Abnal Book 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Abnal_Book_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 46
Chapter 13
THIS BOOK IS ABSOLUTELY FREE 💃 💃 💃
Da laila ta karaso gida, a parlor ta tararda Abnal da sameera, bayan sunyi mata sannu da zuwa laila take tambayarsu inda Mami take, Sameera ta amsata da tana daki tana hutawa, zama laila tayi sannan tayi tagumi da hannun hagunta da Marwan yasa mata zoben, Abnal ne yafara hango zoben cos of the way it was glittering, murmushi ya saki yana cewa
"okay..., someone is about to get hitched" dagowa sameera tayi daga wayar da take dannawa jin abunda Abnal yafada ta kalli laila itama, sai gashi itama ta hango zoben, aikam dirowa tayi kasa tana murmushi tace
"OMG, sissy did uncle Marwan propose to you?" laila na murmushi ta girgiza kanta alamar 'yes' cos dama dan su hango zoben shiyasa tayi tagumi, ihu sameera ta saki tana cewa
"i hope you said yes ?" kallon sameera Abnal yayi yace
"of course she said yes, had it been she said no zakiga zobe a hannuntane"
"that's true, I'm just soo excited shiyasa" sameera tafada, surutun sune yasa Mami fitowa daga daki tana cewa
"wai surutun mai kuke hakane ?"
"uncle Marwan ne yayi proposing to sissy" Sameera tafadawa Mami excitedly, kallonta laila tayi sannan tace
"oh, you're such a parrot" sannan ta kalli Mami ta gaisheta tana cewa
"dana dawo sameera tace kina hutawa kuma banson damunki shiyasa ban shigo daki ba"
"ba komai, mai sameera take cewa na likita yayi miki, ko proposonne..." Abnal ne ya fashe da dariya jin abunda Mami ta kira proposing, sameera da laila suma murmushi suke, laila ce ta bugi Abnal da purse dinta tana cewa
"wai kai kuma mai abun dariya toh?" laila tafada while still smiling
"ai kibarshi, yayi dariyar da kyau" Mami tafada tana zama kusada laila, nuna mata zoben laila tayi tareda mata bayanin komai da Marwan ya gaya mata na turowan dayace yana sonyi, Amma shi da kanshi yace zaizo washegari, addua Mami tayi sannan tace
"toh wannan zoben na menene ko mai amfaninshi?" Mami ta tambayi laila
"ai toh Mami abunda ake yayi kenan, it's part of civilization" sameera ta amsata
"Allah ya kyauta" Mami tafada tareda tashi ta koma daki, sameera hannun laila ta daga ta kurawa zoben ido tana cewa
"anya wannan ba real diamond bane ba, with the way its glittering haka?"
"of course real diamond zai zama, ai harkar na manyane bana talaka irin muba" Abnal yafada, tashi sameera tayi tana cewa bara taje ta daura girkin dare, sameera na fita daga parlourn Abnal ya tashi ya dawo ya zauna kusada laila yayi hugging dinta, bayan sun saki juna ya kalleta yace
"congratulations sissy, I'm so happy for you, you deserve all the happiness in this world cos you've been through alot, and i just hope that this new journey you're about to embark on serves as an opening to many greater things for you, once again congratulations "
" thank you soo much, i really appreciate the love and care you've always shown me, you've always been there as my rock that i can always lean on, through thick and thin you were always by my side, for this i say a very big thank you " laila tafada tana hawaye, goge mata hawayen Abnal yafara yi sannan yace
"whatever good you get, sissy trust me that you deserve it, so please stop this tears cos henceforth, the only tears you gonna be shedding is that of joy" girgiza kai laila tayi alamar 'okay' tana murmushi
"oya come and give me all the full jist, how did he propose and all.." Abnal yafada just to cheer laila up, dariya laila tayi sannan tace
"gossip monger, i know you'll want to know and hear everything"
"oho, whatever you like say, na your mouth, all i know is you will jist me everything" Abnal yafada
"i don hear, i will jist you later, now i want togo and have a chitchat with my momma" laila tafada tana shiga cikin daki.
Washegari as promised Marwan yazo gidansu laila yayiwa Mami bayanin komai na gameda turowan dayake sonyi in yayi tafiya, and shi nan kusa kamar nan da two months shi yakeson ayi bikin, Mami tace mishi gaskiya yayi kusa dayawa dan suma zasuso su shirya, Amma Marwan insisted, yana cewa kar Mami ta damu kanta, all they need is their presence, just to avoid back and forth sai Mami tace taji, but she will have to inform laila's paternal family tukunnan, duk abun dasuka ce, she will let him know, godiya Marwan yayi mata, Marwan ya dade sosai agidan kafun daga baya yayi musu sallama, da kyar shi da laila suka rabu. Bayan tafiyan Marwan Mami ta kirasu Abnal, laila da sameera, suka zauna dan tattauna maganar da Marwan yazo dashi, dan lokacin da Marwan yakewa Mami bayani su Abnal basuwa gurin, yanzu matsalan da suke fuskanta shine KUDI, ina zasu samu kudin biki, dan Mami itama tanaso ace anyi auren dawuri kodan shekarun laila, Amma the money is not there, and tasan cewa dangin marigayi mijinta ba kulasu zasu yiba, Abnal ne yayi magana kamar haka
"ni anawa shawaran, why not muyi amfani da kudin damuka samu daga wajensu, atleast ni personally i still have about 980 thousand naira with me, sai mu hada dana sissy, atleast with that we should be able todo something with it, opposing dinshi laila tayi tana cewa
"gaskiya a'a, we've already budgeted those money for something else, this is what is going to happen and i want everybody to accept what i want to say now please, Abnal you will be traveling with your money, kai daza kayi tafiya zuwa wata kasar da ba dangin uwa ko na uba, you can't go empty handed, while my own money zamuyi amfani dashi to establish a business for Mami, inkai kayi tafiya, ni kuma nayi aure, there will be nobody to help Mami out cos sameera is still in school, so we will look for a less stressful business and establish it for her, pertaining to my wedding, daurin aure kawai zamuyi cos we don't have the money for any other ceremony, kayan daki da sauransu will have to wait , but nan gaba inmu samu kudin sai muyi in kuma bamu samuba sai mu hakura, I'm not gonna kill myself over any tradition, the most important thing is daurin aure, zanyiwa Marwan bayanin komai, if he's okay with it shikenan, if he's not, sai ya jira har musamu kudi sannan sai ayi biki" laila tafada, shiru kowa yayi cos what she said made sense, sai Mami ce tayi magana tana cewa
"toh mun jiki, kiyiwa likita bayani tukunnan duk abun dayace saiki gaya mana, insun yarda ayi bikin ahaka sai muma musan yanda zamu fara shiri".
Da laila tayi waya da Marwan, bayan tayi mishi bayanin komai, sai yace aishi ya riga yace he doesn't need anything from them apart from their presence, sai laila ta amsa mishi dacewa ai its easier said than done, Mami is trying to avoid any form of gori ne shiyasa, dariya Marwan yayi sannan yace
ai islamically its his responsibility to provide both the house and house hold items that they're gonna live in, so shi baiga abun tayar da hankali anan ba, so the concluded decision was za'a daura auren a keffi bayan an kaita sai ayi dinner that will serve as Walima a Abuja.
Ranar da Mami taje gidan dangin mijinta dan gaya musu maganar auren laila, she was not welcomed nor did they give her a listening ear, kawai cewa sukayi sunji amma they don't think they will have the time for the visitors that want to come, kawai taje ayi bikin Allah yasanya Alheri, suma ta ya'yansu sukeyi, Mami was heart broken that day, har kwalla sai datayi data koma gida, dan tunaninta yanzu who will come to her rescue, hakuri su Abnal da laila suka ringa bata cewa she shouldn't worry, with or without them the wedding will hold. Laila ce tayi snapping din ring dinta ta turawa anty zee ta wattsapp, aikam anty Zee na tashi daga aiki ko gida bata karasa ba tazo gidansu laila, nan laila tayi mata bayanin komai gameda turowan da Marwan yake sonyi, murna anty zee taringayi kamar mai, amma dataga yanda laila tayi fuska sai ta tambayeta cewa mai ke damunta, sai laila tace
"anty zee babu waenda zasu karbi bak'in daza suzo"
"bangane babu waenda zasu karbi bakin dazasu zoba, what of your partanal uncles?" anty zee ta tambayeta
"hmm, sunce muje muyi duk yanda zamu iya yi, suma ta ya'yansu suke" laila ta amsata
"you don't mean it, Amma gaskiya basu kyautaba, yanzu ya zakuyi?" anty zee ta kuma tambayarta
"i don't know oo, infact amsana Marwan yake jira yaji yaushe iyayenshi zasu zo, dan gobe in Allah ya yarda zaiyi tafiya zuwa canada, kuma yace yana dawowa shi yake so ayi bikin, I'm just confused and fed up at the same time" laila ta amsa anty zee kamar zatayi kuka, numfasawa anty zee tayi sannan tace
"ga abun dazamuyi nan, babansu zeenat zai dawo yau (mijin anty zee barrister ne a Abuja, so he's mostly not around), zanyi mishi bayanin komai, inyaso sai shi da abokanansa su karbi bakin dazasu zo, ko ya kikace?"
"if you can do that for me i will forever be grateful, nagode sosai" laila tafada tana hawaye
"haba dan Allah mai haka? Please stop it, ai mun zama daya, bara inje infara shirin tarban oga" anty zee tafada tana tashi tsaye, dariya laila tayi sannan tace
"aikam dai, anya bazanzo in karbi darussa daga hannun kiba?"
"ai wannan yazama wajibi" anty zee ta amsata.
Washegari anty zee ta kira laila tafada mata cewa mijinta ya yarda zai karbi bakin daza suzo, so zasu iya zuwa next weekend he will be available, godiya laila taringa mawa anty zee kamar zata ari baki, suna gama waya da anty zee, laila taje tasamu Mami tayi mata bayanin komai, addua Mami taringa mawa anty zee, tace anjima zata kirata tayi mata godiya. Laila bata samu daman gayawa Marwan arananba dan aranar yayi tafiya so his number wasn't going through, sai Washegari Marwan ya kirata, bayan sun gaisa laila tayi mishi ban gajiya, laila tafada mishi abunda anty zee tafada cos she doesn't wanna hide anything from him, Shima addua yayiwa anty zee sannan yace zai gayawa babanshi, so next weekend sai suzo da kayan sa rana, daga nan suka zarce zuwa hiran soyayya.
Bara mu leka Nadia da Abnal
Lokacin da Marwan ya fadawa anty faty da Nadia cewa laila accepted his proposal, they were super duper excited, ya kuma fada musu maganar visa da international passport dayake sonyiwa Abnal kafun shi yayi tafiya, sai Nadia ta tambayeshi cewa
Wa zai aika ya kaiwa Abnal passport da visa din inya gama? Marwan ya amsata da cewa chauffeur dinsa ne zai kai mishi tunda yasan gidan, rokonshi Nadia tafarayi cewa dan Allah ya bari itada chauffeur din suje tare, dan harga Allah she has missed Abnal alot, dukda kullum sai sunyi waya, atimes kuma suyi video call, but she still wants to see him in person, da kyar Marwan ya yarda cewa ta raka chauffeur dinsa, but sai data yimishi alkawarin cewa she will behave herself. Ranar Wednesday ne chauffeur din Marwan zai kaiwa Abnal passport dinsa, already kafun Marwan yayi tafiya yariga yayiwa anty faty da mijinta bayani cewa Nadia will be going with his chauffeur to keffi dan ta duba lafiyar Abnal and she will also be administering some medication for him, da toh suka amsa mishi jin cewa Abnal's health was involved. On Wednesday da chauffeur din zai tafi, ta gidan anty faty yabi ya dauki Nadia sannan suka dauki hanyar keffi, suna hanya kiran Abnal ya shigo wayarta, dagawa tayi bayan sun gaisa Abnal yake tambayarta cewa where is she going this early morning dan lokacin daya kirata was around 7am and yasan cewa Nadia bata fita zuwa aiki not until around 8 or 9am, sai amsa mishi tayi da cewa she has an emergency to attend to in the hospital shiyasa ita tafito dawuri, infact she doesn't have much time now, zata kirashi zuwa anjima inta koma gida, fatan samun nasara Abnal yayi mata sannan ya katse kiran, murmushi Nadia tayi sannan ta ajiye wayarta. Zuwa 8:30am su Nadia suka isa gidansu laila, Nadia was shocked da irin area din, how poor it was, tana fitowa daga cikin motar yan unguwar suka fara aikinsu na kallo, dan kallo daya zakayi mata kasan cewa she doesn't belong to that area, from her outfit to her skin screams of wealth, kwankwasawa tafarayi a kofar gidan dan it was locked, Abnal dake zaune a compound din gidansu yana revising one of his textbooks, shi yafara jin kwankwasawan da akewa kofar gidansu, he was surprised dayaji ana kwankwasa musu kofa this early morning, tashi yayi dan duba waye, yana budewa lo and behold saiga Nadia nan tsaye, he couldn't believe his eyes, Nadia too wasn't expecting cewa shine zaizo ya bude kofar, tana ganinshi wani irin sanyi taji acikin zuciyarta, kamar ta rungumeshi haka takeji amma sai ta dake instead ta dan hade fuskarta tace
"please sir I'm looking for one miss laila, does she live here?" Abnal bai amsa taba instead he stepped aside dan ta samu daman shiga ciki, shiga Nadia tayi da sallama a bakinta, laila da fitowarta daga kitchen kenan ce ta amsa mata sallamarta tana cewa
"who am i seeing like this?" tafada suna rungume juna, bakuwar murya da kamshin turare da Mami da sameera suka jine yasa suma suka fito zuwa sakar gida, zuwa Nadia tayi tadan rutsuna ta gaida Mami, amsawa Mami tayi da fara'a sannan suka gaisa da sameera, sai laila ce tayi magana tana cewa
"Mami ga our famous Nadia nan, yar yayar Marwan"
"Ma Shaa Allah, wacca taringa dawainiya dake da Abnal a asabiti?" Mami ta tambaya dan ta tabbatar
"A itafa, ai she's one in a million" laila ta amsa Mami, godiya Mami tayi mata sosai, sai sunna kai kasa Nadia takeyi wai ita kunya, dariya abun yabawa Abnal, cikin parlour suka shiga Nadia tazauna, Abnal bai shigo cikin parlourn ba, karatunshi yaci gaba dayi, laila ce ta tambayi Nadia abun data keson ci, Nadia ta amsa da anything is fine by her, bread da shayi da kwai suka bata, har Nadia ta gama cin abunci Abnal bai shigo cikiba, and the main reason why Nadia came was because of him, sai sameera da Nadia ce suke hira kamar sunsan juna tun da, laila ce tazo tasamu Abnal tace
"wai bazakaje kasame taba?" ta tambayeshi ahankali dan kar Nadia taji ta, kallonta Abnal yayi yana murmushi
"inje inyi mata mai?" Abnal Shima ya tambayeta
"my friend don't pretend with me, i know you're dying to go and meet her" laila tafada mishi
"you see the reason why i don't want togo and meet her ba? Cos you read meaning into everything" Abnal ya fada mata
"oho dai, nidai katashi kaje kasameta" laila tafada tana barin wajenshi, dariya Abnal yayi yana cewa
"see me see wahala oo".
Tashi sameera tayi tace
"i really would have love to stay behind and get to know you better, but unfortunately i have a test today and I really need to get going if not i might miss it, infact I'm already late"
"haba ai ba komai, kawai let's exchange digits inyaso sai muringa waya, daga nanma we will get to know each other better" Nadia tafada, bayan sunyi exchanging din digits sai Nadia ta kuma cewa
"zo in gayawa chauffeur din daya kawoni ya ajiye ki a school" sameera declined the offer but Nadia insisted, sameera had no choice than to concur, fitowa sukayi suka wuce Abnal din dake zaune, sameera ce tayiwa Abnal sallama cewa ita ta wuce school, adawo lafiya Abnal yayimata, Amma Nadia bata ko kalli indayake ba, bayan sameera ta wuce, Nadia ta dawo cikin gida, tazo wucewa kenan Abnal ya rike mata hannu tareda tashi tsaye a gabanta.
24/12/2021, 2:28 pm - +225 0143689782 left
25/12/2021, 9:57 am - MEEDAH'S COUTURE AND MORE: I just published "Chapter 14" of my story "ABNAL". https://www.wattpad.com/1126780129?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ummuhamdiyah&wp_originator=xHmfD9XdhHcyNlozmXwNuOaLv42JtSe1fMpKUQJ3kAwdxHmOU9X2ozCW2lytbW9SEwm1TQwg68XxDpD2n9r3aLitCLOxVmvqI9evcf603aafI49WXjzVjRLyX8BGQUQG
ðŸâ€Â´Ã°Å¸â€Â´Ã°Å¸â€Â´Ã¢Å¡Â«Ã¢Å¡Â«Ã¢Å¡Â«Ã°Å¸â€ÂµÃ°Å¸â€ÂµÃ°Å¸â€?
Book by :Bilkis Qazeem (ummu Hameedah)
ABNAL
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.