Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 41
Ta dinga sakin tsaki ita kadai a kwance
"Nene tace kishiyar tawa CE babu lafiya?
"E Ali yace yana maida wayarshi Aljihu"
Masha Allah Allah ya in ganta cewar delu ai in kaji dama likitoci suna fadar basu gane wace irin cuta ce ke damun mutum ba to tabbas dama ciki ne da mutum
"Ai kuwa Allah yaraba lafiya cewar Nene"
"Ameen Ameen Ali yace yana Mikewa gami da kallon Nene yace kizo kirakani in je in gaisa da "yan Uwa wallahi wasu gidan bazan iya kai kaina ba
"Tabe baki Nene tayi tace ai ko kaji kunya Ali ni babu in da zani ga D'ija nan kuje tare ma da ita dama bataje ba
Komawa yayi ya sauna cikin kujera yana Sosa kunne da key dinshi idonshi a kan D'ija n yace ok to yi mata magana ta tashi inaso ne yau yau din nan inje in duba jikin Siyama
Hakan yana da kyau cewar Nene dama ina ta yi maka Addu'a Allah yabaka Ikon yin Adalchi a tsakaninsu
D'ija ta hau tashi wannan karon baccin gaske ne ya soma fizgarta Bude ido tayi tana kallon Nene batace komai ba"
"Nene tace ko karyawa bakiyi ba kin kwanta bacci ki tashi Zaku zaga ke da Ali ku gaggaisa da jama'a in yaso in kun dawo sai ki kwanta din
"Nene ki kyaleni dan Allah tafada tana gyara kwanciya"
A'a ya Asalin in kyaleki Nene tafada da rai a bace taci gaba da cewa wannan ita ce damarki ta karshe nan da "yan kwanaki kin zama matar Aure ya kamata kije kuyi Sallama da DANGI!!
Ganin ran Nene ya 6aci yasata Mikewa zauna tana gyara hular kanta rai a bace ta fice daga dakin domin kuwa sai tayi Wanka sannan
Duk yana lure da irin harare hararen data ke masa ita duk a zaton ta baya ganinta
Nene tace ina kuma zakije ki ka fita nazata kaya zaki sanja kawai
Zanyi Wanka ne sannan inzo in karya D'ija tafada domin tasan Ali baya son jira kila in yaji haka zai iya cewa ya hakura yayi tafiyarshi sai taga yakara gyara zama cikin kujera
Zumbura baki tayi ta fice daga dakin cikin zyciyarta tace mutum kamar maye
Nene tace Ai kaji Abinda tace ko sai kajirata tunda kai zata raka"
Yana laluben wakar mutuminsa joe cikin wayarshi yace Ai dole injira kin San Hausawa nacewa Amarya bata laifi insu fa Amma bani ba yafada yana dariya yacigaba da cewa yo ni ko yau a ka kai min Amarya tayi min laifi wallahi Uwarta zanci
A'a Ali cewar Nene dama ina so inyi maka fada a kan saurin hannunka Dan Allah kar in kaima ka D'ija laifi kadan kadinga dukanta. Kasan yarinya CE
"Yace to kar ki damu Amma ita ma kiyi mata Fada babu ruwanta dani banason rashin kunya da gadda ma kin San duk halinta ne in nakafa doka a gidana banaso a karya min duk Abinda nace inaso ta dinga so sai mu zauna lafiya da ita
"Ay duk nasan halinka Ali Dan Allah Ku zauna lafiya ita kuma zan jamata kunne sosai Allah yabaku zaman lafiya da zuri'a dayyiba Allah yabaka ikon yi rike Amanar da nabaka Allah yabaka hakurin da jimiri da daukar dawainiyar mata biyu
Nene tabashi tausayi sosai da Sosai kana yaji dadin addu'ar datake masa sabida haka rage Sautin dake fita daga cikin wayarsa yayi kasancewa a kwai eirpix a kunnenshi! Ya kama hannuwan Nene duk biyun ya riqe anasa yace ki kwantar da hankalinki Nene Wallahi tallahi kinji na rantse miki ko zan riqe miki D'ijan ki da kyau babu cuta babu cutarwa mutukar kikaga wani Abu ya biyo baya bayan Auranmu ba fata nake ba to badaga gareni bane in Sha Allahu naji dadi kwarai da wannan kyautar da kika yi min Wallahi da zaki tona zuciyata kiga yadda take A kan D'ija da kinyi mamaki. Amma babu komai zakiyi mamakina in Sha Allah
Da yar dar Allah satin da a kammala bikin zaku tafi umara ke da delu kuje kuyi mana Addu'a
Bakin Nene yaqi rufuwa sai dariya take gami da Farin ciki tanata shiwa Ali Albarka!!
*muje zuwa*
*kuyi hakuri dani Dan Allah Wallahi ina muku kokari*
π
*A kwai tsare tsaren da wasu daga cikinmu muke gudanarwa mu writer's domin kawo cigaba ta fannin bunqasa har shen Hausa domin ci gabanmu mu Marubuta. Ina fatan dukkanin Abunda zanzo muku dashi zaku karbeshi hannu bibbiyu za kuyi min kyakykyawar Fahimta tananan zan tabbatar da cewa e lailai son da kukewa min kukewa rubutana na gaskiya ne*
*I will Always say thank you very very much to my people*
π
*love you All*
Wallahi ina son Ku ban cire kowa a cikinku baπππ
*Allah ya kara danqon zumunxhi da kauna ta Dan Allah*ππ»
*MRS AHAMAD GWADABE*
π΅ππ΅ππ΅π
*πΎNANA KHADIJA*πΎ
π΅ππ΅ππ΅π
*βπ»WRITEEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
*π Ώ164*
Haka D'ija ta fito ta same su suna ta fama hira cikin farin ciki
Kallon Nene take cike da mamaki ganin irin walwalar data ke kamar wacce a kai wa Albishir da gidan Aljanna
Zama tayi gefen gado tana tabe baki
"Nene tace kinji Dan Albarka ko D'ija ya biya mana Umara ni da delu ana gama daurin Auran Ku zamu tafi"
"Allah yasanya Alkairi shine kawai Abinda D'ija tace taja Bakinta tayi shiru domin so take ta canja kaya gashi a zaune yaqi tashi Dan ma da Hijab a jikinta rigar jikinta ta mai da datayi wankan! Sabida ya hana ta tsayawa ta lalubi Abinda zata rufe jikinta
Satar Kallonta yake tana kici kicin dauko kaya cikin jakarta wacce tazo da'ita
Tafito da Mai tafara shafawa Fuska a murtuke ta kalli Nene tace kice Masa ya bani Wayata tafi sati Uku a hannusa ya kamata yabani Aba ta haka!
Sannan Ni ya tashi Dan Allah zan sa kaya Sam haka bai dace Ai ta kallon mutane tafada tana hararasa!
Wai Harara a duhu kenan Sam Ali bai San me take cewa ba yana can ya shagala da kallon kafarta Wacce take faman shafawa mai
Babu Abinda yake daukar hankalinshi a kafar tata kamar cikar dunduniya gami da sharabarta Wannan yana tabbatar masa da cewar yarinyar cikakkiyar Mace ce domin duk ga Alamu nan sun nuna!
"Nene tace bafa nasan Neman Magana D'ija yaushe yake kallonki Abinda ma idonshi da tubarau Dan Allah yi ki sa kayanki kutafi kada rana tayi yace zaije Abuja ne ya dubo kishiyarki Siyama bataji dadi ba
Cikin basarwa D'ija tace wacece kuma kishiyata ni bani da Kishiya Domin Aunt Siyama "yar Uwa ce Ai sai da son Mutum a zuciyarka zakayi kishinshi Ni ba zaman kishi zanje inyi ba Nene"
"Nene tace to nayi laifi ba kishiyarki ba "yar Uwarki ko wa dai yayi zagi a kasuwa yasan da Wanda yake Marakunya kawai kar kiyi kishin nasa mana ai kinaji kina gani za'a kwaceshi sai ki zama "yar kallo a gidan"
Dariya D'ija tasa tace nifa badake nake ba Nene"
"Oho miki dai Nene tafada tana gyara zama"
Satar Kallon Ali tayi Aiko shima ita yake kallo tun dazu da sauri ya kauda kansa Cikin bacin rai wato yarinyar nan tana nufin bata kishin sa
Ita D'ijan dadi taji da taga ranshi ya baci dama haka takeso
Ta cigaba da shafe shafen ta babu Abinda ya dameta!
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.