Bintoto Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bintoto_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 26 of 33
*Page 46/47*
____________________________
*ALHERI WRITER'S ASSOCIATION*📚🖊ï¸Â
*A.W.A*
_______________________
Basu farka ba sai Asuba,don Maleek ya fara tashi don nufan masallacin gidan da akayi shi d'an dai² wato iya nasu masu gidan da Ma'aikatan gidan. itako Bintoto tun kan ya tashi ta farka,amma ta kasa motsi saboda tsoron kar yayi mata wani abun da shi ba kunya ne da shi ba. Sai bayan fitowan shi daga bedroom din ne ya dauro Alwala oready sannan ya zura Jallabiya wanda yafito sak kaman Balarabe kwarjinin shi da kamalan shi duk sun bayyana don bakaramun kyau yy a cikin wannan shiga tashi ba. tana jin shi ya nufo inda take a kwance yakai Bakin shi dai² kan saman goshin ta yana mai kissing... hadi da saka hannun shi cikin nata yana matsawa a hankali. Hura mata iskan bakin shi yafara yi dai² kunnen ta don ta tashi daga Baccin,wanda ganin bata motsa ba gudun kar ya rasa jam'i yasa shi mikewa hadi da nufan Masallacin.
Itako Bintoto ganin ya fita yasata saurin mikewa hadi da nufan toilet tayo Wanka hadi da Dauro Alwala,wanda duk in ta tuna da Aikin cin mutuncin da Maleek yy mata sai taja masa Allah ya isan ta. A haka ta fito ta nufi inda sallaya yake ta shimfida tana tada kabbarar fara Sallahn subahi. Bayan ta kammala ne tayi adduo'i kan daga bisani ta shafa tana mikewa hadi da nufan wadrop don tasaka kaya a jikin ta. Ba wani adon tayi ba,don Super Tasaka mai ruwan Milk da yarfin cofee brown,fowder ta goga ma fuskan ta sannan a natse ta nufo falon yyn da ta tadda Ma'akatan side din kowa na aikin shi. Gaishe ta suka hauyi yyn da a natse ta amshe su tana mai saka kanta ixuwa side din Innah.
Tfy kadan ta iske Side din yyn da dashigan ta Innah dake aikin kaiwa da dawo ta kalleta cike da mmki tana mai cewa" Bintoto mai yakawoki da sanyin safiyannan?.
Shiru Bintoto tayi tana mai cuno dan karamun bakin ta hadi da cewa" Innah fah naxo naji kin tashi lfy ne...
Hmmm Innah ta nunfasa hadi da cemata" na tashi lfyl Bintoto maxa ki koma side din mijin ki da hantsi sai ki fito. Cike da kunar rai Bintoto ta nufo side din ta,don samm bama tabai ma Innah amsa ba ta juyo. Itako Innah bin ta tayi da kallo tana mai girgixa kai hadi da jin Matsanancin Tausayin Maleek, acewan ta Maleek yana Hakuri da halin Bintoton.
Da shigan ta falon ta cidda shi dai² yana fitowa daga midle falour, tsayawa yy yana jiran isowan ta,fuskan sa bb yabo bb fallasa. Bata bi ta kansa ba tazo tana shirin raba shi ta wuce tana mai cemasa" Fatan ka tashi lfy?.
murmushi yy yana mai kama hannun ta yana kai hannun kusa da bakin sa yy kissing sannan yace" lfy and you? a hasale da irin rainin da iskan cin da yy mata jiya tace" lfy.
Ta fadi tana mai jiran ganin yasakin mata hannu,amma sai yakiya,don ma Daure fuska yy wanda ganin yanda fuskan shi ya sauya yasataji faduwar kirji. Cikin Dakkakkiyar voice din sa yace" Wa kk tambaya da kk fita,da ixinin wah?.
Kallon shi tayi sai ta dan saki wata irin Murmushi na raini tana cewa" Lallai Maleek kama raina mun wayo,tom har ma kana tunanin wani wai abu xai shiga tsakanina da kai ne. tom kasani ni ba son ka nake ba,biyyaya ne nayi ma Dad da mm Queen. don haka kar kayi tunanin saka wata doka da zan bi,kowa yy xaman yan cin kansa,ko kuma ka auro wanda xaka juya ba dai ni ba. tana gama fadan masa haka ta fixge Hannun ta ta wuce tabar shi nan tsaye yana saka da warwara. Tabbas yana son hukunta Bintoto amma tayaya? tambayan da yy ma kansa kenan,nan wata xuciyan tace masa idan kun tare a A.B.J mana,nan xakayi maganin rashin kunyar ta,anan xaka dasa mata soyayyar ka ta dole. cije lips din shi ta kasa yy yana mai tunain abubuwa da dama hadi da tuno da surar jikin ta,wanda shi ne yasa yaji tsikan jikin sa na tashi.
Itako Bintoto bayan shigan ta side din ta Bacci tayi abun ta don sai a sannan datayi masa wannan rashin M. din taji ranta ya kwanta xuciyan ta tayi fari..... niko Mmn teddy nace yaro yaro ne,inkin san wata bakisan wata ba Bintoto.
sai wuraren 11am ta farka loacin ko tuni Su Maleek da Abdulrahman sun bar gidan. ganin haka yasa ta fada bandaki takuma tsalo wankan ta sannan ta nufo Dirning ta cika cikin ta.
Bayannan ne ta tattara hadi da nufan gidan su Uwani yyn da acan aka kaita gidan da Uwanin tayi aure.... Allah sarki rayuwa Bintoto ta tausaya mata sosai,don surfe ta tadda ta tana yi,wai a haka ita acikin kauyen tana cikin mata masu rufin asiri ne.
Sosai sukayi Farin cikin Haduwar su bayan shekaru kusan 8. fira sosai sukeyi ma junan su,yyn da Bintoto bata dawo gida ba sai bayan magriba. wanda sam innah bata san ta ma fita ba.
shiko Maleek bakin sa sam bai mutu ba,da ta dawo sai da ya tambayeta daga inah take,inda bb shakka bare tsoran sa don bata tunanin nan da yan kwanaki xasu tare a gidan su. Nan ta kesanar masa gidan Aminiyan ta Uwani taje,ta fada a gadaran ce,na bb yanda ka iyah.
Murmushi yy mata wanda yake nuni da abubuwa da yawa a tare da shi. A haka kullum suke rayuwa kullum Bintoto tayi ta tsigale masa shi kuma yana kauda kai komai yana barin nan da lokaci kadan dai.
a haka kwanaki suke shudewa kullum sai Bintoto taje gidan Uwani ta dawo kuma cikin tsigale masa da tsiwa yyn da yamma nayi xata garmake kofan ta don tun daga ranar da ya shigo mata ya lagwijeta take tsoran sa,shiyasa duk dare take rufe Bedroom din nata sai kuma safe ta bude.
a haka yake hakuri da ita.
A ranar Juma'a bayan sakkowan masallaci ne Bintoto taga Inna tasa ana ta shirya ta da kayyauka na gyaran Amare,ga wasu adon gold da akeyi mata,Najwa kuwa sai kaiwa da komowa takeyi,itace yima Bintoto wannan yimata wancan.
cike da mmki Bintoto tace" Innah wai ina xanije ne haka?.
kallon ta Innah tayi tana mai cewa" Ahh har kin manta da yau xaki bi Mijinki gidan sa na Abuja.
gagafffgaffff........
kirjin Bintoto ya buga,kawai sai tafara hawaye tuno da irin isakan cin rashin kunyan da tayi ta mawa Maleek. cewa take a zuciyan ta shikenan ni Bintoto na shiga uku,yau Maleek xai yi maganina,yaya zanyi yanxu???...
kauda kai Innata tayi gyefe don a tunanin ta sakarci irin nata ne. A haka kam kafin lokaci kankani tuni Motoci da securities sun cika baki gate din gidan su Innah, A haka tanaji tana gani ta rabu da innah bayan nasihun da tasha wurun Innah. Najwa ce kadai ta rakota har bakin Motocin dasuka xo daukan ta,hadi da ce mata nan kusa xasu kawo masu xiyara. securities suka bude mata murfin moton ta shiga ta zauna. yyn da bayan kaman minti biyar sai jin muryan Maleek tayi suna sallama da Abdulrahman da Najwa. Shigowa yy inda take a zaune hadi da kallon ta yasakin mata wasu irin lafiyayyun murmushi da yake Bayyana abubuwa da dama akan hakan... saka hannu yy ya rungumo ta jikkn shi yana mai matseta da kurjin shi,kaman xai ballata. Addu'a kawai take don tasan hakan dama xai iyah faruwa. shafa ta yake kaman mage yana mai kissing nata hadi da cewa" inason wannan colourn fatan naki fatimah.....
sorry for d late update...
Mmn teddy🧸
[4/13, 1:23 PM] Maman Teddy🧸: *TYPINGâœÂðŸÂ»*
*🌹BINTOTO🌹*
*Na Maman teddy*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.