Romantic Hausa Novels

Matar Shege 1 Complete Hausa Novel

Reading file: MATAR SHEGE (1).txt

Chapter 4 of 21

Page 4

K'arfe goma sha biyu na kammala shirina tsaf,har da kwalliya na yi,na baza turare,na yi kyau sosai kuwa,da kuzarina na yi shirin,duk da idan aka kira tafiyar tawa da sauri ba wurin zuwa ba a yi k'arya ba.Ko girki ban tsaya yi ba,don haka na fara biyawa ta gidan Ummi ko zan samu wani abun

Girki na tarar ta na yi,na gaisheta ya amsa ta na tambaya ta inda zan je,na ce mata babu inda zan je,na zo gaisheta ne kawai

Ta ce"to tashi ki daka min yaji,dama ba son dakan nake ba".

Na d'an kalli agogo,na tashi na ajiye mayafina na hau dakan,ina ta sauri kar lokaci ya yi ban k'arasa ba,bayan na gama ma sai da ta bani yankan salak,abincin ma kad'an na ci,saboda sauri,na ce mata gida zan koma akwai aikin da zan yi.

"Sharad'a" Na fad'a bayan na shiga adaidata sahu

Sai da muka d'au hanya na ji ya ce"phase 1?"

Na ce"ka san wani kamfani a can? Sunan me kamfanin Salim"

Ya ce"na meye kamfanin?"

Na furzar da iska na ce"wallahi ban sani ba"

Ya ce"ai dole sai na san ko na meye,kafin na san sunan me wurin.Yanzu ina za mu yi?"

Na yi jim,kafin na ce"kai ni Sharad'an kawai"

Ya ce"to bari na kaiki phase 1 don ya fi yawan kamfani"

"Na gode" Na fad'a ina duba wayata,da agogo ya nuna d'aya saura kwata.

A daidai wani babban kamfani ya saukeni,na ba shi kud'insa ina kallon wurin da aka rubuta ALBARKA FOOD'S LTD da manyan bak'i,har ya ja mashin d'insa zai tafi na yi saurin tambayar shi na ce"don Allah nan d'in me da me su ke yi?"

Ya ce"kema kamar ba y'ar Nigeria ba? Ai duk wani nau'in kayan abinci taliya,macaroni, couscous, shinkafa,da kika ga an saka ALBARKA to a nan ake had'a shi"

Na sake kallon wurin,ina jinjina kai alamar gamsuwa,sannan na ce"kuma baka san sunan me kamfanin ba?"

Ya ce"ai sananne ne,na san shi,sunan shi Muhammad, amma am fi ce masa Oga Js".

Na d'an tab'e baki na ce"gaskiya ba shi bane,na gode".

Gaba na k'ara,ina ta kalle-kalle kamar y'ar k'auyen da ta fara zuwa birni a ranar,duk kamfanin da na gani komai girman sa ko k'ankantar sa sai na tambayi me kamfanin,ni dai ban ji kamfanin Salim ba,ban yi aune ba na ji kiran sallar azhar,na yi saurin duba wayata na ga k'arfe d'aya da rabi

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Na furta,ina jin bak'inciki,yanzu ya na can ya na cewa na yi masa African time. Na yi ta zagaye a Sharad'a har biyu da rabi,ganin zan yi asarar lokacin sallah na hak'ura na tari adaidaita na koma gida,takaici kamar zan yi kuka

A gajiye lik'is na shiga gidan,ko sallama ban yi ma,don gani nake da na bud'e baki da nufin magana to kuka ne zai biyo baya,sai dai ina shiga na ga abin da ya k'arasa d'ugunzuma zuciyata

Hauwa ce y'ar Mama tsaye a k'ofar d'akina,sanye da doguwar rigata ta yi rolling da mayafina ta na ta d'aukar kanta a hoto,na daskare ina kallon yanda ta ke malkwad'e-malkwad'e kamar musaka,takaici ya rufeni,cikin k'araji na ce"bura'uban nan!"

"Hauwa! d'akina,kika shiga ki ka d'akko kayana,kika saka?"

Ta juyo da sauri,cikin rashin gaskiya ta kalleni,sai kuma ta had'e rai ta zo za ta shigeni,na funcukota na wanke ta da mari,ta d'aga hannu za ta rama na murd'e hannun,aikuwa ta cakumeni mu ka shiga bawa hammata iska,kamar y'an dambe,na yi mata matsiyacin duka don na fita k'arfi,kuma na girmeta,na yi mamakin rashin fitowar Mama,har muka gama,na shige d'aki,Hauwa ta na ta zagina,ni dai ban sake kulata ba,na yi wanka na yi alwala,na tada sallah

Ina sallamewa na ji shigowar Mama gidan,ashe duk budurin da muka yi ba ta nan "Hauwa! Kin gama shirin kuwa? Ko sai ta dawo kina shashanci?"

Ni dai ban fito ba,ban kuma san amsar da ta bata ba,sai can Mama ta shigo d'akina cikin kwantar da murya ta ce"haba Zinatu,Hauwa ai k'anwarki ce,meye kuma don ta rab'i arzik'inki? Wannan ma ai wani girman ne,saurayin ta ne ya ce zai zo su je gaida hajiyarsa,to sai naga tunda masu hali ne bai dace ta je a tsiyace ba,shiyasa na ce ta ari kayanki ta sa,idan ta dawo sai ta wanke miki"

"Na ji!" Na fad'a a tak'aice.

Ta tashi ta fita,ta na min godiya,sai kuma na ji ban kyauta ba,na ma rasa meyasa na harzuk'a haka,kodayake dama a k'ufule nake,kuma ta k'ara b'atan rai da ta shareni

Kwanciya na yi,ina jin yanda k'afafuna suke amsawa,saboda yawon da na sha,na yi zaton ma Salim zai kirani ya tambayi dalilin rashin zuwana,amma sai na ji shiru,ni kuma ban kira shi ba,don ban san abin da zan fad'a masa ba

Zuciya duk a jagule na yi wunin ranar.Na yi ta nazari kafin na samu mafita,wadda nake fatan ita ce kawai za ta sadani da Salim idan na samu dama.

Washegari goma na safe a laundry d'in su Salim ta min,ko gidan Ummi ban je ba,don kar yau ma ta zaunar da ni.Kai tsaye na shiga,na yi ta dube-dube kafin na ga wanda ya bani lambar Salim,sai na yafito shi da hannu,na ja gefe na tsaya,ya zo muka gaisa,na d'an yi jim kafin na ce,
"Magana nake son yi da kai me muhimmanci"

"Ina jinki" Ya fad'a ya na min kallon sama da k'asa.

Na ce"don Allah ina son duk wani bayani akan Salim da rayuwarsa".

Ya d'age gira alamar nazari sannan ya ce"ke d'in wacece? Kuma meyasa ki ke son sanin Oga Salim?"

Na furzar da iska na ce"ba ina shirin cutar da shi bane,kawai ya na burgeni ne,kuma ina son shiga rayuwar shi".

"Ko gwamnati ba ta aikin banza". Ya fad'a ya na yiwa jakata kallon gefen ido.

Duk da na fahimta amma na ce"ban gane ba"

Ya ce"a nawa zan baki bayanan?"

Na ce"dubu biyu ne a jakata"

Ya ce"tabb! Aikuwa y'anmata Salim ya fi 2k,k'ara ki sha bayani"

Na zuge jaka,na zaro dubu uku na ba shi.Ya je ya d'akko kujeru guda biyu ya zauna a d'aya,nima na ja d'ayar na zauna,sannan ya fara kwararo bayani...

"Sunan shi Muhammad Ibrahim Muhammad,an fi kiransa da Salim,wasu kuma su na ce masa Oga Js.Shi kad'ai ne namiji a gidansu,ya na da k'anwa sunan ta Baby,ban san sauran y'an gidansu ba,ita d'in ma na ga su na zuwa nan ne wataran,da alama dai akwai shak'uwa sosai a tsakaninsu"

Na jinjina kai, alamar gamsuwa,ina sake sauraron shi,ya d'ora"wannan wurin wankin nashi ne,J.S shop ma na shi ne,kuma ya na zama sosai a wurin,musamman da daddare,kuma wurin cin abinci na 7:30 ma na shi ne,don an ce yawanci ma da daddare a can yake zuwa ya ci abinci.Akwai kamfanin mahaifin shi a Sharad'a phase I,sunan shi ALBARKA LTD,kuma Salim d'in ma a can yake aiki,a haka za ki ganshi kamar d'an wulak'anci,amma kuma ba haka bane,yana kirki,shi dai kawai ba ya son rainin hankali,kuma ba kowa yake sakarwa fuska ba,a iya sanin da na yi masa,da kuma yanda nake jin labari ba shi da buduruwa ko d'aya,kuma ya na shaye-shaye"

"A yanda na ji duk gidansu babu me zaman banza,ance ita ma Babyn ta na da wani wurin gyaran jiki a nan Sharad'an,na dai manta sunan wurin".

Na jinjina kai,ina tunanin ashe jiya kamfanin na shi aka kaini,na wuce shi a rashin sani

Na ce"na gode sosai, na ji dad'in bayanan ka,ba wani abun kuma?"

Ya ce"e to,zan iya baki hotunan shi,ina da su kala uku,biyun a ranar birthday d'insa na ga ya d'ora a dp,ya na girmama birthday sosai,d'ayan kuma drivern sa ne ya tura min,da yake abokina ne"

Da sauri na bud'e xenda ya tura min,sannan na rok'e shi lambar abokin na shi,da ya ce drivern shi ne,ya saka min,na yi masa godiya,na bar wurin da mad'aukacin farinciki.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_

BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_

*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.