Matar Shege 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR SHEGE (1).txt
Chapter 8 of 21
Page 8
"Na yarda zan yi zaman amsa sunan matar auren,in dai aurenka ne!". Na fad'a kamar wanda ya bani zab'i
Sai ya juyo ya min wani kallo me kama da harara,ban damu ba na d'ora da fad'in" ban damu da gangar jikinka ba,ko ban samu zuciyarka ba babu matsala,ganinka ma kawai zai wadatar da ni".
"Don Allah!" Na fad'a ganin ya tsaya kallona.
Sai kawai ya buga tsaki ya bar d'akin.Na jima zaune a wurin ina hawayen rashin gaskiya,to rashin gaskiya mana,idan ba haka ba har yaushe na fara son Salim da zan ji yanda na ji yau don ya fad'a min ba zai tab'a so na ba? Duka fa ban dad'e da sanin shi ba, ko gidansu ban sani ba bare iyayenshi.Kuma ni da na ke shirin yin aure nan da sati shida me ya kaini jefa kaina a irin wannan matsalar?
"K'addara!" Zuciyata ta ba ni amsar da ta gamsar da ni
Ina nan zaune a wurin manager ya turo k'ofar ya shigo d'akin,ya buga min wata kafirar harara kafin ya ce"wallahi yau da kin sa an kore mu daga aiki sai mun sa an rushe gidan ubanki! Shegiya me bak'ar k'afa,daga zuwanki yau kin b'ata ran Oga,har ya na zancen zai rufe gidan..."
Bai k'arasa ba na zabura na mik'e,hankad'ani aka yi? Tsalle na yi,iska na bi,duk ban sani ba amma ni dai idan na ce k'arasawa ta wurin shi na yi sakan d'aya na yi k'arya,na wanke shi da wani zazzafan mari,don har hannuna sai da ya d'auka,ina huci kamar zakanya na ce"k'arya ka ke yi wallahi! Ubana ya fi k'arfin ka,kuma kai k'aramin d'an iska ne,iskancin lungu ka ke yi,ka biyo ni eriyata ka gani don ubanka!".
Ina gama maganar na fice daga office d'in,zuciyata na tafarfasa,ni na yi zaton ma zai biyoni wallahi,amma sai na ji shiru,watak'il hak'uri ne da shi,ko kuma ya ji tsorona ne oho! Shi dai ya sani
Adaidaita sahu na tare na shiga na fad'a masa inda zai kaini,duk da hasken da ke titi tarwai bai hanani gane dare ya yi ba,na share hawayen da suka zubo min,na kifa kaina da guiwa ban d'ago ba har sai da me adaidaita ya ce min an k'araso
Sauka na yi,ina shirin duba jaka na d'akko masa kud'insa,jaka ta ce d'aukeni inda ki ka ajiyeni,sai yanzu na tuna ko jakata ban tsaya d'auka ba,tana office d'in Salim,takaici ya rufeni kamar na saka kuka na kalli me adaidaita na ce"ka ga na manto jakata a inda na je,don Allah ka yi hak'uri na tsallaka,naje gida sai na d'akko maka".
"Kutt! Amma dai kin san ko yaro ba zai yarda da wayon ki ba ko? Malama sallameni tun ranki bai b'aci ba!" Ya yi maganar ya na fitowa daga ciki ya murtuke fuska
Muna tsaye muna jayayya sai ga hannu d'aya ya zo wucewa.Hannu d'aya abokina ne,tsabar k'arfin sa ne yasa ake ce masa hannu d'aya,don ance duka d'aya yake wa mutum ya baje
Na yi farinciki kuwa,na k'wala masa kira daga inda muke,ya k'araso cikin takunsa na masu k'arfi ya na k'ara bubbud'ewa ya ce"kai! Zinatu tamu,me ki ke yi a ta nan da daddare?"
Na kwashe duk yanda muka yi na fad'a masa
Ya yi wa me adaidaita wata dank'a,ya matse wuyansa ya ce"kai! Har ance maka za a kawo maka kud'inka amma ka tsaya ja da ta wajanmu?"
Ya fizge daga rik'on ya ce"ai hakki na ne,dole ta ba ni,ba wani shege wallahi!"
Hannu d'aya ya ce"kai! To da alama ba ka da iyalai,idan kuma akwai to maza ka musu waya ka sanar da su inda za su zo su kwashe ka"
Sai ya karkace ya zaro wuk'a y'ar k'arama ya cakumo shi
"Na shiga uku! Ni fa ban saka ba don Allah kar ka sa caka masa"
Na fad'a cikin rud'ewa,don har rik'e hannunsa na yi.
Mai adaidaita ya rud'e ya shiga ba shi hak'uri, sai ya hankad'a shi kusa da ni ya ce"au! Ka ce kai shege ne? To duk'a ka bata hak'uri".
Ba shiri ya zube a gabana ya na bani hak'uri, har abun ya bani dariya,na shiga yinta
Hannu d'aya ya ce"za ka ware ko sai na maka d'ayan? Don dai hakkin ka ne da yau babarka ba za ta ganeka ba,k'aramin d'an iska!"
Shi dai bai tanka ba ya shiga mashin d'in ya ja shi a miliyar.Wannan abun shi ya d'an wanke min zuciya ya rage min damuwa,muka jero da Hannu d'aya ina fad'a masa inda na je.
Na yi mamakin ganin gidanmu a bud'e,tunda na san Baba da wuri ya ke rufe k'ofa,na tura na shiga da fargaba.A tsakar gida na tadda Baban ya na zaune ya zuba tagumi,na yi sallama na zo zan wuce shi sum-sum
"Zinatu!" Ya kira sunana da alamun fushi
Na dawo ina d'an rage tsayina na ce"na'am Baba".
Ya ce"daga ina kike?"
Na yi shiru kaina a k'asa
Ya nisa can ya ce"wata rayuwar kuma ki ke shirin shiga ko Zinatu?"
Lokaci d'aya na gane inda zancen sa ya dosa,kuma na ji babu dad'i a raina,da k'yar na bud'e baki na ce"a'a Baba,daga wurin aiki na ke wallahi".
Bai kulani ba ya shige ya je ya rufe gidan,ya dawo ya shiga d'aki.Ni ma na yi d'akina,ko kaya ban canza ba na kwanta ina tunanin ta yanda zan samu jakata da wayata.
Ni dai ba zan koma wurin ba,musamman yanda na mari manager, sai dai na tura Hannu d'aya ya amso min,amma kuma ina tsoron manager ya sa a kama shi fa,da dai wannan zulumin bacci ya kwasheni.
Da asuba bayan na idar da sallah,na je na gaida Babana,ya amsa babu yabo babu fallasa,har zan tashi ya na ji muryarsa ya na cewa"Zinatu! In dai na isa da ke,to daga yau kar ki sake fita ko k'ofar gida,har sai ranar aurenki,ko Habibu ne ya zo ya shigo cikin gida".
Gabana ya yanke ya fad'i,nan take zuciyata ta shiga bugu don kuwa na ji Baba ya na bani umarnin da ba zan iya yi masa biyayya ba
"Amma Baba jiya na manta wayata a wurin aiki,yau zan je na karb'o". Na fad'a kaina a k'asa.
Baba ya min shiru kamar bai jini ba,har tsawon lokaci,ganin haka na san ba zai yi maganar ba,watak'il ya amince ne ko kuma ya yi fushi da maganata,ni dai na tashi na koma d'akina na kwanta ina ta nazari.
Salim gida ya wuce kai tsaye,zuciyarsa na tafarfasa,ya kwana biyu bai shiga irin wannan halin ba,ya na takatsantsan da duk wani abu da zai sa ya tuna farkon had'uwar shi da Junaina,shi yasa ko kad'an ba ya shiga sabgar wata macen.Duk da Junaina ta na cikin rayuwar shi har yau,har gobe ma amma ba ya son tuna farkon k'ulluwar alak'ar shi da ita
Baby ce ta shigo d'akin,kallo d'aya ta yi masa ta san ya na cikin damuwa,ta k'araso ta zauna a kujera ta ce" akwai matsala ne Bros? Me ya ke damun ka?"
Ya yi shiru ya na kallonta,sai ta d'age kafad'a ta ce"ai na sani,wannan yarinyar ba za ta tab'a barinka ka ji dad'in rayuwa ba,ta hana ka aure,kuma ita ta k'i ta aureka! Ka duba fa ka ga yanda ta maida kai,ta na son haukata ka,ta maida kai d'an maye,amma ka k'i rabuwa da ita,meyasa?"
Ya sauke numfashi da k'arfi ya ce"a'a Baby,da gaske na rabu da Junaina,farincikin ki shi ne nawa.Wata ce yanzu ba ita bace".
Baby ta share hawayen da ya zubo mata ta ce"da ka damu da farinciki na da tuni ka yi aure Bros.Ka fito Ammi ta na kiranka".
Daga haka ta bar d'akin ta na hawaye,ya tashi ya bi bayanta ya na jin damuwa sosai da hawayen y'ar'uwar tasa.
K'arfe takwas na safe Ummi ta aiko wata y'ar mak'otan su,na zo ta na kirana,na d'an tsorata da kiran,ina tunanin watak'ila an fad'a mata an ganni jiya da daddare,haka dai na shirya wajan k'arfe goma na tafi gidan
Tun zuwana jikina ya yi sanyi,ganin damuwa a fuskar Ummi,na gaisheta ta amsa babu yabo babu fallasa,na tashi na je d'akin Umma na gaishe ta,wai ko zan d'an y'antu a wurin Ummi,na dawo na zauna na sunkui da kai kamar a gaban malamina na ke.
Shiru na d'an lokaci,sannan Ummi ta ce"wai ke Zinatu me yasa ba kya jin magana? Ni fa gabad'aya na rasa inda ki ka sa gaba,ban san me ki ka d'auki rayuwa,ki fad'a min abin da ya ke ranki!"
Na yi shiru,idona ya ciko da k'walla.Ta d'ora da fad'in"jiya Ummaru ya ke fad'a min ya ganki a kamfani wai kin je neman aiki,da wa ki ka yi shawara Zinatu? Ko mahaifinki ne ya tura ki?"
Sai na ji sanyi a raina,tunda ba laifin jiya da daddare bane,ni har na manta ma mun had'u da Kawu Ummaru,dama na san bakinsa ba zai yi shiru ba,na tausasa murya na fara magana
"Don Allah Ummi ki yi hak'uri, ban yi da wata manufa ba,ni na je neman aikin ne saboda na rage muku wani nauyin akan auren nan,amma tunda ba ko so ba,na bari in sha Allah".
Ummi ta ce" haba Zinatu! Waye ya fad'a miki ba za a yi miki komai ba? Kuma ko za ki nema da kanki tun da ba ki yi ba sai yanzu da aski ya zo gaban goshi? To ki kiyayeni Zinatu,abun naki ya isheni haka!".
Tuni hawaye su ka zubo min,na dinga ba ta hak'uri, har sai da na ga alamar ta hak'ura sannan na ce mata zan tafi, ba ta bari na tafi ba sai da ta bani abin kari na ci na k'oshi.
Mai hali dai ba ya fasa halinsa,ina fitowa daga gidan su Ummi kai tsaye laundry d'in Salim na wuce,yau ma da na je ban sha wuyar ganin wannan ma'aikacin da ya bani bayanan Salim ba,mu ka gaisa na rok'e shi ya kwatanta min wurin gyaran jikin Baby k'anwar Salim
Tiryan-tiryan ya kwatanta min,na yi masa godiya na kama hanya.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.