Complete Hausa Novels

Abnal Book 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Abnal_Book_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 19 of 46

Chapter 19

THIS BOOK IS ABSOLUTELY FREE 💃 💃 💃

Yaune launching din eatery na laila, Almost all the influential people in Abuja were present, har ya'n media anyi inviting dinsu, Alhaji habib yaso Mami tazo amma Mami tace baza tazoba, so instead sameera ce tazo, duk waenda suka halarci luncheon din sai yaba kyaun wajen suke, both Nadia da sameera were looking astonishing, anan ne Yusuf ( Alhaji Habib's first son) yaga sameera kuma ta kwanta mishi, he approached her and they got talking cos Yusuf too is good looking in his own right, harya Kaiga them exchanging digits. All the pictures they took there Nadia sent it to Abnal. The launching was a success, so washegari eatery din zai bude for business.

Washegari  sameera ta koma keffi dan sun kusan fara jarabawa a school, itada Alhaji Habib ne sukaje, da suka isa keffi, Alhaji Habib couldn't believe his eyes when he saw where Mami was living, Amma bai nuna ba a fuskanshi, suna isa ya umarci body gaurds dinsa su tsaya a waje, dama mami tasan da zuwan su. After exchanging pleasantries sameera ita ta shiga daki dan tahuta, Mami kuma ta k'awata gaban alhaji habib da kayan ciye ciye, abunci dan kadan yaci sannan ya fuskanci Mami yace
"baki gayamun cewa yanda kike da kyau haka kika iya girki" murmushi Mami tayi tareda cewa 'ta gode'. Tarihin rayuwarta dana ya'yanta Mami tabawa Alhaji Habib kamar yanda ya bukata, ba karamin tausayinsu ne ya tsirgawa Alhaji Habib a zuciyan shiba, Shima tarihin shi ya bawa Mami, sannan yace shi gaskiya baison a dade ana abu da'ya, he wants them to get married as soon as possible, tunda su ba yara baneba, they know what they want, sai Mami ta bukaci ya bata lokaci ta gana da family dinta tukunnan, duk yanda sukayi zai jita, da 'toh' Alhaji habib ya amsa ta, amma yace dan Allah karta bari abun ya dade. hiran soyayya da yanda yake son Mami Alhaji Habib ya cigaba dayi mata, tun Mami najin kunya har tazo tadan saki jikinta dashi. Alhaji Habib ya dade sosai a gidan, dan sai dare yabar gidan tareda barwa Mami kudi mai tsoka, Mami bataso karba ba, Amma Alhaji Habib was having non of it, sai daya tursasa mata ta karba.

Washegari around 10am bayan sameera ta tafi makaranta, sai Mami ta kira laila dan ta Sanar da ita abun dasuka tattauna da Alhaji Habib jiya, laila na daga wayar bayan sun gaisa, sai Mami take cewa
"ya naji muryarki wani iri?"
"wallahi kawai banji dadi ne, da safennan da ciwon kai na tashi" laila tafada
"Allah ya baki lafiya, maybe zirga zirgan taron da kikayi shekaranjiya ne, dafatan dai kinsha magani?" Mami ta tambayeta
"Maybe, amma nasha magani, yanzu ma ina eatery, dan ba daman inbar masu aiki su kadai for now"
"toh madallah, Allah ya sanya Albarka ya kawo kasuwa mai Albarka" Mami takuma fada, da 'Ameen' laila ta amsa mata, sannan Mami tayiwa laila bayanin abunda suka tattauna da Alhaji Habib jiya, inda Mami take nuna damuwarta cewa gata ita ba iyaye ne garetaba, maganar ya'n uwa ma bai tasoba, dan batada su, she grew up knowing only her parents kafun suma suka rasu, ya'n uwan mijinta ma they are nothing to write home about cos they don't give a hoot about her and her children, infact data dawo daga Abuja, uncles dinsu laila suka zo zasuyi mata diban Albarka, wai maiyasa bata yimusu bayani cewa ga irin mijin da laila zata aura ba, sai d'aya daga cikinsu yake cewa ai dan bata daukesu da daraja ba shiyasa, Mami tatas tayi musu dan ta gaji da irin cin mutunci da suke mata, baram baram suka bar gidanta aranar, yanzu ita bata masan ya zata yiba. Da Mami ta gama yiwa laila bayani, sai laila tace
"Mami da zaki yarda muyiwa anty zee magana da yafi, kema kinsan cewa daga Allah babu kowa garemu inba itaba, inna gama waya dake yanzu zan kirata muyi magana, duk yanda mukayi da ita zan sanar dake"
"toh naji, Allah ya taimaka" Mami tafada, laila ta amsa da 'Ameen' sannan ta katse kiran. True to laila's words tana gama waya da Mami ta kira anty zee, bayan sun gaisa, laila tayiwa anty zee bayanin komai, murna anty zee taringayi tana cewa dama tanada niyyar zuwa ganin Mami dan tun data dawo daga Abuja basu hadu ba, so intaje duk abun dasuka tattauna da ita, she will fill laila in, godiya laila tayi mata, sannan anty zee take cewa tayi hakuri na launching dinta da bata samu daman zuwa ba, Amma babansu zeenat ya bata labarin yanda eatery din ya hadu( cos he attended the launching) ga kuma sakon alert na Marwan data gani, murmushi laila tayi tace ai anty zee ta cancanci komai, cos without her help batasan ya zasuyi ba.
The next day da anty zee ta tashi daga aiki, gidan Mami taje, bayan sun gaisa, anty zee takewa Mami murna tana cewa dan Allah Mami ta saki jiki da ita dan ita ta dauki Mami a matsayin uwa ne, yanzu abun da zai faru shine zatayiwa ubanta magana ya tsayawa Mami a matsayin waliyinta, tunda mami tace ita bata bukatan wani shagali apart from daurin aure, Amma ita zata kawowa Mami mai gyaran jiki da Kuma social worker wacca zata ringa koyawa Mami abubuwan zamani, Amma for now Mami ta gayawa Alhaji Habib cewa ya bata kamar wata daya kafun ayi biki, godiya Mami tayi mata tace insunyi waya da Alhaji Habib duk yanda sukayi zata gayawa anty zee, sai susan next line of action.
Da Mami sukayi waya da Alhaji Habib sai tayi mishi bayanin cewa itafa bata bukatan komai apart from daurin aure, Alhaji Habib yayi na'am da abunda Mami tafada dan Shima bayason hayaniya amma yace shi zai bawa Mami kudin komai, dan tayi lefenta da kanta and shi baya bukatan komai daga gareta, godiya Mami tayi mishi sannan Alhaji Habib yace tunda wata daya ta bukata shi ya bata, kawai date shi yake jira yanzu, Mami tace karya damu da wannan, zuwa jibi ita zata bashi date. Basu dade da gama waya da Alhaji Habib ba saiga sako nan ya shigo wayar Mami, sameera ta kira tazo ta karanta mata, aikam sameera na bude sakon taga cewa alert na kudi ne, 10 million naira from Alhaji Habib wai kudin lefe (karku ce kudin is much, remember Alhaji Habib is a politician so 10m is actually a chicken change to them), sameera da Mami couldn't believe it, laila Mami ta kira ta fada mata, she too was surprised, sai Mami tace ita gaskiya zata mayar mishi tace kudin yay yawa, Amma laila ta hana tana cewa ai ba karba zaiyi ba, kawai Mami ta kirashi tayi mishi godiya, haka kuwa akayi.

Few weeks later

Bikin Mami saura sati biyu yanzu, Mami tasha gyara bana wasaba, sai sheki takeyi, kuma a yau laila ta iso keffi, zokiga murna a wajen Mami da sameera, they were super excited to see pregnant laila, yes you heard right, laila is pregnant, bayan launching na eatery dinta da take jin jikinta wani iri da mami take cemata kodai zirga zirgan launching din datayine, ashe cikine da ita. Laila ta karayin fresh da ita cos JIMPO ORI PRODUCTS din da take amfani dashi ya karbeta bana wasaba, kallo daya mutum zaiyi mata yasan cewa she's in money, bayan ta huta Mami take tambayarta cewa yanzun data bar business dinta, wa zai sa mata ido, murmushi laila tayi sannan tace ai she has staffs, tanada manager, ga chefs da waiters, so her business is in good hands cos her manager is very efficient, mostly duk ranar dataje (dan ba kullum take zuwaba, cos of laulayin ciki, ga kuma online program da takeyi) a office take zama, bawai wani abun take zuwa yiba, adduan cigaba Mami ta kuma yimata, bayan wannan Mami take bata labarin sameera da Yusuf, tace farkon ranar dayazo ita tayi mamaki har ita take mishi tsiya cewa yazo yaga yanda ita takene, dan ita batasan cewa zaizoba, wai murmushi kawai yayi yace ai shi so yake yayi surprising dinta kuma yazo yaga sameera, dan lokacin sameera taje makaranta kuma bata dawo ba, not knowing cewa ita sameera tasan da zuwanshi, not long after Yusuf yazo saiga sameera nan itama ta dawo daga makaranta, in a nutshell sameera da Yusuf are dating, dariya laila tayi bayan mami ta gama yimata bayani sannan tace ai ya kamata by now mami tasan sameera da zurfin ciki, fatan Alheri suka nemawa kansu.

Yaune daurin auren Mami, a central mosque din da aka daura auren laila nanne aka kuma daura na Mami, baban anty zee ce ta tsayawa Mami a matsayin waliyi while babansu Nadia shine waliyin ango, andaura auren bisa sadaki dubu dari biyar, kuma a ranar za'a kai Mami gidan mijinta, sai fatan zaman lafiya. While Sameera  ita kuma alhaji Habib ya nema mata transfer zuwa university na Abuja, amma suna hutu yanzu, in zasuyi resuming she would resume with them, Amma for now gidan laila zata zauna.

Canada

Da akayi launching  eatery din laila, Nadia ta turawa Abnal hotunan su, rigar da Nadia tasa was an off shoulder, duk wuyarta were out and mayafinta kawai daura shi tayi a kafada, amma tayi kyau, da Abnal yagani baice komai ba, sai washegari when they were video calling Nadia tace
"you didn't even say anything about the pics i sent you, had it been i didn't  send it to you now you will be complaining" kura mata ido Abnal yayi na waensu dakiku sannan yace
"i intentionally didn't say anything about them"
"why? You don't like them?" Nadia ta jera mishi waennan tambayoyin
"they're beautiful, but you exposed your body" Abnal yafada, bude idanuwa Nadia tayi kafun tace
"ni kuma? What did i expose? Cos if i can recollect i was putting on a gown and it wasn't even tight fitted"
"but it was an off shoulder" Abnal yafada, murmushi Nadia tayi sannan tace
"ohh that, what's the big deal there?"
" it might not be a big deal to you, but it is  to me" Abnal yafada seriously, Nadia takaita murmushin da takeyi tayi ganin cewa Abnal is quit serious about it, sai tace
"you're such a cave man, i pity your future girlfriend" Abnal bai amsata ba instead sai yace
"promise me something"
"what?" Nadia ta tambayeshi
"that you won't put on clothes that will expose any part of your body again, no matter how little it is"
"and why will i promise you such? It's not as if we are an item" Nadia tafada while smiling
"I'm serious here, please just promise me" Abnal ya kuma fada mata while still staring deeply at her
"see me see trouble oo, irin wannan karfin hali, okay i promise you" Nadia tafada cos the way Abnal is staring at her is making her feel uncomfortable
"thank you" Abnal replied,
"so when will you be visiting sis hassy cos she's through with her exams?" Nadia ta tambayeshi trying to change the topic
"truly i don't know, cos i got a job in a consulting agency as a therapist, so my free time is quit limited, but muhseen will be going to see her tomorrow" Abnal  replied
"wow congrats, shine ko ka gayamun, had it been i did not ask you about sis hassy you wouldn't have said a word" Nadia tafada a shagwabe
"you know that's not true, that was the main reason i called you, but i got distracted when you asked about the pictures you sent me, in ban gaya miki ba wazan gayawa kuma?" Abnal yafada mata jokingly
"i don hear, so your therapy is for who?" Nadia asked
"people with depression, any form or type of depression" Abnal replied
"nice one and good luck with that" Nadia tafada
"thanks, but i will try and squeeze out time to go see haseeba, duk lokacin dazan je i will let you know" Abnal yafada mata.

Lokacin bikin Mami da Alhaji Habib, Both muhseen da Abnal were super excited, yanzu they call themselves brothers, saiga Yusuf Shima yana gayawa muhseen cewa shi yasamu mata which is sameera, da Abnal yaji wannan kuma he was speechless, cos everything was just happening soo fast, if anyone had told him 6 months back that he and his family will be where they are today zai karyata ne, Amma sai gashi within a blink of an eye Almighty Allah has turned their life around, bai da abun cewa sai Alhamdulillah (that's Almighty Allah for you), followed by lailas pregnancy, the day he heard that one, sai dayayi kwalla cos of how overwhelmed he was with soo many emotions.

Nigeria

Mami is enjoying her marital life cos Alhaji Habib is such a caring husband, babu abun daya yarda Mami tayi, yace she has suffered enough, now is her time to sit and enjoy, tuition fees na makarantar Abnal ya fara biya tareda bashi the same amount of allowance dayake bawa muhseen, da Mami takeson tayi complain dan he's already paying for sameeras tuition fee too, sai cewa yayi indai Mami tace wani abun pertaining to duk abu da zaiyiwa su Abnal toh shi zai san cewa Mami batason su Abnal su daukeshi a matsayin uba kenan, da Mami taji wannan she had no option than to keep mute. da Abnal yasamu allowance na farko kiranshi yayi tareda yi mishi godiya, cos Abnal anashi plan din, he wanted to sponsor himself shiyasa ma ya nemi aiki, and Alhamdulillah salary din daza'a ringa biyanshi is in six figures in an changa kudin zuwa naira, dan su acan any profession pertaining to health ana biyansu sosai, ba kamar nan Nigeria ba that government baisan value din health workers ba. So salary dinshi yanzu he will just be keeping it, and laila itama tana tura mishi kudi duk wata, dukda ya gaya mata cewa ta daina cos he's comfortable amma laila bata daina ba, in a nut shell Abnal is just roaming in money.

Allah ya azurtamu da arzikin Halal, Ameen 🤲.
08/01/2022, 1:33 pm - MEEDAH'S COUTURE AND MORE: I just published "Chapter 20" of my story "ABNAL". https://www.wattpad.com/1136513394?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ummuhamdiyah&wp_originator=cy%2Fbp44LphbmrqpZT%2BA2QF3AGPWbxo4sK%2FQg71xZ%2BPLaoS902cjjD23to3sEH7PDDMh74TxpFuaR%2FoSemz5SnKherU9DJgMGFq8AmsHSdQzpHsLb9FLks1ww9l2YIiKr

🔴🔴🔴⚫⚫⚫🔵🔵�

Book by :Bilkis Qazeem (ummu Hameedah)

ABNAL

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.