Complete Hausa Novels

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 6 of 41

Shi ma murmushi yayi yana girgiza kai A fili yace *Khadijatuna kenan manyan mata!*

Tada motar yayi yabar Unguwar ko in ce Kano din domin Abuja ya nufa kai tsaye!!

*To Allah ya tsare hanya Ali*😊😊

*MRS AHAMAD GWADABE*πŸ‘ŒπŸ»
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾NANA KHADJI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*πŸ…Ώ171*

Gudu ya dinga Fafurawa sabida haka nan da nan yaje Abuja

Faruk yayi wa waya Kafin ya shiga Bracck din nasu yake tambayarshi yana gurin Aiki ko Kuwa!

Faruk yayi Mamakin Wayar Ali domin yau tsawon kwana shida kenan da rabon da yakirashi a waya sai shi jiya da ya kirashi yake masa maganar kama"yan fashin da sukayi!

"Yace Eh ina gurin Aiki mana yau Kaga dama ka kirani ne!

Banza Ali yayi masa yabar Maganar da yake tabi ruwa! Yace yaya kuke ciki da Mutanan ne?

Tsaki Faruk yaja yace ba'an ce da kai kazo ba kaqi OK dazu naji Oga dama yana Maganar zai kiranka A waya kazo sabida dole sai an tsaurara musu zasu fadi inda shugabbannasu yake kanaji bayan fashi da makamin da suka Addabi Al'umar musulmi dashi A she har garkuwa da Mutane sukeyi!!

"Ok Ai yanzu haka ina cikin garin gani a gida ma Siyama babu Lafiya Amma yanzu in nafito zan shi go dole zamuyi Waya da Oga!

"Kana nufin kadawo ne Faruk din yafada"

"Yace E mana ma koma tare jibi kenan nafuskanci Mutannan zasu bamu Wahala fa Ali n yafada

"Kwarai kuwa cewar Faruk din yaci gaba da cewa ga Hidima a gabanmu Mtsssss"

"Dariya Ali yayi kadan yace Wace irin hidima kai hidima take gabanka ni tuntuni nagama tawa hidimar"

Ok kasamu yanzu kenan tunda ka tabbatar da kasamu D'ija A hannu dole ka wanko kafa kadawo mana da da muka kasa gane kanka sai faman dacin rai kake wa mutane har dasu gaba kai ko kunya bakaji ba!!

Mtssss Kaga saurara min malam kasan tsawon shekarun da na dauka ina dakon son yarinyar nan a zuciyata da har zaka dinga daurwa wan can Dan Iskan gindi ya shiga go nar da batashi ba sabida kwata kwata kai dashi Baku San kawaici ba!!

"Kyalkyalewa da dariya Faruk yayi yace Haba Alhji Ashe kawaici ka tsayayi kaiii Amma naso D'r tane yasamu yarinyar nan da sai inga inda kawaicin naka zai tsaya!!

"Fuska Alin Yasaki kamar yana gaban Faruk din yace Ai mutuwa ka wai zanyi kawai nasani in har haka ta kasance Allah yasa D'r ba Alheri bane shiyasa ya musanya mata dani

D'r din ne ba Alheri ba?

E" shi din
OK sai nagaya masa bakasan yanzu sirikinka bane!

Nasani Mana Sai me Dan Ubansa ni daya so ya kashe ni da rai na Dan iska kawai!!
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾NANA KHADJIA*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDULWAHABU)

*πŸ…Ώ171*

Dariya Faruk ya dinga kyalkyalawa Ali kamar cikinsa zai yi ciwo

Shima a nasa 6angaran dariyar yakewa kansa yace kai Dan Allah karkafasa min dodan kunne mtsss ko meye Abin dariya oho yakashe wayar yana Murmushi domin a zahiri shima dariya yakewa kansa yanzu inda Dr yasamu nasara yaya zai yi darayuwarshi ta66!!
Aiki jaa!! Yafada A fili sannan yafoto daga motar ya kulleta ya durfafi part dinshi bakinshi dauke da Addu'a kar yashiga ya riski warin nan na Siyama!

Ma'akatan gurin ne suke ta kawo gaisuwa sai da ya tsaya ya Amsa cikin sakin fuska da mutumta mutum kana yasa mukkuli ya Bude gidan!!

"Siyama da Rukyy ne a zaune a falo suna Hira Rukyy ta bararraje kamar wacce take gidanta ko gidan ubanta ga kayan Abinci nan birjiki sunci sun barshi gami da kananu kwalaben na kayan Maye Wanda suka sha!
Rukyy cikin kananun kaya kirjinta duk rabi a waje wando jikinta ya yi bala'in matse cinyoyinta kanta yasha qarin gashi sai tsotsar roci take tana shiryawa Siyama makircin da zata kullawaD'ija in tashigo gidan,!

To Siyama n ma cikin Riga da sket take irin "yan kanta tana zaune kanta babu dankwali tayi parking din gashin ta Wanda da kyar ya hadu guri guda fuskarta takara haske alamu sun nuna tananan tana bleecin din ta farcenta zaqo zaqo har yau Dan bata yankewa tai musu ado da Jan farce ganin Alin baya nan kai da kagansu bazakace "yayan Musulmai ba ne Ar'na sakk!
Rukyy tace Mata tunda kince wan an ruwan ya ki daina fita kamata yayi mu koma gurin Malam ko yadda yace kiyi ne baki yi daidai ba a kasamu matsala Dan wallahi har yanzu kinayin wari duk da irin turararikan da kike amfani dasu masu qarfi!

"Mtssss wallahi narasa yadda zanyi Rukkyy Siyaman tafada tac gaba dacewa yanzu Abin ma ya sauya Wasu irin kuraje ne suke fitowa a gabana masu bala'in kaikayi in suka fara kaikaiyi ko a inane sai na Sosa nakejin dadi gashi Dana gama sosarwa zasu fashe yanzu duk na kwaile fatar gabana!"

Zare ido Rukyy tayi cikin tsoro ta Bude baki zatayi magana sukaji ana kokarin Bude kofaa!

Shine ya An karar da Siyama ta tuna da cewar Ali yace zaizo!!

Nan da nan ta diririce a gigice ta mike tsaye tayi hanyar bedroom dinta da gudu sai kuma tadawo a gigice tana debe kwalaben kayan mayen da suka Sha ta hau tusawa a jakar Rukyy cikin tashin Hankali!!

*MRS AHAMAD GWADABE*πŸ‘ŒπŸ»πŸ‘ŒπŸ»πŸ‘ŒπŸ»
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾NANA KHADIJA*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*πŸ…Ώ172*

Da sallama ya shaga Falon fuskarsa babu yabo babu fallasa!

Gigicewa Rukyy tayi dataga Ali nan da nan ta hau Neman mitsi tsin gyalenta tanaso ta rufe kanta"

Kallo daya yayi musu ya dauke kai !kai tsaye hanyar dakinshi ya nufa cikin zuciyarsa yana Allah wadai da su!

Hada baki sukai gurin yi masa sannu da zuwa!
Sama sama ya Amsa ya wucesu

Da sauri Siyama ta tawo cikin tsarguwa da rashin gsky kanta a sunkuye ta kara so yana shiga dakin tabi bayansa

Gabansa yafadi ganin ta shigo Dan shi kwata kwata yanzu tsoron ta ra6eshi yake!

Ai.ko tana kara sowa kusa dashii yafara jin tashinn qarni!

Da sauri ya juya baya yana kokarin kwance a gogo yace menene kuma kije dakinki zan fito in sameki yanzu Wanka zanyi !

Yaqe tayi tace wai da zan hada maka ruwan Wanka ne!

OK ngd kije kawai zan had a da kaina
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾NANA KHADIJA*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)

*πŸ…Ώ173*

Simi simi ta juya zata fita daga dakin!

Wai wayowa yayi yana Binta da kallon yana ya mutse fuska yace yaya jikin naki?

Cakin Farin ciki ta tsaya tace da sauqi dai "

Masha Allah yafada yana kokarin Bude kofar toilet yace ka fin nafito kiyi kokari ki sallami wancan qawar naki mai makama da Arniya!
Kinji ko!?

To tace jiki a San yaye tafita daga dakin!

Tsaki yaja yashige toilet Abinshi!

Tana ta6e baki ta zauna kusa da Rukyy tace wallahi mutumin nan Dan rainin hankali ne kwata kwata na lura yanzu baya son in tsaya kusa dashi

Rukyy tace ai yana da gaskiya ba zan boye miki ba gaskiya duk Wanda ya ra6e ki dole zaiji babu dadi nima dai Dan babu yadda na'iya ne

Mtss bana son cin fuska Rukyy ! Tafada a fusace!

Humm yanzu dai mubar maganar yaushe zamu koma gurin malam din domin karbo makarin wannan ciwon qila ta bakinnaki ne banyi amfani dashi dai dai ba !

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.