Romantic Hausa Novels

Matar Shege 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR SHEGE (1).txt

Chapter 20 of 21

Page 20

Na ji ya kira sunana a sanyaye,na juyo na kalle shi ina jiran abin da zai fad'a,sai kawai ya tsaya ya na kallo na,ni ma na zuba masa ido son shin na ratsa duk wasu jijiyoyin jikina,wajan minti biyu muna a haka,sannan ya jinjina kai ya d'auke idonsa a kaina ya ce"je ki".

"Na gode" Na fad'a,sannan na fice na rufo masa motarsa,tsaye na yi ina kallon motar har sai da ya b'acewa gani na,na sauke ajiyar zuciya na shiga gida da fargaba.

A tsakar gida na tadda Mama,anti Na'ima,anti Halima,da kuma yayata ta Rijiyar lemo anti Maimuna,na yi sallama na k'arasa inda suke a sanyaye,da na gaishe su ma babu wanda ya amsa,ni dai na d'auki buta na shige band'aki,ina shiga na duba wayata,na dannawa Nazifi kira,bugu biyu ya d'auka ko sallama ban jira ya yi ba,na fara magana
"Nazifi me kuka yi min?"

Ya ce"ya ya? Da fatan komai ya tafi daidai,ban kira ki bane saboda kar a samu matsala".

"Wai da gaske an yi min fyad'e?" Na tambaye shi,cikin zafi-zafi.

Ya yi dariya ya ce"haba Zinatu! Zargi na kike yi?"

Na ce"ka ga kawai ka sanar min!"

Ya ce"wallahi Zinatu babu wani fyad'e da aka yi miki,kuma cikin mu babu wanda ya tab'a ki".

Na d'an ji dama-dama a raina, na ce"ta ya zan yarda da kai,bayan na ga kun canza min kaya?"

"Wallahi mace ce ta canza miki kaya,ba mu ba". Ya fad'a

Sai na yi mamaki,na ce" to wace ita? A ina kuka samo ta? Kuma jinin jikin rigar fa!?"

Ya ce"k'anwar abokina ce,kuma ta ina za mu samu jini? Zob'o ne muka zuba".

Har raina na yarda da zancen sa,ashe ya b'oye min wani babban abu,sai nan gaba za ku ji illar da suka yi min!

Na ce"to amma meyesa duka jikina yake ciwo? Kuma maganin bacci kuka bani ko?"

Ya yi dariya ya ce"ai dole jikinki ya yi ciwo,tunda ba ki tab'a shan irin k'wayar ba,ke ta ma fa sake ki da wuri".

Na ce"amma Nazifi meyasa kuka ba ni k'waya?"

Ya ce"to Zinatu gani na yi idan idonki biyu za ki iya kawo cikas wurin gudanar da aikin,ko kuma bayan mun kai ki,ki ji tsoro daga baya ki lalata aikin,amma wallahi babu abin da aka yi miki".

Na sauke ajiyar zuciya na ce"to shi ke nan,Nazifi na gode sosai, Allah ya biya ku".

"Amin matar oga J.S" Ya fad'a yana dariya. Na yi murmushi na kashe kiran.

Bayan na fito aka tisa ni a gaba,da fad'a kamar za a min ciki da hak'ora,ni dai ban wani damu da hayaniyar su ba,tunda dama na san ta zama wajibi,kuma ko dukana za a yi tunda burina zai cika ba zan damu ba.Bayan sun gama bambamin su,sai kuma suka sakko suna tambaya ta a inda na had'u da Salim har ya min fyad'e,na fad'a musu dama can saurayina ne,kuma ba halinsa bane,shi ma tsautsayi ne ya afka masa.

Anti ta katse ni da fad'in"to idan ma halinsa ne cutar y'ay'an mutane ai yanzu ya yi wanda ba zai kub'uta ba,don kuwa yanzu sati d'aya aka tsayar auren ku".

Na ji zuciyata ta motsa,sai na rasa farinciki zan ji ko akasin sa? Ni dai abu d'aya da na tsana yanzu bai wuce yanda y'an'uwana su ke yiwa Salim kallon macuci ba,na san alhaki a kaina,sai dai na kan ji dama-dama idan na tuna da anyi auren komai zai wuce...

Na tashi na shige d'aki,na kwanta,ina jiyo tattaunawar su,har aka kira la'asar.

Ina idar da sallar la'asar Baba ya shigo,ya kira ni,na zo na tsugunna kaina a k'asa,to shima dai fad'an ne babu k'akk'autawa,kuma ya tabbatar min ranar Asabar za a d'aura aurenmu da Salim, kamar yanda mahaifinsa ya tsara, ya ce min shi ma kuma ya amince don shi ne kawai mafita a gareni.

Washegari da safe Anti Maimuna yi min waya, ta ce na je gidan Ummi yanzu, na shirya na tafi ina ta fargaba.A d'akin Umma na same ta,na zauna na gaishe su suka amsa babu yabo babu fallasa,na yi shiru ina jiran ta inda za su fara tasu tijarar,jin shirun ya yi yawa na ce"Ummi ga ni".

Ta ce"ai na gan ki, me zan yi miki? Ko na kira ki ne?"

Na ce"Anti Maimuna ta ce na zo".

Ta ce"to ki kira ta ki tambayi wurin wanda za ki je,ni dai ban kira ki ba".

Na sunkuyar da kai na ce"don Allah Ummi ki yi hak'uri".

Ta ce"hak'uri ai ke ya kama Zinatu,ke da za ki zama MATAR SHIGE...".

Babu wanda ya sake yi min magana, har dai na gaji da zama na,na tashi na koma gida. Tun daga nesa na hango Habib a k'ofar gidanmu,na k'araso na yi masa kallo d'aya,ina niyyar shigewa ya zo ya tare hanya,sannan ya ce"Zinatu zan yi magana da ke".

Ban ce komai ba,na tsaya sauraron shi

Ya ce"yaushe ku ka had'u da J.S,har kuka yi nisa a soyayya ban sani ba?"

"Ba mu dad'e ba" Na ba shi amsa.

Ya ce"kuma da gaske ne ya yi miki fyad'e?"

Na ce"to kai meye matsalar ka da hakan?"

Ya ce"amma ai kin san ya kamata na sani ko?"

Na ce"saboda me?"

Ya ce"saboda ni zan aureki,kin ga kuwa ya dace na san komai game da matsalar".

Na yi shiru ina mamakin sa.

Ya d'ora da fad'in"saura fa sati biyu ya rage,zuwa gobe na ke son a buga invitation,sai ki lissafi abin da ki ke buk'ata,na baki kud'in,lokaci ya na k'urewa".

Daga haka ya tafi,ya bar ni tsaye da mamakin sa.

SALIM

Tunda ya maida su Zinatu ,gida ya dawo ya kwanta,zuciyarsa fal bak'inciki,ya san dai ko giyar wake ya sha bai isa ya kalli Abba ya ce masa ba zai auri Zinatu ba,shi a yanzu ba ma auren nata ne damuwarsa ba,yanda Junaina za ta d'auki lamarin kawai ya ke ji,ace aure nan da sati d'aya? Anya kuwa za ta yarda da shi?

Ya tashi zaune jin k'irjinsa ya yi masa nauyi,ya je ya d'akko lemo a fridge ya yi had'in k'wayoyin sa,ya fara kwankwad'a.

Ya na cikin wannan yanayin Baby ta zo ta same shi,kasa ajiye jarkar ya yi,saboda burinsa kawai ya shanye ya samu bacci ko zai samu nutsuwa.

Ta na k'araso wa,ta warce jarkar ta jefar,ta zauna ta fashe da kuka, ya dafe kansa ya na furzar da iska. Ta ce"Yaya..."

Ba ta k'arasa ba ya katse ta"wallahi Baby Zinatu sharri ta yi min,ban san komai ba".

Ta ce"na sani,kuma ko na sakan d'aya ban tab'a zarginka ba Yaya,wallahi na yarda shiri ne kawai,saboda son da take yi maka,ga shi har son ya na nema ya zama k'iyayya".

Ta d'ora da fad'in"Yaya shaye-shaye ba mafita bane,da wannan abun da ka zauna ka na sha da alwala ka yi,ka tada sallah ki ka yi ta karatun k'ur'ani,idan ma ba ka da nutsuwar karaton ka kunna ka yi ta saurara,za ka ji sauk'i a zuciyarka".

Haka ta yi ta kwantar masa da hankali har sai da ya nutsu.

HABIB
Da daddare Baba ya kira Habib,ya zo gidanmu,bayan sun gaisa Baba bai b'oye masa komai ba,ya zayyane masa halin da ake ciki,tunda a zaton sa shi bai sani ba,ya d'ora da fad'in "Habib na san ka na son Zinatu,amma a irin yanayin da ta shiga yanzu ya zama dole ka hak'ura da ita,shi wanda ya yi b'arnar shi ya dace ya aure ta,ya zauna da ita".

Habib ya ce" Baba,son da na ke yiwa Zinatu na tsakani da Allah ne,ba gangar jikinta na ke so ba,kuma idan ni d'an'uwanta bai yarda da aurenta a halin da ta shiga ba,waye zai yarda?"

Baba ya ce"ai shi mahaifin yaron ya tilasta masa auren ta,don haka babu wata sauran matsala".

"Shi ne ma babbar matsalar Baba" Habib ya fad'a.

Ya d'ora "wallahi Baba ina jin tsoron kar ayi masa tilas ya aure ta,ba da son ransa ba,kuma ya zo ya na k'untata mata daga baya.Ni fa na ce,na ji na yarda,zan aure ta a hakan kuma mu zauna lafiya ba tare da na nuna mata alamar na sani ba".

Baba ya sauke numfashi ya ce" wata sabuwa! To a gaskiya da farko na yi zaton idan ka ji haka za ka fasa aurenta,shi ya sa ma har na amincewa mahaifin yaron,amma yanzu zan sanar masa da na janye maganar,shikenan komai ya wuce,tunda itama ai da nata laifin".

Habib ya ce"to Baba na gode,Allah ya saka"

"Amin Habibu,ni ne da godiya, ka je ka cigaba da shiri" Baba ya fad'a.

Ina kwance na ji shigowar sak'o wayata,na duba da sauri ganin sak'on Habib ne

_"Zinatu son gaske nake yi miki ba na k'arya ba,don haka ba na jin wannan k'aramar matsalar za ta sa na fasa aurenki.Ki kwantar da hankalin ki,har yanzu akwai maganar aurenmu"_.

_"Habibu! Ba na son ka,kuma ba zan aure ka,Salim zan aura in sha Allah!"_ Na maida masa da amsa.

_"Wallahi sai kin aureni Zinatu,ko kuma ki yi danasani, da nadama mabayyabiya!"_

Ya maido min da amsa.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.