Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 41
Da sauri ta lalubi wayarta ta nemu number Rukyy Bugu daya ta daga tace ya akai yi ne sai you kikaga damar kirana "yar dadi Miji tunda ya hanaki kulani yanzu me kika bugo kice min tafada Muryata na sarqewa da'alama a cake take.
Kinga Rukyy ki bar Maganar nan Dan Allah zuwa yanzu nasan kin Fahimci waye Aliyu shi kanshi fada yake yasan bazan iya rabuwa dake Ba domin bani da Aminiya sama Dake" Katseta Rukyy tayi tace babu wani nan mai yasa lokacin da ya mare ni baki nuna masa matsayina Ba a wajanki sabida ki na jin tsoransa Wallahi ina nan na tama wannan gayan' sai na rama marina da yayi Shi har ya isa ya mareni ya kwana Lafiya Humm to yanzu meye kike nema nasan dai ta kwabe miki Ina Amaryar taki take"?
Tsaki Siyama tayi tace Rukyy baki daddaraba kenan wallahi ina baki shawarar kifita harkar Ali kece zaki Sha wuya Au da ke shirin daukar fansa kike Lailai Rukyy kwakwalwarki bata Aiki kar ki manta waye Ali in da rabon ya daure ki ne mudun ranki shukkenan ni babu ruwana Wallahi taci gaba da cewa Maganar wannan Matsiyaciyar yarinyar ne D'ija Rukyy wani yarinyar nan ta Mara har sau biyu hade da fasamin baki yanzu haka le6ena nakasa har ya Dan kunbura"
Wata "yar iskar Dariya Rukyy ta sheqe da'ita har da riqe ciki tace Lailai Siyama kin zama sorry garin yaya kika zauna har tayi miki wannan Dan yan Aikin Tafashe da dariya tamkar a gaban Siyaman take ,Wallahi shammata ta tayi kin San fa yarinyar "yar iskar yarinya ce tun tana karama take da wayo gami da ibilici"Dariya Rukyy take yi tamkar babu gobe Abin har ya soma bawa Siyama haushi tace bafa nasan iskanci da Wulakanchi Rukyy ya na kiraki domin mu San Abin yi ki mai dani mahaukaci ya kina wa dariya"
Rukyy tace to yanzu mai kike so Ayi tuntuni nafada miki yarinyar nan ita da wannan tsohowar matar a tafe suke a kanki dole ki tashi tsaye a kansu domin daukar Fansa yanzu zama bai ganki Ba a yanzu ne ma zaki mike tsaye ki kurda saqo da lungu ki nemo Farraqu tsakanin ita dashi ta nan ne zaki sami kwanciyar hankali ko babu komai kinga kema kin rama kin rabasu ko da tana gidan su samu rashin kwanciyar hankali kinga sai ki koma gefe ki saka ido kiyi kallo"
Tabbas maganarki gaskiya CE kawata kina ganin mukoma gurin boka bauooje ne ko A kwai wani sabon boka ko Malamin da kika hango mana"
*MRS AHAMAD GWADABE*
π΅ππ΅ππ΅π
*πΎNANA KHADIJA*πΎ
π΅ππ΅ππ΅π
*βπ»WRITTEN BY*
Binta Umar
(NAMAN ABDUL WAHABU)
*π Ώ196*
*Allah ya za6a mana shuwagabbani na gain*ππ»
Rukyy tace Ai kwaisu mana har in dai zaki fitar da kudi kin San dai sai an yi yanke yanke sosai in kina son aikinki yaci da gaggawa, kar wannan ya dameki Kawata Siyaman tafada taci gaba dacewa ni har in dai bukata zata biya ko jinin jikina zanyi basu duk domin inga bayan natsiyaciyar yarinyar Nan, shikkenan yanzu sai ki sanya mana ranar da zamu baza ma Amma fa dole sai kin saki jiki da yarinyar nan tanan zaki Ai watar da nufinki a kanta"
A jiyar zuciya Siyama ta sauke tace kamar kin sani kuwa Wallahi rashin hakurina ne ya sa na takale ta har ta kai ga fasa min baki wani irin kishinta nakeji ji nake kamar in luma mata wuqa nasan tabbas mutuminki yayi Sex da ita ganin yadda yake wani fitar da Annuri Wallahi nake gayamiki tafada cikin huci,
Dariya Rukyy tayi tace kema wasa kike kin San dole ne fa babu Namijin da zai ga yarinyar nan ya kau da kai ballanta shi yana ganin mataarsa ce ko bai yi sex da'ita Ba zaiyi ta6e ta6ensa'
Tsaki Siyama taja tace Dan Allah dai na wannan maganar Rukyy zuciyata zafi takeyi Wallahi wai yau nice a kaiwa kishiya tikisa!!" Ita kanta Abin yana daure mata kai duk ina Asirin yake.
*ni ko nace zakiyi kigama ne Siyama D'ija kainuwa CE da shan Allah*
Sai da suka tsai da ranar da zasu tafi gurin naimo Asirinsu sannan sukayi sallama gami da kashe Wayar,
Ali ko Lokacin da ya fita cikin Mota ya zauna gami da kiran wayar Faruk Yace kafito mana gani cikin mota kasan Yau su Nene zasu koma bayan haka dole zamu sallami baqinmu na Nesa ko"
Faruk yace Ok ganin Fitowa dama yanzu nake shirn kiranka a waya"
Ko da Faruk ya fito kai tsaye motar Ali ya nufa dama bai fito da key din tashi motarba' Bayan sun dauki hanya ne Faruk ya kalli Ali yace yaya Akai ne Ango mijin Mata biyu ga Siyama ga Amarya D'ija nasan dai yanzu kanwa ta kar tsami kwar nafi ya kwanta"
Shiru Ali yayi mishi hankalinshi na kan tukinshi sabida yasan iskanci Faruk zai yi masa,
Dariya Faruk din yasa ganin yadda Ali yake wani basarwa yace nasan Halinka fa Alhji baka da Hakuri Mybe ga mawa Yarinyar Aiki Dan rashin imani"
Dariya yayi kadan hankali a kan tukinshi yace bayan taqi yadda yarinyar"
π΅ππ΅ππ΅π
π΅ππ΅πππ
Kai haba Alhji Faruk yafada yana dukan kafadar Ali"
Allah kuwa Alin yafada da Murmushi a fuskarsa kamar gaske Faruk yace gwara haka ma wallahi domin D'ija mai tsada ce ta burgeni Wallahi gwara ta nuna maka ita ma macace " Wani kallo Ali yayiwa Faruk din yace Wallahi komai isarta sai dai idan ban yi niyya Ba domin kuwa bata fi qarfina Ba kana nufin har wata isa zata nuna min da Abina iyi? Wasa kake Alhji in kaga banyi Ba kawai ban yi niyya bah"
Zata nuna maka mana tunda mallakinta ne Abin shawarar da nake baka kawai ka kwantar da kai ka kwashi gara in Ba haka Ba babu ruwana munanan da kai zakazo kana "yar murya"
Wata Dariya Ali yayi ta rai nan hankali yace D'ijan zanzo in yiwa "yar Murya lailai baka da Hankali Allah shi kyauta duk ranar da na nemi in kusanceta taqi zanyi ne kawai da qarfi in biya bukata ta Dan Ba qarfi na tafi Ba"
Girgiza kai kawai Faruk yayi yace ai shikkenan kaje kayi yadda kakeso Matarta kace Ba ta wani ba Amma kayi wa yarinyar mutane a hankali"
In naqi fa Alin yafada yana ciccije bakinsa sabida tuno Moment dinsu da D'ija na jiya tsigar jikinshi ta riqa tashi nan da nan sha'awarshi ta tashi Sai kawai yayi shiru da bakinshi ya bar Faruk yana ta zubah surutu'
A haka Sukaje gidansu Faruk suka gaigaisa a tsaytsaye Hajiya yakumbo tana ta tsokanar Ali cikin barkwancinta nan ya zauna ya dinga biye mata dama sun saba yace ke yaushe zaki tafi gidanki yakamata ki tafi haka tunda an gama biki tace ai ko baka fada yau din nan a gidana zan kwana ehe!
Cikin wasa da dariya suka bar gidan kai tsaye Family house dinsu Ali suka Nufa'
Nene sun shirya tsaf ita da jama'ata domin tafiya Haka Sukai ta Hidimar saka mutane A mota Nene taja Ali gefe tana kara jan kunneshi a kan Amanarta D'ija kan ya riqe da kyau kuma yayi a dalci tsakaninta da A bokiyar zamanta Siyama, Yace ya kar6a ta kwantar da hankalinta in Sha Allahu babu Abinda zai faru zaiyi iya iya warsa a kansu" Cikin Farin ciki Sune Nene sukayi Sallama suka bar Abuja tare da Fatan Alkairai iri iri da takewa Ali
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.