Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 21 of 41
I donshi jazir ya fita daga dakin nashi dakin ya koma ya dauko glass ya sakaye idonshi tabbas bazai iya jurar kwanakin da ya diba a kan yarinyar nan yin hakan zai qwari kanshi da yawa gwara kawai ya biya bukatarshi ko ya huta da wannan masifaffiyar Sha'awar ta da ta Addabeshi shekara da shekaru Shida ya dauki Alkwarin bazai kwata da ita Ba sai da yadda ta sai ta furta masa Kalmar so Amma yanzu ya canja shawara idan ba'haka Ba wankin hula zai kaishi dare,
Ko da ya koma dakin nata daga bakin kofa yace mata ta fito falo yanzu yanzu zasuyi magana Ko kallonsa batayi bah ta dauke kai tana zumbura baki ita Abin Mamaki yake bata Wai yaya zatayi da wannan mutumin ne dama haka Maza suke basu da kunya koko Ali ne kadai mai irin wannan halin ita tarasa ganewa gaskiya Halin Ali sai shi yayi Abu yanzu sai ya nuna kamar bai yiba ta kusa minti goma kafin ta fita Falon sai da ta sanya Mayafi ta lullube jikinta tsaff sanan Siyama na zaune kusa da Ali suna hira sama sama hankalinshi duk yana kofar dakin D'ija ganin taqi fitowa kamar yakara zuwa yayi mata magana wata zuciyar ta kwabeshi da kar yayi haka kar ya zaqe da yawa kar ta rai nashi yarinyar yana hango fitowarta ya yi saurin dauke kai daga gurin yana Faman ya mutse fuska As'useal ta karaso ta zauna cikin kujera gami da gaishe da Siyama cikin Mutumchi itama Siyaman Fuska a sake ta Amsa kamar gaske tana Jan ta da wasa Amma da zaka tona zuciyarta tafi baqin gawayi yin baki Sabida kishi da yadda taga D'ijan tayi wani masifar kyau D'ija ko Sama Sama take Amsa mata sabida tasan duk makirci ne Wanda yace baya kaunarka da farko to ya dawo yace yana kaunarka Karya ne dole tayi taka tsantsan da Siyama
Gyaran Murya yayi yace Alhmdullah ina so Ku bani hankalinku dukanninku Yawwa Na farko dai ni Ali Ba yaro bane na San Abinda nakeyi dukkaninku a karkashina kuke babu wacce tafi wata a gurina sai wacce tafi kyautata min dukkaninku ina so tunda za6in wadanda suka fi so yu wa ne a zuciyata wato Nene na da Abbah ina girmama waddannan mutane guda biyu dole in girma ma zabinsu Zan baku shawara Ku hade kanku babu batun kishi tunda dukkaninku kun San juna babu bare a cikinku kar inji kar in gani kar Ku mayarmin da gida sansanin yaqi ko na dambe ke Siyama kece babba ki riqe girmanki ke kuma *Khadijatu* ki bata girmanta a matsayinta na wacce ta girmeki kuma "yar uwarki Abokiyar zamanki
Ina fatan kun fahimci Abinda nace yafada yana duba agogon hannushi
Makale Murya Siyama tayi tace in Sha Allahu zakasame mu da kawo zaman lafiya a gidanka bana fatan wani Abu ya fito ta bangarena in
Yace Alhmdullh saura ke *Khadijatu* Tace nima Haka in Sha Allahu yace Good Allah ya shige mana gabah Mikewa yayi stage hade da kara kallon Agogonshi a karo na biyu yace ni zan fita sai nadawo
A dawo Lafiya Suka yi masa dukkanisu har ya kusa fita Siyama ta mike tabishi bakin kofa hade da kama hannuwanshi ta riqe cikin nata tana lumsshe ido tace Hubby Maganar rabon kwana fa ban ji kace komai Ba"
*MRS AHAMAD GWADABE*
π΅ππ΅ππ΅π
*NANA KHADIJA*
π΅ππ΅ππ΅π
*βπ»WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
*π Ώ195*
Ya mutse Fuska yayi yana kallon hannusa cikin nata kana ya zubah mata ido yace wannan kuma ko zaku tsara yadda zaku dinga yi kin San dai babu wacce ta isa in bita dakinta ina Dana wa dakin duk ranar da ko wacce take da girki tazo ta same ni yafada gami da cire hannunsa a nata yayi gaba kunya ce ta lullube Siyama domin batayi zaton Ali zai dizgata haka Ba taga kwanaki ko me tace masa yana bata Amsa baya gwaleta shine dalilin da yasa tayi masa magana yanzu. Jiki a mace ta juyo ko kallon inda D'ija take zaune batayi Ba ta wuce dakinta buguz buguz I ta dai D'ija na zaune tana kallon ikon Allah cikin zuciyatta tace ke har yanzu kinqi ki kama kanki a kan wannan mutumin shekara da shekaru kin San halinsa Allah yasawaqe. Tana kokarin tashi ne ta shiga kchin sai ga Siyaman tafoto buguzun buguzun a fusace tazo ta tsaya kan D'ija tace Ke D'ija kike ko wa ma kada kiji ina maganar raba kwana ki saki jiki kinsamu gidan zama Wallahi ki kwana da sanin zaki fita kina ihu Dan sai na sabautaki tun da kika shiga gona ta ke baki isa in yi zaman kishi dake Ba kin manta wacece Siyama ko bana yafiya hakanan bana manta ranar daukar fansa I Dan a tafe kike ni a can na kwana idan kudi na magani sai sunyi maganinki banza jaka dabba kawai Sai zagin D'ija take tana girgiza jiki kamar zata kai mata duka jira take kawai D'ija ta tanka ta tufe ta da duka domin zuciyar na bata Ali ya kwanta da D'ijan ganin yadda Fuskarsa ke fitar da Annuri,
Shiru D'ija tayi mata Kanta a qasa so take ta kauce ta bata kauce ta bata guri sabida wani irin wari takeji Siyaman na fitarwa tsayuwar ta a kusa da ita ,ganin tayi shiru bata tanka mata Ba yasa ta kara zagewa da zagin D'ijan ta Uwa ta Uba to An zo gurin da D'ija bata taba jurewa Ba wato a zagar mata iyaye ,Cikin Nutsuwa ta dago kai tana Siyama wani banzan kallo tace kai Aunty Siyama dama Fuska biyu gareki yanzun nan fa a gaban Mijinki kika dauki Al'kawarin babu wata baraka da zata fito ta 6angaranki Amma gashi yana Fita kin zama Makaryaciya .A fusace Siyama ta daga hannu zata mari D'ija D'ijan ta kauce tana mata kallon Mamaki Siyaman tace Dan Durun Uwarki ni nake miki karya ke kin isa nayi miki karya ko da kikaji na Amsa a gaban Mijina cewar zamu zauna Lafiya dake Ba gaskiya bane Dan Ubanki ai ni dake Annabi ne da kafiri Wallahi sai naga bayanki D'ija sai naga bayanki D'ija sai naga bayanki D'ija tafada sau uku tana wani ihu gami da zabure zabure tsoro ne ya kama D'ija ganin yada Siyaman take Abu kamar wata mahaukaciya saban kamu sai kawai ta kauce tabata guri bata tanka mata Ba A zabure Siyama ta dawo da ita tana nunata da ya tsanta tace yaya kikayi Shiru ne "yar gidan Mai dattin hula' kafin Siyama ta rufe bakinta taji saukar wani lafiyayyan Mari a fatar Fuskarta kan tadawo daidai D'ija taqara kai mata wani tace zaki iya ta6ani ki kwana lafiya Amma muddun ina nuffashi a doran duniyar nan babu mahalukin da ya isa ya zagar min iyaye in saurara masa WALLAHI A nutse take maganar ,Wani irin Ihu Siyama ta kurma da'Alama kwayoyinn da takesha sun fara ta6a mata kwakwalwa tayi kan D'ija da duka ko ta'ina tana dura mata Ashar kamar "yar Maguzawa!
π΅ππ΅ππ΅π
π΅ππ΅πππ΅
Da qyar D'ija ta bangaje Siyama daga kanta ta tashi daga kan kujerar da tafadi a kai tayi hanyar dakinta Cikin tashin hankali wannan wace irin masifa ce haka yau kwananta daya a gidan Auranta babu kwanciyar hankali wai ita Siyama wace irin macace be? Da Sauri! Siyama tabi bayanta tana fadin Wallahi sai ta rama marin da D'ija tayi mata ta riqe mata hannu Riga GAM tana ta An taya mata zagi irin na tsamar Nama, bakin ciki yayi wa zuciyar D'ija katu tu tamkar tafashe da kuka haka takeji to Amma yin hakan zai sa Siyaman taga gazawarta Kawai sai ta kara shan kunu tace ki sakar min hannun Riga kar kiyagamin ni ban iya halin dabbanci Ba Kuma sai na gayawa Mijinki in yadawo kin San dai halina ai yana nan bai sauyawa ba" tafadi hakane kawai Dan ta tsoratar da Siyaman Amma bata da qudirn fadama Ali wata magana sabuda dole tasan zai zatambayi ba'asin me yahada rigimar,
Jan wuyan rigar tayi sai kuwa ya 6eke tai mata kallon wulakanci tace nawane kudin les din naki kece fatarrariya Har kike maganar kar in yaga miki riga to nayaga mai zakiyi dan Uwark......kafin Ta qareshe zagin D'ija ta kai mata duka A bakinta da bayan hannuta A bazata Siyama taji dukan dan haka bakaramin buguwa bakin yayi bah Nan da nan tasaki hannu D'ija ta mayar da hannuta kan le6enta tana shafawa jin har ya tasa , Da sauri D'ija tashige dakinta tasaka sakata tun kafin Siyaman ta dawo hayyacinta tasan za'ai yi bata kashi ne kawa' Ita ko Siyama Lokacin da ta Ankara D'ija ta gudu Sai ta karasa kofar dakin nata ta rinqa duka da hannu bibbiyu tana Cin Alwashin Sai ta rama Wallahi bata daki banza Ba D'ija najinta tayi mata banza tana zaune gefen gado ta zubah tagumi Hawayen bakin ciki yana fita ita Sam bata saba da wannan masifar Ba ko kadan,
Bayan Siyama tabar gurin dakin ta tashiga ranta a bace tana Shiga ta zauna kan gado sai kawai tafashe da kukan bakinci tana mamakin yaya ma Aikai tabari D'ija tasamu galaba a kanta haka tun ba'aje ko ina Ba har da Marinta kuka take sosai tamkar zuciyarta zata fashe ta mike taje gaban mudubi tana duba le6enta Wanda ya tasa sakamakon bige mata baki da D'ija tayi A fili tace wai yanzu ni yarinyar nan tafasa baki tab'dijam!!
π΅ππ΅ππ΅π
π΅ππ΅πππ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.