar ƴar ƙauye cikakkiyar gaja ga ƙaxan tanta da kuma tayi suna akai.
Shikuma Abdurrahamanu yaɗan taɓa karatun shi irin na ƙauyen nasu. Wanda shi a cewar sa yafi son yaxama ɗan kasuwa, kuma so yake yaxama ɗan kasuwan a ilimance da xamanan ce, don haka shiyasa kullum yake fafatukan neman yanda zaiyi ya cigaba da karatun shi, amma bb hanyan yiwuwan hakan, don dana cikin su ma akeji balle har akaiga xancen karatu.
Bintoto kuwa tun da suka fara gudu basu tsaya a ko'inah ba sai a soron xauren gidan su. Wanda sai da suka É—au a mintoci suna hutawa sannan suka shiga cikin gidan nsu.
Innah ne ta kallesu haÉ—i da cewa"bintoto na daga inah kk wannan haki da kukeyi na mene? Allah yasa ba tonan faÉ—a kukayi ba.
Cikin dawai² uwani tace" ahhh wlh innah bamu toni kowa ba. Kawai dai munyi gudune don muyi saurin dawo wa.
Cike da gamsuwa da maganan tasu innah tace" tohh yanxu bintoto shirya ki tafi gidan kitso wurin kuluwa.
Da tohh tabi innah yyn da innah ta kwace É—aurin da tayi ta gyefen zani ta fiddo naira 30 sannan tamawa bintoto.
Amsa bintoto tayi tana cewa"tohhh innah sai na dawo.
Nan innah ta rakata da adawo lfy.
Da fiton su soro bintoto tace uwani ta tafi gida sai sun haÉ—u gobe.
Yayin da itakuma ta nufi gidan kitso.
A hanyanta ne na xuwa ta haÉ—u da mai irin ice creem É—in nan, nan bintoto ta tsaya tana kallon shi da yaran da suka gyewaye shi, wanda ganin hakan yasa Shi yima bintoto wani irin murmushi sannan yace"taxoh ta amsa.
Aikuwa cikin sauri kunsan bintoto da kwaÉ—ayi nan ta amshe haÉ—i da cigaba da tafiyan ta, wanda kafun ta kai gidan kitson sai da tashanye tass sannan ta isa gidab kuluwa mai kitso.
Cike da xolaye kuluwa ta ringa cewa"ahhh lallae yau xa'ayi ruwa da ƙanƙara bintoto ne agidan.?
Murmushi bintoto tayi haɗi da cewa"ehhh sannan ta gaidata..bata ɗauki dogon lokaci ba, ta farayi ma bintoto kitson, wanda duk ƙaxantanta gashin kan nan nata har gadon baya, kuma irin gashinnan ne ta cikakkun hausa fulani,ga baƙi ga ƙarfi.
Cike da mamaki da faɗuwan gaba kuluwa ganin duk inta tatsaga kan bintoto sai taga kuɗi, kuɗin ma ba ƙananu ba, yasata cike da tsoro tace"bintoto hala innan ki ta aikeki ne.
Kallon ta bintoto tayi haÉ—i da cewa "a'ah.
Cikin sharce gumi kuluwa ta hau fiddo da kuɗin daga kanta tana tarawa daga ƙasa, amma ganin kuɗin yaƙi ƙarewa ne yasa kuluwa tace"kai bintoto maxa tashi kije innan ki ta cire kuɗin da ta aikeki da shi, sannan ki bata wannan. Ta faɗi tana mai miƙa mata kuɗun hannun ta, wanda duk ƴan dubu² ne.
Haka bintoto tasaka hijabi ta nufi gida.
Koda ta isa gida bata tadda inna ba, don haka nan ta nufi kitchen don ta É—ora abun da xasuci.
Haka ko taci sa'a da isarta ta cidda komai na tuwon dare, wanda bb ɓata lokaci ta soma haɗa wuta. Wanda kafin lokaci ƙanƙani takusa gamawa, don har tagama tuwon saura miya.
Zaune take tayi zaman dirshan. Tana aukin ƙurxanan cinyan ta, wanda duk inta murxa datti yake ɓanɓarowa. Dai² Abdurrahamanu na shigowa cikin madafin salati ya hauyi haɗi da cewa " binto dama ƙaxanta kk bamu mukeci?
Cikin xare ido tayo waje ta yi saurin haɗi da cewa"don Allah Abdurrahamanu kayi haƙuri.
Biyo bayanta yy dai ² innah na yo sallama, aiko da gudu ta nufeta haɗi da rumface ta.
Nan innah ta hau lfy maoyake faruwa ne...?
Shiru Abdurrahamanu yy don lamarin bintoto yanxu dary yasoma bashi.
Juyawa yy haÉ—i da nufan É—akin innah, ganin tafiyar tasa yasa innah mai da tambayar ta ga bintoto, amma sai bintoto tace bakomai innah.
Nisawa innah tayi cikin rashin gamsuwa da mganan bintoto tace" tohh ya kitson an maki?
Turo baki bintoto tayi haÉ—i da cewa"a'ah innah wai tace kin aikeni, duk in ta tsaga kaina kuÉ—i take gani, kingama wanda ta ciromun daga kaina.
Ganin kuÉ—i cike a hannun ta yasa inna baki na rawa tajawo bintoto haÉ—i da buÉ—e kallabin kannata, ai ko nan idon ta yacikoro da kuÉ—in nan a lallan kafe.

Salati innah ta hauyi haÉ—i da fara xubar da hawaye. Jiyo salatin innah yasa Abdurrahamanu saurin fitowa yana tambayan lfy.
Ae nan innah ta hau nuna mai abun da tagani daga kan bintoto wanda shima cike da ruÉ—u yajawo bintoto dake binsu da kallo don sam bata fahimci wani abu ba..
Ai yana ganin wannan abu ya maida mata da kallabin ta haɗi da sairin riƙota yana innah muyi sauri muje gidan liman.

Wayyyo bintoto na 😭

Ƴan team bintoto kuyi haƙuri komai xaixo da sauƙi da yardan Allah😭

Kudai cigaba da biyo Alƙalamin Aysha maman teddy don ta warware maku xare da abawa, don tabbas da lauje cikin naɗi....
Sannan naji ruwan comment

*#SHERE T0 ANOTHER GROUPS*

*Maman teddy 🧸*
[4/9, 5:59 PM] mmn Hanif paid: *Tyiping......*

*🌹BINTOTO🌹*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.