Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 2 of 17
Siddiqah ta wayi gari lafiya a gidan babanta Barau Hamza, amma zuciyarta ta ki yin dadi yadda ya kamata duk da gatan da ake gwada mata kamar ana goyonta, ta kowanne bangare zuciyarta ta rasa sukuni don da dazun da safe ma Ummanta ta yi danmalele mai rai da motsi ta aiko Sunusi ya kawo mata har gidan baba Barau. Danmalelen ya sha manja an shirbineshi da yajin tafarnuwa yadda Petel keso, ga salad da tumatur an yanka masa da albasa da cocumber.
Siddiqah wadda rabonta da danmalele har ta manta, watakila tun farkon zuwanta Lagos. Tayi matukar jin dadin samunsa, musamman da Umma ce tazauna ta yi mata shi da hannunta.
Furera matar Baba Barau kuma tana ta cika umarnin Baba Barau na fige kaji da zabbi har sun ginshi sha’awar Siddiqah.
Washegarin rana ta biyu ma cikinta baci ya yi saboda canjin cima da ta samu, ta saba da cin abincinsu na yarbawa fresh veggies. Don haka Danmalelennan sai da ya saka ta zagayawa toilet har sau uku tana saukeshi, sabida uban yajinsa.
Aisha data zo barci sai ta kasa koda runtsawa, saboda tunanin magananun Taiwo. Suka zo suna ta sukarta a kirji kamar allura. Hamma da rashinsa a gefenta, sabonsu ita dashi, na wasu watanni bai yi yawan da za ta kasa barci saboda rashinsa ba, amma abin mamaki barcin baya samuwa saboda tunani da damuwa akan halin data baro Hamma a dakin da Nenne ga sauka. Ita ta san bai mata laifin komai ba, Prince ya darajata ya mutunta yana kuma kan daga darajarta da soyayya abinda kowa baiyi zato ba,
Amma a ranta ta yanke ba ita babu komawa aurensa, duk da yadda can wani nesattaccen sako na zuciyarta ke bala'in kewarsa.
**** **** ****
THE PRINCE
Har ya dauki hanyar dakin da ya baro Taiwo wato inda ta sauka sai kuma ya fasa, ya juya da baya-da-baya ya koma masaukinsa na gidan Kakan nasu.
Wani tunani ne ya shige shi wato kada ya kulata sai a gaban Nenne da Dade, ba zai so su raba abin fada a cikin dangi ba, ya san dakin da su Taiwo suke ciki akwai sauran matan family dinsu a cikinsa ba Firdausi ce kadai a dakin tare da ita ba, alhalin ana musu kallon wadanda suka fi kowa hadin kai, kyakkyawar rayuwa, kaunar juna da kwanciyar hakali a kafatanin zurri’arsu ta Sarki Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni.
Don a yadda zuciyarsa ke tafarfasa dinnan bai san hukuncin da zai yankewa Taiwo yau ba, he is afraid ya kai hanu jikinta da sunan duka, in ya yi ido hudu da Taiwo a lokacin yana iya marinta, kuma abinda zai biyo bayan hakan sai wani ikon Allah ne zai sanyaya shi.
Don haka Prince yayi koyi da maganar Annabi (S.A.W) ne, da ya ce, kada, kar ka yi hukunci a lokacin tsananin fushi.
In kana tsaye ne abun fushin ya sameka ka zauna, in kana zaune ne ka koma ka kwanta. That was why he decided not to talk at the moment.
Amma ya kudurce sai a gaban Dade da Nenne.
Su Nenne na dawowa dakin da Prince yake suka nufa kai tsaye. Nenne ta same shi a kwance, ya rufe fuskarsa da zara-zaran tafukan hannunsa, shi ya tabbata Taiwo ‘yar uwarsa ce, kuma makusanciya mafi girma a gare shi.
Amma wannan attitudes din data ke yi wa iyalinsa na mene ne? ya kasa fahimtar Taiwo. Mene ne haka wai a zuciyar Taiwo a kan matarsa?
In haka ne kawai Taiwo ba ta sonsa da rayuwar iyali kome? Tafi son shi da zama a gwauronsa har gobe, saboda ita tana aure har ta aje masu yi mata addu’a kome da shi zata kashe masa nasa auren? Don in banda haka ai in bata godewa Aisha-Siddiqah ba wadda iyayenta suka lankwasata har ta yarda ta yi biyayya ta aure shi da girmansa ita da yarintarta, bai kamata ta saka mata da zagin iyaye da gori mai tsinka zuciya ba. Ya rasa me ke damun Taiwo a kansa sai ka ce a kanta aka fara tagwaitaka.
Duk da cewa, tun asali halin Maman Kiki wani iri ne da shi kadai yake iya tolarating, amma shi ma yanzu ya yarda Taiwo annamimiya ce. Halinta bai da kyau, she’s full of pride and arrogance, watakila shi ya sa hatta mijinta uban ‘ya’yanta Toafeeq ba ya iya zama inuwa daya da ita na lokaci mai tsaho zai gudu, ya gwammace ya yi nesa da ita. Ya dinga ganinta lokaci-lokaci tunda ta zame masa dole.
In da ya bi hudubobin Taiwo na tuntuni kadan-kadan a kan Aisha, kafin ya gama fahimtar manufarta akan Siddiqah din gabadaya yanzu, da tuni ba su samu fahimtar junan da suka samu shida Siddiqah yanzu ba, da bai samu farin cikin da ya soma dandana da canjin rayuwar da ya soma samu ba.
Shi Aisha ce daidai da rayuwarsa. Ta ishe shi, ta masa daidai, more than enough, tayi kunnen doki da duk wani burinsa a kan macen kwarai. Ba ya so ya yi wa Taiwo hukuncin da a gaba za yi nadama, shi ya sa ya dawo daki, ya jira dawowar iyayensu.
Sai ga Nenne ta shigo dakin nasa fuskarta kamar hadari. Prince ya yunkura ya tashi zaune da kyar, idanunsa sun kada sun yi jazir sun kuma kankance. Nenne ta dube shi idanunta fal takaici da zallar bacin rai, ta ce,
“Hammansu yau na maida Aisha ga iyayenta, kamar yadda na dauko amanarta, tunda haka ku ke so kai da abokiyar tagwaitakarka.
Tunda tsoron Murjanatu ka ke, to shi ke nan, ta kashe maka aure, na amince na kuma yarda ta auro maka Haseenah da uku bayan Haseenah. Tunda itace uwarka ita ta haife ka.
Amma kada ka sake ka saka ni a maganar bikon Aisha, bazani ba, saboda ina tattalin mutuncina a idon masu ganina da kima, ba kaida Taiwo dinka da baku daukeni a bakin komai ba, inaso iyayen Aisha wato Zainaba da Malam Yunusa su yanke duk irin hukuncin da yafi musu daidai”.
Daga bayan Nenne Dade shi ma ya shigo, ya dora daga inda Nenne ta tsaya, ya ce.
“Ni kuma Dade dinku ka riga ka san cewa mijin ta ce din Nenne ne, tunda ta cire hannunta ni ma babu nawa, ko Gombe ba zan leka ba, wai ido da kunya. Sai ka je ka gyara barakar da ka yi sake ta faru da kanka, amma kada ka sake ka saka mu a ciki nida Nenne”.
Daga haka Dade da Nenne suka juya sua fice, suka bar Abdulrasheed na zufa daga zaune, yana tambayar kansa “me zai yi wa Taiwo ya huce?”
‘Yar halak din sai gata ta shigo minti goma da fitarsu Nenne, tana tafe da irin tafiyar nan tata ta kasaita da mulki tamkar dawisuwa cikin basarakiyar tafiyarta.
Murjanatu Taiwo Akanni, ta shigo dakin ta tsaya a gabansa babu alamun ta yi wani abu da ba daidai ba a kan fuskarta. Ta ce,
“Kehinde, wai don mun yi magana a kan yarinyar nan ni da su Ifedayo da Aunty Bola shi ne ta bar gidan? To don ubanta sai me? Sai aka ce da ita mata sun kare? Da ma ni ai so nake ku rabun, tun kafin ta haifa mana jikokin Malam Shehu a hada iri da talauci cikin gidannan. In dai mace ce ni zan samo maka daidai da kai, ko ba Haseenah ba tunda tayi aure ita, za ta sha mamaki don kuwa saidai ta dawo ta ganka da mace, wa za ta nuna wa zafin kai da rashin kunya?”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.