Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 13 of 17
Prince ya gama yiwa Aisha duk wani shirin tafiyarta Qatar tuntuni, a yadda ya tsara washegari Litinin zata bar Lagos ta sameshi a Qatar. Amma sai Nenne ta ce ta daga tafiyar Aisha Qatar sai alhamis, saboda zasu tafi Umrah ita da Dade alhamis din, kuma Qatar airways zasu bi. So zasu taho da ita kawai su kawota da kansu, dama last time bataso tafiyar Aisha ita kadai ba babu 'yan rakiya don dai umarnin Emir ne.
Don haka yanzu da kansu zasu taho da ita su kawota sannan su wuce Umrah.
Prince ko kadan bai so hakan ba, amma dai yace "toh Nenne Allah ya kaimu".
Wannan daga zuwan na Aisha daga Monday zuwa alhamis da Nenne tayi ya baiwa Prince damar yin settling sosai, bayan komawarsa Qatar, don ashe aiki ne damqam yake jiransa bai sani ba, wanda zaiyi in ba shi ba. A cikin ayyukan da ya tarar akwai zuwa consultation na aiki kasar Singapore sati mai zuwa. Kuma in yaje sai yayi sati biyar acan. Tafiyar ta kama masa sati daya da dawowar Aisha gidansa, tunda sai upper week.
Har ila yau, daga zuwan nata da Nenne tayi zuwa alhamis sai ya karawa Prince wani irin dokantuwa da zuwan Aisha fiyeda na baya. Don haka ya shiga gyaran gidansa domin taren Siddiqah. Yasa aka fidda duka furniture din gidan tun daga gado har kujeru ya saka sababbi farare sol. In bai manta ba Kiki ta taba gaya masa ya kamata ya sakawa Aisha sababbin furniture, a wancan zuwan nata Argentina. Tace amarya komai sabo ake saka mata.
Ba furniture kadai ba hatta curtains din gidan da rug carpets saida Prince ya canza da samfurin zamani kirar jiya-jiya (latest arrivals).
Kayan cefane kuwa ba abinda bai sa an ajiye mata ba, tun daga kan gishiri har tsinken sakace, kai har da wadanda Aisha bazata bukata bama daga zuwanta, duk Prince yasa yaron gidansa na Qatar wato Zaid ya ajiye mata.
Wato bayeraben miji in ya tashi soyayya da dukkan zuciyarsa yake yin ta musamman mai shekaru da cikar hankali irin na Hamma Prince, don babu rawar kan kuruciya a tareda shi da zuciya daya yake son Aisha yake kuma hidimtawa soyayyar.
Kai lallai shiri ba dan karami ba na hango Kehinde na yiwa Aisha. Sai mu ce amarya Aisha Allah ya kiyaye hanya ya kawo kazantar daki.
Ya shirya mata lafiyayyen dakin barci dab da nasa, bayan master bedroom da zasuyi sharing. Babu abin da babu na bukatar mace ‘yar gayu a dakinnan na Petel Siddiqah.
Wannan gidan da Prince yake ciki is not a Ranch House, gida ne da Qatar Refinery suka bashi don ya zauna yayi musu aiki. Gidan 'penthouse' ne. Ranch House da Polo Horses dinsa duka suna can Argentina.
To dama Qatar wajen da yake aikinsa ne kawai, baya Polo a Qatar sai ya haura kasashen turai ko Argentina yake yin abinsa.
**** **** *****
Nenne ta gama ma Aisha duk wani shiri da ake yiwa amare 'yan kabilar Yoruba wadanda za'a kai gidan miji karo na farko, har ciccibin nagge Nenne ta dafa mata ta cinye ba tareda ta san ko menene ba. Aisha ta sha mamakin ganin Aunty Taiwo bata koma gidanta ba tun saukarsu, ta tare ma a dakin Princess Fatima.
Kuma da alama zaman gida take. Bata tambayi komai ba amma ta gane akwai matsala a auren Aunty Taiwo yanzu, shiyasa ta dawo gida.
Ranar Alhamis kamar yadda suka alqawartama Prince Nenne da Dade da surukarsu Aisha Siddiqah Yunus, suka daga cikin Qatar Airways, daga filin jirgin saman Murtala Mohammed na jihar Lagos.
Tun jiya Dade ya gaya masa lokacin tasowarsu da landing time.
A cikin jirgin, Dade da Nenne suna a first class Q suites na Qatar Airlines (aisle seats), so sun rufe kofar ya zama kamar daki suna hirarsu, Aisha kuwa na jikin window ta kwantar da kanta akan wuyan seat dinta, tayi shiru cikin tunani, tana tuna waccan tafiyar tata ita kadai zuwa Argentina, da abubuwan tarihi da suka faru cikin tafiyar. Har gobe bata san hikimarsu Dade ta tura ta ita kadai da farko ba a wancan lokacin, saidai da yake Nenne ta gaya mata daga baya cewa Allah ya jikan rai Emir ne yayi umarnin hakan.
Ita da kanta daga baya take tunanin watakila hikimar Maimartaba Emir of Ilorin na yin hakan shine basa son tursasashi yayi welcoming dinta, wato ya zamanto ya karbeta karba irin ta ganin idonsu, su tafi ya canza mata zuwa true colour dinsa, sun barshi yayi deciding yadda zai karbeta don radin kansa.
Bata san meyasa ba tafi jin dadi da kwarin gwiwa har ma da karin ‘self-confidence’ na isa ga Hamma yau, da fara sabuwar rayuwar meaningful aure tare da shi, da ya zama cewa su Nenne ne suka kawota da kansu yanzu.
Har sukayi landing a Qatar, Aisha bata jin me suke cewa cikin hirarsu, wadda suke yi da yarbanci, wani lokacin su cakuda da harshen fulatanci, duk dai suna tattaunawa ne akan sha’anin rayuwar ‘ya’yansu da matsalar auren Taiwo. Da alama a irin wannan trip din kadai suke samun lokaci su tattauna extensively akan ‘ya’yansu irin haka.
Ita daga karshe ma barci tayi, bata farka ba saida aka ce cikin bututun magana kowa ya daura belt, jirgi zai sauka a Qatriyyah.
Prince daga office dinsa kusan duk bayan minti biyar sai ya duba agogon swatch din dake hannunsa, tun kafin lokacin saukarsu ya cika ya yanke duk abinda yake yi ya taho filin jirgin daukarsu Nenne. Jirgin su Aishah na sauka shima yana shiga reception na tarbar baki, don haka Prince baiyi zaman dogon jiransu ba.
Aisha ce ta fara fitowa rike da jakar hannunta data Nenne, kafin su Nenne su biyo bayanta. Prince ya runtse ido ya bude yana kallon beautiful Aishah… tana takowa majestically zuwa gareshi, da wani madaukakin murmushin SO a fuskarta, hamdala yake a zuciyarsa, sai kuma ya hango Nenne daga bayanta itama ta taho, tana taku ita kuma cike da sarauta. Prince ya karasa da hanzari ya fara rungumar Nenne, sannan Dade, kafin ya dawo ga Aisha ya rungumeta itama, yace “Aysha welcome oooo, sai yau Nenne ta gama boyon naki ta kawo min?”
Dade yayi dariya, Nenne ta harareshi, Dade yace “yaushe muka boye ta din? Daga cewa zamu yi mata rakiya?” Duk suka yi dariya, nan Hamma ya karba mata jakunkunan hannunta, ya sake rungumota jikinsa yana cewa “welcome Aysha! Welcome oooo!”. Daga haka suka wuce mota.
Kasancewar Dade da Nenne duk sunada ‘Entry Visa’ na Qatar kuma zasu yi transit na awanni hudu a Qatar sai suka yi amfani da wannan damar suka rako Aisha har gidanta.
Prince na tuki akan hanyarsu ta isa gidansa, amma hankalinsa rabi na kan Aisha wadda jikinta duk ya nuna gajiya da lalaci, ta dauko wayarta daga jakarta ta kunna, ta soma kokarin roaming layinta domin ta samu ta kira Umma da Baba Yunus, ta gaya musu saukarsu lafiya amma ta kasa connecting.
Duk wani motsi da Aisha tayi a cikin motar sai taji idon Prince Abdulrasheed a jikinta, kai har a ruhinta, ita kuma ta ki yarda su hada ido da gangan kada taje ya bata kunya, don tun daga rungumar da yake mata a gaban su Nenne ta san komai ma zai iya (that’s his real identity of Yoruba demon), gashi duk dagowar da tayi sai ta hango Nenne ta cikin mudubin gefenta, wadda ke zaune a kujerar bayanta, Nenne waya take yi da Fatima a lokacin bata maida hankali a kansu ba sam. Aisha ce dai duk ta ji ta takura da idanun Prince dake yawo a jikinta. Kuma idanun nasa sun rikitata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.