Matar Shege 1 Complete Hausa Novel
Reading file: MATAR SHEGE (1).txt
Chapter 3 of 21
Page 3
Habib d'an'uwana ne,mahaifinsa da mahaifina uwa d'aya uba d'aya suke,a unguwar Tudun wada gidansu ya ke,kuma shi ne babba a gidansu,ya na da k'annai mata harda sa'anni na,amma ba ni da wata mu'amula da su,sai dai idan mun had'u a sabga ta y'an'uwa mu gaisa.Ya na so na tun ina cakuikuya ta,tsananin son da ya ke min ne ma ya sa ya fara bani tausayi har na ke sauraron shi,don idan na ce ina son Habib na yi k'arya,sai dai zan iya cewa ya na burgeni da kuma k'auna ta jini.Shi likitan ido ne a asibitin Nasarawa,ba k'aramar wuya ya ci ba wurin shawo kaina har na amince da auren shi,kuma sosai ya ke bin duk wani sharad'in da na gindaya masa kamar mahifiyarsa,duk wata sai ya k'irga dubu goma ya bani,ya ce na yi k'ananun buk'atuna,duk dan kar abun hannun wani ya hure min ido,nasiha ba ranar banza sai dai idan bai zo ba.
Tun ranar da aka saka ranar auren mu,ya tare abokaina Anas da Hamza,wanda na fi shak'uwa da su duk cikin abokaina,ya yi musu gargad'in babu su babu ni,kar ya sake ganin sun kula ni.
Anas ne ya zo har gida ya ke fad'a min,aikuwa nan take na yi wa Habib kiran gaggawa.Aikuwa ya sha madarar bala'i ranar,sosai na nuna masa muhimmancin abokaina,na gargad'e shi kan ko kallon banza ya yi wa wani daga cikin su,to a bakin auren shi,don wallahi a ranar zai kar'bi kud'in auren shi.Nan ya yi ta bani hak'uri, duk ya rikice,har ya so bani tausayi ya ce ya ji,ya yarda,babu ruwan shi da su.
Bayan isha'i ya zo,mun d'an jima muna fira har ya ke sanar min wani satin za a kawo kayan lefe,shirin sa kawai ya ke cikin zumud'i,da farinciki.Ni kuwa tsakanin farinciki da akasin sa ban san wanda zan ce ina ji ba.
K'arfe goma na dare na sake gwada lambar Salim amma har yanzu ba ta shiga, ni sai yanzu na ga ragon azanci na,da ban tambayi wurin da aka ce ya ke aiki ba, sak'o na aika masa kamar haka _"Amincin Allah ya tabbata a gareka,ina yi maka fatan alkhairi,da kuma fatan dawwamar farinciki a zuciyarka,murmushi ya tabbata a kyakkyawar fuskarka har abada"_,
_"Daga Zinatu"_.
Na yi murmushi kamar ina da tabbacin ya gani,na yi addu'a na kwanta da tunanin sa.
Salim ya na zaune ya na chatting sak'on ya shigo wayarsa,ta'be baki ya yi bayan ya gama karantawa,ya na jinjina haukan wasu matan.
Washegari tun da safe na aika masa sak'on fatan alkhairi,kuma na sake gwada kiran layin nashi bai shiga ba,don haka na fita na siyo sabon layi, ina saka shi a waya,ban yi sanya ba na loda kati nadoka wa Salim kira,lokacin k'arfe goma da rabi na safe,har ta katse bai d'auka ba,hakan ya sa na sake danna wani kiran,sai ya d'aga da sallama, na tashi zaune k'irjina yana bugu,don ban shirya abin da zan fad'a masa ba,tunda ban yi zaton zai d'aga ba,haka na daure na amsa sallamar sannan na gaishe shi,ya amsa kafin ya ce"da wa nake magana?"
"Zinatu ce,don Allah ka saurareni". Na fad'a ina fargabar zai saurareni ko zai kashe wayar?
Guntun tsaki ya yi kafin ya ce"to ya aka yi? Ki na ta takura min fa,za ki fara shiga hakkina!".
Da d'an fad'a ya yi maganar,hakan ya sa ni nutsuwa,na d'an yi nazari na y'an sakanni,can na tuna me adaidaita sahun nan... ya fad'a min shi ne yake kula da kamfanin su na Sharad'a,sai na yi saurin fad'in"e... dama akan kamfanin ku ne,na Sharad'a..."
Na d'an dakata don na ji yanda zai d'auki zancen,amma sai na ji ya yi shiru,alamar ya na jira na cigaba
Cikin in'inar da ban san ina da ita ba sai ranar na ce"e da dama, shi ne na ke son...na yi siyayya".
"Siyayya ta me?" Ya tambayeni.
Nan fa k'irjina ya bada ras! Na rasa abin fad'a, tunda ban san sunan kamfanin bama,bare na san abin da ake siyarwa,wannan fa shi ne ga k'oshi ga kwanan yunwa,ga shi ya bani lokacin sa,kuma damata ta na neman kufce min,to aiki ne na fara shi sama ta ka babu shawara...
"Ina da abin yi fa" Muryarsa ta katse min tunani.
Dabara ta fad'o min na ce"idan babu damuwa mu had'u a office mana?"
Ya ce min"ai dole sai na ji yanayin cinikin naki,idan babu yawa ba sai kin ganni ba ma,don yau ina hutu ba na zuwa kamfani".
Na d'an tsorata,don ba na son ya taro jirgina,hakan yasa na yi ta maza na ce"gaskiya da yawa,don za mu yi wajan mota uku".
Sai da na kai k'arshe kuma na ji tsoro,yanzu idan gwalagwalai suke siyarwa fa? Shi ne zan siyi mota ukun? Lallai na iya tarar aradu da ka!
"Zan iya ganinka?" Na fad'a, jin ya yi shiru.
"Ok,gobe litinin sai ki shigo k'arfe d'aya na rana"
Ya katse kiran,bai jira amsata ba.
Hmmm! Na sauke ajiyar zuciya,ina tunanin yanda goben za ta kasance,can kuma sai na zaro ido da na tuna ai ban ma san kamfanin ba,ya ilahi! Yanzu kuma idan na tambaye shi adreshin kamfanin ai na kwafsa,sai ma ya d'agoni,na san dai Sharad'a da girma take,ta ina zan fara neman wani kamfani? Phase 1 zan je,ko phase 2,ko kuma 3 d'in zan yi? Da na san sunan wurin ne ma to da sauk'i,amma gaskiya ba zan tambaye shi ba,don wannan babbar damar da na samu ba zan bari ta kufce min ba.
Da tunanin mafita na yi wunin ranar,ko k'ofar gida ban fita ba,jikina duk ya yi sanyi,ina jiran zuwan gobe.
*MATAR SHIGE...!*
_(Ba ta daraja)_
BY
*SADIYA ABDUL*
_(Maizafafa)_
*☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.