Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 11 of 17
Siddiqah ta dauki gyalen data tanada wanda yayi matukar shiga da kayan jikinta ta yafa wato off white, nan ta dauki karamar 'hand bag' dinta tun tana gida take amfani da ita, ta dauki ledar sakon Oummana ta yiwa Umma sallama. Haj. Zainab tace,
"to sai kun dawo. A gaida Nanin".
Prince ya mika hannun damansa ya budewa Aisha kofa barin hagunsa ta shiga. Malam Buhari na kokarin fitowa don ya rufe ya hutasheshi. Shi da kansa ya rufe mata kofar. Saukin kan Prince yana kara masa kima mai yawa a idon dattijon direban. Ya koma ya zauna ya rufe kofa ya jasu a hankali suka bar Jeka da fari, zuwa babban titin da zai kaisu gidan Sarkin Gombe.
Saida Prince ya san yadda yayi cikin dabara ya sanya tafin hannunshi cikin na Aisha. Ya sarkesu, sannan ya matsesu cikin nasa hannun. Taushin hannun kowannen su ya ratsa su. Suna tafe yana mata hira kasa-kasa amma ta kasa sakin jikinta dashi kamar dazu, don Ummanta ta jaddada mata ta kama kanta, ta rike kunyarta, don gidan su mahaifiyar shi zata je kuma zuwa na farko.
Da yake duhun dare ya shigo ba kowa ya ankara da shigar su sassan Oummana ba. Suka sameta har lokacin akan dardumar sallahrta tun bayan data idar da sallahr Isha tana zaune tana lazimi bata tashi ba.
Shigowarsu tasa ta shafa addu’ar da take yi, ta mike tana cewa "Jabbama da Indo Siddiqah, barka da zuwa, Indo Aisha". Aisha tayi kasa ta zube a gaban Oummana zata fara gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar ta kamo hannunta ta mikar da ita tsaye, ta jata zuwa kan shimfidar fata irin ‘traditional rug’ dinnan da akeyi da fata wanda akanshi take zama a falon, da Tum-tum a kowanne gefe da gefe manya har guda hudu, Nani Oummana ta zaunar da ita a kusa da ita.
Kasancewar Oummana bata zama akan kujera sai wannan shimfidar tata. Prince ne ya zauna a kan two seater, a gabansa akwai karamin centre table dauke da ‘tray’ shake da kayan marmari. Prince ya dauki apple guda daya jawur da ita yana yankawa da karamar wuka kaiwa bakinsa yana ci.
Yana kallon Oummana ta rasa ina taka-saka -ina taka-aje da Siddiqah, kaunar da suke mata itada Nenne, ya tabbata daga Allah ne ta dalilin son da suke yi masa. Domin bayan Oummana ta zaunar da Siddiqah a kusa da ita, sawa tayi hadimanta suka cika gabanta da kayan motsa baki na alfarma, wanda ko tabawa da hannunta Siddiqah ta kasa yi, ji take kamar yau ta fara haduwa da Oummana.
Daga bisani ta gaida Oummana da fulatanci, Oummana ta amsa ta kuma tanbayeta lafiyar su Ummanta da Babanta da iyalin Baba Barau. Siddiqah ta amsa duka, kanta a sunkuye, murya a ladabce. Anan Oummana tace maqasudin kiran nata dama don tayi mata nasiha ne. Nan tace Hamma ya basu wuri. Hamma yace "Nani abin harda kora?" Tace "ai zan kiraka ne inna gama da ita, akwai abinda ba sai ka ji ba".
Prince ya shige dakinsa ya barsu. Oummana ta fara yiwa Aisha fada da nasiha kamar ita ta haifeta.
Nasiha ce ta manya sannan mai shiga jikin yaro, inda tace wa Aisha.
"Idan kana aure yana nufin ka girma. Abubuwa da yawa zasu iya faruwa a rayuwar auren mace, musamman da dangin miji, to idan irin haka ta faru ba komai ake fadawa iyaye ba Indo, sabida gudun bacin ransu.
Sannan shi aure rai ne dashi. In zama bai kare ba mace da mijinta sai su dawo su shirya, su manta komai cikin dan lokaci, amman iyaye basa mantawa.
Don haka toh a kiyaye irin haka anan gaba, kuma koda wani abu ya faru to Aysha kizo ki sameni ni Oummana ko Nennen ku, na tabbatar hukuncin da zamuyi wallahi Umman ki baza tayi ba. Kinji ko Indo?
Sabida Allah shine shaidata, yadda nake jin Hammansu a raina haka nake son ki babu bambanci a wurina, kinji?
Shiyasa nake so nan gaba ba fata ake ba abin Allah ya kiyaye, ko da wani abu irin haka ya faru toh dan Allah Aisha ki koyi magance shi tsakanin ki da mijin ki.
Musamman irin wannan da ya faru da Taiwo, mijin ki na matukar son ki, har Taiwo ta isa tasa kice kin bar auren ki?
Allah yayi maki albarka ya kawo muku yara masu albarka. Shi wannan da baya son sarautar nan tamu, wato ya gado ubansa, Allah yasa ya haifo min wanda zai so sarauta.
A zuciyar Aisha tace "Amin". Sai lokacin ta gane Hamma baya falon ya basu wuri itada Oummana.
Da ya tashi fitowa ba kayan da ya fita dasu ne a jikinsa ba, ya canza su zuwa kananan kaya farar shirt LV da bakin wandon Jeans. Yace "toh Oummana dare ya fara zan maidata" Oummana tace "Aisha nagode Allah ya kara albarka" nan Aisha ta mikawa Oummana sakon Ummanta. Ga Oummana da son Sandal da Oud. Nan tayi ta godiya,ta kuma sa aka miko mata babbar jakar data shiryawa Aisha tsarabar da zata tafi dashi gida.
A hanyarsu ta dawowa ma Prince na makale da kafadun Aisha Malam Buhari na tuki, ya sassauta murya yace "Ayshah! Kin ce bazaki je gida na ki gani ba ko? Koda akwai abinda bai miki ba a canza don shine gidanki da ‘ya’yanmu anan Gombe". Da sauri Siddiqah tace "Don Allah Hamma Abdul a'ah, ba sai naje ba, zan gani next time". Hammah yace "ai shikenan. Kin dade baki je ba.
Wanda ya jure yayi rainon Dan shillansa wajen shekara guda, ai jiran kwana bakwai bazai gagareshi ya fige abinsa ba".
Da haka suka kawo kofar gidan su Siddiqah.
Taimakon da Allah yayima Siddiqah ta fito nan da nan shine Malam Buhari dake cikin motar nan, wanda ya kure radio yana sauraron wata tsohuwar waqa ta Sani Aliyu Dandawo. Da Prince bazai barta hakannan ba sai ya kara cakudata.
Duk da haka cike da damuwa Hammah ya rike hannunta yace.
"Babyyyyy. I will miss you kin sani ko?"
Siddiqah ta dube shi idanunta narai narai tace dashi cikin harshen yarbanci "I will Miss you more Hamma....". Ba zato taji ya kai hannunta ga bakinsa ya sumbata. Da kyar ta samu ta zare hannunta daga cikin nasa ta shige cikin gida ba ko waiwaye. Don gabadaya Hamma ya saka mata wata irin kasala (by just mere looking into his blurred eyes).
Umma da Abba sun sha labarin Nani Oummana, irin kirkinta da karamcinta daga bakin Aisha. Ta fidda kayan da Oummana ta bata har da alkhyabba ta mata da manyan turamen super guda uku da manyan lesika uku. Ga bandir din filtex na Abban Aisha da Baba Barau.
A ranar sai can dare Siddiqa ta bar dakin Ummanta zuwa nata dakin, sun raba dare suna hira don ji suke kamar gobe-gobe ne Petel zata tafi ba kwana shidda masu zuwa ba.
Don Hamma ya tabbatar ma Abban Aisha in sun tafi zasu jima basu waiwayi gida ba, don hutun shekara ya kammala harda kari mai yawa.
Wajejen karfe 12 na dare Siddiqah ta gama komai na shirin kwanciyar ta. Hammah ya kira ta, Siddiqah ta daga hatta muryarta ta canza don barci take ji sosai tace.
"Hammah, baka kwanta ba?" Yace "na kasa barci ne Baby.... Ina missing furar kinnan da kindirmo..." Aisha ta rufe ido tana jin kunya kamar Hamma na kallonta, tana kuma tuna incident din na yau da ya kasa bacewa daga idanunta, feelings din kuma sababbi suka kasa barin ranta. Hamma yace "Baby you know what?" Ta girgiza kai kawai kamar Hamma na kallonta.
Hamma yace "ban taba jin eagerness a rayuwata irinna ranar da zaki dawo min ba. I will be patiently waiting for you and your annoying Jamb.”
Daga ranar da kika dawo ne zamu fara rayuwa. Kinsan rayuwar mu ta Argentina babu komai cikin ta sai introduction na AISHA zuwa cikin lonely and pitiful rayuwar KEHINDE.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.