Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 41
Ai kwan kamar jira yake ya damqe hannun cikin nasa yana sakin A jiyar zuciya bai kalleta Ba yacewa mai photon ya fara yi musu Sosai suka riqa kyau domin sai da ya rungomo kafadunta da hannunshi haka ai kai musu kunya kamar tayi yaya Sai wani mammatsa mata kafada yake wai shinan photo a ke musu sai tsaki takeyi da kyar tasamu ta yakice daga jikinshi ganin anqi gama photon ga mutane suna kallonsu duk ya rirriqeta Shima kasa daurewa yayi Murya a kasa yace mata tazo suyi da Abokansu babu yadda ta iya haka suka shiga tsakiyar Abokanansu ita da su Na'ima a kayi Bai bari an karasa bah ya Silale yabar gurin jiki Amace yarasa Abinda ya kashe masa jiki yanzu yanzu Amma baya rasa nasaba da kamshin da yaji Dija na fitarwa shifa in dai zai shaqi kamshi mutukar yayi mushi nan da nan yake daga masa hankali
Ganin yabar gurin D'ija ta sake sosai cikin jama'a tana Walwalah dasu
Karfe 3 Shaura sun fito domin tafiya tuni wasu motocin sunfarayin a won gabah Jama'a sai Allah sanya Alkairi akewa Abbah gami da yi wa Amarya da Ango fatan zaman lafiya
Ba kwai shaura suka sauka a abuja ana ta kiraye kirayen sallahr magaribah gaskiya sunyi sauri sosai
Gida ya hargitse domin shirye shiryen Walima da Abokan Abbah suka hada bayan sallahr isha !
Hajiya Rakiya ce ta gyara Amare tsaff Cikin kaya iri daya tayi musu irin kwalliyarsu ta kanuri. Cikin lafaya wai zo kaga D'ija sai ta saje sakk dasu Wannan bari mar da suke sawa ta hanci tayi mata bala'in kyau haka hjya Rakiya ta fito dasu gurin suna tashin kamshi. Nan da nan guri ya kaure kowa yana son yaga Amare kowa sai tofa Albarkacin bakinsa yake
Sai da mai gabatar wa yayi magana sannan guri yayi shiru a kafara sauraron Wa'azi daga Sharraan Malamin nan wato Malam Ibrahim khalil Wanda yake Jan kunne a kan riqe Aure da sharaddansa gami da Jan kunne a kan Amare su zauna da mazajansu Amana babu rashin kunya da mai da magana a kan miji suyi koyi da Nana Fadima "yar manzon Allah bata ta6a fita daga cikin gidanta Ba batare da sanin mijinta Ba wato sayyadina Ali sabanin wasu matanmu na yanzu bini Bini sai kiga mace ta zari hijab tashiga makota Ku ta tafi raka makociyarta cefa ne ko a tambayi anguwa daya amma sai ga mace taje sama da guri biyar duk batare da sanin mijiba
Sosai malam ya tsoratar da mata da irin Azabar da Allah ya tanadarwa mace mai irin wannan halin!
Matan dake gurin jikkunnasu sukayi sanyi musamman masu ai kata irin Wannan dabi'arMomyn Siyama da ita kanta Siyaman jiki yayi la'asar !!
*NI KO NACE ALLAH YASA KUNA DA RABON GANEWA*
*DAN ALLAH KUDINGA HAKURI DANI A KAN YANAYIN YADDA NAKE MUKU TYPING A KWAI DALILI NE WALLAHI BA LAIFINA BANE NI KAINA NAQAGU NAGAMA LITTAFIN NAN WALLAHI*
😊
*MRS AHAMAD GWADABE*
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
Sosai Abin ya qayatar gami da birge jama'a Amare da Angwaye sunsha kyautar bangirma daga Abokannan Mahaifansu Nan ma sai da a kayi photon nan tahiri hi sannan guri ya watse !
Washe gari a kacigabah da gudanar da shagalin biki in da Hajiya rakiya ta sanya Amare a daki kusan A wa hudu tana gyara musu jiki gami da yi musu turarar jiki. Sai da tabbatar jikinsu ya karbi turaran sannan ta shiryasu tsaff jikin wani Ubansun les Wanda ya tassama dubu tamanin dinki bubu ne me kamar rariya Amma ba'a matse tsakiyar ba mayafai da takalmar duk iri daya hatta yari da sarqar su basu banbanta Ba gaskiya sun bawa jama'a sha'awa domin kyawun da sukayi Abin kallo ne
Karfe Biyar saura suka fara shiryeshiryen tafiya dinnar Kawayen Na'ima duk sun fi yawa dake tafisu jama'a Cikin shigar dogayen riguna kalar pink suka fito rigar har kasa take tana da dogon hannu Amma na net ne kuma samar rigar shima net a gurin sai wani irin Net mai Dan banzan kyau da suka lulluba a ka da wani uban takalmi mai tsini mai igiyoyi wannan duk Ai kin Faruk ne ko wacce riqe da "yar jaka makale a hannu gaskiya Sunyi kyau haka suka Fito a jere tamkar wasu taurari kawayensu na take musu baya
Ko wane ango shi zai dauki Amaryarshi sauran Abokan nasu su dibi jama'a Ali yana hango D'ija lokacin da suka tawo yaji hankalinshi ya tashi ganin yadda tayi wani tamtsan kirjinta ya tashi gashi shi da yake nesa yana hango Alamunshi ta cikin Net din rigar nan da nan yaji bazai iya jurewa Ba yakira Faruk A waya Wanda yake ta hada hadar saka mutane a mota yace "wai towo ne a idonka lokacin dakaje siyan rigunan da suke jikinsu ne koko wannan ai iskanci ne duba da kyau kaga yadda sassan jikinsu ya fito Allah kasa su koma su cire in bahaka Ba ba zani gurin dinnar din Ba duk yana kwance cikin mota yake wannan sababin
".haba Ali wai meye haka ne yanzu yanzu muka gama fa da kai cewar baza ka bata mana shiri bah ko Ba hakaba meye Laifi yau daya ne fa ai Ba a Kansu a kafara ka qyalesu Dan Allah"
"Kamar yaya kana nufin ina kallo a shiga hurumin Ubangiji impossible dole inyi Magana kasan gurin nan ya tara Maza da mata wani ma baka gayyaceshi Ba zaje gayyar sodi ko ka kamanta da "yan iskan Abokanka daka gayyata kana nufin zasu iya dauke kaine batare da sun kallah Ba wani ma da gayya zaizo yace zai maka photo daga nan shikkenan ko to Ba zai yiwo bah!!
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
🏵🎗🏵🎗🏵🎗
Ganin Ali yana nema ya 6ata Shirin yasa Faruk kwantar da murya yace Dan Allah Dan sanka da Annabi ka bar maganar nan wai kai wane irin mutum ne yanzu yanzu za'ai magana da kai sai ka sanja yanzu idan nace su kuma su sanja kaya waddane zasu saka iyi?
Ko nuffasa bai bar Faruk yayi Ba yace "su ka na dazu mana shine yafi mutumchi dama kuma yafi musu kyau
Tsaki faruk yaja yace Allah ya sawaqe maka Ali kata Ba ganin Amarya ta saka kaya ta maimaita mtsss Dan Allah kar muje kayi mana halinka cikin Abokai kai kanka kasan da A kwai "yan hassada a gefe hakan zai sanya suyi mana dariya. Kashe wayar yayi batare da yacewa Faruk din komai bah
Tuni Nafisan Faruk ta kame a mota tana jiran Amarya kuma Aminiyarta ko lokacin da Na'ima tashiga cikin sakin Fuska da mutumta juna suka gaisa suna hira sama sama
To haka bangaran Fa'iza ma dake matar Dr Hashim irin wayyayun matane tai ta Jan Fa'iza da hira ko da kishi dai ta bar Abin a ranta!
Ban garan Siyama ko tana can dakin Ummi tana shiryawa tarasa irin kwalliyar dazatayi hankalinta ya tashi lokacin data hangi fitowar su D'ija babu wacce ta dauke mata hankali irin D'ija ganin wanin irin madarar kyau zallansa yana zubah fuskarta sai fitar da annuri take shine ta daga hankalinta itama take ta labta kwalliya a fuska lailai itama sai tayi kyau da kyar da tagama ta fito tana wani ya tsine ya tsine ita ga Uwar gidan Aliyu
D'ija ko bayan motar Ali Faruk ya bude mata tashiga da fissimillah kafin ta daidaita zamanta cikin motar yace dawo nan kusa dani Ba musu tafito ta bude kofar gaba ta zauna gabanta na dukan Uku uku nan da nan motar ta rinqa fitar da wani irin mugun kamshi mai dadi ji!
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.