Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 17
Oummana sai gani tayi baqon shekaranjiya ya dawo. Tace "yaya dai Abdulrasheed?" Sai yace "nan zan zauna, sai an bani matata" Ommana sai ta fashe da dariya tace, "ah lallai Indo ta murza kambu, sarauta ta fadi" Prince yace "ai Oummana warwasss! Sarautar nan ta fadi. Aisharku itace mai mulkin".
Me Oummana zatayi ba dariya ba. Tace "sai ka shirya kaje ai" Prince yace "dole ai Oummana… ki mun addu'a ni ko ganinta ma na samu nayi yau". Zuciyar Oummana fessss! Yau ace Abdulrasheed yasan martabar mata a gare shima babbar nasararsu ce. Prince yana fita tasa ai mata kiran uban kasa.
Da Uban kasa ya tashi fada sai ya zarto sassan mahaifiyar tasa, nan Oummana ta fada masa komi da ya faru har dawowar Hamma Gombe yau. Uban kasa yace "wannan ai abu ne me sauki Oummana, ai dan nasan abinda ya faru kenan dana aika tun ranar da tazo. Wulaqanci ba dadi amman sai ayi la'akari da ba laifin sa bane. Ayi masa afuwa".
Oummana tace "ai ina sane da ban fada maka ba. So nake shima yaji a jikin sa, kuma inga gudun ruwan iyayen sa, in har zuwa karshen mako naga babu wani canji se kuje da auta (Abdulmajeed) dan Allah ayi mana bikon Aisha".
Uban kasa yace "bakomi Oummana ".
Shi kuma ya tafi ya sake daukar wanka, yau ma cikin brown filtex yadi, ya daura hular manyan matasa na zamani wato 'Tonak' kalar kayan, ya yi fes cikin shiga ta kamala, zati, haiba, kwarjini da kamala duk sun bayyana tare dashi, ko makiyin sa ya ganshi a wannan lokacin sai yace "fatabarakallahu ahsanil khaliqeen".
Domin yau Hamma a ruwa biyunsa ya fito, Malam Buhari ya daukoshi zuwa Jeka da fari.
Prince yai sallama a gidan su Aysha Baba yunus ya fito yace "laaa Abdulrasheed kai ne tafe?" Yai murmushi yana dukar da Kai, suka gaisa da Baban Aisha, yai masa iso zuwa ciki, Abba ya tambayi su Dade. yace "inace shekaranjiya ka tafi ko baka tafin bane?" Yace na tafi Baba. dazu na dawo". Yace ina Ummanmu?" Abban Aisha yace ta je gidan Baba Barau bikin 'yar sa Maryamu akeyi. Jibi Jumaah za'a daura auren bayan sallar Jumaah. Sun tafi jere wai.
Malam ya dubeshi Yana murmushi ya ce "ka san mata da hidima".
Prince yayi shiru. Cikin damuwa. Malam Yunus yace "Abdulrasheed ba nace zan kira ka ba?". Yace "Babanmu kayi haquri wallahi ko na zauna Lagos bani da nitsuwa, gara dai in dawo Gomben in zauna jiran hukuncin Baba Barau". Malam Yunus yace "ba ance ana ta kiran ka wurin aiki ba?" Yace "na basu excuse sun qara min sati biyu, shiyasa nace gara na dawo nan din". Sai yayi shiru.
Malam Yunus ma duk sai yaji wani iri, yace ba damuwa in an jima zani gidan nasa daman, zan masa magana kaji?"
Prince yace "toh Baba. Nima wai da zuwa zan yi in gaishe shi". Yace "toh babu laifi".
Yana barin nan yace wa Buhari ya kai shi gidan Baba Barau. Ai kuwa ya samu gida makil da jamaa ana ta hidimar jere yau da kawo lefe.
'Yan uwan mijin sun tafi kenan Prince yai sallama, dan Baba Barau ya fito yaje ya fada masa mijin Aisha yazo. Nan aka masa iso zuwa ciki.
Wato duk hayaniyar da ake a gidan Malam Barau Hamza, jikake kamar anyi ruwa an dauke tsit!!!!! akayi. Lokacinda Prince ya keto jamaa ya ya wuce zuwa falon Baba Barau, kwarjinin nan na masu sarauta, gashi dai ba girman kai, amman ana ganin sa an ga basarake, haiba, mulki ado, kai komai ma!!!
Hamma yayi tsugunno a gaban su Baba Furera yai masu gaisuwa jama’u (in general). Auwalu babban Dan Baba Barau da ya shigo dashi yace dasu "mijin Saddiqah ne"". Ga dangin Aisha gabadayansu sun hadu, nan aka sake gaisawa, ya miqe zuwa cikin falon Baba Barau. Nan aka bar 'yammatan family dinsu Aisha da kawayen amarya da santi da lashe miyau, Saddiqah na tsaye jikin window taji muryar sa, ta juyo tana kallon sa ta tagar, har wata rama taga Hamman nasu Firausi yayi, amman ya zuba kyau Masha Allah.
Tana ganin yadda 'yan banzan cousins dinta sai kallon sa suke tace kamar mayu, a ranta ta ce "mayu kawai, mtsw". Da taji ya Auwalu yace mijin SIDDIQAH ne she was proud!!!!
Sai daga baya ta tuna tace fa ta gama auren. Sai ta koma ta zauna a gefen gado, ta fara tunani.
Prince ya isa palon Baba Barau ya zauna a kasa ya gaishe shi cikin girmamawa, shima ya amsa. Ya tambayi su Nenne yace suna lafiya suna gaishe shi ya sunkai da kai. Baba Barau ya dauka zai masa maganar Aisha yaga bai ce komi ba.
Yace "Babanmu ashe biki ake yi". yace "eh wallahi, wa ya fadi maka?" Yace "Baba ne ya fada min dazu. Allah ya basu zaman lafiya. Yaushe ne daurin auren?" Baba Barau yace "jumaa ne in sha Allah". Prince yace "toh Allah ya kaimu. Allah yasa ayi damu", Baba yace "Amin".
Zuwa can kuma Prince yace "Baba inzo daurin auren?" yace "ah me zai hana in kana nan kazo". yace "ai ina nan ma in sha Allah".
Baba yace "toh Allah ya kaimu". Yai shiru dai, can kuma yace "Baba zan tafi kuma dan Allah ina kara baka hakuri. Waman gaddarallahu hakka qadrihi…. Allah ne ya qadarta faruwar abinda ya faru kuma wallahil azim bazan yi kaffara ba, bazai kara faruwa ba. A gafarce ni don Allah. Baba kar kayi min hukunci da laifin yar uwata. Allah ya Kara hakuri Baba sai jibin in sha Allah".
Ya tashi zai tafi, Baba Barau sai yaji duk ya daure shi da jijiyoyinsa, yayi murmushi yace "Abdulrasheed kenan, ni zaka daure ko?" Yayi murmushi shima yace "ah ah Baba".
Su duka biyun suna murmushi suka rabu.
**** **** *****
TAIWO
Ta sauka gidan mijinta a Lancaster da yamma lis, ta isa ga kofar shiga tana ringing bell. Ana bude kofa taga wata kyakkyawar bafullatana da mijinta Toufeeq a bayanta, ga yaranta biyu dasu, da wani kyakkyawan Baby din dauke a hannunta.
Wani irin shock ne ya kama Aunty Taiwo, tace "Toufeeq what is this?" Yayi mata kallon rashin tsoro ya ce mata "matata ce itama. Sunanta Hauwa-Maijidda".
Ya dubi Maijiddar yace mata "Maijidda this is Taiwo, Maman Kiki da Abdulhakeem".
"What???"
Sai ga Murjanatu ta sulale ta zauna a dandaryar kasa a bakin kofa.
Ta daga ido ta kallo matar, sannan yaran, in zata tuna ta taba ganin hoton yaran yace mata yaran abokin sa ne, wanda suka je auren sa a Yola….
A nan komai ya dawo mata, zuwan sa Yola auren aboki, ashe nasa auren ne.
A cikin ranta sai tana ayyana alhakin aisha ke bin ta…. Taiwo tace "hasbunallahu wa ni'mal wakil… Toufeeq......". Sai kuka wiwi.
Toufeeq ya soma yi mata bayani cewa "he doesn't want to hurt her ne, shi yasa yai aure bata sani ba, don yasan ta da bala'i. He needs peace in his life da matar da zata damu dashi.
Yace ta dawo UK tace baza ta bar aikin asibiti ba, toh shikuma he needs someone close to him, wadda baza ta ke bashi ciwon kai ba.
Taiwo ta kara jin muguwar nadama, nadama mara misaltuwa, tace komawa zatayi, Toufeeq yayi ya lallashinta ya kuma fada mata in zata kwantar da hankali ta zauna toh, if not zabi ya rage nata, amman aurensa da Maijiddar sa ba fashi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.