Complete Hausa Novels

Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 17

Taiwo a cikin satin ta dawo Nigeria. Koda ta sauka. Gidanta na Lagos ma kasa shiga ta yi tunda dai Toufeeq ne mamallakinsa. Dole gidan iyayentan dai ta dosa da tarin nadama a tare da ita, don ta kira wayar Kehinde ya ki dauka, ta je gidansa maigadi ya ce mata ya yi tafiya Gombe.
Zuciyar Taiwo bugawa ne kawai ba ta yi ba, da abinda Toufeeq ya yi mata, ta zama tamkar zararriya, har magana zaka ga taan yi ita kadai, tana ta gaya wa kanta alhakin Aisha da Abdulrasheed ne ya hana ta kwanciyar hankalin zaman aure, ya tagayyara nata farin cikin auren.
Domin don wulakanci irin na Baban Kiki ma cewa ya yi saura ta je ta hada masa bomb a gida, don ba wanda ya san ya yi 'secret marriage', ko a nashi family din kuwa, don yarinyar zuri’arshi bazasu barshi ya aureta ba, kasancewar diyar talakkawa ce sosai a garin Yola ya aurota, shekarun baya yaje yin wani project daga European Union ya ganta tana talln fura da nono ya aura. Babanta ma baduku ne.
Don haka daga Nenne har Dade babu wanda ya san dalilin zuwan Taiwo gida rana daya, a taurin zuciya irin nata, da rashin tsoro ko shakkar kowa da kowa ya sani, suka ganta duk ta sauke kai, ta zubda izza, yanayin da suka ganta a ciki ya basu mamaki sosai.
Kuma tana zuwa gida ranar Friday da sassafe taga ana ta shiri su Nenne zasu Gombe. Taiwo ta fashe da kuka ta roki su Nenne suyi hakuri tun ba'a je ko'ina ba taga me tagani.
Nan ta fada ma Nenne komi tas, ai kuwa Nenne batayi mamaki ba don yasan Toufeeq yayi hakuri da Taiwo ba kadan ba, nan ta sake yi mata nasiha mai kashe jiki da huda zuciya. Tace zasu je ne su yi bikon Aisha, Taiwo tace zata bisu tunda itace tai laifin zata je ta basu hakuri. Su Nenne suka ce "toh".
Da hantsin ranar jirgin DANA Air ya tashi dasu Gombe.

A gidan Oummana aka sauka. Oummana se ganin su tayi daga sama dukkansu, tace "daga ina haka?" Nenne tace "sunzo biko" Oummana tace "ai ni daman ido na saka muku, da baku zo ba daman anjima zanje gidansu Aisha da kaina inyi ban hakuri".
Nan Oummana ta hangi Taiwo, aiko Oummana ta ciwa Taiwo mutunci son ranta, tace "Ashe tareda tabbatacciyar kuke tafe?" Oummana tayi Mata tatas. Uban kasa ma da ya shigo ya ci wa Taiwo nasa. Taiwo tai kuka har ta gode Allah idon nan sun kumbura pummm.
Sai ga Prince nan ya shigo around 11am, yana zuba wani irin kasaitaccen kamshi, ya sha fararen kaya, yana riqe da babbar rigarsa a hannu, da hular sa Tonak ash colour, wato kalar zaren da akai aikin kayan, gabadaya suka juyo suna kallon sa.
Surprise yaga Nenne da Dade bai ma kula da TAIWO ba. Nan ya shigo ya gaishe su, har suna hada baki sukace,
"ina zaka je haka?"
Prince yace daurin aure zai je, uban kasa yace "a ina?" Hamma yace "Baba Barau ke aurar da diyar shi" Oummana tace kace "biko kake tayı. Wannan ado haka Hammansu ai dole a baka Aisha Indo yau!".
Prince ya saki wani kasaitaccen murmushi yace "Allah ya amsa bakin ki Oummana" duk suka ce "amin".
Dade yace "muma biko muka zo ai, amman tunda biki ake yau zamu bari sai gobe sai muje, Prince yace "ah ah Dade, yaya kunyi niyyar alhairi zaku fasa kuje kawai yanzu" duk suka hau dariya, uban kasa yace ban san ka da gaggawa ba, yau da gobe ai duk daya ne. Yana juyawa sai yaga Taiwo duk tayi zuru-zuru. Sai yaji ba dadi, yace "lafiya ke kuma haka?" Sai kuwa Taiwo tasa kuka, tazo ta rungume shi tace I am sooo soo soo sorry Kehinde. I love u so much, I became selfish and possessive ban ma sani ba.
I am extremely regretful of what I did, and i will do anything to make it right. Kayi hakuri.
Iyayen na kallon su da Kakar su, da zuciya daya ya riko hannunta, yace "Allah ya yafe mana bakidaya Taiwo, Allah yasa kin canza hali kenan har abada", duk aka ce Amin. Sai suka baiwa kowa tausayi musamman Prince, don yana son yar uwarshi.
Kehinde akwai yi wa mutane uzuri. it was an emotional moment tsakaninshi da Taiwo dinsa yau. Yana yi mata murmushin afuwa itama tana masa na godiya. Daga bisani ya kalli agogo yaga lokaci ya tafi, yace "kai bari in tafi kar nayi latti". Ya saka hula yana musu sallama. Uban kasa yace "ah ah, ai baza ka tafi haka ba, yace da Kawunka zaka tafi ya raka ka. Yau a basaraken ka zaka je musu, ko Baban Aisha Indo ya daina ja maka rai".
Sarki Ahmadu Jallo Umar yayi gyaran murya sarkin dogarai daga bakin kofa ya ce "Ran sarki ya dade, ina kusa", Sarki yace "a kira azo a daura masa rawani, a hada mota, kuma a kira Galadima da Waziri Abdulrashid ya wakilce ni a daurin auren da zashi yau, a hada convoy, a hada dogarawa!!!".
Sarkin dogarai cewa yake "an gama Uban kasar Gombe, maganarka doka ce!".
Nan ya buga babbar riga ya wuce zuwa cika aikin Sarkin sa, jikinsa na zikiri.

Hamma ya bata fuska ya dubi Kawunsa Uban kasa yace "is it necessary? Kar ma suce ‘show off’ ake masu, su sake boye ta a daki?"
Nenne da Oummana me zasuyi ba dariya ba.
Uban kasa ma da Dade sai da suka dara. Wato duk Taiwo ta jawo ya zama a darare yake da duk abinda zai sa a ce ya raina azikin su Siddiqah. Uban kasa yace "ai dai an gayyace ka daurin aure ko?" Hamma yace "eh" Uban kasa yace "toh ni nace ka wakilce ni. Gara yau dai a gan ka a ainahin gaskiyar ka. Sarauta ai ba karya bace Abdulrasheed".
Prince yayi murmushi. Nenne tace "gaskiya kam. Allah dai ya bada sa’a, in an gama daurin aure ka shiga ciki ku gaisa da su Umman Aysha, kace ina gaishe ta". Hamma ya ce "toh Nenne".
Daman Kuma karfe 12:45 ne daurin auren, da an idar da sallar Juma’a za a daura. Ai kuwa kan kace meye wannan sarkin dogarai ya cika aiki, an sanar da maganar zuwa daurin auren, Galadima da Waziri sun shirya, ga dogarawa da motoci na alfarma nan uku an ware, sai motar Uban kasa itama an fito da ita. Cikin ta Prince zai shiga.
A gefe ga masu algaita.

Daga cikin gida kuwa Prince ne zaune za'a nada masa rawani, sai kira yake "shi fa baya son rawani, zafi ne dashi Oummana".
Nani Oummana tace "ai kuwa dole kaso rawani, don kuwa kayi gadonsa hawa biyu". Hakanan Hamma ya zauna aka nada masa farin rawani, an masa irin rufin bakinnan, ya dau 'black Gucci shades' kalar dark brown' ya saka, ga hannun nan na dama yana juyawa yana sheki. 'Patek Philippe Grandmaster Chime' ya saka, not extravagant but extremely classy. Yau sai jinin fulatancin gabadaya ya fito. Masha Allahu kawai za'a ce saboda Nenne tana zaune tana kallon sa ya tashi zasu wuce bata san sanda tace "fa tabarakallahu ahsanal khaleqeen. U'izu bi kalimatillahi tammat min sharri ma khalaq". Ta tashi ta tofa ta shafa mashi. Wallahi tama manta basu kadai bane. Oummana tace, "je ka Allah ya tsare" yace "amin Nani".
Suka fito tare da Uncle Abdulmajeed shima yasa rawani. Amman Kehinde ya haska. Dogarawa an samu abin so, shi dama gashi miskili kuma rawanin ba so yake ba, ai sai shan kunun da yayi yasa komi looks more regal. Suka hau kirari kamar makoshin su ze fita aka shige mota. Hamma yace don Allah a rage convoy din. Sarkin dogarai yace "ai yayi hakuri tunda sarki yake wakilta baza su fita qasa da haka ba.
Ya shige motar Uban kasa shi da Uncle Abdulmajeed sai sarkin dogarai a gaba. daya motar kuma Galadima dayar Turaki da Waziri. Sai ambulance da kuma bus ta dogarai da masu algaita. Aka wuce tiryan_ tiryan zuwa Jeka da fari.
A hanya Prince ya kira Baba Yunus, yace “yazo zai fito Uban kasa yace lallai ya wakilce shi a daurin aure, to dai gashi nan a hanya Allah yasa kar yayi wa Baba Barau laifi”. Ashe a ‘hands free’ yake, Baba Barau na kusa da Yunus yana jinsu, sai Baba Barau yayi masa gyaran murya yace "wato Abdulrashid kallon sarkin bala'i kake mani ko?"
Prince ya zaro ido yace "subhanallahi, ko kadan Baba. Na dai fada ne kada muzo baku sani ba". Yace "to wa ya taba mayar da wakilcin Uban kasa? Wato don na rike maka Indo, shine kake so ni a kore ni daga kasar Gombe ko?" Yace "ah Baba, tsaya kaji.....". Ai kuwa Baba Barau ya fashe da dariya, Mal Yunus yace "wasa yake maka ka ji! Sai kun iso".
Du duk a tunanin su shi da wani aka turo. They have no idea it’s the whole convoy.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.