Matar Shege 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR SHEGE (1).txt
Chapter 7 of 21
Page 7
Ina zuwa manager ya had'ani da wani,ya kaini b'angaren da aikina ya ke,ya na ta yaba kyauna,ni dai binsa kawai nake ina k'arewa wurin kallo,wani holl ya kaini,na ga y'an mata wasu na girmesu wasu sun girmeni,ga kuma sa'annina duk sun ci kwalliya su na zaune,wasu na fira,wasu na danna waya. Wata ya nunawa ni ya ce ta koya min yanda zan gudanar da aiki.Ta matso kusa da ni ta na murmushi ta fad'a min komai,sannan ta d'ora da fad'in"akwai Oga Salim,shi ne me wurin,shi ma ya na zuwa wataran,kuma be cika cin abinci ba idan ya zo,shi ya fi yin shaye-shayen shi,da yake d'an shaye-shaye ne".
Sai na ji kalmar shaye-shayen har cikin raina,na ji ban ji dad'i ba a ganina Salim ya wuce ana danganta shi da wannan kalmar mara dad'in ji,to amma ya zan yi? Tun da halinsa ne dole a fad'a
"Allah ya shirya shi dai" Na fad'a ina sauke numfashi
Ta ce"hmm! Ai ni idan ya zo har na tsani a turani kula da shi wallahi"
"Kula da shi,sai kace wani jinjiri?" Na fad'a a zuciyata
A fili kuma na ce"to ya ake kula da shi?"
Ta ce"ai idan mutum ya shiga ba ya barin d'akin har ya tafi,saboda kai za ka rik'e masa d'an farantin da zai dinga karkad'e tokar sigarin da zai sha,kuma kai za ka had'a masa lemo da maganin tarin nan,idan zai ci abinci sai ya fad'i wanda yake so,ka kawo masa,ga shi ba ya son kallo,sai dai ka duk'ar da kai,ga warin taba shiyasa duk muka tsani a tura mu idan ya zo"
Na jinjina kai,ina mamakin wannan mulki irin na Salim,sai dai sosai hakan ya min dad'i,ko banza zan jima ina ganin shi,kuma zan samu hanyar shigar da kaina cikin sauk'i,na yi farinciki da ba sa son zuwa,ni kam ba warin sigari ba ko na giya ne zan jure.
Muna nan zaune aka yi kiran mutum uku,ni dai ina ta raba ido da fargaba,tunda na ga abun zab'a ake yi,kuma na ga kwalliyata duk ta fi tasu kyau,hakan ya b'ata min rai kad'an.Me kiran mutanen ya na sake shigowa kiran wata na yi sauri na tashi ina fad'in"kai! Ni ce zan je"
Ya ce"ai ke da Oga na yiwa tanadi,amma taho idan kin matsu"
Na yi saurin komawa na zauna na ce"a'a,shikenan zan je wurin ogan"
Ba a jima ba kuwa ya ce na fito,Oga ya k'araso.Na tashi na bi bayansa,sai kuma na ji wata fargaba ta dira a zuciyata,na fara hasashen watak'il Salim ya na ganina zai koreni daga aikin,wannan tunanin ya sanyaya min jiki,haka dai mu ka k'arasa har wani d'aki,ma'aikacin ya ce na shiga yanzu zai shigo
Na hau bin d'akin da kallo bayan na shiga, kujera ce zaman mutum uku,sai wani k'aramin firji da kuma wata loka y'ar k'ara,ga tebur a gaban kujerar me d'auke da k'aramin faranti me kyau sai walwali ya ke,wanda na ke kyautata zaton shi ne na zuba tokar tabar,sai da na kalli teburin da kyau sannan na lura da zanen harafin (J) me kyau sai k'yalli ya ke yi,na kai hannu na tab'a ina tunanin abin da J d'in take nufi.
Ina jin motsin bud'e k'ofa na yi saurin zama a k'asa,nan gaban teburin ina sauraron yanda zuciyata take bugu.
"Assalamu alaikum" Ya yi sallama ya na shigowa,na amsa cikin kashe murya wai ko zan burgeshi
Bai kalli inda na ke ba ya zo ya kwanta rigingine a kujerar,ya fara danna waya
"Ina wuni" Na gaishe shi.
Sai ya juyo ya na kallona,ko so ya ke ya ganeni oho,ya min kallon sakanni ya juya ga wayarsa sannan ya ce"lafiya k'alau".
"Za a kawo wani abun?" Na tambaye shi a d'arare.
Ya yi shiru kamar bai ji ba,sai can kuma ya ce"ina zuwa".
Ganin ya bawa banza ajiyata ya na ta harkar wayarsa sai nima na zuge jakata,na d'akko wayata,na tank'washe k'afa na shiga y'an danne-danne na
Wajan minti talatin mu na haka,sannan ya tashi zaune ya ajiye wayar ya kalleni ya ce"bud'e lokar can ki d'akko min sigari"
Na tashi tsam,na je na bud'e sigarin ce a ciki da yawa,da maganin tari suma kala-kala,sai wasu k'ananun robobi masu murfi,wanda ban fahimci abin da yake ciki ba,gida d'aya na d'akko,na duk'a na ajiye a teburin cike da ladabi
Ya d'auka ya zaro d'aya,ya kunna ya fara zuk'a,ni kuma na d'auki farantin na matso kusa da tebur d'in sosai,sannan na sunkuyar da kai. Ni sai na ji kamar hannuna ya ke ta kallo,ko tsarguwa na yi oho!
Sai da ya shanye su duka,ya na kad'e tokar a farantin,hannuna duk ya sage amma hakan bai sa na ji ina son barin kusa da shi ba
Kamar daga sama na ji muryarsa"Zinatu ki ke ko?"
Gabana ya fad'i,don da na yi zaton bai ganeni ba,ashe ya gane.Na d'ago na kalle shi a d'an tsorace na ce"na'am".
Sai ya kalmashe yatsun sa wuri d'aya sannan ya ce"me yasa ki ke bibiya ta?"
Na yi saurin fad'in"na rantse da Allah ba bibiyarka na ke yi ba Salim,ka fahimceni".
Ya kalleni na y'an sakanni,sannan ya ce"ta ya zan yarda ba Junaina ce ta turoki ba?"
Na ji dam! Na fara nazarin wacece Junaina? Sai kawai sunan na shi ya fad'o min (J.S) to ko dai J d'in ta na nufin Junaina,amma wace ita d'in? Kuma meye alak'ara su?
"Ki na shirya k'aryar da za ki fad'a kenan...". Ya katse min tunani
Bai rufe baki ba na yi saurin fad'in" a'a wallahi,ni ban san wata Junaina ba, kuma ba ni da wata alak'a da ita,babu wanda ya turo ni".
Ya jinjina kai sannan ya ce"ok! To ko dai so na ki ke yi?"
Na ji wani dam! Har numfashina sai da ya tsaya na sakan d'aya,to meyasa zai min wannan tambayar haka kai tssye? wannan ai k'ure ne kuma wace amsa ya kamata na ba shi? Na fad'a masa an kusa aurena,ko kuma na ce masa son shi na ke yi? Kai! Ba zan yi masa k'arya ba,ni dai burgeni ya ke kawai,amma ban sani ba fa ko ya ya kamu da so na ne,kar na je na yi abin da zan yi danasani
Muryarsa ta katseni
"Da ke na ke magana"
"Eh" Na fad'a a tak'aice.
Sai na kalle shi, jin ya yi shiru,na ga hannuna kawai ya zuba wa ido,ban ankara ba na ji ya rik'o hannun nawa me d'auke da zanen J.S,ya k'ura ido ya na kallo na y'an sakanni sannan ya wurgar da hannun ya fara magana
"Me yasa d'azu kika yi min k'aryar burgeki kawai na ke yi? Ba ke ce kika fara furta min kalmar so ba,amma na yi mamakin salonki,kin san meyasa?"
Ni dai na yi shiru kaina a k'asa,na kasa ba shi amsa
Ya ce"ok! Shikenan,ba sai kin ji ba".
Na yi saurin d'agowa na kalle shi,saboda har ga Allah na so na ji dalilin,amma kamar an d'aure bakina na kasa yin magana
Ya tashi tsaye ya na jan d'an bak'in gemunsa da ya k'ara masa kyau ya fara magana"ba na sonki,kuma ba zan tab'a son ki ba"
Na ji wani dum! A k'irjina
Ya d'ora"ke ba ma ke ba,duk duniya babu wata mace da zan so bayan Junaina,ita kawai na ke so kuma ita kad'ai ce matata in sha Allah! Ko na auri wata macen sab'anin ta to fa sai dai ta yi zaman amsa sunan matar aure kawai,don ko gangar jikina ba za ta samu ba bare kuma zuciyata".
Ban san lokacin da na fara kuka ba,sai da na ji d'and'anon gishiri a bakina,na ji wani dunk'ulallen abu ya zo ya tare min mak'oshi,raina ya b'aci sosai,zuciyata ta yi bak'a k'irin,cikin y'an sakannin na fahimci tabbas son Salim na ke yi,da kuma kishin sa me k'arfi.
"Kin gama aikin ki,za ki iya tafiya"
Ya fad'a ya na d'aukar wayarsa,ya saka a aljihu zai fice
Da k'yar na tattaro yawon bakina na had'iya,wai ko zan iya had'iye abun da ya tokare mak'oshi na,sai na samu damar magana.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.