Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 3 of 17
Prince kansa na sunkuye, ya kasa dagowa ya dubi Taiwo domin zuciyarsa cewa ta ke yi ya yi kwallo da ita a dakin, ya dauketa ya nunawa sama ita ya nana da kasa, wata na tuna masa Taiwo dinsa ce fa cikin wani halina ajizanci da batan basira, Taiwo ce wadda ta haifa masa Kiki. Wadda ta tsaya masa a kan komai nasa tun zuwansa duniya, ta yi sharing farin cikinsa da bakin cikinsa, ta tsaya da shi a lokutan rauni, ta bashi farin ciki a sanda duniyar da yake ciki ta yi masa kunci.
Waccan kuwa matarsa ce, barin jikinsa da yake fatan ta zama uwar y'a'yansa nan bada jimawa ba, wadda ko shekara ba ta cika da shigowa rayuwarsa ba.
A yanayin da ake ciki kuwa yanzu dole ya zabi dayarsu ya bar daya, don ba za su taba kara zama karkashin inuwa daya ba, in aka yi la’akari da muggan kalaman Taiwo a gare ta, musmaman da ya bayyana gare shi cewa ita din mai sanin darajar iyayenta ce da kiyaye martabar kanta.
A hankali Kehinde ya dago kai ya dubi Taiwo da rinannun idanunsa da suka kada ‘yan hanjinta. Ya ce, “Maman Kiki, please get out of here before I lose my temper!”
Taiwo ta zaro ido, ta ce, “Kehinde, ni Taiwo ka ke wa tsawa yau?”
Da karfi Prince ya ce, “Get out of my sight please Maman Kiki. I don’t want to touch you da sunan duka. I am disappointed in you, ki daina zuwa inda nake, in ba ni na neme ki ba”.
Taiwo ta bude ido da baki cikin mamaki da razana , shi kuma Prince ya ce.
“Karyar so ki ke min Taiwo, karyar ‘yan uwantaka ki ke min. Karyar tagwaitaka ki ke domin babu ita a ranki. Da kina sona a matsayin dan uwanki da kin so ni da farin ciki da cikar rayuwa kamar kowa, ko yaya ne da kin barni na tsira da farin cikin dana soma samu.
Ki zauna ki laluba zuciyarki Taiwo, zaki tarar babu kaunar Kehinde ko kadan a cikinta yanzu, ko tu daga sanda aka yi masa aure.
Wannan yarinyar da ki ka raina don basu da arziki da sarauta, ki ke kushewa a kunnena da idona dare da rana da zagi da aibantawa da gorin bata isa ba, ita ce din dai matar da Allah ya ga damar bani a matsayin kyautarsa, na ladan hakurina da gujewa saba masa ta hanyar zina, a tsahon shekarun kuruciyata.
Ni kuma tunda ta jure wa tsufana, nima zan jure wa yarintarta da ki ke rainawa, ita ce uwar ‘ya’yana, uwargidana har a gidan aljannah insha Allahu.
Sannan daga yau sai yau kada ki kara yi min zancen iyalina, tunda ba za ki taya ni sonsu ba, kamar yadda nake taya ki kaunar naki, to na shata babban layi tsakaninku har abin da zan haifa. Tunda da bakinki kin ce bazaki taba kaunarsu ba.
Mu yi zumunci wanda ya shafe mu, wanda shi ne dolenmu, ba ruwanki da Aisha-Siddiqah, for your information ki sani “ina matukar son MATATA!
Banida kowa da ya fiyemin ke sai iyayena sai kuma twins da ‘ya’yanki, kune duniyata komai nawa ya kamata ya zama naku ne. Daga yau kisa a ranki tunda kin kashe min aure zan rayu a yadda kike son ganina, kada ki kara ambata min kalmar aure tunda ba ke kika haife ni ba, ba ki da sauran haske a idanuna amma har gobe kina nan a ‘yar uwata sai ranar da ki ka gyara barnar da ki ka yi min”.
(Duka wannan maganar Prince ya furtata cikin harshen turanci ne).
Daga haka ya fice ya barta a dakin idanunsa sun kada zuciyarsa ta tabu. In duniya da amana Taiwo bazata zame masa cikas ga cikar farin ciki ba. Komai nashi nata ne da ‘ya’yanta haka komai yake yi a duniya su yake tunawa da samun farin cikinsu. Bashida wani buri da ya wuce itada ‘ya’yanta amma ace wai abu guda daya da ya nuna yanaso, Taiwo ta gagara son shi.
Dakin Nenne ya nufa, sai ya tarar ta rufe da key ta ciki, don ta san dole zai biyo bayanta da lallashi akan batun biko ita kuma so take ya dau mataki da kansa, tafi son ya gane da kansa Taiwo fitinanniya ce abinda bai taba yarda a baya ko za’a shekara ana fadin cewa Murjantunsa tana da hali. Itada ta haifesu ma ta kwana da sanin hakan amma shi bai taba yarda. Haka ya bi bayan Dade shima a nasa masaukin, Dade ya ki ganinsa a daren don har ya kwanta, dan lekowa yayi kadan ta tsakanin kofar bai bashi hanyar shiga masa dakin ba, ya ce.
“Please Kehinde, ka yi duk abin da ya dace da kanka, but count us out akan maganar Siddiqah da Taiwo, duukansu naka ne, ba wadda zaka zaba ka bar daya, amma akan maganar aurenka mu mun gama sauke nauyin duk da Allah ya dora mana a kanka, don haka duk wanui kalubale na rayuwar iyali sai ka nemi hanyar managing dinsa da kanka”.
Auren Princess Fatima da Princess Firdausi kenan bai zo wa kowa a iyalin Engr. Idris Akanni da dadi ba. Taiwo ta bata musu armashin komai don events na al’ada har uku Nenne ta soke, ta ce za ta koma Lagos. In yaso dangi su kai amaren gidajensu haka, tunda an gama mai wuyar daurin aure, sa yi dinner washegarin tarewa a gidan mazajensu.
Shi kuma Prince ta ki yarda ma ta ganshi har washegari tana doje masa da uzurin mutane sun mata yawa bata da lokacin kebewa dashi, shirin komawa Lagos suke yi itada Dade. Don haka Hamma Abdulrasheed Prince ya zama wani sukuku da shi a gidan, don Taiwo da zai samu ya kara hucewa a kanta da sassafe ta fice ba wanda ya san ina ta yi, kamar ta san ya ci alwashin sake cin ubanta da cin mutuncinta in style, ganin ta jawo hatta iyayensa sun daina sauraronsa akan laifin da ba nasa ba balle Siddiqah data dangwarar masa da wayarsa a inda yake tsaye, balle ya samu damar communicating da ita ya lallasheta kafin iyayensa su yarda su saurareshi asan abinyi a kanta.
Ba da sanin Prince ba Dade da Nenne da safiyar washegari suka kira Taiwo ta waya cewa tazo masaukin Dade suna kiranta.
Ba ta dade da dawowa gidanta ba don ta zame musu, ta yi sammako ta taho gidan ta, shigowarta kenan daga main house din kiran Dade ya sameta, kuma as usual Toafeeq ba ya kasar. Daga ita sai babban danta Hakeem a gaban motarta lokacin da dade ya kira ta.
Tare suka zo da Hakeem, tana sane ta taho dashi wai ko sa ga girman danta da yawan shekarunsa su raga mata, don ta san dai tatsuniyar gizo bata wuce koki ita kuma tunda Kehinde ya ce ya daina ganin haskenta akan Aisha, to kowa ma yayi kadan yasa ta so Aisha (she is very sorry to say) hatta Nenne da Dade saidai suyi mata fada irin wanda suka saba ya bi ta bayan kunnenta a wuce wurin.
Dade ya ce da Hakeem ya je ciki za su yi magana da Murjanatu, don haka Hakeem ya tashi a falon yayi musu sallama ya barsu, ya koma mota ya tafi gida.
Taiwo ta shigo masaukin mahaifinta, a zuciyarta ta rasa abinda ke mata dadi da abinda Kehinde yayi mata akan Aisha, wato ya zabi Aisha a kanta, a kan wata banzar yarinya ‘yar talakawa da bata ko kai matsayin house girl dinta ba Kehinde ya gaggaya mata magana haka. Ta kara tsanar Aisha Siddiqah, ta kara tsanar duk wasu ‘ya’yan malam Shehu irinta. Tana wannan tunanin ta yi sallama a kofar dakin Dade ta isa ga kofar falon ta bude. Taiwo ta ga uwa da ubanta fuskokinsu kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta tuna when last ta ga Dade ya hade fuska irin haka, Taiwo duk ta tsargu, don ta san ba banza ce ta sa suka kirawo ta ba, ko daga fuskokinsu, Dade ne ya fara magana inda ya ce
“da gaske ne abinda akace kin yiwa matar Kehinde?
In haka ne kuwa baki yi halin Nenne Sappa ba Taiwo. Balle me sunanki Olori Murjanatu.
An yi asarar kudin tara dai, kin zama babbar banza da wofi”.
Yana fade cewa cikin fushi mai tsanani da harshen yarbanci.
“Mu ba mu gaji cin zarafin dan Adam ba, saboda kawai Allah ya ba mu sarauta, ya ba mu aron ni’imar rayuwa daga cikin arzikinsa.
Allah da kansa da ya halicci dan Adam ya karrama shi, ke wace ce da za ki wulakanta dan Adam mai daraja a wurin Ubangijinsa?”
Dade yarbanci kawai yake saki tamkar ya fasa kunnen Taiwo, irin zazzafan yarbancin nan mara dadin ji da razanar da wanda ake yi mawa.
Nenne da bata taba ganin bacin ran Dade irin na yau ba, ba ta sanshi da fushi irin wannan ba, don hak ita kanta ta tsorata da temper din da ta gani tare da shi, Taiwo tana durkushe a gabansa, jikinta na rawa da bari, Nenne kuma ta ce cikin daga murya,
“in duniya da halacci har Taiwo ce za ta zagi matar Kehinde? Ko kunya baki ji ba? Iya kara a rayuwa Kehinde yayi miki, keda ‘ya’yanki da zurri’arki. Murjanatu baki kyauta ba sam, kin ci amanar tagwaitaka da zumunci. Haba! ai inda alkawari ko na munafurci ne ya kamata kiso Aisha, tunda kince kina son abunda yake so, ko ba kya son ta bazaki nuna ba ablle gaba da gaba haka, hakan shine adalci ga dan uwanki kuma da abinda kadai zaki saka masa dawainiya da soyayyarsa gareki da Kiki. Wato kiso iyalinsa.
Taiwo a shekarunki sama da arba’in kin san hakan, bakya bukatar sai an tuna miki, amma mun tuna miki, a matsayinmu na iyayenki, ya rage naki ki dauki tunasarwar ko a’ah a wannan gabar, in kuma halin tsiya halinki ne ki yi ta yi duniya ce. Amma ko Kiki duk wautarta ai ba ta rashin hankalin dake uwarta Taiwo ki ke yi”.
Dade kuma yace “Afuwa daya zan yi miki Taiwo shi ne, in kin je kin gurfana gaban Malam Yunusa, kin mayar da kalaman da ki ka jefe su da su daga bakinki mara saiti, kin dawowa Kehinde da matarsa dakinsa”.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.