Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 27 of 41
Na shanyesu sauran na gobe kawai tafada kamar gaske,
Ok dauko mugani , Gabanta yafadi Amma sai tatashi ta hau laluben qarya, tadago kai tace Wallahi kaga duk na dubah cikin drewars din nan ban gansu bah Amma bari in dubah cikin waccan jakar tawa,babu zato Ali ya shigo dakin nata ya hau jawo drewars din nata yana dubah ,gabanta sai dukan Uku Uku yake sabida ,nan take aje kwayoyinta na maye Sam batai tunanin zaizo ya dubah Ba da tini ta kwashe ta boye
Sai da ya lalube su tsaf bai gansu Ba , kamar ance ya dubah ta jikin gadonta , yaje ya jawo ta yana dubawa, idonshi yayi Arba da kwalayen roci da sauransu, Wani irin Faduwar gaba ne yasameshi Amma dayake Namijin duniya ne bai nuna Ba ko Alama yadago hannushi riqe da kwalayen , yana kallonta babu digon Rahama ko na silai a tattare dashi , yace Siyama meye waddanan? Gumi tuni yayi mata famfo jikinta sai karkarwa yake tuni ta nemi yawo a bakinta tarasa ya salance salam sabida razana ,cikin karkarwar baki tace men ene?nima ban Sani Ba, Wani Ba hagon Mari Ali ya kai mata , tayi saurin kaucewa ,yace wato Dan Ubanki ina tambaryarki kina tambayata ni sa'anki, zaki fadamin ko kuwa ? Yafada yana kokarin kwance belt din dake daure a qugunshi yayi kanta gadan gadan,
6uya tayi a saqon gado tana zare ido tace Wallahi tallahi ban San meye Ba yaya Ali kayi hakuri karka dakeni,yace bakinsan meye Ba wani Dan iskan ne ya ajiyeshi su ni zaki rainawa hankali kema shayeshayen kikafara Dan Ubanki yafada gami da kai mata harbi da qafarsa dake sanye da takalimi sau ciki,
Sai ta ruruce da kuka gami da fadin *inallihahi* ni yaya Ali Wallahi banyi Ba babbb bana wa ne Qila Rukyy CE ta'ajemin shi Amma ni bana shan komai ita ma datakeyi ina mata addu'a,
Gaura mata Mari yaso yayi Amma sai ta qudundune fuskarta a gwiwarta bai same taba, yace bana rabaki da Rukyyn Ba tuntuni har yaushe tazo ta'aje baki sani Ba ni zaki rainawa hankali Siyama , Kuka takeyi tana rantse rantsn bata San sanda Rukyy din ta'ajiye Ba Amma yayi binkice,
Ranshi a mutukar 6ace yace Wallahi tallahi Siyama na tabbatar da Abinda nake zargi a tare dake tabbas sai nayi miki hukuncin da baki taba za to Ba,yafada yana huci gami da Mutsike mata "yan yatsu da takalmin kafarshi,
π΅πππ΅ππ΅
π΅ππ΅πππ΅
Hakuri take bashi gami da rantse rantsen qarya domin ta firgita da yanayi ganin yadda yake huci Allah Allah take yafita kar ya daketa domin Alamu sun nuna Allurarshi ta motsa,
A Fusace ya fice daga dakin hannunshi riqe da kwalayen kwayoyin dole ne ya tsaurara binkice a kan Siyama domin kwata kwata bai yadda da'ita Ba Tabbas idan ya tabbatar da zarginsa horon da zai mata Ba na wasa bane, shi zatayiwa haka duk irin kokarin da yakeyi a kanta bata gani Mahaifinta kawai yake dubawa mutumin yana bashi tausayi ganin yadda ya dauki San duniya ya daurawa "yar tashi kasancewar ita kadai Allah yabashi Yanzu Idan yaji labarin nan da wa zaiyi kuka in bashi Ba , domin dai Siyama a gidanshi tafara shayeshaye.
Ko kallon in da D'ija take zaune bai yi bah lokacin da ya shiga dakin nata tasan dai yayi sallama ta Amsa , ya wuce ta a falo ya shige bedroom din ta.
Gabanta yafadi tace waye kuma ya6ata masa Rai haka Ni Khadijatu, domin ta lura fuskarsa kirtif take bakamar sanda yafita Ba,yafi minti goma dashiga taji yana kwala mata kira,
Da sauri ta Mike tana addu'a cikin ranta Allah sa ba'ita bace, tana shiga tace yaya Ali sannu da zuwa,
Banza yayi mata yana zaune gefen gadonta har yaci re kayan jikinshi daga shi sai singlet da gajeran wando , yana daddana Waya , yace je ki dauko mana plate muci Abinci, jiki na rawa ta tafi ,bayan ta kawo ya nuna Mata ledar kusa dashi yace hada mana yadda zai ishemu ,ki zauna kici Abinci sosai Dan na lura dazu bakici da yawa Ba,
Bata ce komai Ba ta zauna kasan kafet ta hau hada Abincin tafito musu da ruwa da Lemo cikin frijin dake dakin,
Yana kallonta takasan idonshi tagama hadawa kanta a qasa tana jin kunyar kallonshi a haka ,yace Oya fara ci mana nima yanzu zan sauko,Bissimillah tayi ta sanya hannu. Cikin Abincin tafara ci gaskiya taji dadin sa sosai Dan haka taci yadda ya kamata duk wata yunwa ta daina ji ,yace yawwa kokefa ,saukowa yayi ya zauna kusa da'ita gami da tankwashe kafafunshi , yace toum tunda kin koshi fara bani nawa yafada gami da tsareta da idanunshi masu kaifi,
*βπ»,,,,,,,,,*
*INA TAYA DAUKICIN "YAN NAJERIA MUNAR SAMUN NASARAR LASHE ZABE. DA MAI GIRMA BUHARI YAYI ALLAH YA TAYA SHI RIQO ALLAH YAI RIQO DA HANNUSA , YA ALLAH KABAMU ZAMA LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI A NAJERIA*
π΅ππ΅ππ΅π
π΅ππ΅ππ΅π
*NANA KHADIJA*
*βπ»WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)
*π Ώ201*
Sun kuyar da kai tayi yace kin bani mana kunyar me kikeji ne "yan mata na Uhm Ai zan can kunya yaqare ko har yanzu da saura sai in cire miki ita babu Matsala"
A jiyar zuciya ta sauke gami da zumbura bakinta ,ta debo Abincin cikin hannta kamar yadda tayi masa dazu ,yace wallahi ki daina zumbura min baki idan Ba haka Ba zan wuce haushi na a kanshi kinji ko?
Saurin gyara bakin tayi tace to ka bude bakinka mana ,Anqi din yafada yana kanne mata ido daya yace dawo nan ya nuna cinyarsa da hannushi,
Gabanta yafadi sai ta maqe kafada irin na yara , yace mai yasa ? Umhum , Cikin zumbura bakin dai tace babu, Dariya yayi qasa qasa yarinyar na burgeshi in tana yin salonta na shagwa6a, bai kara CE mata komai ba ya bude mata bakinshi tafara bashi Abincin , kamar dazu yana lashe Mata hannu"
Tsigar jikinta ta dinga tashi ,da qyar tace Ni ka daina side min ya tsuna babu dadi Wallahi"
Yace karya kike Yarinya nasan dadi kike Ji, idan ke Ba kyaji ni inaji baki San ni Mayan ki bane?π³
*tofa Ali fa ya soma kauce hanya*
Ido ta zubah masa tana kallo cikin Mamakinsa,, yafaga mata girarshi guda yace Billahillazi hakane,ko baki yadda bane yanzu in gwada miki misali"
Da sauri ta daga kai tace na yadda mana"
Sai yasa dariya ganin yadda take zare ido duk ta tsargo ,ita ko D'ija wani mugun Mamaki Aliyu yake bata ganin yadda yake ta sakar mata Fuska kamar Ba wanan mutumin Ba mai dacin rai, wata zuciyar tace mata Ba Dan Allah duk yake miki haka Ba jikinki yake so,tabbas hakane ta Aminta da Abinda zuciyarta tace mata ,sai kawai tahade fuska Dan gaskiya bazata yadda ya yi mata Wani Abun Ba yanzu domin ita kadai ta San yadda yakeji a qasanta,
Tana bashi Abincin yana can bin ilahirin jikinta da kallon kurrula tabbas da gaske Ali mayanta ne domin babu Abinda baya birgeshi a jikinta,
Bayan tagama bashi ne ta gyara gurin tsaff sannan ta zauna can kan Sofa tana ciccin Magani,
Duk yana kallon sauya warta na lokaci guda bai kawo komai ba a ransa ya ce zo nan Ungo, Kallon Hannushi tayi Key din dakinshi ne yake mika mata,
Tace mai zanyi dashi to? Hararta yayi yace daga nan zakiyi min magana ko rashin kunyarki ta tashi zaki sauke a kaina yafada yana gyara fuska'
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.