Romantic Hausa Novels

Matar Shege 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR SHEGE (1).txt

Chapter 9 of 21

Page 9

K'arfe goma sha d'aya a shagon Baby ta yi min,na shiga wurin da sallama,ba wani girma ne da shi sosai ba,akwai ma'aikata su na ta aikin su,da tsirarun mutane da ake yiwa gyaran jiki,na ja kujera na kame ina raba idon ta inda zan ga k'anwar Salim d'in,duk da dai ban tab'a ganinta ba, amma na san idan na ganta zan ganeta,tunda jini ba ya b'uya

"Hajiya me za a yi miki? Gyara,ko kwalliya?". Wata ma'aikaciya ta tambayeni

Na d'an ji dam! Don kuwa dubu d'aya da d'ari biyu ne a jakata,don duka kud'ina su na cikin jakata da na manta ta a d'akin Salim,don haka ban shirya wani gyaran jiki ba

"Amm...Baby ba ta shigo ba?" Na tambaye ta,don ni dai burina na ga yarinyar

Ta ce"ai ba ta zuwa da wuri,da yake ita kwalliya kawai take yi,kin ga kwalliyar an fi yin ta da yamma,sai k'arfe uku take zuwa.Mu mu na yin kitso,k'unshi,wankin kai,da kuma gyaran jiki".

Na sauke numfashi na ce"ga shi kuma kwalliyar na ke so,unguwa zan je kuma sauri na ke yi,don Allah ko za ki kirata ta yi min?"

Ta ce"to bari na gwada,Allah yasa ta na free"

Ta d'auki waya ta kirata,ta yi mata bayani,sai ta kalleni bayan ta gama wayar ta ce"lallai kin yi sa'a,ta ce ga ta nan zuwa".

Na ji sanyi a raina,na yi mata godiya ina gyara zama

Babu jimawa ta zo wurin,aikuwa kallo d'aya na mata na yarda k'anwar shi ce,su na kama sosai,sai dai ita ba fara bace,kuma da alama za ta yi kirki,don sai gaisawa suke da y'an wurin cikin wasa da dariya.

Na gaisheta,duk da dai ba na jin za ta girmeni,ta maido min da gaisuwar ta na murmushi ta ce"ke ce za a yi wa kwalliya?"

Na ce"e ni ce".

Tace"ok,bismillah".

Na matso inda take zaune akan kafet,ta na shirya kayan kwalliyar,ta kalleni ta ce"to,ta nawa za a yi miki?"

Gabana ya fad'i,na dai dake na ce"ta d'ari biyar".

Ba ta yi magana ba ta hau yi min,ni dai ina ta kallon ta, sai can cikin son janta da fira na ce"uhm! Ni fa zan yi kwalliyar ne kawai! Amma ba ni da wayar da zan d'an yi hoto idan an gama"

Ta yi murmushi ta ce"ba ki da waya,da girmanki?"

Na ce"ina da waya,jiya ne na manta ta a d'akin saurayi na,kuma bai kawo min ba".

Sai na ga ta d'an yi damm,sannan ta ce"aikuwa da ya kawo miki".

Ta gama yi min kwalliyar,ta kalleni ta na murmushi ta ce"wow! Gaskiya kin yi kyau,ki na da kyau sosai".

Na yi murmushi na ce"kai Baby! Duk kyauna ai dai ban kai ku ba,ke da kayan ki".

Na yi zaton ma za ta tambayeni inda na san yayanta sai na ga kawai ta yi y'ar dariya,ta d'auki wayarta ta ce na tsaya ta min hoto

Na yi murmushi me kyau,ta d'aukeni,sannan na rok'eta mu yi tare,mu ka yi,mun yi kyau kuwa

Ta na shirin barin wurin na ce"don Allah zan rok'e ki wata alfarma"

Ta ce"ok,ina jinki".

Na ce"lambata zan baki,idan na karb'o wayata daga wurin Salim sai ki tura min hoton".

"Salim?" Ta fad'a da mamaki

Na yi murmushi na ce"e sunan saurayin nawa ne haka".

Sai ta yi murmushi ta ce"nice! Ni ma sunan Bros d'ina ne,kuma ina son shi sosai.Kar ki damu,ki saka min lambar,in sha Allah zan tura miki"

Ta k'arashe maganar ta na mik'o min wayarta,na saka mata lambar na fad'a mata sunana,na yi mata sallama,sannan na je wurin wadda ake bawa kud'in na bata na fito daga wurin da farinciki.

Shabiyu da mintuna na koma gida,na tambayi Mama ko Baba ya shigo da na fita? Ta maka min harara ta ce"ban sani ba! Ko tsoron shi ki ka fara yi yau d'in? Na ga dai ba yau kika saba taka umarninsa ba, shi ma ai da gangan ya ke yi,bai yi miki mari a k'afa ba kuma ya saka ran za ki zauna a gida? Aikin banza..."

Ni dai ban tanka ta ba na shige d'aki,na barta ta na ta yi.Y'an tsirarun kayana na had'a na wanke,na yi kwalimar d'akina,haka dai na yi ta k'irk'irar aiki duk dan kar na gaji da zaman na yi sha'awar fita,don ba a son raina na taka dokar Baba ba,dole ce kawai.

Fess! Ya fito cikin shirin sa na k'ananun kaya,jar riga da bak'in wando,sai k'amshi ya ke zubawa. "Sannun ku Mami,ke da autarki ne ku ke fira?". Ya fad'a ya na murmushi.

Mami ta kalle shi ta ce"Salim ba ka ci komai ba fa,tun safe".

Ya ce"e,yanzu zan je na ci".

Ya kalli Baby da take zaune ta na danne-danne a waya ya ce"my Baby,zan fita".

"A dawo lafiya" Ta fad'a ba tare da ta kalli inda ya ke ba.

Sai ya dafe kai,ya zauna kusa da ita ya ce"na fasa fitar ma,ta ya zan iya fita ki na fushi da ni y'ar'uwa?"

Ta juya kai gefe ta ce"ni fa babu ruwana da kai Yaya Salim,ka je kawai".

Ya ji babu d'adi sosai,ga Mami da take yi masa kallon tuhuma,don ba ta k'aunar duk wani abu da zai b'ata ran autar ta.Khadija(Baby) ita ce auta a gidan,akwai yayyun Salim guda biyu mata,wanda duk sun yi aure da y'ay'ansu,Baby da larurar ciwon zuciya aka haifeta,shi yasa duk gidan kowa ya ke tausayin ta,ake k'ok'arin faranta mata,ko kad'an ba a bari ranta ya b'aci don kar ciwon ta ya tashi,duk cikin gidan sun fi shak'uwa da Salim,kamar ya fi kowa son faranta mata rai,za ta iya cewa bai tab'a saka ta damuwa ba sai bayan had'uwar shi da Junaina.

"Don Allah ki zo ki rakani,zan yi miki wani abun mamaki,kuma na san zai faranta miki sosai".

Sai ta yi murmushi ta ce"ka tabbata?"

Ya na kamo hannunta ya ce"e mana".

Ta tashi ta shiga d'aki ta d'akko mayafinta su ka fita.Ta d'an b'ata rai ganin sun nufi restaurant ta ce"anan za a nuna min wani abun mamaki?"

Ya ce"yunwa na ke ji,mu fara cin abinci tukunna".

Ta yi shiru har su ka k'arasa,sai da ya ja Manager gefe ya fad'a masa kar a turo kowace yarinya sannan ya dawo wurin Baby su ka shiga d'akinsa.

Ta bi d'akin da kallo ta na d'age gira,don ta yi zaton za ta ga hoton Junaina,caraf idanunta su ka fad'a kan jakar mata y'ar k'arama,ta yi saurin k'arasawa ta d'auki jakar

Salim ya ce"ke yanzu daga ganin abu sai ki tab'a ba ki san me shi ba?" Cikin dauriya kawai ya yi maganar,don ya yi mamakin ganin jakar,kuma ya gane tabbas ta Zinatu ce.

Baby ba ta kula shi ba,ta bud'e jakar kud'i ne a ciki sai turare da waya,ta d'akko wayar ta danna aikuwa hoton Salim ya bayyana a fuskar wayar,sai ta juyo ta yi masa kallon tuhuma ta ce"Yaya,wannan jakar waye?"

Ya ji wani takaici,da haushin Zinatu ya rufe shi,ya ma rasa ta yanda zai yi mata bayani,ganin har ta fara hawaye ya ce"zauna don Allah,wallahi jakar me aiki ce,ina jin mantuwa ta yi a d'akina".

Baby ta yi tsaye da jaka a hannu ta na kallon shi,lokaci d'aya tunanin kalaman sa su ka dawo kanta da ya ke cewa'A'a Baby,da gaske na rabu da Junaina,farincikin ki shi ne nawa.Wata ce yanzu ba ita bace'

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ta furta cikin sanyin murya,ta tsaya kallon shi na d'an lokaci,sai kawai ta saka wayar a jakar ta rataya,ta nufi k'ofar fita.Ya yi saurin bin bayanta ya rik'ota ya ce "Baby! Wai ki na nufin ba ki yarda da ni ba? Wallahi da gaske ba ni da alak'a da me jakar nan".

"Amma me ya kawo hotonka a fuskar wayarta? Duka ma me zai kawo ta d'akinka bare har ta yi mantuwa? Haba Yaya,me ya sa za ka fara haka?"

Ta kai k'arshen maganar da sanyi sosai,kamar za ta yi kuka.

Ya dawo da ita,ya zaunar akan kujera ya ce"ki yarda da ni Baby,da gaske ba ni da alak'a da me jakar nan,ni fa ban ma santa ba,kuma ban san yanda aka yi aka samu jakar a d'akina ba, ina tunanin wani tarkon ne dai ake shirin yi min".

Ta yi saurin katse shi da fad'in"don a had'ani da kai? Ko kuma don a had'a ka da matan da ka ke kawowa?"

Ya ji kalmar kawo matan har cikin ransa,ba dan ya na gudun ciwon ta ya tashi ba,da yau sai ya wanka mata mari,ya cije baki ya ce"haba Baby! Ke fa k'anwata ce ba yayata ba,ya zan dinga yi miki bayani ki na neman jifana da wata manufar mara kyau? Oya tashi na maida ki gida".

Ya yi maganar ya na mik'a mata hannu,alamar ta ba shi jakar.Ta maida jakar baya ta ce"ba zan bayar ba,wallahi Yaya sai na ga me jakar nan ido da ido,sai na ji alak'ar ku da har take zuwar maka d'aki,ta yi zaman da za ta yi mantuwar jaka..."

Cak! Ta tsaya,ta yi shiru baki bud'e ba tare da ta k'arasa maganar ba,tunanin kalaman Zinatu na d'azu su ka shiga dawo mata,ta ce ta manta jakarta da wayarta a ciki,a d'akin saurayin ta,kuma sunan saurayin Salim,tabbas Salim d'inta ne buduruwarsa ce

Ta zauna hannunta har karkarwa ya ke,ta dubo lambar da Zinatu ta bata,ta danna kira.K'irjinta ya bada dum! Ganin ga shi a zahiri hasashen ta ya tabbata,don kuwa bugu d'aya wayar dake hannunta ta soma ringing.

Sai ta nuna masa wayar ta ce"Ashe ita ce? To ita ta fad'a min gaskiya, d'azu ta fad'a min ta manta wayarta a d'akin saurayin ta,ashe kai ne Yaya? Yaushe ka fara soyayya da wata bayan Junaina?"

Ya zauna shi ma ya na mamakin ta inda ta samu lambar Zinatu ya ce"ba ni wayar nan Baby".

"Na ce fa ba zan bayar ba,ni zan maida mata da kaina,kawai ka kaini gidansu". Ta yi maganar ta na hawaye

Hankalin sa ya d'an fara tashi,don ba ya son ciwon ta ya tashi,ya sassauta murya ya ce"sister ki tsaya ki fahimceni..."

"Wallahi Yaya ba zan fahimce ka ba,ta ya zan fahimce ka alhalin idona ya nuna min komai? Ba alak'ar gaskiya ku ke yi ba,shi ya sa tun farkon had'uwar ku ba ka bani labari ba ko?"

Ya yi shiru ya na kallon ta.Ta d'ora da fad'in"zan yi maka wata alfarma guda d'aya,ba zan sanarwa da kowa ba,amma fa idan ka min alk'awarin za ka kaini gidansu".

Ya ce"subhanallah! Ba ki yarda ba kenan? Wallahi ban san gidan su Zinatu ba,hasashen ki ba gaskiya bane".

Ta ce"ba abun mamaki bane,na yarda ba ka san gidansu ba,tunda ba ka da niyyar aurenta,shikenan Bros na fahimce ka,amma ni zan nemo gidansu zuwa gobe,zan je za mu yi magana da ita"

Daga haka ta fice daga d'akin cikin sauri ta na rik'e da jakar
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.