Matar Shege 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR SHEGE (1).txt
Chapter 5 of 21
Page 5
Gaskiya na ji dad'in had'uwa da wannan ma'aikacin,ni sai bayan na tafi ma na tuna ko sunan shi ban tambaya ba,bare lambarsa.Tun a adaidaita sahu nake ta kallon hoton Salim kamar an min dole na haddace kamannin sa kafin cikar mintuna,ya yi kyau sosai fiye da yanda bakina zai iya fad'a, gaskiya shi kyakkyawa ne,sai na ji ya k'ara burgeni fiye da da,na d'aura hoton a fuskar wayata,yanda da na danna zan ganshi,ba sai na sha wuyar shiga wurin hituna ba.
Ranar fa na samu assignment,haka na wuni ina k'are masa kallo,ga wani abu da ya ke ta azazzalar zuciyata,wanda na rasa gane ko na mene,kuma gabana ya na d'an fad'uwa idan na tuna da shi.
Gidan Ummi na wuce don na fad'a mata zancen kawo lefe ranar Juma'a,ina shiga na ci karo da Kawu Ummaru k'anin Ummi,ya na shirin fita daga gidan,na d'an rusuna na gaishe shi,ya amsa har ya wuce ya juyo ya ce"ke Zinatu,kamar ke na gani jiya a cikin adaidaita sahu wajan Sharad'a?"
Na ji fad'uwar gaba,don shaf na manta a wajejen yake aiki,na yi saurin fad'in"a'a Kawu,sai dai ko kama".
Ya gyad'a kai ya wuce,na sauke ajiyar zuciya na shige.Bayan mun gaisa da Ummi na fad'a mata Habib ya ce ranar Juma'a za a kawo lefe,Ummi ta ce"too! Ikon Allah,to Allah ya kaimu"
Na amsa da"amin".
Na ce"Ummi ai dai nan za a kawo shi ko?"
Ta ce"a'a,gwara dai akai gidan babanki Zinatu,y'an'uwana duk za su je,daga baya sai a dawo da shi nan d'in ko?"
Na ce"to"
Sai ta ce"kira min Halima a wayarki,sai na sanar musu gobe su zo mu yi d'an soye-soyen tarar bak'i"
Na kira na mik'a mata,su na fara wayar Umma ta k'wala min kira,na fita ina had'e gira.Nasihar ce dai take ta min,ga shi dole na zauna na ji,tunda Ummi ta na nan,haka dai na yi ta kallon bakinta don ba komai ma nake fahimta ba, hankalina ya rabu biyu,ina ta tunanin da ya ke shirin aurena
"Zinatu!" Na ji muryar Ummi
"Na'am" Na amsa,ina saurin tashi,don dama Umma ta isheni
Sai dai ina shiga wurin Ummi, na yi saranda ganin yanda ta k'urawa fuskar wayata ido,na ji wata fad'uwar gaba,tuni na fara tunanin amsar tambayar da ba a kai ga jefo min ba
"Zinatu wannan kuma waye?". Ummi ta tambayeni
Na yi murmushi na ce"kai Ummi! Saif Ali Khan ne fa,wannan na fiml d'in indiyan,ba ki gane shi ba?"
Na fad'a ne ba don suna kama da Salim ba,sai dan shi d'in ne kawai sunan shi ya zo kaina
Ummi ta ce"to ni da kallo bai dameni ba? Yanzu kalle-kalle ki ka koma kenan,maimakon k'arfafa ibadarki,tunda ba islamiyya kike zuwa ba?"
Na ji dad'in yanda ta yarda da ni,ina kwanciya a katifa na ce"a'a fa Ummi,kawai burgeni ya ke yi wallahi".
Ummi ta rik'e hab'a ta ce"e lallai! Ke da za ki yi aure nan da wani lokaci,shi ne har wani ya ke burgeki?"
"Uhm! Inji me ciwon baki" Na fad'a yanda ba za ta ji ba.
"Abba,ka d'an k'ara min lokaci zan zab'a nan ba da jimawa ba in sha Allah!" Salim ne ke yiwa mahaifin shi maganar cikin son kwantar masa da hankali.
Abba ya ce"yawwa yaron kirki! Ba wai ina son takura maka bane ba fa,amma ina son ka fahimci shi auren zai k'ara maka nutsuwa da hankali,kuma kamalarka za ta k'ara cika,babu mamaki ma ka daina wannan d'abi'ar taka..."
Salim ya sunkuyar da kai ya ce"Abba na daina fa..."
"Za dai ka daina,tashi ka tafi Allah ya yi maka albarka". Mahaifin nashi ya fad'a ya na murmushi.
Bai jima da shiga d'aki ba Baby ta shigo da sallamarta,bakin gadon da ya ke kwance ta zauna,ta rik'o hannunsa ta matse kafin ta ce" Bros tashi mu yi magana,na san ba bacci ka ke yi ba".
Ya bud'e ido,ba tare da ya kalleta ba don kar ta fahimci halin da ya shiga,ya ce"Baby! Ina lafiya,ki je ki huta,za ki rakani J.S anjima".
"Ba zan je ba!" Ta fad'a da k'arfi.
"Dama na sani,matsalarka kenan Bros,haba! Kai fa namiji ne cikakke,son kowa k'in wanda ya rasa,akan me za ka na wahalar da kanka akan wacce ba ta da imani? Ta na neman lalata rayuwarka,amma ka k'i fahimta,na tsaneta!"
Sai ta fashe da kuka,ta tashi ta bar d'akin a guje.Ya yi saurin durowa daga gadon ya bi bayanta.
Ranar Juma'a aka kawo kayan lefena,akwati shida da manyan jakankuna guda biyu,cike da kaya kowa ya yaba da k'ok'arin Habib,kuma aka tsayar da rana sati shida masu zuwa
Hmmm! Sati shidan da suka zame min kamar shekara shida,a cikin sati shidan nan komai ya faru,idan na ce komai ina nufin komai da komai,a cikin wa'innan satuttukan ne na aikata kurakurai da dama,wanda su ka jefani halin da nake ciki a yanzu,ko ma na ce k'addara.
To k'addara mana! Duk wanda ya ce so ba k'addara bane,to bai tsinci kanshi a irin halin da so ya sakani ba
Kallo d'aya tak! Ya jefani a manyan matsaloli.
A daren juma'ar su Anti Halima suka kwashi kayan,su ka maida shi wurin Ummi,ni kam ko kallon tsanaki ma ban tsaya na yi musu ba.Bayan sallar isha'i Baba ya kirani,ya ke tambaya ta wasu irin kayan d'aki nake so?
Sai na ji duk jikina ya yi sanyi,tunda na fara gane da gaske dai auren zan yi,kuma da Habib,na kwantar da murya na ce"Baba ba ni da wani zab'i,duk wanda aka samu na gode".
Baba ya ce"to ma sha Allah! Zinatu kin ga dai ni ba me k'arfi bane,sai dai rufin asiri,don haka zan yi miki iya k'arfina.Kuma don Allah ki k'ara nutsuwa,ba na son na sake jin wani ya kawo min k'ararki,ki nutsu mu samu mu rabu lafiya,kema auren shi ne kwanciyar hankalinki".
Na amsa da to, sannan na tashi na koma d'akina,kwanciya na yi rigingine haka kawai na ji saukar hawayen da ban san ko na meye ba.Na d'akko wayata cikin rashin sanin abun yi na kira layin Salim,har ta katse bai d'aga ba, sai na yi masa sak'on fatan alkhairi,nan ma dai bai dawo min da shi ba.
Washegari da misalin k'arfe goma na shirya tsaf,cikin dogon hijjabina har k'asa,na fita na tari adaidaita sahu,ban tsaya ko'ina ba sai ALBARKA
Ban samu matsalar shiga wurin ba,don na sanar musu Salim ya san da zuwa na,sai dai ina zuwa k'ofar office d'in na tarar da wata matashiya,kuma ta ce min sai ya bada izini ake shiga,don haka na dakata ta yi min iso
Na jinjina kai,ina fad'a mata sunana Zinatu,ba ta jima ba ta fito ta ce min na shiga
Gabana ya yi fad'uwar da ban tantace ko ta meye ba,na san dai ba ta rasa nasaba da rashin k'wakkwaran dalilina na zuwa wurin,da kuma yanda Salim zai yi idan na fad'a masa k'arya nake ba kaya zan siya ba,sai kuma uwa uba yanda zai karb'i maganar da zan yi masa yanzun
Da sallama na shiga a nutse, kai sai ka rantse ba ni bace,na tadda shi zaune a kujera ya na danna waya,da jarkar coca cola a kan teburin,sai d'an k'aramin kofi
Ya yi masifar kyau,yau sanye yake da manyan kaya,wani yadi ne dak bulu da bak'ar hula a kanshi,ga bak'in agogo sanye a hannunsa
Idona ya sauka a bayan wayarsa,me d'auki da hoton wata budurwa me kyau,ban san ko wace ba,amma na fi kyautata zaton ita ce Baby
"Wa alaikissalam" Ya amsa da muryarsa me dad'i,ya na min nuni da kujerar da take fuskantarsa alamar na zauna.
"Na gode" Na fad'a bayan na zauna d'in.
Shiru na d'an lokaci kafin na ce"Zinatu ce".
"Na gane" Ya fad'a ya na ajiye wayar.
Na d'an yi jim,na sauke ajiyar zuciya,ina jin wani sanyi da ya ke shiga kowace kafa ta jikina,kar fa ku ce ko sanyin Ac ne,a'a,wani irin sanyi ne da rasa yanda zan yi muku bayanin sa,ni dai na san k'alau na shigo wurin da sai na ce zazzab'i nake yi
Na d'an yi gyaran murya,wai ko za ta k'ara dad'in sauraro na fara magana"da farko dai zan fara baka hak'uri na rashin zuwa na jiya..."
Ya katseni"ai shiyasa nake son ki hanzarta,don yau ba ni da appointment dake"
"Hakane,na gode da bani dama" Na fad'a ina muskutawa,sai gyara zama nake kamar me nak'uda.
"To a gaskiya ba zan b'oye maka ba Salim...ba da gaske na ke ba, da na ce maka zan yi siyayya a kamfanin ku..."
Ya katseni"e na sani,kuma ba na neman dalilin k'aryarki,dalilin zuwan ki yanzu na ke buk'ata".
Na kalle shi,na ga ni ya ke kallo,irin kallon nan na ido cikin ido,nan da nan ya yi min kwarjini,sai na ji duk na muzanta,na ji dama ban zo ba ma,To wai ma me ya ke damuna ne? Meye hakan na ke ta yi? Me zai sa na zubar da ajina na zo har wurin shi? To ko dai son shi na ke yi? Kai ba haka ake so ba,so ba rana d'aya ake fara shi ba,kamar yanda Habib ya fad'a min,na dai fi yarda Salim burgeni kawai ya ke yi...
K'was! K'was! Ya buga teburin gaban shi,da wani had'addan zobe dake yatsan shi na tsakiya.Ban gama dawowa cikin nutsuwata ba na ji ya ce"kar ki min k'arya,don ita ce abin da na fi tsana,kuma idan ki ka min k'arya ba zan sake sauraron kalma d'aya daga bakinki ba.Meye dalilinki na bibiyata?"
Dum! Dum! In ji k'irjina,na sanyaya murya kamar marainiya na ce"wallahi Salim haka kawai na ji ka burgeni,idan ba damuwa ina son k'ulla alak'a da kai,ko da ta abota ce,ka zama abokina don Allah"
K'urr! Ya tsaya ya na kallona,sai kuma ya dafe kanshi da duka hannunsa biyu,ya lumshe ido,ina ta fargabar yanda zai d'auki zance na,har tsawon mintuna ya na haka sannan ya d'ago ya zube idonsa akina.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.