Matar Shege 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR SHEGE (1).txt
Chapter 6 of 21
Page 6
"Ban amince ba". Ya fad'a a sanyaye
Na ji zuciyata ta motsa,na kalle shi,sai ya lumshe ido ya na nuna min k'ofar fita daga office d'in
"Don Allah Salim". Na fad'a a kasalance,idona su ka ciko da k'walla
"Tashi ki fita" Ya fad'a,ya na janyo lokar dake jikin teburin.Ban fita ba,sai ma kallon sa da na tsaya yi,ina son ganin abin da zai d'akko
Wata kwalba ya fito da ita,ta maganin tari ya janyo robar coca cola ya bud'e ya juye maganin a ciki duka,ya jijjiga ya kafa kai ya na kwankwad'a ya na kallona
Ko wani bai fahimtar da ni ba,na san hakan ya na nufin shaye-shaye kenan,cikin inda-inda na ce"Salim! Me hakan ya ke nufi? Me kake sha?"
Ya ajiye robar ya ce"yanayin ku d'aya! Kalaman ku ma iri d'aya ne,ko ita ta turoki ki gwadani?"
Gabana ya fad'i,to ba dai giya ya sha ba,bare na ce har ya fita daga hayyacinsa,ina cikin nazarin na ga ya d'auki waya ya yi kira"zo office d'ina". Abin da ya fad'a kenan
Ba a jima ba kuwa sai ga wani ma'aikaci ya shigo,tun kafin ya k'araso ya yi masa nuni da ni ya na fad'in"fita da ita,kuma ka fad'awa Godiya kar a sake bari ta shigo!"
Na bugawa ma'aikacin wata kafirar harara,ganin ya na shirin tab'ani,sannan na tashi a sanyaye na fita,ina waiwayen Salim idona taf k'walla.
Ina fitowa daga office d'in na ji na kasa rik'e hawayen,ina jinsu su na ta zuba amma ban damu da gogewa ba,ko kuma na tsaida su
Sai dai dab da zan fita daga wurin na gamu da Kawu Ummaru zai shigo,gabana ya yi mummunar fad'uwa,na yi wani wawan ribas na juya don komawa ciki,ashe na makara don kuwa ko taku uku ban yi ba na ji ya kira sunana da alamaun mamaki
Duk k'ok'arin da na yi na ganin na tsaida hawayena kafin na juyo abu ya ci tura,har sai da ya sake kiran sunana sannan na juyo ina share hawaye
"Zinatu me kika zo yi a nan?" Ya tambayeni har yanzu da mamaki a fuskarsa.
Dabara ta zo min na ce "Aiki na zo nema".
Sai ya bud'e baki da mamaki ya ce" aiki kuma? To an d'auke ki?"
Na girgiza kai alamar a'a
Ya ce"banda shirme ki taho neman aiki ba tare da shawara ba? Kuma ba jiya na ji ana zancen kayan lefenki ba? Ko kuma shi Habib d'in ne ya ce ki nemi aikin yi kafin auren?"
Na cigaba da hawayena,ba tare da na ba shi amsa ba. Sai ya wuce ya barni tsaye ina goge hawayen
To bayan na fita daga wurin a maimakon na yi gida,sai na yi 7:30 restaurant,ina ta rarraba ido bayan na shiga wurin,sai na je wurin wani da nake kyautata zaton ma'aikaci ne,tunda ga shi da uniform me d'auke da sunan wurin,na yi masa sallama ya amsa
Sannan na ce"don Allah zan iya ganin manager?"
Ya ce"e ba matsala,ga office d'in shi can".
Na shiga k'ofar da ya nuna min da sallama,aka amsa ana yi min izinin shigowa,wani matashi na gani kwance akan doguwar kujerar dake office d'in
"Hajiya barka da zuwa" Ya fad'a ya na tashi zaune
"Barka" Na ce,ina zama a wata kujerar
Na ce"alfarma na zo nema"
Ya ce"to,ta mene?"
Na d'an cije baki kafin na ce"don Allah aiki nake nema a wurin nan".
Ya ce"tabb! Aikuwa baiwar Allah, ba mu jima da k'ara ma'aikata ba,yanzu dai sun wadata gaskiya ba ma buk'atar k'ari".
Na yi saurin fad'in"don Allah ka taimakeni,ko da shara ce ko wanke-wanke"
Ya ce"zancen kike so"
Na tausasa murya na ce"don Allah ko kyauta ne ni zan dinga aiki,idan ya so duk wata ka dinga rik'e albashina,na bar maka...".
Ban k'arasa ba ya tareni"ok, ba sai ta kai nan ba,zan iya baki aiki,amma fa ba wanda kike zato bane idan za ki iya duk wata za ki samu kud'i fiye da zaton ki,amma nima za ki na bani wani abun k'arshen wata"
Na yi saurin fad'in"e na yarda, in dai a wurin nan ne".
Ya ce"a anan ne ba matsala.Wurin namu b'angare biyu ne,akwai wurin da masu kud'i suka fi zama idan sun zo cin abinci,to za mu saka ki a cikin wa'inda za ki na kai musu abinci,wasu kuma sukan buk'aci wata ta zauna ta tayasu fira,ke wani ma idan firar ta yi dad'i har ya buk'aci ki raka shi wani wurin,to ta nan ne ake samun kud'i daga hannunsu,ga kuma albashinki me tsoka,dad'in dad'awa ma ku da kayan gida za kuna zuwa,amma fa sai kin kula da kwalliya mai d'aukar hankali".
Na jinjina kai bayan na gama sauraron sa,na ce"babu matsala zan yi".
Ya ce"yawwa! Amma dutyn dare za ki na yi,saboda na ga kina da kyau sosai,Allah yasa dai za ki iya aikin".
Na yi murmushi na ce"kar ka damu zan iya.Yaushe zan fara zuwa?"
"Tun daga yau" Ya bani amsa,sannan ya tambayi cikakken sunana,na fad'a masa,ya tashi ya rubuta a wani littafi,mu ka yi musayar lambar waya sannan ya ce zan iya tafiya.
Na yi masa godiya,na fito daga wurin ina jin wani farinciki sosai.
Yanzun ma ba gida na yi ba,kasuwar sabongari na wuce na yi siyayyar kayan kwalliya kala-kala da turaruka masu k'amshi,domin inganta aikina.Gidan Ummi na wuce kai tsaye,bayan na gaisheta na tashi na yi alwala na yi sallar azhar,don lokacin k'arfe d'aya saura kwata, ta zubo min abinci na ci kad'an na tashi zan tafi,ta ce min"kin ga kayan naki kuwa?"
Na gyad'a mata kai,alamar e,ta na murmushi ta ce"Habib ya yi k'ok'ari sosai,Allah dai ya baku zaman lafiya".
Ban amsa ba na fice ina yi mata sai gobe.
To daga nan kuma gidansu Kamisu na wuce,wani a k'asan layinmu da mu ke mutunci da shi,na yi sa'a kuwa ya na nan,zaune akan benci na tadda shi a k'ofar gida,na zauna a bencin nesa da shi,ina tambayarsa ya garin
Ya ce"normal wallahi,kin yi wuyar gani, sai jiya nake jin ashe auren ya kusa?"
Na yi murmushi na ce"haka aka ce".
Ya ce"a,ban gane haka aka ce ba?"
Na yi y'ar dariya na ce"share kawai,kamar na ji ance k'anwarka ta na yin lalle ko?"
Ya tab'e baki ya ce"wai Nana? Ko yanzu ma shi na fito na barta ta na yi"
Na ce"yawwa! So nake don Allah, d'an kad'an za ta yi min"
Ya ce"ok,mu shiga to"
"A'a,ta fito dai ta min,sauri nake".
Na fad'a ina d'akko wayata da ta fara ringing. Habib ne me kiran,na d'aga,bayan mun gaisa ya ke ce min yau zai shigo da daddare,na ce masa a'a sai dai da yamma,don ina da abin yi da daddare,ya amince muka yi sallama
Na kalli Nana dake tsaye na ce" yawwa Nana,kinga ba me yawa bane,da na iya rik'e lallen ma da kaina zan yi, harafin (S) kawai za ki zana min babba a nan"
Na yi maganar ina nuna mata bayan hannuna.Nana ta zauna a benci nima na zauna,ta zana min kamar yanda na buk'ata,sannan ta cike tsakiya da jan rani,hannun ya yi kyau sosai kuwa,na mik'a mata d'ayan na ce shi kuma ta zana min J.S,nan ma ta zana min,sannan ta saka min a y'an yatsuna ,na yi mata godiya na ce ta zuge jakata ta d'auki d'ari biyar,ta ce a'a na bar shi,ta shige gida.
Kamisu ya kalli lallen ya ce"amma Zinatu na ga dai sunanki daga Z ya fara".
Na yi murmushi ina kallon hannun da na shanya shi s titi na ce"hmm! Share kawai Kamisu,wai ka ji y'an drugs sun k'wamushe Salisu ko?". Daga haka mu ka shiga wata firar.
Da yamma Habib ya zo kamar yanda na ba shi lokaci,ya kwashi surutun sa ya k'ara gaba,don ni kam duk rabin hankalina ya na ga yanda aikina zai kasance,ya ce dai da daddare amma ban san ko k'arfe nawa ake tashi ba,yanzu idan za a kai dare sosai wace k'aryar zan yi wa Baba akan fita ta kullum? Wannan tunanin ya d'an sanyaya jikina,amma fa bai canza min k'udirina ba.
Ana fara kiran sallar isha'i,ina kammala shirina,doguwar riga na saka dama duk ta fi burgeni cikin kayana,na zauna na rangwad'a kwalliya,na nad'e kaina da mayafi kalar takalmin da zan saka,na baza turare bayan humrar da na yi wankanta,lokaci-lokaci nake kallon k'unshin hannuna na yi murmushi, kamar dai an bani tabbacin yau zan had'u da shi,na saka takalmina me tudu,na rayata jaka y'ar k'arama na fito
Mama Saude da ke kwashe tuwo ta bud'e baki ta na kallona,na tsuke fuska ina shirin wuceta na ji ta ce"Allah me iko! Zinatu wannan kwalliyar fa? To ko dai dawo da bikin yau aka yi bani da labari?"
"Wurin dinner k'awata zan je" Na fad'a don kar ta had'ani da Baba,na fice daga gidan cikin sauri-sauri.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.