Complete Hausa Novels

Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 1 of 17

AISHAH-SIDDIQAH

4

SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com
TUNASARWA/JAN HANKALI
Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”.
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.
–Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki.
KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali.
GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa. Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.

KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
-Takorinku

AISHA SIDDIQAH 4
Haseenah na ganin fitowarsa ta mike tsaye with great excitement a kan fuskarta. A take sai Aisha taga Hamma ya wani irin daure fuska. Gabadaya ya koma babu annuri. Ya fito a basarakensa sosai. Yau sai taga ma Hamma yafi mata kama da yarbawa akan Fulani. Fuskar nan ba rahma ko kadan ko kankani. Yace cikin wata irin murya.
“What are you doing here?” Haseenah tace “kayi hakuri Prince, just give me few minutes of your time. Ta’aziyya ce nazo nayi maka na Emir. Aunty Taiwo ta gaya min kana Argentina, nikuma na zo yin wani project daga office dinmu, nace zan zo har gida in yi maka ta’aziyya kuma in yi amfani da wannan damar in baka hakuri Prince. Am sure she told you sakon dana bata gareka”.
Sai Hamma ya zauna gefen Aisha yana kokarin cooling anger dinsa, ita kuma Aisha taji kamar an kada mata kararrawa a cikin kanta, domin nan take ta ayyana itace tsohuwar budurwarsa Haseenah Ambursa, wadda Kiki ta bata labari. Don haka nan take sai ta mike, amma sai Hamma ya rike hannunta, ya saka idanunsa cikin nata yace “ina zaki mu da zamu fita kuma?” tace “naga kayi bakuwa ne Hamma, zan kawo mata ruwa da lemo ne in baku wuri”.
Sai Prince yace mata “zauna, ba shan ruwa ya kawota ba, yanzu zata tafi”.
Ya mayar da ita zaune inda ta tashin, zuciyar Aisha tayi mata nauyi, ba don komai ba sai don tuno soyayyar da ake bata labarin Hamma ya yiwa Haseenah, har shine silar da yaki aure shekaru goma sha uku, a zuciyarta tace ita daman matar cushe ce a gareshi, kila yanzu Haseenah ta dawo rayuwarsa kenan, dan bond din da suka fara developing ita dashi zai bi iska. Zai tashi a banza. Mai wuri ya zo mai tabarma sai ya nade kayarsa.
Sabon takaici ya lullubeshi na yadda akayi Haseenah ta samu address dinsa na Argentina gun Taiwo, ta shigo gidansa na Sunnah bada izninsa ba. A ran sa yana ayyana yadda zai ci uwar Pareto ciki da waje, da yake budewa kowane kare da kowanne doki gidansa ba tareda ya masa izni ba.
Haseenah ta roki samun privacy na tanaso suyi magana ita da shi, wani asararren kallo yayi mata yace.
“I have got nothing to hide from my wife”.
Nan duk Haseenah tabi ta sha jinin jikinta, cewa wannan sabon Prince Kehinde Abdulrasheed ne, ba wanda ta dade da sani ba.
Jikinta yayi mugun sanyi. Ala dole ta fara fadin abinda ya kawota akan idon Aisha.
Na farko ta bashi hakuri, kan abinda ya faru shekaru sha uku a baya, tace babu ranar da bazata wayi gari ta kuma wuni tana nadama ba, amma bata da excuse, bata ma son kawo shi. Ta yarda kaddararsu ce tazo a haka amma ba don rashin so tayi masa abinda tayi ba”.
Sai Haseenah tayi shiru, sannan ta kalli idanunsa tace “Kehinde, you will always be the one that has got my heart, and I am so sorry for being the reason you stayed this long without a wife.
Na tabbata nima hakkinka keta bina na kasa aure sai yanzu, ina ji a raina kullum in har ba na nemi gafararka ba zan fara rayuwa ne akan karya. Ka yafemin. Yarinta ce da shaidan suka taka rawarsu gareni a lokacin.
Amma na maka alkawarin cewa na dau darasi na domin Tokumbo bai aure nib a bai kuma kara waiwayata ba bayan ya gama kwasar rabonsa a tare dani”.
Prince ya kalleta sai yaga tana share hawaye, a zuciyarsa yaga zallar nadama a tare da ita da talalar Ubangiji bayyananniya. Haseenah duk ta tsofe, wannan kyan duk ya dushe. Ba dai cikin wahala take ba, amma kuma duk kyannan na kuruciya babu shi a tareda ita.
Sai kawai ya daga kai ya kalli Aisha, a take sai yaji duk wani bakin cikinnan na Haseenah yana ‘melting’, har ya zamo babu shi babu sauransa ko kadan a tare dashi.
Yayi duba ga irin kyawun da Aisha tayi a gabansa, tana sanye cikin shirin atamfa ‘super exclusive, looking beautiful and innocent, yaga cewa in bai yafewa Haseenah bama kamar ya yiwa Allah butulci ne. Saboda ya bashi abinda ya fita sau dari. Wannan shi ake kira “blessing in disguise”.
Da wannan tunanin sai kawai Prince ya dubi Haseenah yace.
“Haseenah Allah ya yafe mana bakidaya, yes I was hurt, amman in gaya miki gaskiya I have no ill feelings towards you now, Allah ya wanke min zuciya yayimin sakayya da AISHAH-SIDDIQAH...”.
Ya dan kalli Aisha da itama shi take kallo, yace “na yafe miki Haseenah ko don albarkacin Aishah.
Saboda ba don kinyi abinda kika yi din ba, da ban hadu da ita Aisha ba, so in this way, I must say a big THANK YOU! Allah kuma yasa ku zauna lafiya keda mijinki din”.
Prince sai yaga Haseenah tana kallonsa kawai, ta sake share hawaye tace “thank you”. A ranta tana mai kissima babban rashin datayi na Prince Kehinde, wanda ta tabbata ko shugaban kasar Ingila taaura bazata maida kamarsa ba.
Prince ya mike ya dubi Aisha yace “muje ko?” Sai Haseenanma ta tashi tace “to na barku lafiya, Madam Aisha bye, till next time”. Prince yace “a’ah Haseenah babu next time, please, kamar yadda nace “I have no ill feelings towards you, haka babu alaqa, na yafe miki, but please don’t show up in our house again”.
Tace “in sha Allah. You really deserve to be happy, Aisha congrats to you, you don’t know what God did to you!”.
Daga haka sai tayi wani murmushi mai daci ta tafi.
Aisha a ranta taji dadin yadda Hamma ya hanata tafiya, ya girmamata a idon Haseenah, amma duk da haka wani irin kishin Haseenah take, ta hau ayyana irin mugun son da Prince yayi mata, data tuna hakan sai taji wani bala’in haushi a makogaronta.
Ta koma tana cewa a ranta meyasa ma take jin haushin? Itada ba son Hamma take ba. wata zuciyar tace “ai dai mijinkine da so ko babu SO. Haka dai, duk ta zama confused, taga cewa ko Ishaq da take ikirarin ta so, bata jin wannan zafin zuciyar a kansa da wata.
Haseenah na fita, Aisha ta zame hannunta daga na Hamma, ya kalleta yace “muje” tace “nidai na fasa zuwa ko’ina, sai ka dawo kawai, I don’t feel like going out any more” Hamma yace, “Why?” tace “hakanan, ban jin dadi sai wani lokacin”.
Ta soma warware daurin kallabin data yi.
Nan Hamma yaso ya gane meke faruwa. Ya tuna ranar da yaji tana maganar Ishaq, abinda yaji a ransa, balle ita yau dungurungum Haseenar ce tazo. Sai yace.
“Aisha listen to me, Haseenah wata long chapter ce a rayuwata da bani ko son tunawa, don Allah ki fahimta, don’t read too much into it”.
“Bakomai” inji Aisha. “Ba sai ka min bayani ba Hamma, matar so ce tazo ban hakuri, love of your life akace ko…. so don’t owe me any explanation.
Ni daman ai matar huce haushi ce, so me zai kai nima jin zafin zuwanta? Har zaka tsaya bayanai. Ba komi Hamma bari in yo sallah”.
Ta wuce.
Prince yana kiran sunanta “Aisha, Siddiqah…Aishah…” tace “ba komai Uncle”.
A ransa yayi tsaki yace shi dai Allah ya isa tsakaninsa da Taiwo, ya samu sun fahimci juna yana zaman zamansa ta kwanto masa kura.
Yace to wai ita Aisha yanzu har ta san kishi? Ko dai itama ta fara sonsa ne? sai yace “shima fa haka yaji ranar da tayi maganar Ishaq.
Haka Hamma ya zauna yanata tsaki buhu-buhu shikadai.
Yaje dakinsa yayi sallah ya dawo dakinta yayi knocking, tun kafin ta bashi iznin shiga yasa kai.
Yana shigowa tana fitowa wanka daga ita sai tawul, ta juya a firgice zata yi baya ta koma tace “Subhanallah Uncle lafiya?” A ransa yace “wato Haseenah ta zo, kalmar Uncle ta dawo, kai! Taiwo Allah ya isa!”.
Ashe a fili Hamma ya fada, yana bude ido sai ya ga Aisha bata nan ashe ta koma toilet din ta rufe ta bar shi a wurin.
A wunin ranar bakidaya abun duk ya dameshi, gashi Aisha taki yarda ta tsaya ma yayi mata bayani.
Ta zama wata sumu-sumu a gidan. Ta takure kanta, abin duk yabi ya addabeshi.
In ya tuno kalmar nan ta “Haseenah matar so” da tace sai yace “Omooo!”
Daga ranar da Haseenah tazo, dan taya shi kwanan da ya samu ana yi duk an daina. Ta koma dakinta bakidaya.
Yau Hamma ya dawo can dare, ya zo ya sameta a falo tana barci a kujera, ya tasheta yace “Aisha tashi muje daki ki kwanta mana” Aisha ta bude ido fal barci, tace “yau dai ka kwana a gadonka Uncle”.
Ya rasa yadda zaiyi da ita dole ya wuce ya kyaleta, don ta kwashe dankwalinta ta koma nata dakin.
Washegari Nenne ta kirata Aisha ta amsa suna gaisawa, Nenne ta ji ta wani iri, da ta matsa da tambayar meke damunta? Aisha tace bata jin dadi ne.
Hajiya Nenne mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta dauka ciki ne keda Aisha ta soma murna baka da zuci.
Ta kira Prince tace “Hammansu ashe Aisha bata jin dadi?” Sai kawai yace “eh” sai gata ta fito falon domin ta dora abinci, yana kallonta lokacinda take fitowa suna wayar shi da Nenne.
Sai yace da Nenne gatanan ma ta fito, ina jin girki zata yi”.
Sai Nenne ta hau fada “itada batada lafiya zaka sa girki? A barta ta huta. Naji muryarta tayi kasa sosai. Kai da zakayi ta lallabata Hammansu, kasan me juna biyu hutu takeso”.
A ransa Prince yace “me Nenne ke nufi ne?”
Ita Aisha bata ji ba, yace “juna kuma Nenne? What’s that?” tace “kunje asibiti?” yace Nenne daga kwana uku ne zuwa yau fa” Sai Nenne ta hau fada tana cewa “har kwana uku tana fama da ciwo baku je asibiti ba? Ina Aishar? Bani ita” yace “gata” yana karasawa kusa da ita da wayar a kunnensa.
Nan Prince ya mikawa Aisha wayar, Nenne ta hadasu su duka tana surfesu da fada, “Aisha ki ajje sokoncin nan kuje a dubaki, haka zaki zauna da ciwo? To dai ciki ba’a masa haka, Allah ya raba ku lafiya”.
Ai jin ciki sai Aisha ta yanke da kakkaifar wukar hannunta bata sani ba, tayi maza ta jefar da wukar, tsabar firgici, shima Hammah yace “ciki kuma Nenne?” tace “eh mana. Ba shine ba?” Sai yayiwa Aisha wani kallo, ya kece da dariya.
Yace “Nenne yaushe tace miki ciki ne da ita?”
Sai Nenne tayi shiru, sai kawai Hamma ya sake fashewa da dariya ya kashe wayar.
Aisha itama abin ya dan bata dariya, ta dan dara ba shiri, ta kalli Hamma yana kara kyalkyacewa (he looks amazing), kamar bai ma san kalar kyan da far’a take yi masa ba.
A wannan dan dakikan da take kallon Hamma Prince, sai taji (her whole world feels complete). Wannan din mijinta ne da ya hada komai da dan adam ke burin samu, kyau da nagarta, nasaba, ilmi da arziki da kuma kyan hali.
Sai kawai zuciyarta ta hasaso mata haka yayi rayuwar soyayya da Haseenah, ita to da aka cusa masa ma ya sake yanzu yake kula da it aba karamin dadi take ji ba, to wannan wane irin dadi Haseenah tayi ta ji a ranta sanda suke tare suke soyayyah yana kula da ita?
Sai kawai far’arta ta koma, Siddiqah ta mayar da annurin fuskarta ta sake dinkewa tsaf.
Ganin haka sai ya kashe gass din data kunna, ya kama hannunta suka wuce (sitting room).
A tare suka zauna a two seater, Hamma yace “Aishah, bana son mu gina rayuwarmu akan zargi da rashin communication.
Ko me nayi miki banso kina fushi dani, just tell me. Kina ji na?” Aisha tace “yes” don taga ya kawar da wasa, he is serious now.
Yace “menene yake damunki tun ranar can kike ta attitudes?” tace “babu komai” “ko ki fada min ko in kira Nenne, ita in ta tambaya na tabbatar zaki gaya mata” tayi shiru dai, da ya matsa sai tace “Uncle ko ka kira Nenne ni ba abinda kayi min, hakannan dai kawai ban jin surutu”.
Hamma yayi shiru, daga bisani ya sunkuyar da kai, yace “kan zuwan Haseenah ne ko?”
Sai Aisha ta mike tace “bari in karasa girki na”. Sai kawai ya janyota ta fado cinyarsa duk ta daburce tana kokarin tashi kawai sai taji yayi hugging dinta ta baya gabadaya.
“Don Allah Uncle ka sake ni….” yai shiru, jin baida niyya itama ta share tayi shiru, baka jin komai sai bugun zuciyoyinsu. Can kuma Hamma yace (in a cool tone).
“Yes, Haseenah was my girlfriend, naso aurenta, amma (she did something bad) da ya raba mu. The worst thing da kika sani za’a yiwa masoyin gaskiya.
Kuma a kanta ne na rufe babin mata a rayuwata, wanda hakan yasa I feel Kaman duka daya suke, dalilin ma kenan da yasa ban kuma neman wata ba, kuma ko an bani cikin ‘ya’yan ‘yan uwana a family sai ince banaso….
Toh Aisha har saida Nenne ta nemomin aurenki da kanta, aka yi ban sani ba, don ta san inna sani bazan yarda ba, amma tun ranar dana je asibiti duba Nenne, na ganki, na yaba dake a raina Aisha, har na gayawa Nenne, nace wacece wannan yarinyar mai hankali haka….
Kinga dai kudin goro na yiwa mata, but you stood out, I was impressed with you”.
Long story short, tun a lokacinma da bansan ke matata bace, naji kin burgeni da attributes dinki, kuma zama dake da nayi na dan lokaci na sake ganin me Nenne ta ganin min.
Aisha naga meyasa iyayena suka nemo min aurenki suka aura min. Kamar yadda kikace addu’ar Nenne a filin Arfah ce ta fado a kanki wannan haka ne. don haka ke zabin Allah ce a gare ni.
You are a light in my life and I am telling you you are shining so bright. Kinga duk ciwon dana ji na rashin Haseenah? To yanzu godiya nakewa Allah da nayi wannan rashin nata, don I wouldn’t have met you…
So don Allah ki cire maganar Haseenah a kanki, babu abun fushi a wurin, You my Dear kin zama ‘ife mi, orun mi, iyawo mi’ kinji Aisha?”
Sai ta daga kai. A zuciyarta wani sanyi na zuba, ashe haka ake ji in mijinka ya fifita ka kan kowa? That’s the Yoruba husband in action. Sai taji haushinnan yanata tsiyayewa… yana bin rariya, ta gyara zata tashi ya kara riketa, yace,
“kin fahimceni yanzu?” Tace “yes Uncle” yace “Uncle ya dawo dai? Don Allah ya koma.
Ni ina murna kina ce min Hamma, daga nan in zama honey, watarana in dawo Sweetie, shine kuma za’a koma Uncle dinnan, haba babyn Nenne da Dade”.
Sai kawai Aisha ta saki murmushi.
Tace “naji Ya Hamma” yace “ko kefa?” Sai tace “me kace dazu da yarbanci?”
Sai yace “ashe kina ji? To ki koya ki fassara mana”.
Aisha tayi dariya, sai lokacin Hamma yaji sanyi a zuciyarshi har da ajiyar zuciya.
Bakinsa daidai saitin kunnenta yace “Babyn Nenne da Dade kuma Babyn Hamma ko?” Prince ya fada yana jin wani cool feelings for her, sai ta tashi da karfi zata wuce kitchen don kunya sosai ta lullubeta, tana ‘yar dariya.
Hamma yayi maza ya dawo da ita jikinsa. Yaji dadin yadda yana mata bayani ta sauka, kuma da gani har ranta abin ya wuce. She’s a very understanding person.
Sai Prince ya sake rungumeta sosai ta bayanta, yayinda take zaune a kan cinyar sa. Itama Siddiqah sai tayi mukus…. Hamma ya kwantar da kansa bisa masangalin wuyanta… yana sunsunar kasan wuyanta, duk sunyi shiruuuu na wani lokaci, kamar ruwa ya cinyesu. Bugun zuciyoyinsu kawai kake ji wadanda ke bugawa a lokaci guda.
Murya a sanyaye Aisha tace "Hamma, thank you for the explanation, nasan ba dole bane kayi min bayaninnan, amman naji dadi da kayi min din, domin ya wanke min zuciya.
In sha Allahu kuma nima bazan qara fushi ba kan maganar nan".
Prince yayi murmushi, voice dinta yana caressing din sa, gabadaya wata kasala ce ma ta sauko masa, yana ta kokarin dannewa.
Ya dai kasa magana yai shiru, ya rufe ido, listening to her soft sound, tana masa wannan maganar cikin lumana da gamsuwa da abinda yace mata, and the softness of her skin dake kwance a jikinsa yana kara tasiri a tare dashi.
Sai Hamma ya samu kansa da dan murza hannunta …. jin shirunsa yayi yawa bai amsa ta ba, sai Aisha ta juyo kadan haka ta dubeshi. Sai ta ga Hamma da ido a lumshe, kamar mai jin barci.
A tsanake tayi kokarin tashi daga cinyarsa, ya kuwa rike ta gam, ya dan bude idon yace "ina zaki?" Aisha tace "abincin zan qarasa" yace "kashe gass din, we will eat out today, just stay here…".
Aisha tayi shiru, ta koma jikin Prince ta kwanta tayi lamoo! Yace "please Aisha..... muje outing din?" Tace "toh ai bacci kake ji naga", Hamma yace "bacci? Did i say so?" Ta ce.
"To ai Hamma idonka rufe yake fa tun dazu, ina ta maka magana bakaji ba, gashi ma muryar bacci kake yimin".
Prince bai san sanda wani kasaitaccen murmushi ya kufce masa ba, he so much loves her naivety. And she is observant, but totally ignorant ga halin da yake ciki.
Yes, yanayin sa gaba daya ya canza, wata muguwar sha’awa ce ta saukar mashi. It seems with every word she says kara yayyafa ma wutarsa petrol take, amman babyn Nennen bata gane ba. Wannan childishness dinnata yana kara burge shi.
Hamma yace "Ayshaaaaa…" tace "na'am Hamma" yace "ba bacci nake ba, I am just in a mood!" Ya fada yana mata wata kallo, mai shiga rai da sanya kasala.
Har sai da Aisha ta tsargu don ya kara jawo ta jikin sa sosai, this time around juyo da ita yayi tana facing dinsa gabagadi. Aisha tayi shiru, yace "baza ki tambayeni what mood ba?" Tace "toh Hamma bacci kake ji, kuma ka kafe kai baka ji" ta dan turo bakin ta gaba, tana fada cikin shagwaba 'yar gaske.
Ai kuwa Prince ya sa ido yana kallon bakin da take turowa so soft and luscious, bai san sanda yace "I really really want to kiss you saddiqa… "ya matso dab da fuskar ta, har suna jin numfashin juna, ya kalle ta, cikin idonsa kadai ta ga tsantsar al'amuran dake cin zuciyarsa da gangar jikinsa. An yi sa’a itama ta juyo kenan sai kawai Hamma ya hade bakinsu wurin guda ya soma kissing Aisha-Siddiqah in a serious tone and passionate manner.
Da kyar Aisha ta samu ta zame daga Hammah, ta mike jikinta yana rawa a daburce tayi hanyar kitchenette. Hamma da kyar ya iya mikewa yanakokarinsaita kansa. Yabi bayanta yana cewa cikin basarwa,
“you know what? Jeki shirya kawai ki bar girkinnan, we are going out, ma ci a waje”.
Tace “toh”, sai ga Nenne ta sake kira.
Tace “ni Hammansu dazu maganar bikinsu Princesses na kira zan maka na manta, an saka rana, kwanaki goma masu zuwa. Don Allah ka taho da Aisha, kuma kuzo da wuri. Asabar ne daurin aure wato ranar addu’ar arba’in din Sarki”.
Prince ya ce “toh Nenne, in sha Allah”.
Itama Aisha sai murna lokacin da Hamma ya gaya mata zasu tafi gida Lagos sati mai zuwa, tace “bikinsu Firdausi za’a yi?”
Yace “eh, za’a hada da addu’ar arba’in na Emir. Shine babban burinsa kafin rasuwarsa wato auren twins din gidanmu”.
Siddiqah tayi ta murna har ‘yar rawa ta shiga takawa a wajen, ta manta shaf a gabansa take, irin murnar zata gida dinnan, after a long while.
Hutun Prince ya dade da karewa, zuwan Siddiqah ne yasa ya kai har wannan lokacin a Argentina.
Sun fita a daren sun shakata, suka ci abincin dare a wani Arabian Cuisine sannan suka dawo gida.
Aisha ta nufi dakinta tayi wanka ta sha rigar barci mai dan kauri purple ta fesa turarukanta masu dadin kamshi ta nufi dakin Prince.
Nan ta tadda shi daga shi sai short nicker akan sofa yana shan ‘chamomile tea’ kafin ya kwanta. Ta na shiga Hamma ya dago yana dubanta da wani kallo da bai taba yi mata ba, domin sha'awar matarsa ce zallah yau cikin idanunsa da duk abinda yake yi. Aisha ta juya da sauri zata koma ganin ba suttura a jikin Hamma sai gajeren wando, ga kunya data kamata sai ya aje kofin hannunsa, yace Aisha wait, ya taso ya isa gareta ya kamo hannunta ya shigo da ita cikin dakin yana cewa.
"Ya kinzo turakar miji neman albarka kuma zaki koma?"
Aisha duk ta daburce ta rikice tarude, sabida yanayin da Hamma ke mata magana yau ya sha banban dana koyaushe. Ba don ta kasance mai karfin ji bama, da bazata ji shi ba.
"Dama-dama... zuwa nayi ince maka Hamma saida safe".
Hamma ya dora hannuwansa biyu bisa kafadun Aisha hagu da dama yana murzawa. Ya dan mutstsuka jijiyar wuyanta cikin wani salo na tasowar muguwar sha'awar da baisan akwai a tareda shi ba, saida Aisha ta runtse ido sabida tasowar tata sha'awar ta diya mace, kafin hannunsa ya kai kansa saman kirjinta.
Yace "saida safe dinma ai irin haka ake fadarsa Ayshahhh, ba da fatar baki ba. You my dear I want to kiss you again today!".
Hamma ya fada admiringly idanunsa akan siraran lips din Aisha, yana musu wani inviting looks. Aisha ta kusa narkewa bakidayanta domin a lokacin Hamma ya matsota sosai ne a jikinsa, ya isa cikin nutsuwa ya hade bakinsu wurin guda ya soma sumbatar Aisha a tsanake, sannan ya koma kissing hungrily.
Ashe namiji duk dadewar sa babu aure, ba sai an koya masa sumba ta auratayya ba? Ko da kuwa ya fidda rai da ita, ko bashi da sha'awar ta, sanda zata sameshi zai ji tane tana sarrafashi.
To hakan ce ta faru da Prince Abdulrasheed yau. Da ya samu kissable lips din Aisha yau ya dinga tsotso tamkar Allah ya aikoshi, saida ya ajiye kishirwar shekaru masu yawa na kuruciya dana shiga girma.
Aisha kyale Prince tayi ya yi yadda duk yake so yau, ya jagwalgwala ta iya son ransa a duk ta inda yake so. Ya tsotse duk abinda yake so. Kuma shi da kansa yayiwa kansa limit. Don yana ganin in ya kauda budurcinta any moment zata iya conceiving, shikuma yana ganin kamar bata yi kwarin da zata haihu ba. Tunda har ya samu wannan access din zai iya karawa Aisha lokaci.
A kwanaki goma da suka biyo bayan wannan ranar, wata wawuyar shakuwa ce ta shiga tsakanin Hamma da Aisha. Suna kwana a gado guda, Hamma saida ya san yadda yayi ya fara raba Aisha da dukkan sittirun jikinta in zasu kwanta, yana rabar Aisha da dabara da wayau da simple hugs, da light kiss masu sawa ta saki jiki da shi, su yi barci manne da juna. Tun Aisha matukar jin nauyi da tsoro har ta soma sakewa da Hamma sosai. Don ta lura ba shi da nufin abinda take tsoro. Kusan sati biyu kenan irin rayuwar da suke yi a cikin gidan kenan, full of understanding, intimacy and love, Hamma ya zama baya iya barci bai raba jikinsa dana Aisha ba, bai sumbaci bakinta da kirjinta yadda yake so ba amma bai taba wuce hakan ba yake takawa kansa birki, don a ganinsa har lokacin Aisha bata yi girman data isa ya dora mata hidimar dake cikin aure yanzu ba kada tazo haihuwa ta samu matsala.
Amma me? A na I gobe zasu tafi Lagos komai kwace masa yayi, ya kasa controlling kansa yadda ya saba duk kuwa da yana tausayawa Aisha, da kyar da roko da magiya harda kuka Aisha ta kwaci kanta a hannun Prince domin kuwa gani take duk ranar da hakan ta faru ba wata wata mutuwa zatayi, in tayi la'akari da irin yanayin da Prince ke shiga a irin wadannan lokutan akanta.
A satin dasu Prince zasu dawo Lagos Dade yasa aka je aka shirya gidan Prince na Banana Island, wanda ke daura da gidan mahaifinsa, Prince ya jima da sayen gidan bai taba amfani dashi ba, tun kafin saukarsu Dade ya gayawa Nenne in sun zo a gidansu zasu sauka. Yasa aka gyara gidan aka shigar komai da zasu bukata.
Tun saura kwana uku daurin aure suka sauka a Lagos. Gidan ya debi murnar zuwan su ba babba ba yaro, kowa murnar zuwan Hamma yake yi, ga ‘yan biki sun soma isowa daga sauran jihohi. Kiki ce kawai bata samu zuwa bikin Aunties dinta Princesses ba, don tana shirin rubuta jarrabawarta ta karshe a Informatics a lokacin.
Aunty Murjanatu Taiwo tana Ilorin, sai bayan addu’a zata taho Lagos tare dasu Nenne in sun je. Dade yace su Hamma su fara sauka a Lagos su huta kwana biyu, in yaso sai su dunguma duk gidan zuwa Ilorin su samu adddu’ar Sarki ranar asabar, wadda ta kasance kuma ranar daurin auren su Fatima.
Nenne ta rasa ina taka saka ina taka aje da surukarta Aisha, wata sabuwar kauna da soyayya Nenne take yiwa Siddiqah musamman data gane suna zaman lafiya itada Hamma, Aisha ta samo kansa shima ya samo nutsuwarta, Nenne bata taba jin Hamma cikin farin ciki da nishadin data ji shi ciki ranar da suka yi waya itada su, tana tsammanin Siddiqah ciki gareta ba. don haka tun kafin saukarsu a Lagos yau Nenne da kanta ta shiga kitchen ta shirya abincin tarbar Hamma da Aisha, ta hada dana Dade, girki tayi masa na musamman data tabbatar Hamma ya dade bai samu irinsa ba, wato (Locust Beans Stew) da suke kira Dindin da (Ofada Rice).
Bayan saukarsu da kadan Dade yace ma Prince a gidansu zasu tare, yasa an shirya musu komai da zasu bukata. Don haka ana gama cin abincin dare Dade yace Firdausi ta dauko keys din gidan ta baiwa Hamma, ta yiwa Aisha rakiya kuma.
Anan Nenne tace “a’ah Dade, ita kam Aisha ta zauna ta huta anan, a bari sai bayan biki sannan ayi tarewar. Ta jima bata nan akwai bukatar ta huta tukunna”. Ai kuwa nan da nan Prince ya canza fuska. Domin a yau kam yayi niyyar angwancewa da amaryarsa Siddiqah babu daga kafa. In yaso idan ciki ya samu ya tayata nakudar. Yanzu kuma Nenne tana wani zance wanda zuciyarsa ta gaza dauka, wai Aisha ta zauna da ita har bayan biki, duk kokarinsa na rainon da yayi tayi wata da watanni ba’a gani ba, sai rana daya da ya saka ran hutawa.
Har dai rashin jin dadin hakan ya gaza boyuwa a fuskarsa, ‘yar damuwa ta nuna a fuskar Prince, amma dai bai yi magana ba. saidai tuni Dade da yake shi namiji ne ya ramfo shi.
Lura da yanayinsa da Dade yayi, sai yace.
“Kehinde kodai kafi so ku tafi tare yanzu ne?” Zuruf! Aisha tayi tace “Dade ayi hakuri don Allah ni nan zan zauna gun Nenne har a gama biki, nayi kewar Nenne for long”.
Taki dago ido balle Prince ya kalli kwayar idanunta. Domin ta riga ta san Prince ya gama kaiwa kul a a dalcinsa. Daren tahowarsu da yaya ta tsira? Balle yanzu a gidansa na gado? Takaicin abinda Ausha tace yasa shima ya hadiye, yace “a’ah Dade, ba wata matsala a kyaleta ta sha zamanta”.
Amma Kai da ji kasan shagube ne yayi. Ya ajje spoon ba don ya koshi ba, sai don bazai iya cigaba da ci ba’a gane ransa ya baci ba, da abinda Aisha tayi masa a gaban kowa ta nuna bata damu dashi ba, ya mike yace zai je gidansa ya huta. Bai sake kallon inda Aisha take ba ya nufi hanyar fita falon.
Anan ne Nenne ta dubi Aisha tace “raka shi zuwa mota mana Aisha” Hamma, wanda a lokacin har ya kai bakin kofa cikin matukar kulewa zai fice, yace.
“A’ah Nenne na yafe, ta zauna kawai, na gode”.
Wannan gwasalen da Hamma yayiwa rakiyar Aisha, duk ya faru akan idon amare Princess Fatima da Princess Firdausi, don tare aka zauna cin abincin har dasu gabadaya.
Abin yayi matukar yiwa Fatima dadi, na yadda Prince ya nuna bai damu da Aisha a gaban kowa ba. ita bata fahimci haushi yaji don Aisha tace da bakinta bazata bishi ba. Har ta samu abin adarwa a gaba.
Fatima na komawa dakinta ta kira Aunty Taiwo, tana mayar mata da yadda aka yi, da irin gwasale tayin binsa gidansa da Prince yayi ga Nenne da Aisha, sai Taiwo tace da Fatima, “ewo, to dama nifa na san Kehinde sarai, nafi kowa saninsa, saninda ko Nenne bata yi masa ba, ba son zama da yarinyar nan yake ba, biyayya yake yi musu don a rabu lafiya da kafaffun iyayenmu da basa shawara, su Nenne ke faman cusa masa ita kamar dusa, kamar ance lafiyayyun mata ‘yan asali na manyan gida sun gama karewa a duniya.
Na rantse idona idonta a Lagos ko Ilorin in ta sake tazo, sai nayi mata wulakanci da kaskancin da bazata kara kuskuren zuro jiki cikin zuri’ar Akanni ba, balle ta wani kwashi siraran kafafunta tazo mana biki irin wannan na girma”.
A dakinta na baya wato dakin Kiki aka sauketa, kafin ta kwanta saida ta kira Ummanta ta gaya mata saukarsu lafiya a Lagos, sannan ta kira Hamma don tayi masa saida safe ta kuma bashi hakuri da kalamai, amma sai ta samu ya kashe dukka wayoyinsa.
Haka ta kwana da tunani da damuwar Hamma a ranta.
Washegari da safe ita da Nenne ne suka shirya abin karin Dade da Hamma, sai wajen karfe goma na safe Prince yazo gidan kuma a gurguje suka karya shida Dade zasu fita, bayan yabi Nenne dakinta sun gaisa, yanaso ya tambayi Aisha amma ya dake. Sai gata tana shigowa dakin Nennen dauke da lemun tuffah da sassanyar madarada tanbulan na tangaran akan karamin tray, ta gefensa ta wuce zuwa ciki, taci ado har ta gaji gabadaya ta saje da ‘yammatan amarya da suka cika gidan tun jiya.
Ta ajiye a gabansa, don tun safe take dakon shigowarsa duk ta damu, tace a ladabce “Hamma ina kwana?” Yayi mata wani kallo yace “lafiya kalau, yaya gajiyarki?” Nenne aka kirata a waya sai ta fita daga dakin tana amsa wayar.
Aisha bata yi aune ba taji Prince ya kamata ya mikar daga durkuson data yi a gabansa ya jata zuwa kusurwar dakin ya matseta sosai a jikinsa, sannan ya manne ta a kirjinsa da wata zazzafar hug, ya rage tsaho ya sumbaci lips dinta lightly, yace,
“Aisha jiya banyi barci ba isashshe saboda rashin ki a gadona Aisha, I missed you and your sweet lips, me yasa kika yimin hakane wai?”
Ya yi mata wani kallo na so da sha'awar da baisan yaushe ya fito daga idanunsa zuwa nata ba, saida Aisha taji tasirin kallonnan har spine dinta, tsigar jikinta saida ya tashi yarrr, Hamma ganin haka ya sake manne bakunansu wuri guda yana kissing lips dinta hungrily, wannan karon zazzafar kiss yake extending Wanda ya rikita Aisha bakidayanta. Duk da haka tunanin a inda suke ya hanata nutsuwa ta amshi sakonnin nasa. Aisha ta soma kokarin kwatar kanta tana fadin.
“Please don Allah Hamma ka bari, ka sakeni kada Nenne ta dawo. Dakin Nenne ne fa!”.
Hamma yace “I don’t care, ai gara ta gani ta san yadda kuka taru kuka kwareni jiya, I missed your warmth, shine jiya kika ce nan zaki zauna ko? Don kawai kinga ina shirin angwancewa? Wannan ai mugunta ne Aisha.
Hummm! Ni na manta ma I am pissed at you na tsaya Ina romancing dinki”. Aisha tayi wani murmushi kawai ta kalleshi “ni dai don Allah Hamma ka sakeni kunya nake ji” ya sake mata kiss a kasan wuyanta sannan ya saketa jin kamar motsi a bayansu. Ashe Firdausi ce ta shigo neman Aisha, ganin abinda ke faruwa tayi maza tayi excusing kanta da gaggawa ta juya tana murmushi.
Firdausi na fita Nenne ta dawo, sai Aisha ta gusa ta basu wuri. Har Hamma ya gama gaisawa da Nenne ya fita daga gidan, wanda ya soma dinkewa da baki musamman kawayen amarya dana Nenne, bai kara ganinta ba. Kuma a washegarin ranar first flight ya tashi dasu zuwa Ilorin, shida Dade, Nenne, Aisha da amaren domin su samu addu’ar arba’in kuma a dauro auren a fadar Ilorin.
Da hantsin ranar suka shiga Ilorin Emirate, Aisha tana like da Nenne duk inda tasa kafa nan take mayaswa. A yanayin kalar fatar jikinsu da kamanninsu na Fulani sai suka fita dabam a gidan, kamar ‘ya da uwarta. Wadanda basu san matar da aka aurawa Prince bama a gidan a ranar suka ganta, masu yabawa nayi haka masu gatsinen yarbawa na kankantar Aisha. Amma maganar rashin wayewa ya fara barin jikin Aisha ta yi fes da ita ta kara cikowa ta fara cika idanun mai kallonta. Prince yana can fada tareda Uncles dinsa do a ranar ne ake shawarar wanda za’a bawa sarauta a cikin ‘ya’yan Emir. Idris Akanni y ace a’ah, ko dama Emir ya dade yana gaya musu su cire Idris da dan sa daga sha’anin sarauta. Basu kara yarda da hakan ba sai yau da Dade ya fitittike yace bazai karba ba, baida ra’ayin sarauta ko kankani, don haka ya barwa kaninsa mai bi masa wato Abdulyaqeen Akanni wanda shine Turaki of Ilorin.
Da wannan aka bar zancen cewa washegari bayan addu’a arba’in din za’a zarce da bikin nadin sarautar da daurin aure.
Da farko a dakin da Nenne ta sauka Siddiqah take amma da Aunty Taiwo tashigo yiwa Nenne barka da zuwa, suka gaisa, ta tambayeta Hakeem tace yana fada, tana kallon Siddiqah a kaikaice, taga alamar a dakin Nenne take nufin zata sauka sai tace da Nenne cikin yarbanci da tayi tsammanin Siddiqah bata ji sam.
“Nenne keda surukar taki daki daya zakuyi sharing ne? Ai ba’a yin haka a gidannan, ta tashi ta koma cikin matan ‘ya’ya, haba Nenne don Allah ki dinga jan ajinki akan yarinyar nan”. Nenne tayi sakatoto tana duban ‘yarta Taiwo kafin ta samu abin cewa Aunty Taiwo tace da wata baiwa dake gefe ta dauko kayan Aisha ta kai dakin da ta sauka.
Jin tace a kai dakin da take yasa Nenne tayi shiru bata tanka ba, koba komai zata so a samu shakuwa da fahimta tsakanin Murjantu da Aisha, bata son yadda Taiwo ke treating matar kanin nata.
Taiwo tace Aisha ta biyo ta, kamar kada ta mike don ba tun yau ba jikinta ya gama bata Aunty Taiwo bata sonta ko kowa bai gaya mata ba. Amma jin Nenne bata ce a’ah ba, kuma Taiwo dinnan diyar Nenne ne da bata da maraba da Hamma, sannan Maman Kikinta sai kawai ta zari hand bag din ta da mayafinta tabi ta nata dakin.
Babban bedroom ne a wani sashe na cikin gidan sarautar, dakuna ne a jere wasu na fuskantar juna duk iri daya, yawanci matan Uncles din Abdulrasheed da matan ‘ya’yansu in suka zo sha’ani duk anan suke sauka, dakin da suka shiga da Aunty Taiwo ya ji kayan alatun rayuwa na gargajiyar sarauta dana zamani, ga iya kwandishin mai ni’ma nata aiki, akwai tafkeken gado da wardrove, Aunty Bola matar wani Cousin dinsu da Aunty Iyabo matar Turaki da Fatima da Firdausi ne a dakin suna hira lokacin da suka shiga dakin. Jikin Aisha a sanyaye matuka don yarbanci kawai kake ji yana tashi a gidan da sauran dakunan, koda suka shigo ma duk ta tsangwami kanta duk da Firdausi na tsokanarta da fulatanci tana cewa duk ta wani takure, tafi son koyaushe gta like da Nenne, tace ta saki jikinta nan duk iyayen Hamma ne sai su kannensa. Fatima ta Harari Firdausi tace da turanci don kowa yaji “in taga dama ta daure jikin don Allah, kinsan bata son shiga cikin yarbawa kada su cinyeta, ba abin raini a wurin yarinyar nan irin Bayerabe. I wonder yadda na jita shiru kamar an aiki bawa garinsu tun isarta gidan Hamma kuma”. Ifedayo ta zaro ido tace “kamar yaya bata son yarbawa? Ewoo! Bata son kabila ta auri dan su, dan ma babban jikan sarkin Ilorin da muke fatan ta zama uwa ga kowa namu watarana?”
Aunty Bola tace “ke ko Ifedayo! Ai ‘yammatan hausawa ba don so suke aure ba, kwadayin su ba inda baya kaisu. Balle taji sarauta zam, taji Prince na kasashen turai ai nan ‘yammatan hausawa dana fulani suka fi kauri. Sai an yi auren kiga ba soyayyar da zata dauwamar da farin ciki a cikinsa”.
Kamar an yiwa Aunty Taiwo kunni, ko kuwa allura akan gyambon ta, ta dubi Aisha ta kyabe baki, tace “ku bar ganin laifinta, iyayenta ne manyan kwadayayyu da basu san darajar kansu ba balle na abinda suka haifa, amma ba ita ba, tunda ita batama san shi ba ko kafin a auro ta, su da suka dauki wannnan teenager suka aurawa Kehinde wanda a haife ya haifeta sune suka fiddo kwadayinsu da zalamarsu fili, ta yaya zaka aurawa danka wanda baka ko taba gani a zahiri ko a hoto ba? Sai kawai don jin su waye iyayensa.
Wai daga haduwar kan hanya aka baiwa Nenne sadaqarta ta aurawa danta saboda an ga mamora a jikinta.
Ni tunda nake ban taba jin aure na rashin mutunci irin haka ba, ban taba ganin auren rashin sanin darajar Da irin naki ba, ai a al’adarku ana lefe, ana yiwa amarya kayan hana gori, amma ke ko lefen bana jin an yi miki, ke suturar da zaki saka ma a gidanmu mu muka yi miki, da tsummokara kikazo, ko wanka babu, aka bi aka asirce mana uwa, bata zance sai naki, amma ku duba kuga daga shan jar miyar Ewedu har ta fara washewa, ku kuke kayan daki amma ke haka aka daukoki zikau! Aka kawo mana.
Mun miki komai domin mu suturtaki, mai nuna sadaqarki suka baima Nenne ta likawa Kehinde ta karfi da yaji.
Kuma shi ba so yake ba, ya fada ya kara bashi da lokacin soyayyah, bazai taba son ki ba saboda ya dade da gama soyayya tun a kuruciyarsa, akwai wadda yayi shekara da shekaru yana so tun samartakarsa har girmansa bai aureta ba. kuma har gobe ita zuciyarsa ke so.
Ni nasan Kehinde wallahi, babu kuma wanda zai gaya min waye Kehinde, ko a kafa aka daura masa ke nan gaba kadan zai kwance ya yar.
Kawai kun ga arziki da sarauta kun nace, watakila ma kuna tunanin Kehinde zai yi sarauta ne, to in gaya miki gaskiya inma wanan kukewa keda iyayenki to kije ki gaya musu Kehinde bazai yi ba.
Da aka aura masa ke aka kawoki guidanmu saida ya jingineki kusan shekara guda, saida su Nenne suka gaji da ajiyarki a daki ne suka tattara ki suka danna masa ganin wankin hula zai kaisu dare.
Da zuwanki gidansa na fahimci kun soma juya masa kai, iyayenki nata surkulle ga dukkan alamu, har wani dora ki yayi a status baya ko jin faduwa a ganshi dake a matsayin mata.
Nayi rantsuwa ni Taiwo abokiyar tagwaitakarsa, inma asirinku ne ya fara cinsa ko zan daina barci sai na warwareshi da karfin addu’a, in asiri kuke shiga jeji kuna jefa masa mu addu’a muke kwana yi, yadda kuka ganshi haka zaku kyaleshi. Kakan kakanmu Shehu Alimi, ya dade da tofe zuri’ar shi da kul’aquzai, daga duk wani sharri na masu nufin Kehinde da wani surkulle na magauta da irinku makwadaita”.
Duk maganar nan Taiwo na yinta ne cikin sassaukan turanci da fulatanci ziryan, don ma Aisha ta fahimta sosai.
Siddiqah dai tana zaune banda kallon bakin Taiwo ba abinda take yi. Kirjinta yana harbawa zuciyarta na matsewa. Fuskarta na rinewa daga yellow zuwa jazir.
Saida Aunty Taiwo ta gama cin mutuncinta tas, su kansu su Fatima da Firdausi wadannan maganganu na Yayarsu Taiwo sun san firgitasu domin sunji sun yi zafi da tsauri sosai. Firdausi jikinta rawa ya fara yi ta soma cewa “haba-haba Aunty Taiwo? Haba ke kuwa don Allah Maman Kiki? Wannanba girmanki bane”. Ganin yanayin da Aisha ta shiga ya firgitasu. Babu ko digon hawaye a fuskarta amma tsigar jikinta duk ta tashi yarr, tsokar fatar bakin ta har raurawa takeyi amma ba kuka ba.
Taiwo zata wuce toilet ta bar su a wurin suka ga gabadaya jikin Aisha ya dauki kyarma, idon nan ya koma kamar garwashin wuta ya kada yayi jazur… Ga dukkan mamakinsu Aisha ta mike da hanzari ta sha gaban Aunty Taiwo dake neman wucewa toilet wato ta gama zagin banza, ta sha lafiya zata wuce harkokin gabanta.
Aisha ta tsaya gaban Aunty Taiwo, gabadaya ta koma Aisha-Siddiqarta fitinanniya, masifaffiya, ta Billiri ikon Allah! Gang leader mara tsoron kowa, sannan mara kara wato mai keke - da kekenta da kowa ya sani, ta kalli Aunty Taiwo cikin ido ta soma magana cikin sarkewar numfashi.
“Na rantse yau kinci albarkacin haihuwa, kin ci albarkacin Kiki a wajeana, kinci albarkacin dimbin qaunar da ‘yar ki ta nuna min.Sannan kinci albarkacin girma da shekaru.
Sannan kinci albarkacin Nenne, mafi girma kuma kinci albarkacin tarbiyar da iyaye na suka bani akan wanda ya girmeni!!!
Kinci zarafin dattako da tarbiya da kamalar da Nenne take dashi kuma ta baku ku ‘ya’yanta, kin ci amanar tarbiyyar data baki!!!
Aunty Taiwo ta saki baki galala! Tana kallon yarinya karama haka kamar diyarta Kiki, ta tsaya a gabanta tana maida mata da martani, yarinyar da bata wuce second born dinta Kiki ba, duka mutanen dakin ma su Ifedayo da Aunty Bola sun sha mamaki domin basu zaci zata iya tankawa Taiwo ba sam, da yake cikin turanci take maida mata martanin duk suna ji, kallonta suke, shock duk ya kamasu.
Firdausi ta soma bata hakuri daman tunda Taiwo ta fara zuba rashin mutuncin Firdausi tana ta cewa “haba aunty Taiwo, ki bari bai kamata ba” Taiwo ta ce mata “shut up malama! Kada ki kara saka min baki in ina magana”.
Ganin haka gudun kada akai ga duka sai Princess Firdausi ta dauki wayarta jikinta nata kyarma ta yiwa Hamma text, tace maza ya bar duk abinda yake yi yazo don Allah ga Aunty Taiwo na cin mutuncin Aisha tana neman wulakantata a gaban dangi”.
A take Hamma ya kira Firdausi immediately, ai kuwa Firdausi ta saka masa a handsfree, yana iya jin muryar Taiwo na karasa wassafa ma Aisha… “ki dake ni mana ‘yar Mallam Shehu! Shine zan san kinyi fushi na zagi makwadaitan iyayenki da suka yi miki auren sadaqah.
An zagi iyayen naki, wata tsiya ne su? Ko zaki rama eh? Ke a karan kanki da dan hankalinki kinga dacewar ki auri Kehinde?
Banda kankanba irin ta talakawa da kai kai inda Allah bai kai ka ba, ina ke ina zuri’ar Akanni?
Ai da kin tafi kin auri mai kora shanu a kauye shine daidai ke…. Amma ba dan Sarki babban jikan Sarki ba…”.
Hamma be kashe wayar ba a haka ya karaso hankalin sa a matukar tashe. Aisha ta wuce ta gaban Taiwo a zuciye, ko ganin gabanta bata yi. Wani irin tafasa zuciyarta keyi. Babu kuka ko digo a idonta zuciyarta ta bushe. Bata so ta kara wata kalma bayan wannan don zuciyarta na iya bugawa a lokacin.
Firdausi ta kula da hakan ta taso ta biyo bayanta da sauri tana Siddiqah tsaya don Allah…. ko jinta batayi ba ta bude kofa, sai karaf! Tayi karo da mutum tsaye a bakin kofar.
Data daga kai ta kalle shi da idanunta kamar gauta sai ta kawar da kai, ta sake juyowa tana kallon Taiwo data biyo bayanta…. ganin Kehinde yasa Taiwo tsayawa standstill. Wani irin bayyanannen bacın rai ne a fuskar sa, zata iya rantsewa tunda take da shi bata ta a ganin wannan yanayin a tare dashi ba.
Ya bude baki zai yi magana sai jin Aisha yayi ta juya tana cewa da Auty Taiwo….
“Kuma kamar yadda kike ta tutiya kan cewa baya sona, haka zalika nima baya cikin lissafina balle na irin mazan da nake so, ki tambayeshi kiji biyayya duk mukayiwa iyayen mu, saboda sun isa da mu. Daga yau na bar miki shi. Gashinan ki jika shi ki shanye….”.
Tana gama fadin hakan ta wuce ta bar musu dakin, ga dukkan mamakin Taiwo sai taga Prince ya bi bayanta yana “Aishah Please wait…Don Allah tsaya…” ko kallonsa Aisha bata yi ba ta kara sauri, ta kara da gudu-gudu, shima ya daga kafa ya bita yana “please listen to me Aisha….”. Yayi sa’ar riko gefen gyalenta, Aisha ta juyo a fusace tace “cikani, daga yau na gama wannan auren”.
A lokacin sun kawo kofar dakin data baro Nenne. Kalaman Aisha na karshe a kunnen Nenne suka sauka, inda tace.
“na gama auren nan, na barwa Aunty Taiwo dan uwanta Kehinde ta jika ta sha, har abada baa auren!”
Da sauri Nenne ta taso suka game ita dasu a bakin kofar, ganin yanayin da Aisha ke ciki da rudewar dake fuskar Hamma saida gaban Nenne ya fadi.
Ta kama hannun Aisha suka shiga cikin dakin Prince da hanzari ya rufa musu baya.
Nenne na jin irin numfarfashi da ajiyar zuciyar da Siddiqah ke sassaukewa a jejjere, ta durkushe a gabanta, ta hada hannayenta wuri guda cikin roko tace.
“Nenne ke uwace mai adalci a wurina, babu abinda zaki sani in ki yi, amma don Allah ki barni naje gun Ummata. Nayi rantsuwa a gidanmu zan kwana yau. Kar kisa nayi kaffara.
Ni Nenne wallahi Allah tun ranar da kika kawoni Lagos da niyyar zaki kaini asibiti, har aka kai ga maganar aure, aka yi aka dawo, duk da banaso har raina, ban taba jin zan iya yi muku gardama ba. kuma na karbi kaddarar auren a haka, nima ai da wanda yake so na din nake kuma son shi aka raba mu amma ban yi bore ba.
Amma Nenne yau Maman Kiki ta tabo martabar wadanda ba’a iya taba su in hakura, inna hakura ma ji zan yi kamar nayi gagarumin laifi ga iyayena, don haka Nenne don Allah zan tafi, na rantse bazan kwana garin nan ba”.
Jikin Nenne yayi sanyi kalau, at the same time she is so proud of Aisha, domin ta haifu, ta cika diya.
Prince na kallon Nenne da dukkan hope na cewa zata lallashi Aisha ta shawo masa kanta ta saurareshi. Shi meye laifinsa a ciki? Amma sai gani yayi Nenne ta dauki wayarta tayi kira.
Bai dai san wa ta kira ba yaji tana “lallai-lallai a nemo jirgin zuwa Gombe yanzu, idan ma babu direct a nemi na Abuja daga nan sai ta kara shiga wani”.
Sai Prince ya dubi Nenne a firgice, yace “Nenne me kike nufi? Gidan zata tafi da gaske? Ta gama auren fa tace, ni kuma fa Nenne?”
Gabadayansa a daburce yake, kansa da duk wani lissafinsa ya kwance, duk wani azanci da tsinkaye da kunyar idanun mahaifiyar tasa sun kwace daga hannunsa.
Nenne bata ko bashi amsa ba tace “Aisha dauki kayanki kinji, muje driver da Dade suna waje suna jira zasu saka ki a jirgin Gombe”.
Dadi sosai ya kama Aisha sai lokacin ta samu hawaye suka zubo, tafe da wata sassanyar ajiyar zuciya, tace “nagode da uzuriki, amma ni Nenne yadda nazo haka zan koma Gombe, ko tsinke bazan dauka ba”.
Ta dauko wayarsa da ya bata daga jakarta ta russuna ta ajiye a gabansa ba tare data kalli yanayinsa ba. Saura kadan Prince yayi hauka a cikin kansa, musamman ganin Nenne tasa hijab ta kama hannunta suka fice suka barshi tsaye a wurin.
Sai kawai ya fito daga dakin shima a matukar fusace, ya san yayi kadan ya dakatar da Nenne yanzu, a yadda yaga fushinta da bacin ranta irin wanda bai taba gani ba, to balle kuma Dade mijin tace din Nenne, wanda sai abinda Nenne tace yake amfani dashi. Don haka maimakon yabi bayansu, dakin su Taiwo ya nufa. Yana tafe da sassarfa yana tambayar ransa me zai yiwa Taiwo ya huce?
Ance ba’a raba hanta da jini, ance blood is thicker than water… wai ba’a batawa da ‘yan uwa saboda mace, komin son da ake yi mata. Amma shi yadda yake jin matukar bacin rai da soyayyar Aisha data bijiro masa yanzunnan, mai raba shi da Taiwo dinsa yau sai Allah.
**** **** ****
Tun kafin su Nenne su karaso jikin motar daya daga cikin direbobin Emirate da Dade ya kira ya bude musu kofar gidan bayan wata jibgegiyar mota baka wuluk suka shiga har Aisha wadda hannunta ke cikin na Nenne. Direban ya ja motar cikin nutsuwa suka bar fada. Har sai da suka dauki hanyar airport din Ilorin sosai, suka yi nisa fintinkau da masarautar ta Ilorin, sannan ne Aisha ta ji ta (at ease) kuma bugun kirjinta ya soma lafawa, Aisha ta yi ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali, saboda abinda take so Nenne ta yi mata nan take, Nenne ta dubi halarci, kauna da amana ta yi mata kan ta rufe baki. Me za ta ce da Nenne Sappa? Ban da Allah ya ja kwananta?
Tana jin Nenne da Dade suna magana amma da harshen Yoruba suke yi, (which means) ba su so ta fahimta sosai, don kuwa yarbancin mai zafi da sauri da sauri sosai suke yi. Amma a cikin dan abinda take tsinta yanzu a harshen ta fahimci kamar Dade na rokon Nenne ne akan ta bari a yi komai a hankali kada ta biyewa fushin Siddiqah, ta bata hakuri su wuce Lagos don yana so ya fahimci meye matsalarta data sa aka taso tafiya Gombe haka bagatatan, suna tsaka da sabgar biki, kuma daga ina matsalar take?”
Sai taji Nenne na cewa, “A’ah Dade, yi hakuri ka barta ta tafi, ni a wurina tafiyar Siddiqah Gombe yau ba makawa sai wani babban ikon Allah mai karfi da ya gagari iyawata, matsalar daga Taiwo take, zaka fahimci komai daga baya don ba yau matsalar Maman Kiki ta fara akan Siddiqah ba, na yau din na fahimci yayi tsamari ne tunda har kaga Siddiqah tayi fushi, amma a halin yanzu bazan iya yarda da komai ba banda cikawa Siddiqah burinta”.
Ta Lawanti International Airport. Dade ya yi ma Siddiqa tikiti, babu ko waya a hannunta haka ta shiga jirgin, Nenne ta gaya mata tana sauka Malam Buhari direban Nani Oummana zai zo ya dauke ta daga gidan Sarki. Ya kaita har zuwa nasu gidan.
In kaga idanun Siddiqah a lokacin a soye suke kamar gyada marau-marau, babu ko kyallin hawaye a cikinsu. Na Nenne ne fal kwalla, suka yi sallama ta shiga jirgin Mangal. Dade dai yana gefe yana kallonsu ya rasa abin da ke masa dadi, don Nenne har zuwa lokacin ba ta yi masa wani cikakken bayani da zai gamsu da tafiyar Siddiqah Gombe kuma ita kadai ba, don ta ce ita ma ba ta gama fahimtar matsalar ba kawai ta yi wa Siddiqah abin da ta ke so ne kada hawan jini ya kama yarinyar, a yanayin da ta ganta kamar mai tashin iskokai sanda ta ke rokonta ta maida ta gida. Hakika Nenne ta tsorata, kuma ta dauki laifin duka ta dora a kan Abdulrasheed, duk da a hargitsatstsen bayanin Aisha ta fahimci ita dasu Taiwo ne.
Siddiqah na sauka a Gombe ta tarar da direban Nani Oummana watau Buhari ya dade yana jiranta, wanda dama ta sanshi, duk zuwan da suke yi Gombe da ma shi yake daukarsu zuwa gida haka in zasu koma Lagos shi yake kaisu airport.
Suna tafe a hanya Siddiqa banda ajiyar zuciya ba abin da ta ke yi. Wata irin ajiyar zuciya mai tafe da numfashin fushi da bacin rai. Ji ta ke a ranta, daga yau aurenta ya gama karewa da Prince Abdulrasheed ko za’a mutu ko za’ayi rai.
Nenne kuma a sanyaye ta kira Hajiya Zainab, bayan tasowar Siddiqah sukuma suna hanyar komawa Emirate, ta gaya mata komai a sakaye. Inda ta ce (murya ba karsashi) “Zaynaba ga Siddiqah nan zuwa, ki yi wa Mallam Yunus bayani, Siddiqah ce ta daga hankalinta sai ta taho gida, muna tsaka da bikin twins a Ilorin.
Ta ce ba ta bi ba’asin maganar ba tukunna sai sun koma gida daga raka Siddiqah, ta dai biye wa Siddiqa ne don kada ta yiwa kanta illah, in ta koma gida daga airport din zata bincika ko me yake faruwa kuma za ta dauki matakin da ya dace, insha Allahu.
Nenne tace ma Umman Siddiqah. “For now Zaynaba, ba don ni ba ina so ku taimakeni, ku tausasawa bakuncin na Siddiqah zuwa gareku, ku karbeta babu tambaya babu tuhuma, naga kamar tana da iskokai idan ranta ya baci, ku karbeta da hannu bibbiyu kada ku ce mata don me, yanzu zan koma gidan Kakannin nasu Hammansu, in binciki Taiwo da Firdausi inji me ya faru, saboda na tara al’umma ciki da waje suna jirana da ni da kaina zan rakota, in yaso idan an gama biki an kai amare dakunansu zamu san kwakkwaran matakin dauka.
Tun daga nan Hajiya Zainab ta san cewa ba lafiya ba. Bata san Siddiqah da wasu iskokai ba amma tana da fushi in an kaita bango mai wuyar sauka. Don a saninta Siddiqah ta gama kwantar da hankalinta da auren Prince. Kullum ta kira ta sai ta ce “Hamma na gaisheta, Hamma kaza da kaza.
Ko kwanaki biyun bayannan sun yi waya ita da Siddiqah tana farin ciki tana dariya ta ce mata sun sauka a Lagos ita da Hamma Prince. Bikin kannensa Princesses. Amma bata jin zasu biyo ta Gombe in an gama, don yace daga gama bikin immediately Qatar zasu wuce bakin aikinsa don hutunsa ya dade da karewa. Har tace ma Umman da zata yarda da ta sa Hamma ya kawo mata Umma har Qatar taga muhallinta. Umman tace mata a lokacin “ashe ni Zaynaba kenan na zama ba bafullatana bace tunda zan biki gidan miji”. Siddiqah tayi ta dariya tana fadin “Umma fulani fa sun waye, sun daina irin wannan yanzu, balle ni Petel dinki wadda ni ce ta fari nice auta, bakiga yadda Nenne take kula da Hamma ba shi da yake babban dan ta ma, bata iya wuni guda bata san me yake ciki ba”.
Haka kawai kuma ba za ta zo lokaci guda suna tsaka da biki mai muhimmanci irin wannan ta dagawa Nenne hankali ta ce lallai a maido ta gida ba. Ruwa dai baya tsami banza. Koma dai mene ne za ta jira isowar Siddiqah lafiya, ta gaya mata me akayi mata ta ji.
Mallam Buhari direban Oummana yana kashe motar a kofar gidan su Siddiqah, tayi wuf ta bude kofa ta fice. Siddiqah ko sallama ba ta tsaya yi wa Malam Buhari ba ta shige gidansu ba godi bare an gode. Shi kansa Malam Buhari yayi mamaki don ya san ba haka yasan yarinyar ba. A tsakar gida suka yi kacibus da Ummanta, wadda jin dirin tsayuwar mota ya sa ta tasowa da sauri har tana tuntube. Da wata irin azama Siddiqah ta shiga gida tayi karo da Umma, ai kuwa ta rungume Ummanta sosai, Umman ma ta rungumeta tana hamdallah na saukarta lafiya.
Sai a lokacin Aisha ta samu kuka dan gaske ya balle mata. Umma na cewa cikin fillanci, “Petel dina, mi ya hwaru? In ji dai lafiya lau kike, ba wasu iskokai, kuma kin zo lafiya baki samu matsalar komai a hanya ba?”
Aisha babu baki sai na kuka, wanda tun a Ilorin ya tokare mata a makogaro, sai yanzu da ta ji ta a kirjin Ummanta, ta samu ‘yanci da sukunin fitar da shi, ko ta ji sakayau da sanyi a kirjinta.
A haka suka karasa cikin falon Umma, Hajiya Zainab na rike da ita ta zaunar da ita a doguwar kujera, itama ta zauna a gefenta. Siddiqah an samu abinda ake so, wato anzo inda za’a yi shagwaba son rai, a kuma biye mata, nan ta yi ta rusawa Haj. Zainab kuka, tana cewa auren ta da Hamma ya kare, Umma ko za’a yankani ba zan koma ba.
Ita gara a ce ita aka taba aka ciwa mutunci basu ba, da ko daga ido bazata yi ba kuma abin ba zai dame ta haka ba.
Hajiya zainab ta ce, “Yi shiru Petel ki gaya min Abdulrasheed din ne ya yi miki laifi ko waye? Me yayi miki haka? Mutumin da na lura yana da kirki sosai”.
“Babu abin da ya yi min Nenne sai kyautatawa ta alkhairi da mutuntawa cikin alfarmarsa”.
Umma ta kara shiga duhu tace “to Petel din Umma, gayamin menene ko wanene?”
Daidai lokacin Malam Yunus ya shigo gidan, yana ta sauri kamar ya tashi sama, don har ya fita wajen aiki Prince Abdulrasheed ya kira shi a waya, yana tambaya cikin jin nauyi da murya mara amo da karsashi, bayan ya gaisheshi yadda ya saba kira lokaci-lokaci ya gaisheshi tun bayan rasuwar Emir da suka hadu a wajen makoki a Ilorin, sai ya tambayi Malam Yunus din,
“ko Aisha ta iso gida lafiya?”
Abban Aisha ya ce masa, “Siddiqah kuma? Ba dazu aka ce min kuna Ilorin ba? Ita da wa tazo? Kai ban san komai ba, amma bari inyi hanzari in karasa gidan in duba”.
Sallamar Malam Yunus ta sa Aisha tashi zaune daga jikin Umma. Ta sauko kasa tana gaida Babanta shikuma ya zauna a kusa da ita. In ta tuna irin kalaman Aunty Taiwo a kansa bata sanin sanda ta ke jin sababbin hawaye sun bulbulo mata. Ta durkushe gaban Malam Yunus tana ta sabon kuka.
“Petel in ki ka yi haka ba ki kyauta mana ba, ba ki kyauta wa Hajiya Sappa ba, in wani laifi mijinki ya yi miki ai tsakaninki da shi sulhu ne, bai kamata ki daga musu hankali ki ce komai dare sai kin taho gida ba, zo mu zauna zo mu saba shi ne aure.
Ina ta yabonki sallah kinyi zamanki kin kwantar da hankalin ki a gidan aurenki kada ki kasa alwala mana Siddiqahrmu Petel ‘yar Ummanta. Yanzu dai gaya mana me ya faru? Don Abdulrasheed bai gaya min komai na dalilin tahowarki ba, ya dai kira ni don jin saukarki lafiya? Kuma daga ji yana cikin damuwa a kan tahowarki. Ya ce ayi hakuri yana tafe gobe insha Allah bayan daurin auren kannensa”.
Aisha ta kara sautin kukanta, har da zambarwa tana cewa, “ko Hamma ya zo yayi a banza, don ba zan bi shi ba, na dawo gaban talakawan iyayena kenan, na gama wannan auren tunda a kansa aka ci mutuncin Babana da Ummata da bana hada su da kowa.
Aka yi muku zagin da ba zan iya hakura ba a bainar jama’a. Aka yimin gorin suttura harda na lefe, wallahi ko Hamma shi ya saura da namiji a duniya na bar wa Aunty Taiwo dan uwanta”.
Ta kwashe komai ta gaya musu, jikinta har tsuma yake da tana fadi, ko kalma daya ba ta cire ba cikin muggan maganganun Aunty Taiwo.
Shi kansa Malam Yunus sai da jikinsa da zuciyarsa suka raurawa. Abinki da bafullatanin usuli, sanin kowa ne Bafullacen mutum baya daukar kaskanci da raini ko kankani amma ya kanyi kara da alkunya.
Malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Yunus duka jikkkunansu sunyi mugun sanyi, kuma rayukansu sun yi karshen baci don basu taba jin abinda ya taba mutuncinsu irin wannan ba. Kuma wai daga wadda tafi kowa kusanci da Abdulrasheed din. Amma kokari suke su shanye hakan akan fuskokinsu daga idon Petel, don kar su kara dugunzuma ta.
Sanin kansu ne Petel bata iya bacin rai ba, bahagon hukunci take yi in aka kaita makura, sannan bata da rufi akan komai, bata boye abinda bai mata ba wai don ta faranta maka wannan halinta ne na tun asali keke-da-keke, kuma bata da kara bata kuma damu itama ayi mata ba.
Murya a sanyaye Malam Yunus ya ce.
“Haka abin ya zama? Ashe ana maida manufar alkhairi zuwa ta sharri da wulakanci da tozarci?
Sha zamanki Petel, duk da cewa aure rai ne da shi to ina rokon Allah ya kawo karshen wannan daga yau.
Allah shi ne shaidata na bada aurenki gare su ne darajar mutuncin Hajiya Sappa, ban yi la’akari da dukiya, sarauta ko wani abu nasu ba, karewar ma da na ji hakikanin ko su waye Akanni, a tambayi Yaya Barau cewa nayi ban yarda ba, ba kuma zan yarda ba. Na yi tattaki na tafi wajen Malam Hassan a kan maganar ki da Ishaqa shi kuma ya kwance min zani a kasuwa.
A dalilin haka Yaya Barau ya fusata ya ce a basu, ba Yarbawa ba ko Ijaw ne, saboda dalilai masu karfi akan Haj. Sappa. Amma ban da haka wallahi-wallahi na fi karfin kwadayi a wurin kowa, nafi karfin kwadayin sarauta ko mulki ko neman suna, ita ma Hajiya Sappa ta sani, banida wata manufa a kan auren nan sai ta tunanin zasu rike min ke da mutunci da martaba tunda su suka zo suka ce suna so cikin mutunci.
Amma tunda haka suka ce, to Petel share dakinki ki zauna, su kawo min takardar sakinki, dama Ishaqa ya dawo Gombe, ki gama iddah ki auri daidai ke.
Petel ke kadai muke da, ke kadai Allah ya bar mana, bayan ‘wabi’ na ‘ya’ya goma! Ta yaya za mu yarda ki wulakanta a gidan aure ko a duniya? Bayan ba wai bamu da abinda zaki ci ki sha ki suturta bane? Aure ne kawai wanda ya zama dole akan diya mace? Ko da muke talakawa a kansu, su masu mulki da dukiya wallahi bazasu kira matsiyata ba, ba kwadayayyu bane mu da zuri’ar mu duk fadin garin Gombe kowa ya san masu wadatar zuci ne, masu sana’ar da zasu dogaro da Allah da kuma kansu”.
Ran bafillacen ya baci, yana fulatanci yana gamutsawa da Hausa. Umma dai kasa magana ta yi, don ta tsorata sosai da yadda Malam Yunus ya fusata, ya sa Petel a gaban motarsa nan take suka dauki hanyar gidan Baba Barau suka bar Hajiya Zainab ta rasa abinda ke mata dadi.
Ba ta so a ce Petel dinta ta zama bazawara, at a very tender age ko a kirata sauta ga wawa, kuma bata so ya zama su Mallam Yunus sun yanke hukunci kawai daga bakin Petel gabanin jiran Dade da Nenne, da shi kansa Abdulrasheed din yace zai zo gobe.
Sun samu Baba Barau a gidansa a turakarsa yana cin abinci, ya yi mamakin ganin Aisha. Amma fuskarsu kadai ya kalla ya san ba zuwan ziyara ta yi ba, ba kuma na dadin rai ba. sai ya ture kwanukan abincinsa gefe yana cewa “Indon Legas saukar yaushe?”
Wajen zama ya bai wa kaninsa, sannan Aisha ta tsugunna gabansa ta gaida shi, ya ce, “In ce ko lafiya na ga Indo kamar daga sama? Ba ance min kun bar kasar ba zuwa turai?”
“Yanzu dai Petel ki fada masa komai da bakinki ya ji”.
Aisha ta maimaita wa Baba Barau kalaman Murjanatu kakaf. Da yadda ta tada bori sai ta taho. Baba Barau ya sunkuyar da kai na ‘yan dakikai, kafin ya dago ya ce, “Na ji, kuma sun yi da dan halak. Kin haifu Indo, daya tamkar da dubu ga iyayenta, kuma mun gode da wannan karramawa da kika yi mana. Allah yayi miki albarka tunda arziki, mulki da daular da kika samu kanki ciki rana daya basu sa kin sarayar da mutunci da martabar mu ba.
Ni kuma na yi miki alkawarin yadda na hada wannan auren haka zan tsaya in kwato miki martabarki. Taiwo ta ke ko Tuwo, sai ta san ba’a cin zarafin bafillace a kwana lafiya don ko sune Qaruna da Fir’auna don mulki da dukiya kin gama auren dan su”.
Ya ce, “Kuma a gidana za ki ci gaba da zama, don Zainaba tsaf kawarta za ta kalallameta ta zugeta su maida ki. Tunda uwarsa da ubansa kadai ke son auren. Shi dinma nataba ganin kafarsa a gidannanya zo gaishemu? Kullum saidai ace baya nan kamar wani tsuntsu. Don Zaynaba kam sanyin halinta bazai bari ta kwato miki ‘yanci ba, kuma kin san kawancennan nasu itada Sappa sai Allah”.
Farin-cikin goyon bayan da ta samu kadai daga iyayenta dattawan kwarai ya wanke mata zuciya ta saki numfashi na samun kwanciyar hakali. Ta san da wasu iyayen ne cewa zasuyi zasu maida ta kada sarauta da mulki ta wuce ta kansu.
Baba Barau ya sa murya ya kira matarsa Furera, ta shigo ya ce, “Maza Furera share wa Aisha dakin can na kusa da naki, ki kuma kama kaji a yanka ki mata farfesu yanzun nan. In kuma gashi take so sai a kaiwa Ayuba ya gasa mata. Ko me ta ke son ci a yi mata (baba Barau na kiwon kajin gidan gona masu yawan gaske a wani bangare na gidansa)”.
Sai bayan fitar Baba Furera ya tambayi Aisha, “bani wayarki kada ma ya kiraki. Shin kina da iddarsa a kanki??”
Kunya sosai ta kama Aisha. Ta sunkuyar da kai ta kasa amsawa.
Baba Barau ya ce, “Magana nake yi da ke Indo”.
Aisha ta girgiza kai a hankali, wato babu iddar Prince akanta. Wayarta kuma tace ai a wurin ta aje masa abarsa. Ba waya a hannunta yanzu.
Baba Barau ya kara fusata ninkin ta baya, yayi kuta ya ce, “Allah ne shaidata, ni ban yi la’akari da komai nasu ba na yarda na ba su aurenki, amma in suna ganin akwai wata manufa daga gare mu, ko in hankali bai kwanta ba gara da suka maido ki gabanmu da wurwuri.
Amma miji ya jingine mace mai lafiya har watanni tara babu sunna, kuma da sunan aure, sannan suna tare a gida daya ai wannan auren ma da alamar gurbacewarsa.
Babu inda zaki koma kin zo gida kenan inyaso su biyo ki da takardarki ni za’ayiwa iya shege da wulakanci?.
Idan kuma sun ki, na rantse ko da shari’a sai na raba auren nan. Mu za a wulakanta? Mu ake wa kallon kwadayayyu matsiyata?”
Baba Barau har ya fi Malam Yunus daukar zafi. Nan ya tafi ya bar Aisha a gidan Baba Barau yana ta ja wa Furera kunne kan lallai kullum ta kama kaza da zabuwa ta yi wa Aisha farfesunsu da suya ko gashi.
Nenne ta kira mahifiyarta ta ta gaya mata Aisha ta taho Gombe, sakamakon abinda Taiwo ta yi mata, da abinda ya biyo baya, wato tahowar Aisha gida.
Nenne ta nuna ma Oummana damuwarta sosai kan abinda ya faru a bikin na Princesses dinta, ga jama’a sun gayyato daga ko’ina ba damar ta barsu ta taho, sai an kai amare, shi ne Nani Oummana ta tace ta kwantar da hankalinta su gama bikin twins lafiya.
**** **** ****

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.