Complete Hausa Novels

Nana Khadija Part 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Nana_Khadija_Part_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 35 of 41

Daga kai Siyama tayi cike da bin Umarni sannan tayi hanyar Fita da gudu kamar yadda A ka Umarce ta tayi ,domin yanzu Dan tsoran da take ji duk ya kau burinta kawai a yanzu bai wuce taga karshen D'ija ba!

_A kwai tarin kalubale nan gaba A kwai tarin soyyaya mai ban mamaki nan gaba A kwai tarin bakin kishi nan gaba A kwai tarin Rikici nan Gaba , Sadaukarwa tsantsa duk A ciki yanzu a kafara labarin_

*zan da kata tukkuna da yawa daga cikinku basu toru katinsu ba gashi lokaci yayi harda doriya a kai*

_INA SAURARON KU DA RA'AYOYINKU_

~*ANA MUGUN TARE*~😘

*✍🏻,,,,,,,*
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾NANA KHADIJA*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

*✍🏻WRITTEN BY*
*[Binta Umar*]
~*[MAMAN ABDUL WAHABU*~]

~_*MRS AHAMAD GWADABE*~

πŸ’πŸ’πŸ’
*ZAMANI WRITES ASSOSIATION*
πŸ’πŸ’πŸ’

*πŸ…Ώ207*

~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~😘

Rukyy ko ta na zaune babu digon tsoro ko kadan A tare da ita,

Gudu takeyi tun karfinta tun kafin ta kai bakin kogin ta hango wannan matar A yashe a gurin tamkar matacciya ga zigidir hai huwar Uwarta,sai gabanta ya tsannata faduwa haka tazo ta sallake ta takarasa bakin kogin tafara Aikin da'a kasa ta ,Wannan qadangaran kuwa na bakinta Sam bata San sanda ta cinye shi domin tun da tafara gudun take ji tamkar ba'ita ba jikinta yayi mata nauyi gashi kamar janta akeyi,

Tana dagowa bayan tagama Wanka taji kamar an rarradawa kagafunta tabarya sai karkarwa suke kanta tayi bala'in joya wa ji kake timmm tafadi a gurin tamkar gawa tabi sawon wannan matar,

Kamar Wanda A ka tsikara ya mike yana kallon Rukyy ,Cikin yanayi maganarshi yace mata ta biyo bayanshi

Kai tsaye baki ruwan suka nufa tundaga Nesa ya hangesu kwance tamkar mattatu ,da sauri yakarasa gurin hannunshi riqe da jelar kare da wasu tarkacan ya hau zagaye musu a ka yana wani sam batu dashi kadai yasan mai yake fada,

A gigice suka mike dukkaninsu bakinsu sai motsi yake sun gaza furta ko kalma daya

Ya. Mike yace su biyo bayanshi ,Cikin Mawuyacin hali Siyama ta mike da taimakon Rukyy kafafunta dai karkarwa sukeyi

Wai baccin nan da tayi , tayi mafarki da wata irin hallita mai ban tsoro ta haukanta tana saduwa da'ita , Cikin garari da Tashin hankali take kokarin guduwa ,sai taji wannan Mummunar hallitar nace da'ita daga Ya Aureta Shi Mijinta tace,

Kar dai Maganar bokan ya zama gaskiya,

A daddafe suka kara sa dangar Dan bori yace dukkaninsu suka kayansu bukatarsu ta biya tunda Aljani Dan duna ya Auresu yanzu babu sauran komai,

Jiki na rawa suka sanya kayan ,Siyama Cikinta yayi nauyi sosai sai kifta ido take idan ta tonu da sifar da tagani cikin mafarkinta na yanzu sai gabanta ya yanke yafadi

Rukky tafito da Uban kudi ta'aje gabansa tana ta zabga godiya
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
~*DEDIGATED TO:MY FAN'S*~
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

Ya dauko wani koko Cike da jini bakikkirin dashi ya mika ma Siyama yace gashi nan duk in da kika San da qazanta a gurin nan zaki je ki binne shi gaba da da kokon da Jinin duk ki fadi bukatunki a kan Yarinyar ,
Sannan kar ki kuskura ki ki cika sharudan da na gindaya miki mutukar kika kuskure daya daga ciki to tabbas kuna cikin hadari dake da danginki domin shi Aljani babu ruwanshi da cewa wannan ne yayi min laifi kan mai Uwa da wabi yake yi zai iya karar daku gaba daya ,ni kaina ba zai kyaleni ba

Hannunta yana karkarwa ta karbi kokan Cikin bushewar maqogaro tace Uban duna Mai "yayan turawa zan cika Umarni da izininka Duna ya bani sa'a

A taikace dai anan suka bar wannan matar da tun farkon zuwansu su ka gani da Alama ita ma irin bukatarsu daya da Siyaman,

Da qyar suka fito daga cikin dajin A daddafe Siyama ta shiga mota hannunta riqe da wannan koko sai karkarwa yake,

Rukyy tace yanzu nan zamu sami bola mu biya Almajirai su binne mana Abinda yake hannunki ke kuma dole zaki hau kan bolar kiyi Abinda A ka Umarce ki

Tace kwarai kuwa idan mukace zamu tafi da wannan Abin ina zamu samu bola ni tsoro nakeji ma kar wani tsautsayin ya Afka masa"

Sun Fara shigowa Cikin gari Rukyy ta hango wata tsohowar bola tace kinga wata bola can anan ya da ce mu Ai watar Aikinmu,

Kwarai kuwa to yanzu ina zamu samu Almajiri?Siyaman tafada tana waige waige ta cikin motar

Can suka hango gungun Almajirai sun tawo ko wanne riqe da kwanonshi

Rukyy tace yawwa ga wasu can da sauri tafito daga cikin motar ta jingina a jiki har suka karaso ,ta tsayar dasu cikin sakin fuska ,tace Dan Allah ga Aiki zakuyi min zan baku dubu dai dai kunji"

Da sauri babban cikinsu yace wane irin Aiki ne Hajiya?

Tace waccan bolar zaku tona min tsakiyarta ,zan binne wani Abu,ko tausaya min kishiyata CE tayi min Asiri shine nima zan rama idan dubu dayan tayi muku kadan zan qara muku wata Akai"

Sukace to ba damu wa Hajiya zamuyi miki ,Kan kace kwabo sun hau kan bolar tsakiyarta suka samu wani dogon sanda suka fara tona wa, sosai tayi zirfi san nan suka sakko , sukace an gama Hajiya

Jiki na rawa Rukyy tafito da kudi ta raba musu sannan tace suyi tafiyarsu,

Guri yayi tsitt dake dama can hanyar baka sa fai mutane suke bin ta ba sabida yadda a keyin yawan gamo Sam gurin bashi da kyau ,ga shuri (gidan tururuwa) kusfakusfa A gurin

Rukyy tace maza kifito kije ki binne yanzu babu idon jama'a

Da sauri Siyama ta bude murfin motar hannuta dauke da wannan koko ta dirfafi katuwar bolar nan ga duhun magariba ya karato

Haka ta dinga hawa bolar duk tsayin ta bai dame ta ba sai da ta tadda gurin da suka tona sannan ta tsaya riqe da kokon tafara Surutai kamar yadda A ka Umarce ta duk tafadi bukatarta a kan D'ija sannan ta sunkuya ta sanya kokon ta mayar da tarin bolar da'a ka tono ta rufe gurin staff

Ta sakko Cikin Sauri jikinta sai zabga wari yake tafada mota tana sauke Ajiyar zuciya Rukyy taja motar cikin Azama suka bar gurin!

*✍🏻,,,,,,,,*
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
~*DEDIGATED TO:MY FAN'S*~
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—

Yamma tayi sosai lokacin da suka karasa gida A gajiye Siyama tace Rukyy ta'aje ta a gida kafin ta wuce ,Ai ko haka A kayi bata shiga da motar ba A waje ta ajeta ,ta joya ta tafi tana kara jadda dawa Siyama dole gobe ma ta San yadda zata fito domin su daura in da suka tsaya,

Buga katon get din tayi ,da sauri wani soja ya taso ya bude kafadarshi rataye da bindiga

Ganin ita ce sai ya matsa ya bata guri domin shigewa gami da gaisheta

Sama sama ta Amsa ta wuce ciki tana bin ilahirin motocin dake gurin A aje ,gabanta ya fadi ganin motar Ali wannan ne ya tabbatar mata da cewar ta dawo,

Ai ko ga gabanta yana faduwa ta durfafi hanyar part din nasu

Karo suka kusa yi dashi fitowarshi Sallah r magariba ganin lokaci yayi jikinshi sanye da jallabiya ruwan toka kanshi sanye da hula irin ta larabawa As'usel Hannushi manne da carbi mai ma dannai

Sauri tayi tabashi hanya bakinta yana rawa tace yaya Ali sannu kadawo A she?

Harararta yayi yana tabe baki yace ke zan wa sannu ,ae daga ina kike?

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.