Complete Hausa Novels

Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 10 of 17

Sukayi bacci mai dadi da mafarkan juna masu dadi yau.
Da safe su Nenne suka wuce. Shi kuma jirgin sa se karfe shidda na yamma.
Yana yin sallar la’asar ya sallami Oummana da Uban kasa, yace daga nan zai biya wajen Aysha daga can ne zai wuce airport, gobe ne jirgin sa na Argentina da dare sha biyu na dare
Uban kasa da Nani Oummana suka masa addu’a sukayi masu fatan alkhairi. Oummana tace lallai yace ma Aisha tazo mata. yace “toh, na bata waya zata kira ki”.

Yau dai Prince wankan kananan kaya akayi. Duk ya zama dan yaro karami.
Da ya iso gidan Abba baya nan sai Umma. Suka gaisa, yace yana so yaje ya sallami Baba Barau. Umma ta ce Aisha ta raka shi. Nan ta saka hijabi Mal. Buhari ya kai su.
Suka shiga suka gaishe shi. Hamma yace “anjima kadan ze tafi” Baba Barau yayi masu nasiha. Ya saka masu albarka, yace in ya isa yayi settling ya kira shi sai a shirya mata tafiya ko bayan sati ne, sabida ya kimtsa. Da sauri Prince yace “ai Monday zata taho, Baba ba abin da za a kimtsa”. Baba Barau yayi dariya yayi masu sallama.
Suka fito suka dawo gidan su Aisha, a parlon Abban ta. karfe hudu lokacin, 5 ze tafi airport jirgin 6:15 ne.
Nan ya lalace a wurin ta, ta kawo masa abinci ya dan tsakura yana hira yana abubuwansa. Itama dai yau Siddiqah sakar masa jiki tayi yana kissing dinta tana mayar masa, abin nasu wane jiya. Ga Abba baya nan so free suke jinsu. Ita Ummanta ma bacci ne ya dauke ta. ta saba bacci tsakanin azhar da la’asar.
To dai romance kawai ake a falon nan, can Aysha tace washhhhhhh can kaji Kehinde yana kiran babyyyy…..
Malam Buhari daga waje ya duba agogo, yace shikadai, “yaran zamani, sai jirgin ya tashi ya barshi”. Mukuma nida team of editorial board dina muka ce “ko ina girman Prince Kehinde?” Domin gabadaya Prince ya zama yaro mai tashen balaga, a nan duk ya lalace, sai ji yai wayarsa na kara.
Mal. Buhari na tuna masa jirgi bazai jira shi ba. Nan dai ya dawo hankalin sa ya nutsu ya dauka.
A ladabce Malam Buhari yace “Yallabai, na ga biyar da rabi ne, ba shida bane tashin jirgin? Ka san akwai dan tafiya”. Yace “ina zuwa”, a gajarce yayi maza ya kalli agogon sa. 5:40 yace “Baby kinsa nayi missing flight dina” tace “ba ruwana” ya rungumo ta, ya dau wayar sa yayi dialling wata number, suka gaisa, yace “yanzu zan bar Je ka da fari, zan samu jirgin?” yace “to ba komai, a yankar min wani ticket na morning flight gobe”.
Aisha ta zare ido tana kallon sa…. ta tashi ta zauna, yana kallon ta lovingly, tace “Hamma da gaske ka rasa jirgin?” Yace “cewa yayi saidai inyi gudu, ni kuma ban son hanzari shine nace ya yanko min na gobe da safe.
Bari in tashi in tafi ina kallon ki haka dinnan bazan iya barin gidan nan ba”.
Aisha ta mike, shima Prince haka.

Har sunzo kofar gidan Prince yace “ina fa da gida a garin nan, ko muje ki gani?” Yana mata wani kallo ta ce “noooo!” tayi cikin gida ta barshi.
Har ta shiga gida sai ga message din sa, yace “anjima zai zo ya kai ta fadar Gombe, Nani Oummana tana son ganin ta”. tace “toh”.
Sai ga wayar Mal. Yunus, yace “Abdulrashid an tafi?” Yace “wallahi Abba nayi missing flight dinne, sai da safe. Karfe 6 ne amma nace se 5 zan tafi airport, toh kuma hold up” Abba yace “assha. Allah yasa haka shi yafi alkhairi” Hamma yace “amin”. Yace.
“Toh sai ka kaita wajen Oummana din da kan ka kawai. Daman nace zan kai ta anjima”. Prince ya ce “toh shikenan Baba”.

Suna tafe a hanyar zuwa fadar Gombe, Malam Buhari na gulmar Prince a ransa. Yana cewa wato jinkirin aure ga namiji ba sauki gareshi ba, ranar duk da ya samu mata ko yaya take komai yarintarta sai Allah, domin kamun kazar kuku mace take musu, dubi dai yadda 'yar yarinya ficiciya ta tashi kan Yallabai Abdulrasheed, yana can ya like mata ya lalace har jirgi ya tashi ya barshi.

Yawan shekarun nan nasa, matsayi da girman sarautarsa (mulkinsa na gado gaba da baya), da 'fame' din nasa na Polo (as African Polo Legend) duk an tashi kansu cikin dan lokaci ya dawo yaro daidai ita.
Domin tareda shi Malam Buhari din Nenne tayi ta zaryar nemawa Prince auren Aisha. Bata Lagos bata Gombe, har saida ta tabbatar sun daura auren sun daukota Ilorin.

Nani Oummana ma sai daga ido tayi taga Prince ya dawo. Bayan sun riga sunyi sallama ta karshe cewa daga can zai wuce airport ya tashi gida Lagos. Ba suyi dashi zai dawo ta nan ba.
Oummana tace "Yaya haka Hammansu? Mantuwa kayi?"
Ya zauna yana cewa "to ya za'ayi? Jirgin ya tashi ya barni Oummana". Wani miskilin murmushi Oummana tayi masa, tace "garin yaya toh? Kana can kana soyayya ko?" Hamma ya dukar da kai yana ‘yar dariya yace, "kusan haka, ai bakya karya Oummana" Oummana ta sake yin murmushi irin nata, ita tasan watarana za'ayi haka. Domin da alama AISHA INDO SIDDIQAH! Ta shigo rayuwar Yarima da zafinta. Zata murza kambu son ranta, ranar duk da Prince ya shiga komarta. Yarinyar nada tarin baiwa da kullum take tuna mata da auren Nenne da Dade.
Kusan tace tarihi ke maimaita kansa akan Abdulrasheed Dan Idris dan Abdulrasheed Akanni. Tana fatan wannan soyayya da Prince yake yiwa Siddiqah ta dore musu har tsufansu, su zama (typical replica) na Sappa da Idrisu.

Ganin Oummana bata ce masa komai ba sai murmushi take zabgawa yace cikin basarwa da hadiye kunyar da yaji.
"Amma gobe in Sha Allah bazan yi wasa ba Oummana, morning flight dani zai tashi karfe 6am, ko sallama bazan je mata ba".
Oummana me zata yi ba dariya ba, tace "to ni me kaji nace ne? Ko nace kayi laifi ne? Haka akeso abubuwa suyi daidai. Saika koma ka daukota ka kawomin ita yau da kanka. Daman nafi so in ganku a gabana tare". Yace "In sha Allahu Oummana, Baba Yunus ma da kansa yace yace inje in daukota in kawo miki, dama na gaya musu kinason ganinta.
Da nayi sallahr Isha zan koma na taho miki da ita".
Ya wuce zuwa dakinsa na sassan Oummana kai tsaye toilet ya fada don yin wanka, don yasan a yanayin da suka kasance da Aisha yau, bai yiwuwa yayi sallah yanzu bai yi wanka ba.

Saida Umma ta tashi daga barci taga Siddiqa a zaune a gefenta, tace "har ya tafi?" Tace "eh Umma, gashi har jirgin Lagos da zai hau ya tashi ya barshi. Dole sai gobe zai tafi gida".
Sannan cikin jin kunya ta gayawa Ummanta Hamma yace zai dawo su tafi wurin Oummana anjima, ta aikoshi tana son ganinta.
Nan Haj Zainab ta hau tunanin me zata baiwa Aisha ta tafiwa da Oummana, karshe tunaninta ya tsaya a kan turarukan ‘Oud’ da ‘Sandaliyyah’ na jiki dana turaka data sayo a Saudiyyah. Su ta saka a kyakkyawar leda tace Aisha ta kaiwa Oummana tsaraba.

Kafin sallahr Isha Siddiqah ta yi wanka ta kara shiryawa cikin wani tattausan cotton lace mai tsananin taushi da adon kananan duwarwatsu, kalarsa Orange ne da adon (milk color) furanni, tun lokacin hajjin bara Ummanta tazo mata dashi daga Jeddah, sannan tayi sallah Maghreb da Isha.
Aisha ta dauko turarenta Fahrenheit ta feshe jikinta dashi. Kana iya jiyo sanyin kamshinsa tun daga dakinta har tsakar gidansu zuwa dakin Ummanta.
Daidai lokacin Baba Yunus ya dawo, Siddiqah tayi masa sannu da zuwa ta karbi ledar hannunsa yace mata balangun Ayuba ne ta juye su ci ita da Umma shi sun ci shi da Baba Barau. Ya kuma ce ta shirya Hamma ya kira shi zai zo yanzu su wuce gun Oummana, Mallam Yunus ya gyara zamansa akan kujera yace "toh Indo nasan ba sai na maimaita miki ki kula da kanki ba, kuma ba sai na gaya miki ki zama ambassador din kanki da kanki ba a wurare irin wadannan.
Waje ne da yake bukatar nutsuwa da kamewa wadanda bana jinki a kansu Siddiqah. Tunda gidansu mahaifiyar sa ne".
Aisha tace "toh in sha Allah Baba". Daidai lokacin Sunusi ya shigo yace "wai mijin Aisha yazo daukarta, suna cikin mota".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.