Complete Hausa Novels

Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 5 of 17

Baban Aisha nan take yace da Sunusi ya raka su gidan Baba Barau din. Sunusi ya saka takalmansa ya shiga gaban mota, Prince na owner’s side, Malam Buhari yaja motar suka tafi, don gidan Baba Barau ba nisa sosai, layi biyu ne tsakaninsa da dan uwansa.
A zaure suka tadda Baba Barau yana cin abinci, ga fura mai sanyi a gefe an ajiye masa a kwanon silba a gefe. A nutse Prince ya yi sallama a zauren. Baba Barau ya amsa duk da bai taba ganinsa ba, don haka da fara’a sosai Baba Barau yake wa hamshakin bakon nasa da bai san ko waye ba barka da zuwa, ya ce.
“Zo nan bisa buzuna ka zauna”.
Prince har da cire hula bayan ya cire takalmansa ya ki hawa buzun ya zauna a kan kafafunsa tankwashe a gabansa. Ya fara gaishe shi da hausarshi da ba ta da kwari.
Baba Barau ya ce, “Ban gane dan nawa ba, daga ina kenan?”
Nan Prince ya gabatar masa da kansa da cewa shine Abdulrasheed daga Lagos. Baba Barau ya kara neman karin haske, don har lokacin bai gane ba, Prince ya kasa magana sai da kyar ya iya cewa “Mijin Aisha-Siddiqah”. Ai nan da nan Baba Barau ya hadiye duk wani annuri da ke fuskarsa, Prince ya kara gaishe shi a ladabce, ya bashi hakuri akan zuwan Aisha. don yana da labarin Baba Barau a bakin Aisha, wani Yayan babanta da ba ya daukar wargi kuma ba ya yarda ko Babanta ya bata mata rai. Yadda Baba Barau ya maida walwalar fuskarsa ne ya sa Prince jin wata irin shakkarsa. Amma hakan bai hana shi fadan abin da ke gabansa ba, ya fara da bada hakuri sannan ya ce masa wallahil azeem shi Aysha tafi karfin wulakanci a garesa. Dalilin ma da ya bari sai yau ya taho kada cece-kuce yayi yawa ne cikin taron bikin. Ya kuma tabbatarwa Baba Barau ya magance matsalar Taiwo. Kuma yayi alkawarin baza’a kara ba. a wannnan gabar Baba Barau kansa ya yaba da hankalin Prince. Ya ce “naji, amma dai a hakura kawai da aurennan, kaima daman ba so kake ba itama haka, to kuma kaga akwai mutunci tsakanin iyayenku mata kada auren nan ya zama silar matsalarsa”.
Murya na rawa Prince yace “Baba ni ia son Aisha…” Baba Barau ya dakatar dashi yace “Abduulrasheed maganar gaskiya yaranmu basa auren wulakanci, munada hakuri amman banda wulakanci, kuma abinda yasa Aisha dawowa gida haka to babba ne, inda duk za’a taba maka iyaye bazakaso zama ba. so ina bayan Aisha kan duk abinda ta yanke, kaje zan neme ka zanyi shawara”.
Jiki a sanyaye Abdulrashid yace “toh Baba, nagode, zan iya ganinAisha yanzu?” Baba Barau yace “a’ah”. Sai yayi shiru na dan lokaci cikin damuwa daga bisani yace “to shikenan Baba zan tafi nagode”.
Suka koma gida, ya kwashe komai na yadda sukayi da Baba Barau ya gayawa Nani Oummana.

Da kyar Nani ta rarrashe shi ya dan ci abinci ya yi mata sallama ya wuce gidansa.
Nani sai ta dau waya ta kira Nenne suka gaisa, Nani ta yi mata ban gajiyar biki da ta hidima, Nenne ta ce, ai har sun dawo Legos, ta kansile da yawan events din bikin da ba su zama dole ba saboda Taiwo data bata ciwon kai. Tana son kashe auren Hammansu babu gaira babu dalili.
Nani ta ce, “Amma Dadensu ya kyauta min da ya wanke ja’ira mai halinsu na yarbawa, mu dai kam Murja ba ta dauko mu ba, can musu cikin Akannin”.
Nenne ta ce, “Ai ko a Akanni babu irin Taiwo. Ita kadai ce da halinta, mijinta ma hakuri yake da nature dinta ba tun yau ba. Tun yana kawo kararta ana sulhu har ya gaji ya yi nesa da ita, sai ya yi watanni uku bai waiwayo ta ba”.
Nani ta ce, “Addu’a za ku dinga yi mata da nasiha ba fushi da ita ba. A shekarunta dai ta yi girman banza”.
Sun dade suna tattaunawa a kan sha’anin Taiwo, har Nenne ta ce, “Ban da abin Murja ma Aisha ba ta ki Hammansu ba saboda ratar shekarun da ke a tsakaninsu sai shi ne zai ki Aisha?
Aisha son kowa kin wanda bai samu ba, na bi sarauta da kudi da gudu, na kama wa Hamma Aisha ne saboda nagarta da iyaye na gari, idan kuwa har Aisha ta fada wa iyayenta abin da Murja ta yi mata, to abu ya baci. Don ba kowa zai yarda a taba mutuncinsa a wanye lafiya ba, shi ya sa daga ni har Dade muka ce babu mu a 'yan biko wai ido da kunya. Shi da ya bar Murja ta ke taka rawa cikin rayuwarsa sai ya nemo ta ta yi masa biko”.
Nani kuma ta ce, “Hamma meye laifinsa? Ana hora shi ne kawai da laifin da ba nashi ba. Ya je bikon ai ga shi ya dawo ba nasara, ya yi min shame-shame a falo kamar gawa. Duk sonsa da fura tunda ya zo bai sha ba”.
Nenne ta ce, mu kyale shi ya yi ta bikonsa shi kadai, ya fi sanin darajar wahalar da aka yi masa aka yi masa aurenta babu ko kobonsa”.
Nani kuma ta ce, “A’a za ta sa uban kasa ya shiga maganar, idan Abdulrasheed ya kasa.

Kwanan sa biyu a Gombe. Rana ta farko da yaje ga yadda suka kwashe da Baba Barau, don haka ya sake kwana a Gombe. Washegari ya sake komawa wajen Baban Aisha da Umman ta, ya gaya musu yadda sukayi shi da Baba Barau, ya Kuma roki Abban Aisha don Allah ya taya shi baiwa Baba Barau haquri.
Malam Yunus ya lallashe shi ya ce ya koma gida zai ma Yayansa magana, dan har ga Allah yaji tausayin sa.
Prince ya saki jiki da iyayen Aisha kamar ba jiya ya fara zuwa ba. Sukayi developing good bond. He is open minded, ga kuma hankali. Amman kana ganin sa kaga damuwa.
Abban Aisha yace masa kar ya damu yaje gida zai saka baki. Kuma kada yaje gidan baba Barau yau tunda jiya ya je, zai neme shi da kansa, yace yayi haq9uri har ya neme shi din.
Prince ba yadda ya iya haka ya dawo Lagos bai san makomar aurensa ba.
A daren ranar yana tareda iyayen sa a falon gidansu. Dade ya tambaye shi "toh ya akayi a gomben?" Nan Prince ya fada masa komai, yace murya ba kuzari "nidai Dade ba don Taiwo yar uwata bace da na mata Allah ya isa, finally i have a glimpse of happiness, ta lalata min shi, wannan wani irin rashin sa’a ne?" Prince ya fadawa Babansa in a heartbreaking manner.
Yasa hannu ya dafe kan sa. Sai ya ba Dade tausayi matuka. Suna haka aka kira shi daga Qatar, Dade yana jin sa yace musu bashi da lafiya su qara mashi 2 weeks.
Sai bayan ya aje wayar ne Dade yace masa "toh ka koma mana sai ka dawo daga baya? By then itama ta huce Aysha din". Prince yace "Dade ko na koma bani da nitsuwar yin aikin, gara dai inyi ta fama ko zata haqura. in kuma taqi haqura sai na koma din.
It seems that’s the life my own twin thinks i deserve, a lonely, sad life, unworthy of pure happiness… and apparently you and Nenne too....".
Prince ya furzar da numfashi me daci a kasalance ya tashi zai wuce gidansa. Dade yace "why will u say that?" A marairaice Prince yace "toh ba cewa kukai ba ruwanku ba Dade? Ni iyayen aysha basu sanni ba ku suka sani. And if we are being honest I am nothing but good to Aysha.
Ita in yarinta ya debe ta ba se a duba ni ba. Ni da ba ni nayi laifin nan ba and also ba ni nasa Taiwo ba. Amman duk laifin ya dawo kaina kuma kunyi shiru kunce ba ruwanku. Gaskiya i won't forgive Taiwo for this Dade she really did hurt me…." ya tashi zai tafi ya juya kenan sai kuwa sukayi ido hudu da ita. Taiwo. Jikinta yai sanyi, tazo ne immediately don Dade ya aika a kirata dazu.
Ko kallonta Prince baiyi ba ya fita ya tafi gidan sa.
Nan iyayen sukayi mata tatasss, don Nenne ma taji me yace ma Dade tana daga dakin Dade din, kamar yadda Taiwo taji itama tana shigowa. A ranta ta fara nadama. Ga nasihar da iyayen ke mata suna kuma nuna mata ta butulcewa son da Kehinde yake mata in har itace zata saka shi a wannan halin.
To duk wannan ya taru yasa Taiwo ta damu, a lokacin ta baiwa iyayensu haquri ta koma gida ta wuce ta sai tiket din tafiya UK.
Bayan fitarta ne Dade da Nenne suka kara tattauna maganar, suka aje lallai Friday zasu je Gombe takanas suyi bikon nan da kansu. Alamu sun nuna fa Hamma yana ta iyo a kogin soyayya. Babansa kuma yasan basu iya so ba, gara ya taimaki magajin sa. Nenne har sallahr nafila tayi ranar ta godiya ga Allah ganewa data gama yi Hamma Abdulrasheed yana son Aisha, ga kuma irin matakin da ya dauka kan Twin dinshi Taiwo da cikinsu da ita kanta Taiwo din babu wanda ya zaci zai iya hakan akan Taiwo. Ta san ko da wasa bazai kara barin wani ya taba Aisha ba, dan haka zasu shirya nan da kwana uku suje Gombe, yau talata, toh ranar Friday ko Saturday zasu je gombe.
Shi Prince bai sani ba ya tafi gidansa haka ya kwana zuciya ba dadi. Sai asubahi ma bacci ya dauke shi, yana tashi yaga ba amfanin zaman Lagos. Bari kawai ya koma Gombe din sai yayi jiran hukuncin Baba Barau a can.
Nan Hamma ya hada 'yar akwatin tafiyarsa ya kira nenne a waya yace zai koma Gombe. Nenne tace ko lafiya ince ko? Prince yace "toh Nenne ai gara ina can in yi ta matsa musu kawai Nenne. Idan Kuma har lokacin basu yarda ba zan tafi inyi reporting wurin aiki…
Tawakkaltu Alallah… na fawwala wa Allah".
Nenne sai taji ta kuma jin tausayinsa masa je ka Hammansu Allah ya ba da sa’a kaji, Allah kuma yai albarka albarka Annabijo".
Prince yace amin Nenne". Ya tafi a ranar ya hau jirgin Gombe.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.