Romantic Hausa Novels

Matar Shege 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR SHEGE (1).txt

Chapter 2 of 21

Page 2

Ringing d'in wayata ne ya tasheni,na wartsake da hayaniyar masu siyan waina,ban fara kawo tunanin komai a raina ba sai na Salim,rintse idona na yi ina sake tuno yanda na ganshi,na d'an jima a kwancen ina sak'e-sak'e kafin na tashi,ban kalli wayar ba bare na duba me kiran,na saka k'aramin hijjabi na fita don shiga wanka.

Karin kumallo bai dameni ba,to ina ma na ke da gatan da za a bani? Mahaifiyata ce kawai me min tilas na ci abinci,ko na rana ma ni ce na ke yin girkina,don tuni na samawa kaina y'anci daga wulak'ancin Mama akan abinci,idan na rage kuma na mik'a mata,babu kunya ta ke kar'ba ta ci,don babu laifi ta na da kwad'ayi.

Hoda kawai na shafa,bayan na shirya cikin doguwar riga ta atamfa,na yafa wadataccen mayafi,na saka takalmi, na d'auki jaka,ina dab da fita na sake jin ringing d'in wayata

"Y'ar wahala,har na manta da ke". Na fad'a ina d'akko ta,kamar yanda na zata Habib ne me kiran

"Wahala ta aure ka,tunda ka nace". Na yi maganar kafin na daga kiran.

"Hmmm!". Ya sauke ajiyar zuciya,kafin ya ce,
"Saura k'iris zuciyata ta fashe Zinatu".

"Har dagargajewa sai ta yi" Na fad'a k'asa-k'asa.

"Me ki ka ce?" Ya tambaya

Na yi guntun murmushi na ce"me ya hana ka zuwa jiya...?"

"Wane ni da taka umarnin ki? Na kira ba ki d'aga ba, kuma kin gargad'e ni na daina zuwa sai na sanar miki".

Na yi murmushi na ce"hakane fa! To ya kake?"

"To gani nan dai,lafiya ba lau ba,wallahi Zinatu ba na jin nutsuwata za ta dawo idan ban mallake ki ba,wata biyun nan jin sa na ke kamar shekara biyu,kuma..."

Na yi saurin katse shi da fad'in"kai! Dakata,na ga ka d'ebo fira,ni kuma wani uzurin na ke ka katseni,ka zo yau da daddare sai mu yi zancen ko?"
Ban ma jira cewar sa ba na katse kiran,na jefa wayar a jaka,na fito na na rufe d'akina da mukulli.

"To sai ina kuma?" Mama ta yi maganar daga y'ar rumfar da ta ke suya.

"Inda Allah ya nufa". Na bata amsa ina ficewa daga gidan.

Kai tsaye gidan su mahaifiyata na nufa,a d'aki na tadda ta ta na shara,na zauna ina gaishe ta bayan na kar'bi sharar na k'arasa mata.

"Zinatu!" Ta kira sunana a nutse

"Na'am Ummi" Na amsa ina maida hankalina wurin ta.

Sai ta ce min"anya da gaske za ki yi auren kuwa?"

Na yi d'an murmushi na ce"me ki ka gani Ummi?"

"Na ga kamar ba kya shiri,ga abu sai matsowa ya ke". Ta fad'a ta na tashi ta d'akko min leda wai tukwane ne ta siya min,za ta had'a da wancan kayan.

Sai na yi murmushi na ce"Na gode Ummi,Allah ya saka".

Ba ta amsa min ba ta tashi ta had'a min shayi,ta mik'o min,na sha fin rabin kofin,sannan na tashi ina yi mata sallama.

"Ba za ki gaida kakar ki ba?" Ummi ta tambaye ni.

Na d'an cukume,don ba ma shiri da mahifiyar Ummi,ni fa duk wanda zai fad'a min gaskiya bayan mahaifiyata,to fushi nake yi da shi.Labulen d'akin na d'aga ko sallama ban yi ba,zaune na ganta ta na linkin kaya,na saki labulen kawai na juya,duk da mun yi ido hud'u da ita,sai na d'an d'aga murya ina fad'a wa Ummi bacci take yi.

Na d'an jima tsaye a bakin titi,ba wai abin hawar na rasa ba,a'a kawai ina jinjina wurin da zuciyata take bani umarnin zuwa ne,daga baya dai na yi shahada na tari adaidaita na antaya,ina fad'a masa inda zai kai ni.

Daidai wurin da na ga Salim ya faka motar sa jiya na tsaya ina waige-waige,amma ban ga ko mai kama da motar ba,cikin k'arfin hali na shiga wurin ina had'e gira,don kar ma wani ya kawo min raini.Ma'aikacin da na fara cinkaro da shi na tambaya"don Allah Salim ya shigo?"

Sai ya zaro ido ya ce"waye ya ce miki kullum ya ke zuwa?"

Na sake had'e rai na ce"mun yi da shi ne za mu had'u a nan,na yi mamakin rashin zuwan shi"

Na yi maganar ina daddana wayata,na kara a kunne,tsaki na ja na ce"ka gani ko? Tun d'azun na ke kiran shi a kashe,kuma shi ma yau ya na son ganina dole,kai Salim matsala ne!".

"Mu ga lambar?" Ya tambayeni.

Na d'an ji dam,amma ban nuna ba,na maze na ce"mu ga ta wayarka?"

Babu musu ya mik'o min wayar bayan ya nemo lambar,na ji wani farinciki na kalli lambar na ce"ka ga kuwa ba ita bace a wayata,shi dai ban san adadin lambobin shi ba,kamar d'an kidnapping".

Tass! Na kwafe lambar,na bashi wayarsa ina yi masa godiya.Cikin farinciki na fita daga wurin kamar an yi min albishir d'in cikar wani babban burina.

Saving d'in lambar na yi da Salim na jefa wayar a jaka ina murmushi.

Kai tsaye kasuwa na nufa,na yi siyayyar abin da ba ni da shi na kayan abinci,na yi cefane na har da kaza,saboda yau ina cikin farinciki.A tsakargida na tadda Mama ta na tsintar shinkafa,duk sallamar da na yi ta rangad'awa ba ta kalle ni ba,bare ta amsa,da alama dai yau tambotsen take ji,murmushi na yi na shige d'akina,ba tare da na yi mata magana ba.

Tunda na fara aikin girkin Mama ba ta kalli inda nake ba,ta na ta fama da hura murhu,ga shi bakinta ya k'i mutuwa sai mita take yi,wai ita ta gaji da wannan bala'in na girki a murhu,na gama abin da zan yi na shige d'aki,don risho d'ina a d'aki yake saboda gudun satar kalanzir da Mama take yi min.Dab da kammala soya miyar na ji Mama ta na k'wala min kira "Zinatu! Zinatu!"

"Ya aka yi?" Na tambaya daga inda nake.

Sai gata ta bankad'o rik'e da roba ta na fad'in"wai da na ga kin fita ba ki karya ba...shi ne na ce to bari na rage miki waina"

Ta min maganar ta na ajiye min wata sandararriyar waina,had'i da lek'a tukunyar miyar da ke kan risho.

Na yi wata dariyar rainin hankali na ce"kin ga Mama...to ina ruwanki da cikina? Yau na saba fita ban ci komai ba?"

Sai ta gyara d'aurin d'ankwali irin na marasa gaskiya ta ce"ai wai da na ga yanzun aure za ki yi..."

"Idan ba na karyawa auren ba zai yiwu ba ko?" Na katse ta.

Sai ko ta had'e rai ta ce"ke ba fa na son raini,don ma kin ga ina lalla'ba ki? To kar ki ci d'in!"

Na yi murmushi ina d'aukar kwano na zuba mata abincin,na mik'a mata"k'amshi dai ki ka jiyo,shi ne ba za ki iya fad'a kai tsaye ba"

Ta k'ar'ba,ta fice ba tare da ta tankani ba.

Bayan na gama cin abinci na yi sallah,sai na kwanta na janyo wayata,wadda ta fara yi min kwarjini saboda bak'uncin lambar Salim da ta samu.Na jima ina kallon lambar kafin na yi k'undunbala na danna kira.

Har ta katse bai d'auka ba,hakan ya sa na sake kira a karo na biyu,nan ma dai amsar d'aya ce,aikuwa aiki ya ce min muje! Nan na yi ta jera masa kira,kamar ba gobe,sai kace wani game aka bani,ina jira in yi over.

Sai da na yi guda tara cif! Ina shirin yin na goma na ga shigowar sak'on shi.

Da hanzari na duba don na ji ko wani uzurin zai bani na rashin d'agawar shi

_"Waye ne?"_ Abin da ya ke rubuce a sak'on kenan.

Na yi saurin mayar masa da amsa kamar ya sanni na ce _"Zinatu ce"_.

_"Wace kuma haka? Daga ina?"_ Ya sake tambaya ta.

Tsaki na yi na sake kiran lambar ko zai d'aga,na yi sa'a kuwa ya d'aga,na wani kashe murya don gaskiya ba ni da zak'in murya na ce"Assalamu alaikum".

Tsaki na ji ya ja,a maimakon amsawa ya ce"malama tafi kai tsaye ba ni da lokacin shirme!".

"Subhanallah!" Na fad'a a zuciyata,da alama dai zai yi wulak'anci.

Sai da na yi gyaran murya sannan na ce"Zinatu ce".

Ya sake jan wani tsakin ya ce"kin kirani ne don ki koya min sunanki? To na haddace,menene wai?"

Gabana ya d'an fad'i,na shiga tunanin abin da zan fad'a masa,don ni kaina na san ba ni da wani dalili me k'arfi,na yi ta maza na ce"amm...jiya na ganka za ka shiga laundry,sai na ga ka burgeni,na so na yi maka magana ban samu dama ba,to kuma da daddare..."

K'itt! Na ji ya kashe wayar,tun kafin na k'arasa,na yi saurin sake kira amma sai na ji ta k'i shiga,ina dai zargin a blacklist ya sakani.

Na yi shiru ina nazarin yanda zan yi,kamar wadda aka min umarni, na fara rubuta masa sak'o kamar haka,

_"Idan ba ka ji dad'in maganata ba ka yi hak'uri don Allah,in sha Allah ba zan sake yi maka makamanciyar wannan maganar ba"_.

Ina ta jiran amsar shi amma shiru,kamar an aiki bawa garinsu,ina nan zaune ina nazari har aka kira la'asar ,na tashi na gabatar sannan na yi wanka na saka hijjabina har k'asa na fita waje,kai tsaye gidan su Hamza na yi,na tsaya a k'ofar gida na yi sallama da shi,a nan dakalin k'ofar gidan mu ka zauna mu na ta fira kamar abokai,sai magriba na tafi gida,don Habib ya fad'a min ana sallar isha'i zai shigo.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.