Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 41
💜💜💜💜💜
💛💛💛💛💛
"Nene tace ooo duniya ina zakije damu yaran zamani sai a barku in kuna hira da samari har aro murya kuke ko makale ta Allah ya kyauta muku ummmm!!!!
"Tashi Fa'iza tayi tabar dakin Kunneta makale da wayar ganin Nene tana Mata hayaniya taki ta kyaleta ta yi hira da habibinta
"Na'ima ta kalli D'ija tace to kinga yadda A ke soyyaya ko yarinya babu Abinda kika iya sai shirme haka zamu kaiki Siyama ta mayar dake gora a gidan
A kull !! Bakinki ya sari danyan kashi inji Nene taci gaba da cewa Ai babban goro sai magogin karfe D'ija na baza tayi goranci ba a ko ina ballan tana a gidan Ali D'ija na Mowa ce a ko'ina to kaji!!!
Mtssss D'ija taja ta gyara kwanciya gadon Nene gami da lumshe ido ita kadai tasan Abinda yake damun zuciyarta
Da kallo suka bita Nene takama Baki tana kallon N'ima da ido tace tashi ma ni kinzo kin dameni kinga waccan kwallar ta aje kubude a kwai ganyan Magarya da kaikayi debu su ki tafasa ko wanne daban daban zaku fara Amfani dashi ne dukkaninku
Mikewa Na'ima tayi ta dauko ledar magungunan tayi waje dasu a hannuta tasamu babbar tukunya ta zuba ruwa sosai ta daurasu a kan wuta
Delu ce tashigo cikin Sallama suka gaisa da Nene cikin mutumci delu tace A,a Uwar masu gida har yanzu bata tashi ba ne ?
"Wai gowa D'ija tayi tana dariya kadan domin delu mutuniyarta ce tun tana yarinya tace tuntuni natashi delu ina kwana??
"Lafiya lao Uwata kun tashi lafiya"
Lafiya lau D'ijan tace ! Nan Delu ta zauna ta dinga kwantar wa da D'ija hankali har da yi Mata misali su a lokacinsu su basa sanin miji ake daura maka Aure dashi
"Nene tace kwarai kuwa nima Abinda nake fada mata kenan tayi hakuri in Sha Allahu ita CE da riba
Nene tace yawwa Angama hada kayan gumbar nan ko delu!??
Eh duk an hada an ma fara Aikinta karshenta ma kiga anjima an kawo ta inji delu.
Tace Ai nasa Sallau yatafi can ruga ya samo mana nono mai kyau yanzu nan zaki ganshi ya dawo jarka biyu nace yasamo
Yawwa delu inji Nene tace maganar wannan bakar zumar fa ??
Eh itama za'ayi in Sha Allahu ni da kaina zanyi ta kin San yaran yanzu duk basu Santa ba tunda tamuce ta mutan da !!
Hakane cewa Nene tace Allah dai yasaka da Alkairi ya bar zumunxhi
Babu komai cewar delu ai duk an zama daya Allah dai ya sanya Alkairi yabasu zaman lafiya
*Amin Amin*
Nene tafada Fuskarta dauke da Murmushi
*MRS AHAMAD GWADABE*👌🏻👌🏻👌🏻
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🐾 *NANA KHADIJA* 🐾
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
✍🏼 *WRITTEN BY*
_Binta Umar_
( _MAMAN ABDUL WAHAB_ )
🅿 *163*
"Kunneshi Makale da Waya ta fito daga dakinsa cikin shigar kananu n kaya jins ne da shart duk blue ne sunyi masa bala'in kyau rigar ta kamashi sosai. Power din shi a murmurde kanshi da hula hana sallah ya Manna bakin glass baka ganin ko qwayar idonshi shi ko yana ganin kowa tarr!
A haka ya shiga dakin Nene cikin Sallama ya zauna cikin kujera yana cigabah da Amsa wayar da'ike
"Ya jima yana wayar kana ya kashe gami da mayar da ita aljihun gaban rigarshi.
Fuska babu yabo babu fallasa ya gaishe da Nene hakama delu.
Delu tace Ango kasha kamshi kai tun yanzu kafara kamshin kenan.
Kallonta yayi ta cikin glass din yace delu kenan kamshi ai sai Ku tsaffi.
Dariya delu take ta ba gaira babu dalili ta gyara zama tace wane mu ai zan kawo maka Amaryar taka sai karasa wane kalar kamshi takeyi domin zan hada mata turare mai kama jiki irin na mu na da!.
"Yar dariya Ali yayi yace ai kam sai ki bada himma Dan ni kam ina son kamshi Ammafa ba ko wanne ba Dan in naji tana kamshin turaran "yan bori ko ro ta Anyi.
"Daga delun har Nene dariya sukasa delu tace kai dai bari ai da kanka zakace ta sammaka irin shi in kaji kamshin sa.
Girgiza kai yayi yana duba a gogo kamar ko dayaushe yace Allah ya tsareni da shafa turaran mata badani ba yafada yana kallon D'ija dake gado a kwance.
Kallon Nene yayi yace ita kuma bata tashi ba ne har yanzu?.
Ta tashi mana cewar Nene tanajin ka !! D'ija ke D'ija tafada gami da jan Dan ya tsanta.
D'ija naji tayi shiru ganin Nene taki ta kyaleta ta Bude ido tace menene Wai Nene? Wallahi bacci nakeji.
Cikin dariya Nene tace ai ! Dama Ali ne yake tambayarki zaku gaisa.
Mikewa zaune tayi tana masa kallo mai kama da harara duk a zatonta baya ganin irin kallon datake masa sabida glass din dake fuskarsa a ya tsine tace ina kwana ya Ali!!.
Shiru yayi yaqi Amsawa yana kare mata kallo tacikin glass din kamar babu gobe.
Sai data kara Maimaitawa sannan ya Amsa ciki ciki Fuska babu Walwala
Komawa tayi tai kwanciyarta tana Dan Jan karamin tsaki.
Saurin dauke idonsa yayi daga kanta ganin yadda hular dake kanta ta same ta sauka kafadarta bakin gashinta ya bayyana
"Bai kara kallon in data ke ba domin kar yazo yayi abin kunya a gaban su Nene?.
"Yace Nene mai kuka girka ne na karii yunwa nakeji"
Kafin Nene tace komai delu ta mike tsaye cikin A zama tace Lailai kam babu zama Maigida bai karya ba ni Delu!!
"Tace mai zan kawo maka ? Cikin sakin Fuska yace komeye ma zanci Uwargida sarautar Mata
Cikin sauri tafita tana dariya gami da cewa Ai ko yanzu zan hado maka Abinci
Tana fita Ummi ta shigo suka gaisa da Nene cikin mutumchi kana ta fita daga dak in bayan sun gaisa da Ali tana kara jadda damasa cewar ya daure yaje su gaisa da "yan Uwanta suna ta cigiyarta duk da cewa duk dangi daya me
Yace kar ki damu Ummi zanje insha Allahu daga na mike a gurin nan
"Bayan Ummi tafita Ali ya kalli Nene yace gaskiya delu tana da kirki sosai ina son mutum Wanda ya San Abinda yake
Cikin dariya Nene tace delu kenan ai mutuniyar kirki ce ga tsafta ai duk tsafa tata delu ta kusa tafini
Kwarai kuwa cewar Ali tsafatar ta ne ma yasa nake cikin Duk wani abu da zai fito daga gareta kin sanni dai da tsamtsami
Kan ya rufe baki delu ta shigo hannta dauke da kayan kari ran ka ta kaff ta aje agaban Ali!!
Gami da jera masa komai yadda zaiji dadin ci
Ai kuwa Ali kasa ya sauka ya tankwashe kafafu yafara kwasar girgin tsofaffi
Ya na ci delu na bashi labaran ban dariya Nene na samusu baki kadan kadan !Sai ga Ali ya zage yana faman tulluqa dariya kamar cikinsa Ai ciwo domin wani abin in delu tayi sai ka dara dole
Lokaci guda yaji yana bala'in kaunar matar tasan duk yadda zatayi tasa mutumn cikin farin ciki!!
D'ija ma Dariya take kyalkyalawa a 6oye domin batayi bacci ba duk tanajin Abinda suke yi ita ma tana kaunar delu sabida Abin dariyarta in tanayin Abu kamar gaske.
"Wayar Ali ce ta katse labarin da delu ke yi ! Daga wayar yayi domin ganin waye!
Siyama ce babu Abinda ya canja a yanayinsa ya daga wayar kana yana cigaba da cin Abincinsa
Daga daya bangaran Siyama cikin kwantar da murya tace Oga na Dan Allah kadawo wallahi bani da lafiya sosai munje hospital da momy na naga dr yace kwata kwata lalura ta bata asibiti bace yanzu narasa yadda zanyi tafashe da kuka wur Jan Jan
Dake ya Bude muryar wayar dukkaninsu sunji mai maganar har D'ija gabanta ne yafadi jin muryar Siyama!!
Tabashi tausayi yace Ok toum kinga please ki dai na kuka komai yayi zafi maganinshi Allah zanzo in Sha Allah dama ina so in zauna dake zan tambayeki wasu Abubuwa before in tafi Amma Allah bai nufa ba kiyi hakuri in dawo sai musan meya ke faruwa ko
Dadi ne ya kama Siyama jin Ali yana rarrashinta sai ka wai ta hau shagwaba ta babu gaira babu dalili!
Biye mata yadinga domin yabawa D'ija haushi ai ko taji domin wani bacin rai ne yazo ya tokare mata a maqogaro jin yadda Ali ya sake yake hira da Siyama Abinda da bayayi sai wani rarrashinta yake
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.