Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 38 of 41
Suna fitowa tayi sauri ta dauke kanta ta sunkuyar ,har suka karaso tsakiyar farlour suka zauna ,D'ija tamkar ta koma cikin Ali tana katararsa,
Mi ko min romot din nan yafada yana mikawa Siyama hannunsa'
Da sauri ta mike ta karasa kujerar da yake zaune ta mika masa jiki na rawa,
Tana sane ta saka kafarta ta take wa D'ija "yansunta da karfi tayi sauri ta cire tamkar ba ita tayi ba.
Kara D'ija tasa domin dama a tsorace take Sam bata kawo Siyama ce ta take mata kafa ba,takara kama dantsen Ali ta riqe tana zare ido
Wani kallon banza Siyama tayi mata tana cije baki na mugunta,
Da sauri ya jiyo yace ya *Ya Allah* Yace wai ke sai kin fasa min kunne na ne da I face ifacen ki kin San fa bana son hayaniya ko,yafada cikin rarrashi ji yake tamkar ya cire mata Abinda take ji a jikinta
Ya kalli Siyama yana hade fuska yace gafara malama kinyi tsaye a kan mutane mtssss naga randa zakiyi hankali ke dai"
Qi tayi sai ta tsuguna gaban D'ija ta kura Mata ido kamar gaske tace kanwata ya jikin? Sannu kinji yaya Ali Anya kuwa zazzabi ne kadai yake damunta naga sai ihu takeyi tamkar sabuwar Mahaukaciya kuma lafiya kalau na fita na barta ko D'ija tafada tana kallonta
Tamkar ya gaggaura mata mari haka yaji cikin ransa wani bacin rai ya turnoko masa D'ijan tashi Siyama take jifa da wannan kalamar Lallai Siyama bata da Mutumchi wallahi sai yaji duk Dan tausaya mata da yakeyi yafice fitt daga zuciyarsa ,yayi mata wani kallon banza yace kin kauce daga gurin nan ko sai na sa6a miki ne ke da ita dai za'a samu sabuwar Mahaukaciya,
Simi simi ta wuce tana kyalkyala dariya cikin ranta tace wallahi mudun ina raye babu ko babu zaman lafiya da juna duk inda zan shiga in fita sai na shiga domin ganin na farrawa tsakaninku.
Saudiya Qur'an ya kamo cikin sa'a kuwa muryar shahararran Mahaddacin Alkur'anin nan na qasar saudia Abdurraham Sudais yana kwararo karatun sa cikin Suratul khafi , ko minti daya ba'a kara ba Siyama ta mike a zabure jin kanta yana wani mugun hautsina mata tayi hanyar dakinta tana hada hanya,
Ali ya daka mata wata muguwar tsawa yace ina zakije kika tashi firgigit haka sabida an sanya karatun Al'kur'ani ko shashashar banza kawai,
Ko tako uku Siyama bata yi ba da nufin komawa domin sama sama take jin Ali da Abinda yake cewa ta yanke jiki tafadi a gurin tamkar mai lalurar farfadiya haka take ta wani birgima kumfa ta cika mata bakinta taff!!
*✍🏻,,,,,,,,,*
Wani irin mamaki ne ya kama Ali ganin irin iskancin da Siyama takeyi a cewarsa ,sai kawai ya zuba mata ido yaga iya gudun ruwanta ,tabbas Siyama tafara zama mahaukaciya ya ke fada a zuciyarsa
Ita ko D'ija ae bata San sanda ta buga tsalle ta haye jikin Ali ba tayi dare dare kan cinyarshi tana zare ido taki kallon in da Siyama take domin Abinda takeyi din yayi bala'in firgitata,
Hararata yayi kadan yana tabe baki ciki zuciyarsa yace hakan baza tazo ta hau jikina ba sai dole Amma dubi yadda take faman da quma ta tun dazu,
Yana sane ya Dan zame cinyarsa kadan D'ijan tayi taga taga zata fadi tayi Saurin riqe masa wuya da duk hannuwanta biyun tana marairaicewa bakinta sai motsi yake yi da qyar tace yaya Ali dubi fa irin Abinda Aunt Siyama takeyi tamkar mai Aljanu Dan Allah mubar gurin nan wallahi tsoro take bani"
Shan kunu yayi yace babu inda zamu rabuda Mara mutumchi tagama iskancinta a nan gurin,
Sai tafashe da kukan data ke makalewa tace bafa haka akeyi ba Yaya Ali dubah fa ni da bani da lafiya ka kula dani ita mafa hakkinta a wuyanka yake yanzu idan ta mutu a wannan yanayin kacewa Allah me ranar lahira?
Fuskarshi ya cusa tsakanin wuyanta yana shaqar qamshin fatar ta tamkar ya lashi fatar haka yake ji,da qyar muryarshi ta fito yace to Alarama D'ijatu wa'azi kike yimin min ko ko Umarni kike bani? Uhum?
Hankalinta ne yafara dawowa jikinta jin yadda yake goga mata fuskarshi a jikinta gemunshi sai tsikarinta ya keyi ,sai tafara kokarin sauka da ga jikinsa tana gyara baki ,tace ni na'isa in yi maka Wa'azi Abinda kasani ne nake kara tuna sar da kai shi,
Bai ce mata komai ba ya mike ya durfafi inda Siyama ke kwance tagama birgimar da takeyi bacci ne ya kwasheta tamkar mattaciya baka ganin komai sai bugawar nunfashinta bakin ta duk wata farar kumfa ta bushe
Yafi minti goma a tsugune a kan Siyama yana Nazarinta yarasa ma da'abinda zai misalta wannan Abinda tayi yanzu yasan dai tabbas A kwai Aljanu tunda Allah ya fadesu cikin Al'kur ani mai girma,Amma shi a iya saninsa da Siyama bata taba yin iska ba ko a labari yaji tunda duk rabin rayuwarta a gidansu tayi ,dole zai San hakan,
Amma in sha Allahu gobe dole zai zaunar da ita ya tuhume ta sosai,
Hannuwanshi biyu yasa ya kinkimeta yana kauda kai kwata kwata bayason shaqar qamshi qamshin da qarni qarni da yake fita a jikinta babu dadin ji ,yayi hanyar dakinta da ita ,da Sauri D'ija ta taso ta biyo bayanshi Dan baza ta iya zama ita kadai ba'
Sai yau zata taba shiga dakin Siyama tunda take,
*✍🏻,,,,,,,*
A jeta yayi kan bed din ta ya joya da nufin barin dakin ,D'ija na tsaye bakin kofa kamar kace kyatt ta falla da guda,
Hannuta ya kama suka fita daga dakin gami da jawa Siyama kofa,kai tsaye dakinshi ya nufa,
Suna shiga ya nufi toilet domin watsa ruwa yakeso yayi duk da cewar garin babu Alamar zafi duba da yadda damuna ta sauka yanzu haka ma hadari ne a garin Alamun ruwan sama daf yake da ya sauka iska sai kadawa takeyi.
Wannan karon D'ija bata bishi ba zama tayi gefen gadon tana bin dakin da kallo,
Ya waigo yana kanne mata ido daya yace zo ki cuda min baya na ko har kin bar jin tsoran ne?
Shiru tayi masa tana gyara baki na sabo,
Shima bai kara cewa komai ba ya shige toilet din a fili yace D'ijatu sarkin rigima kenan.
Cikin sa'a taji tasamu nutsuwa sai tafara nanata *innalillahi* cikin zuciyarta,
Idonshi a kanta lokacin da yafito domin yayi mamakin yadda ta zauna ita kadai ganin yadda take ta zabure zabure tun dazu
Saurin kauda kan ta tayi ganin yadda yafito dagashi sai towul daure a qugunshi ya rataya wani a wuyanshi yana goge kanshi da jikinshi,
Tabi bayanshi da kallo lokacin da ya nufi Can gurin Mirrow din shi, turare ya dauka yafara feffeshe jikinshi dashi ko mai bai shafa ba, cikin zuciyarta tace Dan jaraba dubi komai ba'a shafa ba ana saka turare kamar ce kai yaya Ali da feleqe yake wallahi,
A kwan ko kallon mai din bai yi ba taga yabude siff din shi ya fito da wata Vest irin ta Unporm dinsu na soja da wandon ta 3Queater ya fara kokarin sawa duk yana lure da kallon da take masa ta qasan idonshi
Sai tayi saurin dauke kanta domin baza ta iya kallonshi a yanayin da yake ciki ba,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.